← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 154

Sashe 109

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falon Ummi kuwa ana gabda kiran sallan magriba Ameena ta dawo,
so a nan ma tayi salla,
magriba da ishan,
ita da Raliya Ummi kuwa na cikin É—akinta,
Hayatuddeen kuwa yanzu ya shigo shida abokinshi Khamis wanda suna can yawonsu ne motar Khamis ta samu ƴar gyara shine suka miƙata wurin kanikawa,
to kasan cewar suna kusa da gidansu Saifuddeen É—in ne shiyasa Hayatuddeen ya jawoshi suka taho.

A tare suka shigo da Ahmad,
a falon suka zauna suna hira,
koda Ummi ta fito Khamis kamar mutumin kirki haka ya duƙa ya gaidata a mutunci,
cikin kula Ummi ta amsa, kana ta juyo ta kalli Ameena dake zaune cikin kula tace.
"A a Ameena ina sarkin kukan?".
Murmushi ta É—anyi tare da cewa.
"Yana can wurin Amminshi nima tunda na dawo ban gansuba, shiyasa nai sallana ananma dan nasan da zaran sunji motsina za suzo su liƙa minshi ya hanani salla akan lokaci yace sai yasha nono".
Dariya Ummi ta É—anyi kana tace.
"Dama ai haka iyayen yara suke,
kuma yau wuni yayi kuka inaga ya fara gajiya da barinshi da akeyi duk yau ya gigitamu".
Hayatuddeen ne ya É—an kalli Ummi tare da cewa.
"Ato gobe in zaki tafi ki tafi dashi kar a shiga haƙƙinshi".
Murmushi Ameena ta É—anyi kana tace.
"Gobe kam ma ina off, zamu wuni a gida ya kontar da hankalinshi".
Raliya ce ta miƙe tare da cewa.
"Ai yama yi ƙoƙari wlh".
Ahmad kuwa hankalinshi na kan system É—inshi,
Khamis kuwa murmushin yake É—anyi,
dai-dai lokacin, Saifuddeen ya shigo,
da sauri Hayatuddeen yace.
"Kai masha ALLAH Hamma na kayi kyau".
Wani irin yalwataccen Murmushin Saifuddeen yayi wanda da zaran ka ganshi kasan yana cikin farin ciki,
gaban Umminshi yazo ya gaidata in boddy language É—insa cikin kula tace.
"Ina sarkin kukan?".
Ido ya lumshe tare da mata alamar yayi bacci.
sai kuma ya É—an juyo ya kalli Khamis dake gaidashi,
amsa mishi yayi yana mai ƙara karantar yaron,
sai kuma ya kalli Ahmad dake, ta aiki yasan tabbas aiyuka sunyiwa Ahmad yawa sabida sunata harharde komai da komaine nasu,
wuri ɗaya nanda wata uku cikon shekara zaiyi kuma yana son ya ware haƙƙin Hayatuddeen da Adda Rahma da Raliya da Raihana ya basu nasu tunda kowa yasan haƙƙinshi daya mallaka
Dan ma Allah yayi tuntuni ya warewa Bappa Ali da Goggo dada nasu,
ya bar musu wannan filin na suka bawa MTN hayarshi,
inda bappa Ali kan karɓi hayan shekara biyu kana goggo dada ta ƙarɓi na shekara ɗaya kamar dai yadda shariya ya tsara.

Hannu ya bawa Ahmad sukayi musabaha, kana ya juya ya kalli Hayatuddeen dake ta tuttura baki wai Hammanshi bai ƙulashiba,
murmushi yayi kana ya ɗan shafa gefen fuskar daya fara tara ƙasumba,
yayi kyau sosai cikin shigar ƙananan kaya rigarshi mai kalar sararin samani da ratsin fari sai ya fito kamar adon gajumare a cikin sararin samaniya wondonshi baƙine mai ɗan rashin ruwan ƙasa-ƙasa.
Sosai siffofin girma suka fara bayyana a jikin autan Ummi,
in boddy language É—insa yace.
"Fushin me kakeyi zaka bata fuskarka da yawan tura bakin nan da kakeyi gashi yanzu bakinka ya zama ƙato".
Da sauri yace.
"To na bari dariya sukayi baki É—ayan su.
Ameena kuwa wani irin daÉ—i takeji dan,
duk sansa zasu haÉ—a ido sai yayi mata signal da girarshi É—aya, kana ya É—an zaro mata harshe.

Ummi ce tayi nufi dinnin area tare da cewa.
"Kuzo muje muci abinci".
miƙewa sukayi baki ɗayansu suka nufi dinnin table ɗin,
har Khamis da Hayatuddeen ya kamo hannunshi,
Raliya ce ta É—an kallesu bayan sun zauna cikin kula tace.
"Adda Zaleeha fa?".
Ido Ummi ta zubawa Saifuddeen cikin yanayin tambaya,
gane abinda take nufi yasashi mata alamun shi yana tsamman tana nan ai,
Raliya ce ta miƙe tare da cewa.
"To bari inje in kirata."
To sukace kana Ummi tace.
Ameena tasa musu.

A hankali ta shiga cikin ɗakin Zaleeha da sauri ta ƙarasa ciki hangota konce a kan gado,
cikin kula ta sunkuyo kanta tare da cewa.
"Aunty Zaleeha! Aunty Zaleeha".
Da kyar ta buÉ—e idanunta da takejin suna ciccikowa da hawaye dan haka take in dai bata da lfy tofa sai hawaye,
cikin tsoro Raliya tace.
"Aunty Zaleeha bakida lfy ne?".
Kai ta gyaÉ—a mata murya na rawa tace.
"Zazzaɓi nakeji, ƙirjina kuma nata bugawa".
Cikin tausayawa Raliya tace.
"To tashi mu tafi cikin gida kici abinci sai muje asibiti ko a kira Ya Adnan yazo ya dubaki".
Hawayen da suka cika mata idone suka silalo kana a hankali tace.
"Ya isheni bana jin yunwa, kije kuci abinci".
kai ta girgiza tare da cewa.
"A a kam me kikaci daya ishekin bari inje gayawa Ummi."
tana faÉ—in haka ta fita.

Tana shiga ta samu Ameena na zuzzuba musu abincin cikin sanyi tace.
"Ummi Aunty Zaleeha fa ba lfy, gaba ɗaya jikinta sai karkarwa yakeyi zazzaɓi takeji".
Juyowa sukayi baki É—aya suna kallonta cikin mmki Ummi tace.
"Ikon Allah bata da lfy kuma itacefa tai girgin nan lfy-lafiya ta gama komai, ta tafi taje tayi wonka ne, ta bar Adeel a nan da babanshi ya dawo nema ya É—aukeshi suka tafi."
Ahmad ne yace.
"Ummi Ciwo ba wuya ai."
Shi kam Saifuddeen shiru yayi ya zuba musu ido a ranshi yake cewa.
"Uhummm uwar tsoro zazzaɓi tsoro ko, zanyi mgninki ne yarinya, Allah ya ƙiki kiyi gangancin shiga ɗakina wannan al'kwarari ne duk randa ƙafarki ta kaiki ɗakina bazaki fito da budurcinkiba".

Ameena ce ta ɗan yuƙura alamar zata tashi,
cikin kula Ummi tace.
"Ina zakije?".
A hankali tace.
"Ummi zanje in duba Ammin Adeel ne, ko akwai taimakon da zan iya mata".
Cikin jin daÉ—i Ummi tace.
"Zauna muci abincin, in mun gama muje mu dubata,
Ke kuma Raliya É—ebi abincin ki kai muku kuci da ita".
To Raliya tace kana ta É—aukar musu abinci ta juya ta fita.
Ameena kuwa har ga Allah taji, ciwon Zaleeha a ranta sabida koba komai Zaleeha na nuna kulawarta kanta da É—an ta.
Saifuddeen kuwa ji yayi tamkar ya ruggume Ameena a wurin, kimarta da darajar ta keta hauhawa a idanunshi,
yana hasaso yadda rayuwa zatayi musu sanyi in Ameena ta kwantar da hankalinta.

A haka suka fara cin abincin.

Ba jimawa Raliya ta dawo da kular abincin cikin sanyi tace.
"Ummi taƙi taci fa,
jikinta zazzaɓin yayi zafi".
Kusan a tare Ummi da Ameena suka miƙe,
suka nufi side É—inta.

A hankali suka shiga Ummi na gaba Ameena na baya,

Suna shiga Ameena ta É—an sunkuyo kanta, cikin kula tace.
"Ammin Adeel Sannu zazzaɓi haka ko zamu tafi asibiti ne?".
Cikin ƙarfin hali tace.
"Yauwa sannu Ummu Adeel ngd".
Gefenta Ummi ta zauna tare da cewa.
"Tashi ki zauna".
Yunƙura tayi zata tashi da sauri Ameena taimaka mata ta zauna,
a hankali Ummi tace.
"Yaushe ya fara miki?".
Ido ta lumshe tare sunkuyar da kai dan bata son suga hawayenta a hankali tace.
"ÆŠazune".
Ameena ce ta amshi zancen da cewa.
"To bari in kawo miki mgni".
Da sauri ta jujjuya kai tare da cewa.
"A a zai bari bar shi kawai Ummu Adeel".
Ido ta dan zuba mata ganin yadda taketa gyara Adeel konciyarsa a hankali tace.
"To ko allura za'ayi miki".
Da sauri ta gyara zamanta tare da ture blanket É—in wai dan ta nuna musu alamun cewa ta worke,
garin hakan har ta tada Adeel.
Hannu tasa ta É—aukoshi tare dayin murmushin dole tace.
"Ah ah babu komaifa na worke karki damu".
Ta ƙarishe mgnar a fili a ranta kuwa cewa tayi.
"Uhumm nasan muddin kikamin Allura yaseen nasan zanyi kuka, in kuwa nayi kukan naji kunya gaban uwar miji da kishiya da ƙannen miji, babuma ya Hayatuddeen in ya tasoni gaba naga ta kaina".
Murmushi Ummi tayi dan ta gano tsoron allurar takeyi,
Cikin kula tacewa Ameena.
"Je ki kawo mata mgnin ta haÉ—iya".
da sauri Amina ta fice ta nufi É—akinta.
Jim kaɗan sai gata da magungunan ita da kanta ta ɓalla ta bawa Zaleeha ta shasu da tea ɗin da Raliya ta kawo mata.

Koda tasha a take sai tai ta É—an gyatsa, ganin yadda Ameena ke kula da itane yasa Ummi fita ta koma ranta fal farin cikin.
Alhamdulillah burinta da addu'arta ga Ameena ya karbu Allah ya sassauta mata kishinta.

Ita kuwa Ameena hannu tasa ta karɓi Adeel tare da cewa.
"Kawoshi ki samu ki huta,".
Shafa kanshi tayi ta miƙa mata shi kana ta koma ta konta,

Raliya ce ta É—an kalleta cikin kula tace.
"Ya Ahmad yace in miki sannu da jiki".
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa.
"To, ngd".
Shiru suka ɗanyi ganin alamun ta fara lumshe ido alamun zatayi baccine yasa Ameena ta miƙe gyara mata rufuwanta tayi tare da cewa.
"Sai da Safe Ammin Adeel Allah ya ƙara sauƙin" .
"Amin Amin ngd matuƙa".
Zaleeha ta faÉ—i tana kallon Ameenan
Raliya ma miƙewa tai tabi bayan Ameena bayan ta mata saida safe.

Saifuddeen kuwa falon Ummi ya dawo ya zauna shida Hayatuddeen da Khamis,
cin boddy language É—insa yacewa Hayatuddeen ya bashi wayarshi.
Cikin É—an Mamaki yace.
"Wayata kuma Hamma me zakayi dashi?".
Fuska ya haɗe kana ya kalli Khamis tare da mishi alamun ya miƙo mishi wayarshi.
A daburce Khamis ya miƙa mishi,
Ganin haka shima Hayatuddeen ya miƙa masa tasa wayar dan a zatonsa baisan code numbers ɗinsuba.

Shi kuwa yana amsar woyoyin ya zurasu a al'jihunshi kana, ya turawa Sule text cewa yazo ya maida Khamis gidansu.

Zuru-zuru sukayi da idanu sabida sun sha jinin jikinsu gashi ya haÉ—e musu fuska ba alamun wasa,
Shigowar Sule ne ya sasu,
juyowa garesu, jin yana ce musu.
"Khamis Hamma Saif. Yace kazo in maida kai gida dare yanayi".
Da sauri Khamis ya miƙe tare da cewa.
"To gani nan zuwa, sai ya kuma juyo ya kalli Hayatuddeen ya mishi alamun ya amsar mishi wayarshi, cikin tsoron Hamman nashi yace.
"Uhum Hamma Saifuddeen zai tafi ka bashi wayarsa".
Wani irin kallo ya watsa musu wanda yasa dole sukayi shiru.
sai kuma ya musu alaman sai gobe yazo ya amshi wayar.
To sai dai a zatonsu bashida damar sanin me woyoyin nasu suka ƙunsa
Da haka suka fita.

Bayan Khamis ya tafine, shi kuma Hayatuddeen ya biya wurin Zaleehan ya mata sannu da jiki.
Chapter 109 · 0% Book details