← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 154

Sashe 105

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saifuddeen kuwa sosai yayi bacci, dan bashi ya farka ba sai wajajen ƙarfe 10, bathroom ya shiga ya sakeyin wanka sannan ya kimtsa kansa cikin, wasu haɗaɗɗun riga da wando, sai baza ƙamshi yake haka ya nufi sashin Ummi, dan yunwa yakeji sosai.
Ummi ce da Zaleeha kaÉ—ai zaune afalon, Ummi nakan kujera, ita kuwa Zaleeha tana ta kaikoma acikin falon, sai faman jijjiga Adeel dake kuka yake,
shigowarsa cikin falonne yasa Ummi cewa.
"Yauwa gama babansa nan, Zaleeha miƙawa babansa shi ko zaiyi shiru, tun ɗazu ya cikamu da ihu, bansan meke damunsa ba, bacin kuma ƙiwa ba halinsa bane." Ɗan kallon Saifuddeen ɗin Zaleeha tayi, sai kuma ta sadda kanta ƙasa.
Shikuwa ahankali yaɗan lumshe kyawawan idanunsa da suka sauƙa akan haɗaɗɗiyar surar jikinta, hips ɗinta wanda ya cika sket ɗin jikinta, yayi masifar kyau da tsaruwa yake kallo, jiyayi tsikar jikinsa sun mimmiƙe, asanyaye Zaleeha ta karaso inda yake, ɗan sunkuyawa tayi daniyar ajiye masa Adeel ɗin akan cinyarsa, hakanne yasa beautyful breast ɗinta suka ɗan bayyana ta saman wuyan rigar, ganin kyawawan saman breast ɗin nata yasa yaji wani abu na yawo ajikinsa, wajen miƙa masa Adeel ɗin ne kuwa, hannunta ya gogi nasa, take sukaji wani irin shock, hakanne yasa cikin sauri ta zare hannunta tare da komawa gefen Ummi ta zauna,
É—aga Adeel É—in yayi yana yi masa wasa, take kuwa yaron yasoma sakin murmushi, harma da É—an dariya,
Ummi ne tace.
"Kuji ja'irin yaro, wato yaga Babansa shine harda dariya, dama kenan mu kakewa ƙiwa." Murmushi kawai Saifuddeen ɗin yayi, yana riƙe da Adeel ɗin, ya ƙarasa dinning area, ganin haka yasa aɗan kunyace Zaleeha ta tashi, ta ƙarasa dinning table ɗin, cikin nutsuwa take seving ɗinsa haka nan take jin kamar ta zauna kusa dashi, shikuwa idanunsa ya zuba mata, dan sosai tayi masa kyau, yau ɗin zallan yarintarta ya bayyana sosai, gashi kayan jikin nata sunyi mata cif-cif, har gabansa ta kawo masa plate ɗin abincin, ɗan ɗagowa tayi, hakanne yasa idanunsu sarƙewa acikin na juna, rolling eyes ɗinsa yayi, take taji wani irin yaarrr yaarrr ajikinta, saboda yanda abun ya ƙarawa fuskarsa kyau, wani irin kallon shauƙin daya bita da shine yasa, takusa yin tuntuɓe wajen barin dining area'n,
wani ƙawataccen murmushi ya sake, tare da ɗauke kansa ya maida hankali kan abincinsa. Nan kusa da Ummin ta dawo ta zauna, suna ɗan taɓa hira da Ummin, har ya kammala cin abincin, koda yazo fita, akan cinyanta ya ajiye Adeel ɗin, sannan ya fice. Yana fita kuwa Adeel yasa musu kuka, haka suka dinga rarrashinsa ita da Ummi, saida yayi bacci kafun suka samu salama, Zaleeha kam tuni kukan Adeel din ya ruɗata, har tanajin ƙwalla sun cika idanunta, sam batason kukan Adeel ɗin.

Saifuddeen kuwa yana fita daga part É—in Ummi'n, kaitsaye gidan ya bari, dan suna da meeting É—in da zasuyi.

Adeel kuwa wunin yau gaba ɗaya kuka ya dinga musu, da ƙyar suke iya rarrashinsa.

Ameena kuwa yau da wuri suka tashi, a hankali suke tafiya ita da ƙawarta Samira, har suka iso bakin harabar inda suke aje motocinsu, shiru Ameena ta ɗanyi tare dacewa Samira.
"Yau baki fito da motarki bane?".
Murmushin Samira tayi tare da cewa.
"Eh yau a napep nazo, Æ´ar uwatace motarta na wurin gyara, kuma sunada biki a danginta, shiyasa na bata nawan".
Cikin fidda numfashi Ameena tace.
"Uwar gidanki ko?".
Kai Samira ta gyaÉ—a mata alamar eh,
cikin sanyi Ameena tace.
"Kinji dadi Samira inamw ace nima Allah zai yaye min kishi in samu in saki jikinda uwar gidana, dan wlh ita dai irin kice."
Murmushi Samira tayi tare da cewa.
"Uhum Ƙawata ai abin mai sauƙine muddin kika sauƙaƙawa kanki to Allah zai sauƙaƙa miki in kuwa kika tsananta wa kanki zakisha wuya, ni da uwar gidana wlh ko ƴan uwa sai haka, bamu da matsalar komai sabida mun sawa ranmu haƙuri, bawaifa bama kishin bane, no ai kishi kumallon matane, amman kishinmu mai tsari mukeyi, ina gaya miki ki saki ranki da abokiyar zamanki zakuji daɗin zama, tunda keda kanki kin shaida min ita bata da kishinki asalami ke gani kike wai kamar bata son mijin nakune, to wlh Ameena bawai bata son mijinku bane ba mamaki ma ta fiki sonshi kawai dai ta iya takunta ne, babu mamaki ma ta fiki sonshi sai dai wata ƙil ita sonta irin son nanne da zaka so miji ka kuma so duk abinda yake so, kawai dai ta iya sarrafa kantane."
Cikin sanyin jiki Ameena tace.
"Shiga motata muje in sauƙeƙi dama ina son muyi mgna".
kai ta gyaÉ—a mata kana suka shiga Mota,
shiru sukayi saida Ameena ta dai-dai ta hancin motarta kan titi kana ta juyo ta É—an kalli Samira cikin sanyin jiki tace.
"Wato ko Samira ni kaina nasan zuciyata bata min adalciba akan Ammin Adeel, na yarda na gane tana masifar son ɗana so kuma na gaskiya, kana tana kawar da kanta akan harkata da mijinta tamkar bata san me mukeyi ba, bawai ina jin na tsaneta bane a a wlh ni kaina ina sonta sai dai ina masifar kishinta,ina son Abban Adeel wani irin son da ni kaina bansa adadinshiba shiyasa nake kishinsa bana son yayi nesa dani, kinga tsabar zugar kishi wallahi yanzu sai yayi ta bina yana son haƙƙinshima sai inji to ai yanada wata matar."
Juyowa Samira tayi ta fuskanceta da kyau cikin wayewa da iya salon kishi na Musulunci tace.
"Kin wahala kin ɗorawa kanki dala ba gammo, ke ƙawata in banda tsaurin ido irin namu na mata ki samu mace da mijinta kice zaki zafafa kishinki yo in dai ita bata zafafabaai ke kuma bai dace ki zafafaba me ruwanki da ita zamanki da ban nata da ban, tsakaninku babu babbancin matsayi ku duk matanshi ne, ki dena sawa ranki yafi sonta, ko ganin wani ƙira nata, ki gyara zuciyarki zakiji daɗin zama da kowa a gidan".
Shiru Ameena tayi jiki a mace dan ta Æ´arda da batun Samira tasan gsky take gaya mata,
ita kuwa Samira cikin kula ta kalleta tare da cewa.
"Ni kam Ameena kiyi haƙuri ba gulma bane menene ya rabaki da mijinki na fari wanda kika cemin yayanki ne ɗan baffanki kuma a wurin iyaye shi kika girma".
Wani nannauyan ajiyan zuciya Ameena ta sauƙe tare da maida numfashi,
ganin haka yasa Samira cewa.
"Sorry bawai na matsa bane in san sirrinki,ina son in fahimci wani abune inji ko laifin ya Amir ne".
Kai ta rausayar cikin sanyi tace,
"Akwai kam, akwai laifinshi".
Cikin kula Samira tace.
"Menene laifin nashi?"
Hankalinta ta maida kan tuƙin da takeyi kana ta fara bawa Samira labarin.
"DADY Baban Ya Amir ƙanin babane uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, babanane babba,
Allah ya azurta babana da dukiya da ilima kana da Æ´ara dan mu Æ´aranshi mun kai goba.
Yayinda Dady kuma Allah ya bashi tarin dukiya da ilimi amman É—anshi É—aya ne rak a duniya wato ya Amir É—in,
Mommo matarshi tana masifar sona tun ina ƙarama ita ta roƙi Mamana da Babana aka bata ni,
shine sanadin da yasa na girma a Abuja dan iyayena asalin Æ´an Jada ne.
Ya Amir ya tashi cikin tsananin so da gata shiyasa ya zama sangartacce, kana Ya Amir irin mazananne masu azabar jaraba mace bata isarsu da wuri,
Kuma tun ina ƙarama yake sona sabida Mommonshi ma tace shi tayiwa kamu,
haka kuwa muka taso yana sona nima ina sonshi, to matsalar ya Amir É—an bunsurune baya iya rayuwa saida mace.
Amman ni a lokacin ban saniba hakama Dady bai saniba, amman ita mommo mamanshi ta sani ganin ya tsananta bunsuranci yasa tace, kawai ayi aurenmu in ƙarisa karatuna a gudanshi, ita a nata zaton tunda jarabace kuma mace yakeso to ai in an aura mishi ni zai daina neman mata.
Kuma koda yaji batun aurenmu da iyayenmu suka tayar yaji daÉ—i sosai.
Madadin iyaye ke tsuma amarya tofa shi ya Amir shine ma ke seyo min abubuwan gyara ya kawomin, kuma sosai na dage ina gyara kaina
Alhamdulillah kuwa akayi aure lfy lafiya, muka tare a anan cikin gidan namu side É—inmu nacan nesa dana Dady.
Chapter 105 · 0% Book details