Sashe 111
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
12 dai na rana, Zaleeha na cikin baccinta taji ana jan ƙafarta da sauri ta buɗe idonta.
cikin mmki ta tashi ta zauna ganin ƙawarta Rashida,
cikin jin dadi tace.
"Rashida kece a gidana kai yau naji daÉ—i".
Dariya Rashida tayi tare da cewa.
"Iye amarya Hamma Saif kina hutawanki wannan bacci haka, nayi sallama yafi baki biyar ba amsa".
Musussuka ido tayi tare da fuskarta Rashida data zauna kan bedside cikin, yanayin bacci tace.
"Wallah jiya da dare ban samu isasshen bacci bane, zazzaɓi ne ya rufeni".
Dariya Rashida tare da cewa.
"Ni bance ki gaya min abinda ya hanaki bacci ba".
miƙewa tayi da sauri ta nufi falo da nufin kawowa Rashida ruwa, bin bayanta Rashida tayi,
koda ta ciro goran ruwa a firiji da kuma juice,
tsakiyar falonta suka zauna ita da Rashida,
bayan tasha ruwa suka gaisa cikin sanyi tace.
"Ban san kin dawoba sai shekaran jiya Ya Ishaq ya gaya min, wai ashe tun randa Adda Maryam ta rasu kika dawo.
Nace meyasa bai gaya min da wuriba, sai cemin yayi wai suka sani ko zaki sake guduwa".
Kanta ta sunkuyar cikin sanyi ta kamo hannun Rashida murya a sanyaya tace.
"Kice ma Ya Ishaq bazan sake guduwa ba har gaban abadan sai dai in mutuwace ta gudu dani, kice masa tun a forkonma kaddarar zuwan Ummu Adeel da haifan Adeel ne ya korani da kuma sanadin musuluntar mutun har goma shabiyar.
Kuma da tasirin zugar ƙawa da da kuma ƙarfin ikon uwa.
Dan Allah Rashida ki bawa ya Ishaq haƙuri a bisa mugayen furucina garesu".
Kai Rashida ta girgiza tare da cewa.
"Ya Ishaq ya yafe miki Zaleeha yanzuma tare dashi mukazo, yana side É—in Ummi ne,
yana jiran amininshin ya dawo zasu iso wurinki."
Ido ta zubawa Rashida cikin sanyi tace.
"Rashida kodai da Malam Ishaq za'ayi bikin ne?".
Murmushi Rashida tayi tare da gyaÉ—a mata kai alamar eh.
Wannan abu sosai ya sata jin daÉ—i, nan sukaci gaba da hira cikin hirar ne ta kalli Zaleeha tare da cewa.
"Bilkeesu tazo ko?".
HaÉ—e fuska Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bana buƙatar zuwanta Rashida nayi dana sanin ƙawancena dan Bilkeesu ba ƙawar arziƙi bace".
Sosai Rashida tayi daÉ—in yadda Zaleeha ta sauya ta kuma gane gskyar waye bilkisu, cikin wasa da dariya tace.
"Yau dama lalle nazo inyi miki tunda baki bari an miki lallen aureba yanzu zan miki".
Baki ta ɗan taɓe tare da cewa.
"Kaiyya barni kawai banda lfy mafa".
bata kulataba ta jawo hand bag É—inta ta É—ebo sajan ta fara kiciniyar kwabashi.
A can falon Ummi kuwa sosai take hira da Ishaq yayinda shi kuwa yake ruggume da Adeel,
Ameena kuwa tunda suka gaisa suka ɗan taɓa hira ta koma kitchin ita da Raliya.
Cikin kula Ishaq yacewa Ummi.
"Ummi gobe za'a kawo miki kayan lefen ki ganshi kafin a kaishi".
Fuska cike da mamaki tace.
"Ishaq har an gama haÉ—a lefen bani da labari, haka zakayi min?".
Murmushi yayi cikin sabonsu yace.
"To Ummi ni kaina jiya naga lefen, ni duk a zatona sai next month za'a haÉ—a lefen, kawai jiya Saifuddeen yaje ya shida Aunty kubra suka sai komai suka kai gida ni sai da Umma ce ta kirani take sanarmin".
Sosai Ummi taji daÉ—in halaccin ÆŠan nata,
cikin happy tace.
"A to yayi kyau Allah ya bar muku zumuncinku yara da jikoki".
Amin Amin yace cikin jin daÉ—i dai-dai lokacin kuma Saifuddeen ya shigo nan sukayi ta hira, sosai Ishaq yaso yayi godiyar amma Ummi ta hanashi.
Cikin yadda suka saba mgna yacewa Saifuddeen tarefa suke da Rashida tana side Zaleeha ne,
dariya Saifuddeen yayi kana ya gaya Ummi ai da amaryar sukazo tana É—akin Zaleeha. Ameena da yanzu ta fito tace,
"A a ashe da amaryar ake tafe shine ba'a gaya minba inje in ganta".
Dariya yayi kana yace.
"Uhum kuma yanzuma ta kirani tace in kai mata Adeel love".
Cikin sakin fuska tace.
"A akai matashi, bari in ƙare aiki zanzo mu gaisa".
Kai Saifuddeen ya gyaÉ—a kana suka fita suka nufi sashin Zaleeha.
Koda sukaje, hira suka kama sosai Zaleeha ta saki jiki da Ishaq, cikin kula take ce masa.
"Malam Ishaq ina mutanena? Nayi kewarsu, ina son aikina, amman na rasashi".
Gyara zama yayi tare da cewa.
"Baki rasashiba in mijinki ya yarda, dan har yanzu bawai sun sallameki bane".
Murmushin jin daÉ—i tayi ta É—an kalli Saifuddeen, tura baki yayi alamun karki wani kalleni".
jin sallamar Ameena ne yasa suka juyo gareta,
trayn abincin ta ajiye musu tare da kallon Rashida cikin Æ´ar fara'arta tace.
"Amaryarmu barka da zuwa".
A kunyace Rashida tace.
"Yauwa Ummu Adeel ya Adeel".
"Lafiyar shi lau sai rigima".
Ƴar dariya tayi tare da cewa.
"Zaku bamu shi ai in munyi aur.."
Sai kuma tayi shiru, Ishaq ne yayi murmushi tare da cewa.
"Bari in karasa miki in munyi aure ko".
mayafinya taja ta rufe fuskarta,
cikin dariya Ameena tace.
"Ga Amminshi in ta yarda dai mun baku".
Da sauri Zaleeha tace.
"A a kam ban yarda ba sai dai ki haifo wani ki basu wannan kam is my on".
Dariya suka É—anyi kana Ameena ta ce musu.
"To ga abinci".
Har taje bakin ƙofar fita Zaleeha tace.
"Ngd Ummu Adeel".
Murmushi Ameena tayi tana mmiki yawan godiyan Zaleeha ta lura É—abi'artace ko me akayi mata sai tayi godiya, muryar Zaleeha ta kuma ji tana cewa.
"Yauwa kuma in kin gama aiki Rashida zatazo tayi miki lalle naga kina son lalle".
Cikin jin daɗin dajin ƙaunar Zaleeha tace,
"To ba matsala in ta gama tazo ni na gama sai yamma kuma zan shiga kitchin É—in".
To rashida tace.
Kana suka ci gaba da lallensu shi kuwa Saifuddeen da Ishaq falonshi suka shiga nan suka ci abinci.
Ita kuwa Rashida sosai ta ƙenƙesawa Zaleeha zanen lalle, kana ta miƙe da nufin zataje tayiwa Ameena, cikin kula Zaleeha tace.
"Yauwa Rashida dan Allah kiyi mata mai kyau kar nawa yafi kyau sabida kar taji ba daɗi taga ko kin fifitani danni ƙawarkice".
Cikin fidda numfashi Rashida tace.
"Allah mai iko kai Zaleeha Allah ya bani irin kishinki".
Murmushin kawai ta É—an yi a ranta tace.
Kishin da yake sani inji kamar ba nunfashi a jikina, inba dagewa nake ina dannewa ba ai wata ran sai dai su ganni a sume.
Koda sukaje a falon Ummi aka zanawa Ameena lallen ganin yamma tayine yasa Zaleeha ta shiga kitchin tana goye da Adeel dan yana son kwaɓa lallan Mamanshi.
su kuwa nan suka zana lallensu ita tayi girki da Raliya ma an zana mata a hannu.
Sosai Ummi taji son Rashida a ranta dan ta gane Æ´ar mutuncice.
Ishaq kuwa da Saifuddeen tare suka fita Sai da yamman suka dawo,
Nan Ishaq ya É—auki Rashida suka tafi da direbanshi har gida suka maida ita.
Suna nan falon Ummi gab da magriba Hayatuddeen da Khamis sukazo nan suka ce ya basu woyoyinsu,
Ameenan ya aika É—akinshi yace taje ta kawo mishi, wayar Khamis,
koda taje tayi mmkin canjin gadon data samu,
amman sai ta tuna Ummi tace mata, ya bawa Goggo Dada tsohon gadonshi so sai bata kawo komai a rantaba duk da tajin wani sashi na zuciyarta na raÉ—a mata wani fitinan.
Koda taje wayar Khamis ya karɓar miƙa mishi,
cikin tsoro Hayatuddeen yace..
"Hamma nawa fa".
Fuska a haÉ—e ya mishi alamun bazai bayarba,
ganin haka Khamis yayi sumai-sumai ya tafi shiko autan Ummi ya tura baki kana yana mai jin fargaba dan yasan dole akwai abinda yasa Hammanshi karɓar wayar.
Ganin magriba tayine duk suka watse kowa yayi haramar al'wala.
Bayan sunci abincin dere sun ɗan taɓa hira kamar yadda suka saba, kowa ya nufi makoncinya,
Zaleeha tana zuwa É—akinta wonka tayi ta É—an kimtsa kana ta konta bacci.
Ameena kuwa sosai ta kimtsa da tayiwa daren yau É—in shirin tarban mijinta da kyau.
Hayatuddeen kuwa har ya konta ya fito ya nufi ɗakin Ummi a bakin ƙofa suka haɗu tana ƙoƙarin fitowa zata rufe ƙofarta.
ido ta zuba mishi ganin yadda yaketa zumbura baki cikin haÉ—e fuska tace.
"To uban zumbure-zumbere me hakan?".
Kanshi ya ɗan tonƙoshe cikin sanyi yace.
"Ba Hamma Saifuddeen bane".
A daƙile tace.
"To me yayi maka?".
Cikin son kuka yace.
"Kwace wayata yayi ni Ummi kice masa ya bani wayata".
Fuska ta haɗa sosai cikin faɗa da bai taɓa ganin ta mishiba tace.
"Bazai bayarba, ya kwace kuma ya kwatu! In kanada ƙarfi ka danneshi ka ƙwata! yanzu kai auta in kana da hankali zakayi fushi da duk hukuncin da Hammanka ya yanke a kanka da wani abu na kane!?, anya kuwa kodai zargina dai-dai ne baka da gsky tsiya kake shukawa a woyar to kaji da kyau nice nace ya ƙwace wayarka ya binciki me kakeyi dan na lura ko ƙura'ani baka yawan dubashi kamar yadda kake duba waya, gaba ɗaya alamomin rashin gsky sun baiyana a kanka, bakasan idona dana Hammanka a kanka yakeba, to wlh a hir! ɗinka!! ko bayan raina!!! Saifuddeen shine madadin uba a gareku musamman kai kaɗai kayi mishi gardama a kan komai, domin yayi maka dukkan abinda uba keyiwa ɗansa, shi ya tare maka maraicinka kai baka san maraiciba duk ƙarfin maraicin a kansa ya sauƙa shine Garkuwa ku ko Rahma da take babba a kanshi yana hukuntata yasata abu kuma dole tai ko bata so bare ku ƙannenshi. wuce ka bani wuri".
Sum-sum ya wuce domin ya gano an ramfoshi.
Saifuddeen kuwa, wonka yayi ya kimtsa kana ya nufi side É—in Zaleeha,
koda ya shiga batayi bacciba tana riƙe da wayarta,
hotonshi kuma take yawan zubawa idanu, Allah ya sani akwai wani abu da yake mata gizo a fuskarshi, da tanada dama da fuskarshi ta zahiri zata zubawa ido ko zata samu ta gano abinda take son tunowa, tana ji kamar ta taɓa ganin makamanciyar fuskarshi.
batayi auneba taji yasa hannu ya amshi wayar, tashi zaune tayi ta zuba mishi ido.
Shi kuwa hotonshin ya zubawa ido,
fuskarshi ya nuna mata da Æ´ar yatsarshi alamun gani kalleni a zahiri,
cikin jun kunya ta kauda kanta,
shi kuwa, murmushi yayi dan yana hango wani abu a ƙasan Idanunta hannunta ya kamo yasa mata wayar sannan ya mata saida safe ya juya ya fita.