← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 154

Sashe 28

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Can wajen Saifuddeen kuwa fitowarsa daga wanka kenan,  cikin nutsuwa ya gama goge jikinsa, inda ya sanya towel ya shiga tsane lallausan sumar kansa, wanda yaji aski irin na zamani, uwa uba yasha gyara sai ƙyalli yake, yana kammala goge jikin nasa, ya ɗauki body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi, cikin nutsuwa ya shiga shafawa, yana kammala wa, ya shafe jikinsa da wani irin body oil spray mai matuƙar ƙamshi,  take gaba ɗaya ɗakin ya gauraye da ƙamshin sa,  ahankali ya tura wheellchair ɗinsa har zuwa gaban haɗaɗɗen drawer ɗinsa,  buɗe drawer'n nasa dake shaƙe da kaya yayi,  hannunsa yakai zuwa ɓangaren da ƙananan kayansa ke jere,   wani crazy combat jeans Black colour haɗi da wata D&G t-shirt mai kyaun gaske ya zaro, daga cikin tarin kayan nasa, sosai drawer'n nasa ke cike da kaya, sai kace wani kanti, wani kayan ma har mantawa yake dasu, dan ma duk bayan wani ɗan lokaci yana kyautar da kayayyakin da sosai musamman wa mutanen ƙungiyar su Jonapwd.
Cikin yanayinsa na nutsuwa ya zura kayan ajikinsa, wanda suka matuƙar amsar farar fatarsa,  wani silver watch ya sanya ahannunsa, sannan ya buɗe wata ƴar glass drawer dake nan cikinsu yake aje caps ɗinsa, wata baƙar facing cap mai kyau ya zaro, inda ya ɗaura akansa, take yafito yayi wani daban dashi, ga wani irin kyau da yayi, ahankali ya tura wheelchair ɗinsa zuwa inda yake aje takalmansa, wasu flat shoe masu kyaun gaske ya zura acikin fararen ƙafafunsa, wayoyinsa da kuma laptop ɗinsa ya ɗauka, parfumed ya shafa, sannan yanufi hanyar fita daga ɗakin,  ahankali yake tafiyar da wheelchair ɗin nasa, har yasamu kansa acikin falon Zaleeha'n, ko ƙofar ɗakinta bai kalla ba haka yafice daga cikin part ɗin nasu gaba ɗaya,  direct ɓangaren Umminsa ya nufa.
Kusan karo sukayi da Hayatuddeen wanda ke ƙoƙarin zuwa part ɗin nasu, ƙiransa shida Zaleeha akan cewa suzo suyi break, don su atunaninsu zuwa lokacin ta dawo.
Duban Saifuddeen ɗin Hayatuddeen yayi, cikin ƙaunar Hamman nasa yace.
"Wow Hammana kaga yanda kayi kyau kuwa!."
Murmushi Saifuddeen yayi tare da duban Hayatuddeen, irin duban nan mai É—auke da yanayin magana, alama yayi masa cewar.
"Uhummm ."

Kai Hayatuddeen yajinjina masa tare da cewa.
"Fiye da kullum ma kuwa, wani lokaci Hamma nakan tambayi kaina, me yasa kai ba mace ba amma kowani kaya kasa saikayi musu kyau, saidai kuma idan na tuna da cewa Hamman nawa Namijin gaske ne, sai naji kaina ya ƙara girma, saboda samun ka amatsayin Hamma yafiyemin komai."
Murmushin daya bayyana tsantsar kyawunsa yayi, cikin ƙaunar ɗan uwan nasa yasanya hannunsa inda yakamo kumatun Hayatuddeen ɗin.
Dariya Hayatuddeen yayi tare da zagawa bayan hamman nasa inda ya turosa zuwa cikin falon, da shigowarsa cikin falon har falon ya ɗauki ƙamshin oud ɗin dake jikinsa.
Har gaban dinning area Hayatuddeen ya tura hamman nasa,  inda Raliya da kuma Ahmad ke zaune, Raliya ne ta gaishe da yayan nata,  cikin ƙauna da kuma ganin ƙoƙarin ƴar uwar tasa na haɗa musu break fast kullum da takeyi ya amsa mata, yana tunanin gashi tasa an sallami mai akin wai duk a kanshi dan sun san yanada tsantsani.
  Dai-dai lokacin Ummi ta fito daga cikin ɗaki, ganin Saifuddeen zaune yasa ta ƙara faɗaɗa fara'arta cikin kulawa tace.
"Kunfito ko, ina Zaleeha'n, nace yau itama tazo cikin mu tayi break dan duk anzama É—aya."
Ummi taƙare maganar tana me jawo kujera ta zauna.
Kallon Hayatuddeen Saifuddeen yayi, cikin body language yayi masa alama kan cewar yaje ya ƙirawo Zaleeha'n, kai tsaye hayatuddeen ya tafi don ƙiranta.
Koda yaje part ɗin nasu, haka yayita knocking a ƙofarta, amma shiru, jin shiru ne yasashi tura ƙofar ɗakin ahankali, ɗan tsayawa yayi abakin ƙofa, da ɗan ƙarfi yace.
"Aunty Zaleeha kizo muyi break, kin san dai bana iya jure yunwa."
Jin shiru ba'a amsa shi bane yasanyashi ƙara kutsa kansa cikin ɗakin, nan yashiga dube dube kozai ganta amma shiru, kasa kunnensa yayi wai ko zaiji motsin ruwa a toilet, nan ma dai shiru, hakan yasashi juyawa kawai yafice daga ɓangaren nasu gaba ɗaya.
Yana komawa yace musu baiganta ba, har ɗakinta ya shiga amma bakowa ciki,  fuska ɗauke da mamaki Saifuddeen ke kallonsa, to ina Zaleeha zata je kenan,  kallon Ahmad yayi wanda yake ƙoƙarin saving ɗin kanshi, yana cewa.
"Maybe bata dawo daga fitan da tayi bane."
Gane abun da Ahmad ɗin ya faɗa ne, yasa shi ɗan lumshe idanunsa,  Ummi ne ta dubesa, cikin kulawa tace.
"Dama kasan da fitarta ne? dan Ahmad yace yaga fitanta tun da sanyin safiya koma ince asuba."
Idanunsa ya rumtse tare da girgizawa Ummi'n kai, alaman "A'a."  ɗan jim Ummi tayi take kuma, wani tunani yazo mata inda ta raya aranta cewa ko gida Zaleehan taje, nan dai tace tasan cewa zuwa anjima zata dawo.
Raliya ne tayi saving É—insu inda suka soma cin abinci cikin nutsuwa, shidai Ahmad hakanan jikinsa ya basa wani abu daban, yasan babu dalilin da zai kai Zaleeha gida awannan sanyin safiyan, idan da ace akwai dalilin ma to tabbas yasan da zuwa yanzu ansanar dasu.
Haka suka kammala break fast ɗin nasu cikin nutsuwa, Ahmad ne ya miƙe dan yana so yaɗan fita, shikuwa Saifuddeen cikin falon na Umminsa ya koma, inda ya sauƙa daga kan kekensa, kwanciya yayi akan doguwar kujera tare da jawo laptop ɗinsa, ya ɗaura akan cikinsa, nan ya buɗe cikin nutsuwa yashiga yawo a internet, Hayatuddeen ma zama yayi akusa da hamman nasa inda ya jona game a tv plasma ɗin dake cikin falon, hakan yasa kowa da inda ya bada hankalinsa, Ummi kuwa ɗaki ta koma dan tanason kimtsa wasu kayyakin gudumowan biki da aka kawo mata, nan Raliya ta bita inda suka shiga aikin tare.

Sosai yabada hankalinsa akan aikin da yakeyi, hakanne ma yasa har lokuta suka ja batare daya sani ba, inda Hayatuddeen kuwa tuni ya kwanta akan carpet yayinda bacci ya ɗaukesa, da dukkan alama jiya kusan kwana yayi yana chat, don abu ɗaya ne ke saka Hayatuddeen bacci da rana, shine idan bai samu enough bacci da dare ba, to dole da rana zaiyi bacci, wai abun ma yazo masa da sauƙi don yau basu da lectures sai ƙarfe 2:00 pm, shi yasama yaji gwamma yayi baccinsa, kafun time ɗin.

Ummi ne tafito daga cikin ɗakinta, duban Saifuddeen tayi, ganin kaman baisan da zuwanta ba yasa ta shafi gashin kansa, ɗago da kansa yayi inda ya dubeta, ganin Umminsa ya sashi narke fuska,  akasalance yayi mata alaman sannu da fitowa, hakanan yake aduk sanda zaiga Umminsa, to fa raki da shagwaɓa kawai zai dinga yi mata, wani lokaci ko Hayatuddeen bai  kai Saifuddeen yawan shagwaɓa ba.
Kansa Ummi ta shafa, cikin kulawa tace.
"Inajin gabana yana É—an faÉ—uwa tun É—azu, ya kamata kaje ka duba Zaleeha kota dawo."
Fuskansa yaɗan kwaɓe, tare da tashi zaune miƙa yayi inda yayiwa Ummin alaman cewa ya gaji, murmushi kawai Ummi tayi tare da ƙwala ƙiran Raliya, wanda ta shiga kitchine don ɗaura musu lunch, don a time ɗin kusan ƙarfe ɗaya ake nema.
koda Raliya'n tazo, cewa da ita Ummi tayi, taje ta duba part É—in nasu Saifuddeen ko Zaleeha ta dawo.
Da "To." Kawai Raliya ta amsa, nan tafice daga cikin falon, koda taje part ɗin, haka tayi ta kwaɗa sallama amma shiru ba amsa, alaman bata dawo ba kenan,  haka ta fito daga falon, koda ta kawo compound ɗin gidan, parking space ɗinsu ta duba, nan taga babu motar Zaleeha'n, alaman kenan bata dawo ɗin ba, nan ta koma inda ta faɗawa Ummi cewa "Zaleehan bata dawo ba."
ÆŠan jim Ummi tayi nan tace.
"To bari dai zuwa yamma, idan bata dawo ba sai muƙira gidansu mu tambaya, ko wani abunne ya faru."
Shidai Saifuddeen ƙala baice ba, saboda ae Zaleehan bata maidashi miji ba, because da zata fita kanta tsaye ta fita, babu neman izini ba komai, wannan yasa shima bazai shiga cikin shirgin nemanta ba, sauƙa daga kan kujeran ma yayi, inda ya hau kan wheelchair ɗinsa, da kansa ya tashi Hayatuddeen, inda yace yaje ya ɗauro alwala yazo su wuce masallaci, don yin sallan Azahar, part ɗinsu yaje inda yayi alwala, koda yafito yasamu Hayatuddeen tsaye nan suka wuce masallacin dake kusa dasu.

Ummi kam dai hakanan takejin wani abu dangane da tafiyan Zaleehan, sosai take fargaban abun da zuciyarta ke raya mata, aranta tana fatan ma Allah yasa ba hakan bane.
Saifuddeen kuwa koda suka dawo masallaci, part É—insu ya nufa, nan ya nufi bedroom É—insa, inda ya kwanta ya É—an huta.
Chapter 28 · 0% Book details