← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 154

Sashe 44

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe tara dai-dai jirginsu zai tashi.
Baba Malam, Bappa Ali, Dirankadi, Malam Adam, Baba Bello, Ishaq, Ahmad, Wareesu, Saleesu, Hayatuddeen, sune waÆ´anda zasuje É—aurin auren, sai kuma Adda Rahama da Aunty Meena, wanda sune zasu É—auko amarya.
Ƙarfe tara acikin jirgi tayi musu, inda suka ɗaga zuwa garin na Abuja.

Sun isa Abuja ƙarfe goma dai-dai, inda kuma za'a ɗaura auren ƙarfe 11 na rana dai-dai.
Ya Ahmad ne yazo É—aukansu kai tsaye Asokoro gidansu Amarya suka nufa.
Nan suka tarar da ƙofar gidan ɗinke da jama'a, ƴan ɗaurin aure.
Alhaji Naseer da kuma mahaifin Ameena Alhaji Sadam su suka tarbesu cikin mutum tawa, inda su Adda Rahama kuwa suka wuce cikin gidan.

Kamar yanda aka sanya lokaci, ƙarfe sha ɗaya dai-dai jama'an dake wajen suka shaida ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena, akan sadaki naira dubu hamsin.
Nan fa jama'a suka dinga sanya alkahiri, da nema musu zaman lafiya.

Acan cikin gida kuwa, amarya Ameena tayi kyau don an tsantsara mata meckup dai-dai misali, inda ta suturce jikinta da shiga ta al'farma, balaifi tayi kyau don kuwa sam bata da muni, saidai kuma bata da azababben kyau.

Jirgin ƙarfe ɗaya zasu biyo don dawowa Gombe, hakan yasa Dady wato Alhaji Naseer da kuma mahaifinta suka jata gefe inda sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki.
Harma da ɗan guntun ƙwallanta.
Daga haka su Adda Rahama suka kamata, inda aka sanyata a mota, Æ´an uwanta biyu ne zasuyi mata rakiya.
Akwai auntynta wanda ake ƙira da Aunty Zubaida, sai kuma ƙanwar mamanta, Aunty Zainab, nan dai suka ɗunguma dukansu zuwa airport.
Ƙarfe ɗaya kuwa dai-dai jirginsu ya tashi, zuciyar Ameena cike da kewar gida.

Sun iso cikin garin Gombe lafiya, inda lafiyayyun motoci har guda shida suka zo É—aukarsu, Baba Malam dai kaitsaye gidansa aka wuce dashi shida Malam Adam, sai kuma Dirankadi da Ishaq, wanda suma kaitsaye gida suka wuce.

Koda suka ƙaraso, sosai ƴan uwan Ameenan suka yaba da kyaun gidan nasu Saifuddeen, nan dai kaitsaye part ɗin Ummi aka wuce da ita.
Tarba mai kyau Ummi tayi musu, tare da nuna musu ƙauna, haka ta jawo Ameenan jikinta cikin kulawa tayi musu addu'an samun zaman lafiya, da kuma zuri'a ta gari.

Daga nan kuma Adda Rahama tayi musu jagora zuwa ɓangaren Ameenan.
Nan ma sun yaba da tsaruwan part É—in nata.

Kasancewar waƴanda sukai mata rakiyan ba kwana zasuyi ba, ƙarfe 5 na yammaci dai-dai sukabi jirgi inda suka koma Abuja.

Nan fa akabar Amarya Ameena ita kaÉ—ai aÉ—akinta.

Yayinda Æ´an tsirarun mutanen da sukazo bikin, tuni suma sun koma, domin dama Ummi batayi wani gayya ba, Aunty Mina ma tabi Bappa Ali sun koma dukku.
Haka gidan ya rage, daga Ummi, Adda Rahama, sai Raliya da kuma Hayatuddeen.
Shikuwa Saifuddeen tuni dama yana ƙule acikin ɗakinsa.

Koda akayi sallan Isha kuwa, saiga su Ahmad da Ishaq wai sunzo yi masa rakiya zuwa É—akin amarya, abun ma dariya ya basa, nan dai ya haÉ—e gabar da yamma, inda yace.
"Baya buƙatar rakiyan nasu."
Duk yanda sukaso rakasa wajen Amaryar ƙiyawa yayi.
Haka suka tafi suna masa dariya.

Part É—in Ummi ya nufa inda yasamesu zaune su dukansu afalo.
Cikin salon shagwaɓansa, ya dubi Ummin, gane abun dayake nufi yasa tace da Raliya ta ɗauko masa flask ɗin coffe ɗinsa, don dama tuni ta haɗa masa.
Yana amsa kuwa ya juya inda ya nufi part É—insa.
Ta ɓangaren Zaleeha yabi inda yashiga falonsa, kai tsaye ɗaki ya wuce, kayan jikinsa yaɗan rage sannan yasha coffee ɗin, kan gadonsa ya haye tare da rufawa kansa blanket, sam babuma maganar zuwa wajen Ameena acikin ransa, don kuwa ko Zaleeha dayake mutuwar so, ranan farko baije ɗakinta ba balle wata Ameena da yasan jira take ta ganshi ta mishi fyaɗe dan ya dai san abinda take so.

Can ɓangare Ameena kuwa koda tayi sallan isha, komawa tayi ta zauna jigum, kaɗaici ne ya dameta, tun tana zaune harta gaji ta kwanta, take kuwa bacci ya ɗauketa.

Washegari.

Tunda ya fita sallan asuba bai dawo gidan ba, can ya zauna amasallaci inda ya shiga rera karatun alƙur'ani.

Ameena kuwa tana idar da sallah, É—akinta ta kimtsa, sannan ta zura doguwar hijabinta ta fito.
Nanne ta shiga ƙarewa ɓangaren nata kallo.
Ganin wata ƙofa acikin falon nata yasata buɗewa, nan ta tsinci kanta cikin wani haɗaɗɗen falo wanda haɗuwarsa ya zarce misali, ƙamshinsa kaɗai da taji yasa ta fahimci cewa ɗakinsa ne.
Ƙarewa falon kallo tayi sosai, sannan aɗaɗare ta nufi wata ƙofa dake cikin falon, wanda tana kyautata zaton cewa bedroom ne.
Aɗan ɗaɗare tayo knocking, amma shiru ba'a amsa mata ba, tunowa da tayi cewar bazai jita ba koda yana ciki hakan yasa tatura ƙofar ahankali tare da tura kanta ciki, ni'imtaccen ƙamshin daya daki hancinta ne yasata lumshe ido, ƙara kutsawa cikin ɗakin tayi, baki ta buɗe tana ƙarewa aljannar duniyar ɗakinnasa kallo, komai dake cikin ɗakin ya haɗu, ganin baya cikin ɗakinne yasa taɗan sauƙe ajiyar zuciya.
Komai dake cikin É—akin nead, kan gadonne kawai dayake aÉ—an hargitse, cikin nutsuwa ta shiga kimtsa masa gadon nasa, sabon bedsheet ta shumfuÉ—a masa, kana ta sake share É—akin.
Nan ta fesa air freshner'n da ta gani asaman mirror'n É—akin.
Take ɗakin yasake ɗaukan ƙamshi.

Fita tayi daga ɗakin inda kaitsaye ta wuce ɓangaren Ummi don ta gaida ita.
Tana shiga kuwa ta samu Ummin afalo.
Cikin ladabi ta rusuna har ƙasa tagaishe da Ummin, cikin jindaɗi haɗi da ƙaunarta Ummi ta amsa mata, tare da tambayanta ya kwanan baƙunta.
Cikin al'kunya tace.
"Alhamdulillah."
Dai-dai lokacin kuwa saiga Saifuddeen din yashigo wanda dawowansa daga masallaci kenan.
Afakaice Ameena tasaci kallonsa, shikuwa bai kalli inda take bama saima gaishe da Ummi da yayi.
Fuska É—auke da murmushi Ummin ta amsa.
Cikin matsanancin nuna girmamawa Ameena.
Tayi ƙasa da murya aladafce tace dashi.
"Ina, kwana!."

Muskarshi ya ɗan yamutsa tare da taɓe fuska, a hankali ya ɗan ɗago ida nunshi ya kalli fuskarta, kauda kanshi yayi dasauri kana ya...!

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: [8/25, 1:58 PM] A: SpeÉ—É—bl
Ya buÉ—e lips É—inshi a hankali tare da haÉ—esu alamar lfy.
Lumshe idanunta tayi ganin yadda ya motsa jajayen laɓɓansa tabbas tasan zuciyarta tayi kewar ganinsa, sosai taga ya ƙara kyau da kuma cikar haiba, kwarjininsa ya sake bayyana acikin idanunta, don kuwa ga sajen dake kwance akan fuskarsa ya kwanta lub-lub, gwanin ban sha'awa.
Aladaf ce ta miƙe daga durƙuson da take, cikin nutsuwa ta nemi hanyar fita daga cikin falon.
Har zuwa yanzu ko inda take bai kuma kalla ba, Ummi kuwa tana kula dashi sarai.
Ameenan na fita Ummi ta dubeshi da kyau, cikin kulawa da nazartan shi da kyau tace.
"Bazan dai gaji da tuna maka cewar Ameena amana ce agare ka, saboda duk wata matar mutum amanarsa ce, saboda haka kada kace wai don itaɗin ba zaɓinka bace zaka wuƙalanta-ta."

Ɗan ɓata fuska yayi tare da shagwaɓewa, kana ya gyaɗa kanshi alamu to ƙoƙarin ƙarasawa dinning area ya somayi, duban tsab Ummi tayi masa, cikin kulawa tace.
"Ina kuma zaka? ai dai mungama yin break fast da kai, kana da mata saboda haka nasa Raliya ta sa muku abincinku daban a food flask ta kai maka kaje can kaci abincin da matarka."

Kasancewar yana kallon fuskar Ummin tasa, hakan yasa shi fahimtar me take cewa.
Shagwaɓe fuska yayi, tare da ɗan waro idanunsa waje.
Sam bai tsammaci haka ba, haƙiƙa yafara tunanin cewa. Aurensa da Ameena zaisa su Ummi su ɗauke duk wani tallafin da suke basa.

Kamar wani ƙaramin yaro haka ya ɗan tura baki.
Dai-dai lokacin Raliya tafito daga cikin kitchine hannunta É—auke da babban food flask É—in da abincin nasu ke ciki.

Dubanta Ummi tayi tare da ƙwalawa Hayatuddeen ƙira, cikin mintuna kaɗan Hayatuddeen ya fito daga cikin ɗakinsa.
Kulan Ummi tace da Raliya ta basa, yakai can ɓangaren Ameena'n.
Hakan kuwa akayi inda Hayatuddeen ya karɓi kulan ya fita.
Ganin da gaske suke, yasa Saifuddeen ɓata fuska, ganin yanda Ummin nasa ta tsaresa da ido ya sa shi tura kekensa, kai tsaye ya nufi hanyar barin falon.

Ameena kuwa tana barin part ɗin Ummi kai tsaye part ɗinsu ta dawo, anan cikin falonta ta zauna, inda ta kunna babban tv plasma ɗin dake cikin falon, ɗan lumshe idanunta tayi, tare da sauƙe ajiyar zuciya, har zuwa yanzu tana mamaki, wai ita Ameena ce ke zaune cikin gidan su Saifuddeen kuma take amsa sunan matarsa tabbas wanda ya mance Allah ya wahala.

Hayatuddeen ne ya shigo cikin falon bakinsa É—auke da sallama.

Fuska cike da murmushi Ameeena'n ta amsa masa.
Ƙarasowa cikin falon yayi, tare da aje mata haɗaɗɗiyar kulan dake hannunsa agabanta.
Cikin kulawa yace.
"Matar Hamma na ina kwana."
Hararan wasa ta watsa masa, tare da cewa.
"Yau kuma da wani salon ka ɓullo."

ÆŠan dariya yayi tare da kama waist É—insa, cikin salon tsokana irin nasa yace.
"Eh mana, nasan ae yanzu haka daɗi kikeji kin auri min Hammana ko, shiyasa ae na faɗa miki hakan, don ki ƙara jin daɗi da kyau."

Murmushi tayi tare da cewa.

"Nidai zan so ganin ranar da zaka zamo very gentle man Hayatu."

Idanu Hayatuddeen ya É—an zaro, cikin sangarta yace.
"Hayatu? nine ma Hayatu, gaskiya banson Hayatu, ae da Hamma ne bazaki ce masa Saifu ba."

Dariya sosai Ameena tayi, don dama ta faÉ—i hakanne don kawai taga rigiman Hayatuddeen É—in, sosai sakalci da kuma sangartansa na auta ke burgute.

Cikin zunɓura baki Hayatuddeen yace.
"Dama hira nazo tayaki tunda kuwa kika ƙirani da Hayatu na fasa."

Cikin dariya tace.
"To menene sunanka idan ba Hayatu ba? dan ma banƙiraka da Hayatutu ba."
Jin haka yasa Hayatuddeen ƙulewa, bakinsa ya turo gaba, cikin halayensa na auta, yace.
"Keda Hamma na."
Daga haka yafice daga cikin falon.
Murmushi Ameena tayi tare da girgiza kanta, sosai takejin dadin hira da Hayatuddeen din.

Duban kulan daya kawo tayi, tare da buÉ—ewa.
Kasancewar kula ce irin me hawa huɗun nan, hakan yasa ko wanni ɓangare da kalan abincin dake cikinsa.
Ganin abincin nada yawa ne hakan yasa ta tabbatar da cewa, bana ta ita kaɗai bane, jitayi zuciyarta tayi mata sanyi domin koba komai zasu keɓe waje guda dashi.
Komawa tayi ta zauna tana me jiran shigowansa.
Chapter 44 · 0% Book details