← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 154

Sashe 14

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Adda Rahama takamo hannun nasa ta riƙe tana murmushi, hannu tasa ta shafi gefen fuskarsa take ta buɗe wata ƴar purse ɗinta, fararen ƴan dubu-dubu miƙaƙƙune suka cika cikin jakan, haka suma su Raihana da Raleeya da Aunty Kubra gaba ɗayansu jakakkunansu suka buɗe, kuɗaɗen suka ciro inda suka soma yiwa ɗan uwannasu da amaryarsa ɓarinsu, kuɗi suke zuba musu sosai har kaman basason kuɗin, yayinda wajen ya cika da kiɗa haka masu vedio da kuma photo sunatayi, abun sosai yake ƙayatarwa, shikansa Saifuddeen saida yasha mamakin yanda ƴan uwannasa ke ɓarar da kuɗi wajen yi masa liƙi, suna cikin yi musu liƙinne, Dr Adnan da kuma Ahmad, haɗi da Saminu da General Abbas mijin Aunty Kubra suka ƙaraso. Hohoho idan bakwayi kuban waje, domin kuwa sosai suka shiga taya matansu likin, nanfa abun yaƙara girmama mutane da yawa sai sakin baki sukayi suna kallonsu, Ahmad kuwa har kamo Raleeya yake suna ɗan taka rawa atare, sosai suka nunawa Saifuddeen ɗin ƙauna, kafun daga bisani mazajensu suka janyesu inda sukabar kan dandamalin, nanfa mc yabawa gaba ɗaya abokan ango dama. Nanfa akeyinta rigiji rabgi , domin kuwa gaba ɗayansu da rawa suka shigo cikin filin, hakanne yasa gaba ɗaya hall ɗin aka ɗau sowa, don sosai abun ya ƙayatar, babuma kamar ishaq, Aziz, Ahmad, Salisu, Warisu tumbuleƙe, Mudassir, Jabeer, Hisham, kai baki ɗayansu dai wanda suke rawa sosai, babu wani kunya ko ɗar, acewarsu ranan da suke jirane tazo, Ibrahim, Wareesu, Saleesu, Saminu, da kuma Aziz da sauran school friend ɗin Saifuddeen ɗin kuwa suma sosai suka taka, Ishaq ma da ba gani yake ba haka ya gwada basirarsa wanda ya burge kowa, Ahmad ne ya jawo Saifuddeen zuwa cikinsu, har tsakiyarsu ya jawosa bisa kan wheelchair ɗinsa, nanfa suka kewayesa sukayi mishi zube suna rawa tare dayiwa junansu ɓarin kuɗi, ko ina dake cikin hall ɗin tafi haɗi da shewane ke tashi, domin sosai salon na abokan Saifuddeen ya tafi da kowa, sun bala'in burgewa. Koda suka gama bidirinsu suka koma, nanfa mc yayi gyaran murya tare da ƙiran masu gayya da aiki, ginshiƙai kuma ƙannen ango. Hohoho inji hausawa sukace abu namu maganin akwaɓemu. Su Hayatuddeen da Zakariyya Imran da Sulaiman kana isma'il da Faruq ɗan Adda Rahma. Manyan ƙanne, yara matasa masuji da ƙarfi ajikinsu, ƴan matasan da suke ji da tashen tasowarsu, salon rawar tasuma ta dabance don kuwa saida ango da kansa yashiga tafa musu, don da wani irin ƙayataccen rawa suka shigo cikin filin, nanfa aka somayi musu ihu ana ƙara zugasu kansu na ƙara girma, harta Isma'el ɗan Alhji Kaburu dayake kurma saida ya taka, sosai Hayatuddeen da abokansa Imran, Sulaiman, Isma'il da ƙanin amarya Zakariyya rawa irin ta zamani sukeyi mai ɗaukar hankali, hakanan jama'an wajen sukaji kwaɗayin yi musu liƙi, don kuwa rawan nasu yayi kyau sosai, nanfa jama'a suka soma yi musu ɓarin kuɗin. Ango Saifuddeen kuwa sai wani ƙasaitaccen murmurshi yaketayi hannunshi rike da hannun Zaleeha daketa mutsutsun kwacewa, yayinda hawaye ke zubo mata tabbas taron ya haɗu iya haɗuwa irin haɗuwa na kece raini da nunawa sa'a taso ace da wanda take sone take zaune a yanzu ,domin har tsikar jikinta tashi yakeyi yadda hall ɗin ya ricaɓe aketa ɓarin kuɗi, ita da kanta tasan babu ƙaranta a bikin ta kuma yarda komai na alfarma akeyi ta gamsu da ranta mijinta kuma kekyawane irin kyau na kece raini da nunawa sa'a ta kuma gamsu mai cikekkiyar tsabta ne da gayu, kuma masoyine na gaskiya dan taga salon zazzafar soyayyarshi to amman mijinfa bashi da maraba da ginennen taɓo kuma duk haka tasan yazo a ƙirerren lokacine wlh da yazo kafin haɗuwanta da wanda ya taimaketa tabbas yanada nagartar da dole ta soshi to amman a makere yazo, kuma sai takeji can cikin zuciyarta kamar wani abu ke sarrafa mata zuciya, bata dawo daga duniyar tunaniba taji sauƙan tattausan yatsunshi kan haɓarta da sauri ta ɗan juyo ta kalleshi sai kuma tayi maza ta lumshe idanunta ganin ya ɗaga mata girarshi ɗaya tare da kashe mata ido kana ya ɗan kaɗa mata harshe alamun, ya dai, kana ya ɗan nago hannunta dake tsarke da nashi bayan hannun nata ya juya tare da manna mata wani irin sassanyan kiss. wow nanfa masu hoto suka koma kansu. Cikin farinciki Hayatuddeen yaƙarasa wajen Hammansa nanfa yasanja salon rawarsa, hannun Hamman nasa ya kamo, ahankali yake juya kujeran Hamma Saifuddeen ɗin nasa, hakan yasa abun yaƙara armashi, murmushin farinciki kawai Saifuddeen ɗin keyi, haƙiƙa ƴan uwa da abokansa sun nuna masa tsananin gata, nanfa Hayatuddeen da abokansa suka ciro kuɗaɗen al'jihunsu suka soma zubawa Saifuddeen da Amarya Zaleeha, Zakariyyane yaƙarasa jikin ƴar uwartasa ahankali ya kamo hannuwanta tare da jawota tsakiyan filin, tayi matuƙar mmkin ganin Ya Aminu Ya Ahmad Ya Habu Aunty Shatu Aunty Lubna da Adda Maryam dasu Amira ƙannen ya Aminu sun mata zobe ita da ango Saifuddeen suna mata yayyafin kuɗi, Zakariyya kuwa nan ya riƙe duka hannuwanta, cikin tsananin ƙaunar ƴar uwartasa yasoma ɗan jijjigata hakanne yasa Zaleeha taɗan saki murmushi, nan taɗan soma ƙafafunta, ganin haka yasa gaba ɗaya su Hayatuddeen suka ke wayeta suna rawa, bisa dole Zaleeha ta biyesu suka ɗan soma takawa,don kuwa ansanya musu wata daddaɗan waƙa, wanda ko baka da niyar yin rawa saika taka, bare ita Zaleeha uwar son waƙa da kiɗi haka yasa taɗan saki jikinta bayan anyi musu ɓarin kuɗi sosai takoma kan kujeran ta zauna tana me maida ajiyar zuciya. Haka dai akayita shagulgula masu ƙayatarwa yan ƙungiyar jonapwd sunyi matuƙar bada mmkin irin kuɗaɗen da suka liƙawa ango, nairori kam awannan rana sunyi kuka sosai, an ɓarnatar dasu baɗan kaɗan ba, sai wajen ƙarfe 10:00 pm, aka kammala gudanar da diner'n, nan kowa yasoma ƙoƙarin tafiya gida, don dayawan mutane amatuƙar gajiye suke, babuma kamar Saifuddeen, wanda dama shi sam bai iya jure wahala, abu kaɗan ke gajiyar dashi, sai yaji duk yazama very weak bare kuma ga hidimar da yasha, yanzuma babu wani abu dayake buri da fatan gani kamar Umminsa, so kawai yake yaje yayi mata complain ɗin gajiyar dake damunsa, kamar yanda sukazo amota ɗaya haka komawarsu ma takasance amota ɗaya, saidai har suka iso gidan ko ƙala baice mata ba, gaba ɗaya gajiya ke damunsa, itama Zaleehan agajiye take hakan yasa ta lafe jikinta ajikin kujeran motar tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci.
Chapter 14 · 0% Book details