← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 154

Sashe 93

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Acan falon Ummi kuwa cikin nutsuwa suka kammala break fast ɗin, Zaleeha da Raleeya ne suka kimtsa dinning area'n, inda Raleeya ta zuba kwanukan da suka ɓata acikin injin wanke wanke, nan falon Ummi suka zauna suna ɗan taɓa hira. Ganin lokaci na ɗan jane, yasa suka sake komawa kitchine ɗin, lunch suka ɗaura, basu wani yi girki me wahala ba, hakan yasa cikin mintuna kaɗan suka kammala, Raleeya ne ta haye sama dan agajiye take jinta sosai, itama Zaleeha part ɗinta ta nufa, Adeel ɗauke akan kafaɗanta, koda ta isa ɗakinta, akan gado ta aje Adeel ɗin sannan ta jefa masa ɗan ƙaramin pillow dan yayi wasa dashi, kayan jikinta ta rage, sannan ta shiga wanka, koda ta fito wata ƴar riga marar nauyi tasanya, sannan ta haye saman gadon, jawo Adeel jikinta tayi tare da ɗaurasa akan cikinta, ahankali take shafa bayansa, ahaka har bacci ya ɗaukesu. Ahankali yaɗan buɗe idanunsa, wanda suka ɗanyi ja, saboda baccin da yayi, wayarsa dake ɗaure kan bedside ya ɗauka, ganin ƙarfe 12:15 pm yasashi tashi zaune, wheelchair ɗinsa ya jawo tare da hawa kai, kaitsaye toilet ya wuce, wanka yayi ya fito sanye da rigar wanka ajikinsa, ɗan ƙaramin towel ne ahannunsa, yana tsane gashin kansa, koda ya kammala body lotion me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa, wasu riga da wandon shadda na getzner ya sanya wanda sukai masa masifar kyau, tsab yagama shirya kansa tare da fesa turare, wayarsa da kuma laptop ɗinsa ya ɗauka sannan ya fice daga cikin ɗakin.
Kaitsaye part É—in Ummi ya nufa.
Babu kowa a falon Ummin, ko ina shiru, dan tun 11 Hayatuddeen ya tafi school, Raleeya da Ummi kuwa kowa na É—akinsa.
A falon ya É—an tsaya jim ya É—anyi dan yasan a irin wannan lokacin Ummi ma bacci takeyi,
A hankali ya juya ya fita, a harabar gidan ya ɗan tsaya kamar zai wuce wurinsu Sule sai kuma ya juya ya nufi side ɗinshi da matanshi ƙofar falon Zaleeha ya buɗe ya shiga a hankali yake sarrafa keken nashi, shiru falon nata sai sautin AC da kuma karatun ƙur'an da ta saka wanda yake tashi a hankali,
kamar zai juya ya fita kuma sai yaji zuciyarshi nayi mishi jagora zuwa cikin É—akin nata,
a hankali ya tura ƙofan,
tare da sarrafa kekenshi cikin nitsuwa ya isa tsakiyar É—akin, ido ya zuba mata ganin yadda take konce ruggume da Adeel,
idonshi ya lumshe tare da fidda sassanyan numfashi, a ranshi yace.
"Uhumm to wannan konciya a bakin gado ai juyi ɗaya zakiyi ki yarmin da yaro ƙasa ki fasa min kanshi."
dan gaba ɗaya ƙarfin konciyar nata a bakin gadon ne, sarrafa kekenshin yayi a hankali ya iso bakin gadon, cikin nitsuwa yasa hannu ya tallafi Adeel tare da ɗauke shi daga kan ƙirjinta,
ya É—an roggofo da niyar kontar da Adeel É—in bayanta kenan,
cikin bacci taji kamar yaron zai faɗo ba tare data buɗe ido taɓa tayi maza ta ruggumeshi,
madadin ta ruggumi É—an sai ta ruggumi uban,
da sauri ya kontar da Adeel daketa bacci sai, ido ya É—an zaro jin yadda ta ruggumeshi gam a jikinta,
idon ya zuba mata, yana mai maganar zuci.
"Wayyo Allah zata lalata min al'wala".
Ita kuwa Zaleeha cikin baccin ta fahimci wannan ba Adeel ta rugguma ba, da sauri ta buÉ—e idanunta tare dayi sauri ta sakeshi, ido ta zazzaro kana ta mirgina baya,
da sauri ya riko hannunta ganin zata mirgina kan Adeel,
cikin mayen bacci tace.
"Bacci zanyi".
Ido ya tsura mata tare da jujjuya mata su kana ya mata mgna da yarensu na kurame.
"To na hanaki baccin ne, daga zuwana kin shaƙoni kin ruggume."
Ya ƙare kwatance dayi mata nuni da rugguma,
baki ta É—an tura tare da cewa.
"Ni ai Adeel nake son rugguma ba kaiba".
Sake hannunta yayi tare da mata alamun.
"Karya kikeyi".
ita dai gefe ta koma ta konta tasa Adeel a gaba,
shi kuwa juyawa yayi ya fita dan baison worwore al'walanshi.

Yana fita ta maida ajiyan zuciya tare da shafa kan Adeel kana sukaci gaba da bacci su.

Shi kuwa suna fita shida Sule kasuwa suka wuce,
Nan ya zazzagaya shagunanshi dan duba hada-hadarsu dan sun kusa suyi zaman lissafin cinikin shekara da ribar da suka shigar da sanin zakkar daya dace su fidda,
Sai da ya gama zagayawa shida Ahmad da Mudassir kana da Warisu.
Sannan ya wuce, ya gaggaida su Alhaji Yawale, Ba miskila, Alhakin Isha, Alhaji kabiru, uban gidansu na dilan leda Alhaji Aliyu, domin baya mance duk matakin da yake ciki a rayuwa sanadin pure water da leda dasu magine ya kai wannan matsayin.

Daga kasuwa ofishin su na Jonapwd ya wuce,
yana shiga ciki ana ƙoƙarin shiga sallan azahar, nan ya shiga jam'i akayi salla.
Bayan an idar ne ya wuce ofishin Ishaq, tare da jagoranci Sani,
cikin yadda suka saba mgna yake mishi bayanin Malam Ishaq yana cikin G.S.U sai dai yanzu zai dawo,
aiko suna nan zaune Ishaq ya shigo,
Murmushi yayi tare dabin gefen table É—inshi ya matso kusa da kujerar da yasan nan Saifuddeen ke zama hannu ya bashi tare da cewa.
"Ango mai mata biyu, sai yau aka tuno mu?".
Hannunshi Saifuddeen ya kama tare da rubuta mishi,
"Kai Isha banda sharri last week mafa nazo dani akayi mitin".
Murmushi Ishaq yayi lakacin daji saƙon aminin nashi, gyara zama yayi kana yace.
"Eh ai yanzu zuwanka sati-sati ne."
Murmushi sukayi baki É—aya kana sukaci gaba da hira,
A nanne Saifuddeen ke cewa Ishaq ya kamata fa ya tsaida batun aure duk abokansu sunyi aure sai shida Mudassir suka rage,
a nan Ishaq ke ce mishi su shirya shima nashi nan tafe dan sun gama dai-dai tawa da Rashida ƙawar Zaleeha,
sosai Saifuddeen yaji daÉ—in haka dan yasan Rashida tanada mutumci da kima,
nan dai sukayi tashan hirarsu ta abokai.

Sai da yamma ya baro wurin Ishaq kana, ya nufi gida.

A gidan kuwa tuni Zaleeha da Raliya sun gama aikin abincin dare.
Amina ma ta dawo wurin aikinta

Duk suna zaune a falon Ummi sunata ɗan taɓa hira.
Duk da Ameena najin zuciyarta babu daɗi dan har yanzu data dawo dataje ɗakinta saida taji ƙamshin turaren Zaleeha a jikin rigar Adeel amman ta danne.

Shi kuwa Saifuddeen kai tsaye side É—insu ya wuce ganin magrib ta gabato, ruwa ya É—an watsa kana ya zura jallabiya ya fito ya nufi masallaci,
Hayatuddeen na biye dashi a baya,
a bakin gate suka samu Ahmad ma nayin al'wala daga nan suka wuce masallaci.
Sune basu dawo gidaba saida akayi sallan isha.

Suna dawowa suka zauna duk sukaci abinci,
daga nan Ahmad ya haura sama dan a matuƙar gajiye yake, in ya ɗanyi bacci kafin Raliya ta gama hiranta ta dawo zaiji dama-dama ya samu raya daren

Hira suke ɗanyi yayinda Zaleeha ke zaune ƙasa kan carpet, tasa Adeel a kan cinya tana yanke mishi farce.

Ameena kuwa ta zuba musu ido,har ranta tasan ba soyayyar ganin ido Zaleeha keyiwa É—anta ba,
to amman ita ta kasa jin ta dena kishin Zaleeha a ranta, ganin yadda tayi zugum tayi tagumine yasa Ummi ta kalleta cikin kulawa da nitsuwa tace.
"Ameena zo".
Tana faÉ—in haka ta wuce tayi cikin É—akin ta.
Cikin sanyi Ameena ta miƙe tabi bayanta,
a bakin gado ta samu Ummi na zaune, cikin yin ƙasa da kai ta ƙaraso cikin ɗakin,inda Ummi ta nuna mata nan ta zauna sunkuyar da kanta tayi a hankali tace.
"Ummi gani".
ido Ummi ta zuba mata sai kuma ta gyara zama cikin kulawa da son gane matsalar Ameena tace.
"Ameena meke damunki?".
A hankali ta jujjuya kai alamun babu.
Cikin kula Ummi tace.
"Kinga Ameena kada kiyi min haka,kinji ni matsayin Æ´a na É—auke ku,muddin kinada matsala ki gaya min, in inada damar yaye miki ita zan yaye miki ita in kuma bani da dama, zan tayaki da addu'a da shawarwari, dan haka gaya min meke damunki yadda bazan so Ahmad ya tozarta Raliya ba bazanso Saifuddeen ya tozar takuba, gaya min me yayi miki,ni nasan na isa dashi".
Cikin rauni da sanyin murya tace.
"Babu abin da yamin Ummi,wlh Hamma bai min komaiba".
cikin gamsuwa Ummi tace to menene matsalarki meke damunki?".
Kai ta É—an rausayar tare da cewa.
"Ba komai Ummi wlh Hamma bai min komaiba."
Cikin kula Ummi tace.
"To Alhamdulillah dan ni shi na zarga, tunda kuma kince bai miki komaiba, shikenan, amman ki saki ranki ki dena sa damuwa a ranki, bana son ganin kina tagumi kinji ko tashi kije kuyi hiranku da Æ´an uwanki".
Cikin jin daɗi da ganin daraja da kimar Ummi da mijinta ta miƙe ta fita tana mai yin mgnar zuciya.
"Ameena ki sassauta wa kanki kishi bayin Allah nan basu rageki da komaiba wacce kikeyi dominta ma bata saniba".
A hankali ta fito falon gefen Zaleeha ta zauna, cikin kula Zaleeha ta kalleta tare da cewa.
"Ummu Adeel bashi yasha nono naga yanata mutsu-mutsu".
Murmushi ta É—anyi kana ta É—auke shi ta bashi nono.
Shikuwa Saifuddeen ido ya zuba musu a yadda suke jeren,
hamdala yakeyi da godewa Allah daya azirtashi da matan da ko wacce da nasabarta,
murmushi yayiwa Ameena tare da jinjina mata kai alamun tayi kyau.
kauda idonta tayi dan sai take ga kamar ba'a yayi mata ya za'ayi yace tayi kyau bayan ga Zaleeha kusa da ita bata san cewa kowa da irin sirrin kyanta ba.
ganin yadda ta tsuke fuskane ya sashi jin ba daÉ—i.
"To wai me nayi mata,ko dai ta daina so nane yasa duk abinda nai mata sai ta juyashi marar daÉ—i".
Yana cikin mgnar zucin yaga ta miƙawa Zaleeha Adeel ta miƙe ta fita,
da ido ya bita,
Raleya ce ta kalleta cikin kula tace.
"Aunty Ameena har zaki shiga?".
Kai ta gyaÉ—a mata, jin Hayatuddeen yace.
"To saida safe Aunty Ameena".
Yasa ta É—an juyo tare da cewa.
"To auta Allah ya bamu al'khairi".
Baki ya tura tare da cewa.
"Wai auta nida har inada yara sai kuyi ta cemin auta yanzu in Adeel ya fara mgna shima ba sai yabi bakinku yace min autanba".
Murmushi tayi ta fice,
Zaleeha kuwa dariya ta É—anyi tare da cewa.
"Ya isa ya cema auta ai kai Appinshi ne".
miƙa yayi tare da konciya bisa kujerar da yake.
Chapter 93 · 0% Book details