← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 154

Sashe 74

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kanta ta É—an jinjina cikin muryarta dake rawa tace.
"To Ummi, amma kullum zuciyata ƙara karyewa take, gani nake kaman Baba Malam bazai taɓa yafe min ba, tsoro nakeji Ummi, idan na mutu Baba Malam na fushi dani, samun aljanna zaiyi min wahala, kuma kowa nace ya roƙamin Baba Malam sai yaƙi, har Daddy (Malam Adam) shima nace ya bawa Baba Malam haƙuri, amma yace shi babu ruwansa, shima fushi yake dani."
Ɗan jim tayi tare da sakin sheshsheƙa, asanyaye tace. "Zakariyya yace duk wanda na ɗauko dan yabawa Baba Malam haƙuri, bazai haƙura ba, har saidai in Hamma Saif ne ya rakani.
Dan Allah Ummi ki roƙamin Hamma Saif ya yafemin, ya rakani mu bawa Baba Malam hakuri, idan Baba Malam baiyafemin ba, nasani haske bazai taɓa ziyartan rayuwata ba ." Taƙare maganar cikin yanayin ban tausayi, ga kuma hawayen da gaba ɗaya suka gama jiƙa mata fuska.
Hannayen Zaleehan Ummi ta kamo cikin yanayin kulawa haÉ—i da tausayawa tace.
"To kidaina kuka, insha Allah zan faɗa masa, kuma nasan zai yafe miki, sannan kuma zai rakaki kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, ki tsaida kukan haka kinji."
Ummi ta faÉ—i maganar cikin lallashi. kanta ta jinjina, saboda ta É—anji sanyi aranta. Jan jikinta tayi ta zauna anan kusa da Ummin.

Ahankali ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, dan alokacinne dawowarsa daga masallaci, kusan atare suka ɗago kansu suka kalleshi, hakanne yasa idanunsu faɗawa cikin na juna, lokaci guda ya kawar da duk wata annuri dake kan fuskarsa, itama asanyaye ta yi ƙasa da kanta, cikin haɗe fuska ya ƙaraso cikin ɗakin, dan ma Ummi ta riga da ta ganshi ne, da ace bata gansa ba babu abun dazai hanashi komawa inda ya fito.
Ƙarasowa kusa da Ummin nasa yayi, haɗe hannayensa biyu yayi, kana cikin body language ɗinsa ya gaida
ta.
Amsa masa gaisuwar Ummi tayi tana É—an sakin murmushi.
Asanyaye Zaleeha ta ɗago kanta, cikin wata irin murya me ɗauke da sarƙewa, akaron farko kenan na tarihin rayuwarta da zata fara gaida shi, cikin sheshsheƙan kukan daya taso mata tace.
"Ina kwana." kasancewar yana iya kallonta ta gefen idanunsa ne,yasashi fahimtar abunda tace, amma sai ya share yayi kamar baigani ba, saima sake haɗe fuskarsa da yayi, tare da ƙoƙarin soma ciro wayarsa, daga aljihun rigarsa. Ganin hakane yasa Ummi sa hannu taɗan taɓashi, ɗago da kansa yayi ya kalli Ummi'n.
Da idanu tayi masa nuni da Zaleeha kana tace. "Bakaga Zaleeha na gaisheka bane."
Ai tunma kafun Ummi ta gama rufe bakinta, yasake maida kansa ƙasa, dan bama yaso ya fahimci abunda Ummin ke ƙoƙarin faɗa, ahankali ya tura wheelchair ɗinsa, ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ko inda Zaleehan take bai kuma kallo ba. Baki buɗe Ummi ke kallonsa har ya fice daga cikin ɗakin, kanta kawai ta girgiza, tare da sakin ɓoyayyen murmushi, sarai tasan gano ƙasan zuciyarsa cewa wannan fushin nasa da yakeyi da Zaleehan hukunta yakeyi har cikin zuciyarsa, kuma yanayi ne dan ya gwada mata ɓacin ransa, akan abun da ta aikata, sannan kuma ya nuna mata kurenta ta kuma sani shima mutunne kamar kowa yanada zuciya kuma zai hukuntata muddin ta ɓata mishi.
sanin irin zazzafar soyayyar da Saifuddeen ɗin keyiwa Zaleeha yasa Ummi sanin cewa bazai taɓa iyayin haƙiƙanin barranta da ita ba.
Itakuwa Zaleeha asanyaye ta miƙe, cikin sanyin da ayanzu ya zama tamkar ɗabi'arta tace.
"Ummi ina Raleeya, da Hayatuddeen."
É—an murmushi Ummi tayi tare da cewa. "Raleeya na kitchine, Hayatuddeen kuma kinsan yau weekend yanacan yana baccin nasa da baya gajiya dashi."
Kanta taÉ—an jinjina, sannan tace.
"To bari inje kitchin É—in in taya Raliya aikin".
Da sauri Ummi tace.
"A a jeki kwanta". Zata kuma yin mgna Ummi tace.
"Nace kije ki konta ki huta".
ganin yadda Ummi tayi mgnar cikin bada umarnine yasata cewa.
"To Ummi bari naje na É—an kwanta."
Kai Ummi ta jinjina mata, saboda duk wani koke koken da tayi adaren jiya, Ummin najinta, hakanne ma yasa tasan cewa Zaleehan bata wani samu ishashshen bacci ba. Tana fitowa daga ɗakin Ummin kuwa, sukai karo da Hayatuddeen wanda da dukkan alama yanzu tashinsa, dan sai hamma yake ta zubawa tare da miƙa.
Ganin Zaleehan yasashi sakin murmushi, ƙarasowa yayi tare da kamo hannunta, cikin kulawa yace.
"Good morning my beautyful Aunty, ya jikin naki?"
Kanta taɗan jinjina masa alaman da sauƙi, idanunta ne suka sauƙa akan Saifuddeen wanda ke zaune akan kekensa ya basu baya, yana ta faman aikin danna wayarsa, saurin ɗauke idanunta daga kansa tayi, tare dayin ƙasa da kanta.
Dai-dai lokacin Raleeya ta fito daga cikin kitchine, gaisawa sukayi cikin kulawa kuwa Raleeya ke tambayarta jikinta, nan tace mata da sauƙi. Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zaleehan, tare da zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun falon, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha dan Allah minti biyu, ki jirani anan ina zuwa."
kai ta jinjina masa tare da sadda idanunta ƙasa tana wasa da ƴan yatsun hannunta.
Ameena ce ta buɗe ƙofar falon ta shigo bakinta ɗauke da sallama, shirye take tsab acikin kayan aikinta, ga kuma kekyawan ɗanta Adeel da ke riƙe ahanunta, shigowarta falon kuwa yayi dai-dai da fitowan Ummi daga ɗaki.
Jin ƙamshin turaren Ameenan ne ya sashi ɗago kansa ya kalleta.
ƙarasowa cikin falon tayi, da ganin Zaleeha kuwa sai taji gaba ɗaya ranta yayi ƙunci, ɗan durƙusawa tayi, aladabce ta gaishe da Ummi', fuska ɗauke da fara'a da kulawa Ummi ta amsa tare da miƙa hannu ta karɓi Adeel dake ta yi mata dariya irin tasu ta yara.
ÆŠago kai Zaleeha tayi, karab kuwa suka haÉ—a idanu da Ameena'n, kasancewar dama idanun Ameena'n akanta suke, ta tsareta da idanu kamar ta samu tv. Cikin sanyi Zaleehan ta janye idanunta, tare da cewa Ameena'n'.
"Ina kwana." zazzaƙan muryar Zaleehan da Ameena taji shiya sanya bugun zuciyarta tsananta, wanda har yasa ta kusa daburcewa, cikin in ina ta amsa da "La fi..ya." dan zata iya rantsewa cewa bata taɓa jin murya me daɗin a zahiri irin ta Zaleehan ba.
Kallon Adeel dake hannun Ummi Zaleeha tayi, cikin sa'a kuwa yaron shima kallonta yake, murmushi tayi masa sai kawai ya buɗe baki yana mata dariya, wani irin kyau yaron yayi mata, musamman ma yanda dimples ɗinsa suka lotsa da yana dariyan, lokaci guda taji ya shiga ranta, hakan yasa ta miƙa hannu dan ta ɗaukeshi, babu ƙiwa kuwa yazo wajenta, karɓansa tayi tana sakin sassanyan murmushi. Ummi ne itama tayi murmushi cikin kulawa tace.
"Lallai Adeel yaga ɗiyarsa, tunda dai baiyi mata ƙiwa ba." Kallonta Zaleehan tayi da ɗan mamaki, kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ai me sunan Baba Malam ne."
Wani irin farinciki ne ya cika zuciyar Zaleehan, sai kawai ta rungume yaron ajikinta tanajin sonsa sosai aranta haka nan sai takeji kamar itace ta haifeshi in ba gizo idonta ke mata sai takega kamar yaron yana kama da ita, musamman dimples É—insa irin nata ne sak.
Dai-dai nan Hayatuddeen ya fito daga kitchine hannunsa ɗauke da cup, wanda aka zuba yoghurt acikinsa, akusa da Zaleehan ya zauna tare da miƙa mata yoghurt ɗin, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha amsa kisha, al'ƙawari nayiwa Zakariyya cewar yau sai nasa kinci abinci, saboda haka dan Allah kisha kafun agama break fast." ɗan marairaice fuska tayi, sai dai kuma ita kanta tasan cewa tana matsanancin jin yunwa, hakanne ma yasa ta amsa, tare da ɗan sha kaɗan, kan Adeel da har yanzu ke kan cinyarta take shafawa, sosai yaron ya shiga ranta tana jin sonshi da ƙaunarshi har cikin ranta.
Duk wannan wainar da ake toyawa Ameena idanu kawai ta zuba musu, itakam Allah yasani bata gajiya da kallon Zaleeha, to itama da take mace, bata gajiya da kallonta, inaga kuma Namiji haka yasa kishinta kuma ninkuwa a ranta.
Hayatuddeen ne ya É—ago kansa ya dubi Ameena'n, murmushi yaÉ—an saki cikin kulawa da girmamawa ya fuskanceta tare da cewa. "Aunty Ameena ina kwana."
itama murmushi'n ta mayar masa tare da cewa.
"Lafiya Auntan Ummi, ya rigima." murmushi kawai yayi, batare da yace mata komai ba, ya maida hankalinsa wajen Zaleeha tare da kissing goshin Adeel dake kan cinyar Zaleeha, wanda da dane kuma ta tabbatar tsayawa zaiyi yayita mata rigima, amma yanzu gaba É—aya hankalinsa naga Zaleeha.
Hakanne yasa asanyaye ta juyar da kanta ɓangaren Saifuddeen, ai kuwa idanunsu ne ya haɗe, dan dama kallonta ya keyi, murmushi ta sakar masa, domin tuni haushin nasa da takeji ya gushe, ayanda take matsanancin sonsa batajin zata iya dogon fushi dashi bare ta ɓata rawanta da tsalle, shiɗin ma murmushi yayi mata tare da miƙa mata hannunsa, ganin Idanun su Ummi baya kansu yasa ta kama hannun nasa, gamamakinta sai gani tayi yajawota dab dashi, har jikinsu na gogan na juna, kasancewar jiyan ba'a ɗaki ɗaya suka kwana ba, hakan yasa bata gaishesa ba sai yanzun, ahankali tace.
"Ina kwana." Kansa ya jinjina mata alaman lafiya, sannan ya tallafo haɓarta, kiss ya ɗaura mata akan kumatunta da kuma bakinta, baruwansa da wani jin kunya wai dan su Ummi na falon bare yasan idon Ummi baya kansu.
Gaba ɗayansu sunga abun da Saifuddeen din yayiwa Ameena hakan ne yasa suka janye idanunsu gefe, Zaleeha ma da tsautsayi yasa ta ɗago, idanunta sun gane mata abun da ya faru, kawar da kanta gefe tayi, tare da ƙara manne Adeel ajikinta, ko ajikinta itakam, bata ma ji wani abu adangane dasu ba, saidai zuciyarta ta tsegunta mata cewa. "Halan Ameenan matarsa ce kenan." Ummi kuwa, tashi tayi gaba ɗaya ma tabar falon, dan ta gano cewa wannan sabuwar kulawan da Saifuddeen ɗin ya fara bawa Ameena agabansu wani salone, kawai yayi ne saboda wata manufarsa ta daban. Ameena kuwa da gangan ta kamo lips ɗinsa itama ta tsotsa, cikin sanyin murya tace. " I will miss you dear" sake manna masa wani kiss ɗin tayi, sannan ta ɗan janye daga jikinsa, Hayatuddeen kuwa baki ya sake yana kallon ikon Allah,
Zaleeha kuwa sam bata ƙara ɗago kanta bama sai wasa takeyiwa Adeel wanda da ka gani kasan tana jin son yaron har cikin ranta.
Ƙarasowa inda suke Ameenan tayi, tare da sanya hannu ta ɗauki Adeel, tana sakin murmushi me ɗauke da ma'anoni kala kala, haka ta saɓa Adeel akafaɗanta ta fice daga cikin falon, wani irin farinciki takeji acikin ranta, wannan kiss ɗin da Saifuddeen yayi mata agaban Zaleeha ji take kaman kyautar zuciyarsa ya bata a gaban Zaleeha ji takeyi ya gama mata komai dan ko ba komai ya nunawa Zaleeha itama matarsa ce kuma yana sonta murmushi kawai take tayi.
Chapter 74 · 0% Book details