← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 154

Sashe 129

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Babu musu kuwa Adda Rahama da Ameena suka koma falo.
Duba Zaleehan tayi, sosai, ganin babu rauni sosai aƙasan nata yasa ta bata wasu magunguna tasha, wata alluran kashe zafi da zogi tayi mata, sannan ta ɗaura mata drip tare dasa alluran zazzaɓi.
Cikin abun da baiwuce 10 minute ba bacci ya É—auki Zaleeha.
Dr Fateema na fitowa daga É—akin su Ameena suka nufota cikin sauri. Ameena ce tace.
"Dr Yajikin nata?." ÆŠan murmushi Dr Fateema'n tayi, tare da cewa.
"Ku kwantar da hankalinku, jikinta da sauƙi, dan harma ta samu bacci, kuma bawani babban damuwa bane, kunsan dama yawanci irin haka yana faruwa idan akayi dis virgin ɗin mace, mussamman idan ya zamana namijin yaje mata da ƙarfi, ko kuma manhood ɗinsa ya zamana, yafi ƙarfin privet part ɗinta, wanda sai ahankali ne kuma zata saba, thank god ma babu rauni sosai ajikinta, yanzu dai tana da buƙatar hutu, so please abarta taɗan huta." Jinjina kai sukayi su dukansu cike da gamsuwa,
Ameena kuwa ido ta rumtse jin hawayen kishi zasu zubo mata a ranta tace.
"Ashe da kam duk kishin banza nakeyi nagodewa Allah dayasa bai kusanceta tun ina kan jahilin kishin nanba na sani da mutuwa zanyi. Har waje kuwa Ameena ta raka Doctor É—in.
Saida taga tafiyarta sannan ta dawo gida tana tafe tana mgnar zuciya da share hawaye.
"Ai kam dole taji azaba dan Abban Adeel ingarman namiji ne".

Ganin Zaleehan na bacci, yasa Adda Rahama jawo ƙofan ɗakin ta rufe, sukuma suka koma sashin Ummi.

Suna zuwa kuwa suka samu Raleeya ta kammala breakfast, da ƙyar Adda Rahama tasa Saifuddeen ya ɗanci wani abu acikinsa, dan yace musu ji yake bayansa na harbawa. Ɓangaren Zakariyya kuwa suna gama waya da Hayatuddeen, cikin gida ya wuce, anan falon Baba Malam yasamu Mama da kuma Mamy, harma da Ya Ahmad, anan yake sanar musu cewa, jikin Saifuddeen ɗin ya tashi.
Sosai Baba Malam ya shiga damuwa, nan yace su Mama su shirya idan akayi sallan azahar zasuje su dubashi.

Ameena ma ta kira Daddy ta sanar mishi batun jikin Saifuddeen kuma yace yana nan tafe gobe,
hakama ta kira Mamanta ta sanar mata, inda ta haÉ—ata da Ummi suka gaisa, ta jajanta mata jikin Hamma Saif É—in kana tace suma in Allah ya nufa gobe zasu taho.

Kusan atare motocin Su Wareesu dana Ishaq Salisu suka shigo cikin gidan.
Dan dukansu Ahmad ya ƙira ya sanar musu. Koda suka shiga cikin gidan, Raleeya ce tayi musu jagora zuwa ɗakin Hayatuddeen ɗin.
Lokacin da sukaji muryan Saifuddeen wanda ganinsu ne ya sashi buɗe muryarshi ya amsa Salllamarsu da ƙarfi yadda duk zasuji muryarshi ai kuwa dukansu babu wanda bai ji muryar tashiba.
Hannu yasa ya kamo hannun Ishaq dake ƙoƙarin kamo nashi cikin tsanyi yace.
"My Ishaq gani nan kusa da kai".
Wani irin riƙo Ishaq yayiwa hannun Saifuddeen cikin tsananin farin ciki yace.
"Allahu akbar Allah mai iko da girman buwaya. Buwayi gagara misali Alhamdulillah ko yanzu na mutu Allah ya cika min burina laruran Aminina sun ragu".
Wani irin raunine ya baiyana a fuskar Saifuddeen murya na rawa yace.
"Ni kuwa ina roƙon Allah ya aramin rai da lfy, ya nuna min lafiyarka inga kaima kana gani da idanunka".
Kusan a tare Ahmad da Salisu ds Mudassir da Warisu sukace.
"In sha Allah, shima Allah zai bashi lfy".
Salisu kuwa tuni hawaye sun wonke mishi ido sai yake tuno irin gogormoya da suka sha shida Saifuddeen a cikin bulayin neman halal ɗinsu a lokacin badon ƙarfin imaniba sai su kauce hanya, sabida tsananin uƙubar talauci da wahalar rayuwa
hannu Saifuddeen yasa yana share masa hawayenshi, shi kuwa sai maimaita kalmar Alhamdulillah yake tayi.
Warisu kuwa murmushi yayi tare da cewa.
"Ya Allah ka nuna mana randa zaka tsaya da kafafunka kamar yadda ya jiyar damu mgna da muryarka".
Amin Amin yace kana ya kalli Salisu tare da cewa.
"Haba Salisu godewa Allah zamuyi ba kuka ba".
Cikin sauri duk suka rinƙa maimaita Alhamdulillah,
Ahmad ne yayi dariya tare da cewa.
"Daga dare ɗaya Zaleeha tayi sanadin dawo mana da bakinshi da kunnenshi, a dare na biyu kuma ƙugu kam zai ida ɓalgawacewa in mutun bai jira kanshi ba".
Dariya sukayi baki ɗaya dan sun gano kurman baƙin da Ahmad ya musu,
shi kuwa Saifuddeen mare ƙeyan Ahmad yayi,
lokaci ɗaya kuma ya riƙe hannun Ishaq da karfi dan sarawar da yaji ƙugunshi nayi cikin dakiya yace.
"To mugaye masu cewa Allah yasa ƙuguna ya ida ɓalgacewa, kunji daɗinku ya ɓalgace ɗin".
Dariya sukayi baki É—ayansu.
Ganin alamun yana cikin ciwo ne yasa suka sarara mishi suka koma falo.

Kafun sallan Azahar tuni gidansu Saifuddeen ɗin ya cika da jama'a, ƴan uwa da abokan arziki da maƙota, harma dasu Bappa Ali da suka samu isowa, acikin gidan fuskar kowa ka kalla zaka ganta ɗauke da zallan farinciki, da kuma jindaɗi.

Kusan ƙarfe 3 na yamma, su Baba Malam suka samu isowa gidan. Tarba me kyau Ummi tayi musu, inda Baba Malam yashiga har ɗakin Hayatuddeen ya gaishe da Saifuddeen ɗin. Mama ma haka ta gaishesa tana ta faman sunne kai, dan kunyansa takeji.
Ahamad ne yaja Baba Malam gefe ya sanar dashi buÉ—ewan kunnen Saifuddeen.
Sosai Baba Malam yaji daɗi, sam baiga laifin Saifuddeen ɗin ba kuma da yace a ɓoyewa Zaleeha hakan, dan yasa komai Saifuddeen yana yinsane cikin hikima da kuma dalili tabbas yasan yanada dalilin da yasa yace a ɓoye matan.

Jin cewar Zaleeha na kwance bata da lafiya, yasa Mamy zuwa ta dubata, Mama kam da Baba Malam basuje ba, saboda abun akwai nauyi sosai.

Har zuwa tafiyansu kuwa Zaleeha bacci take batasan ma da zuwansu ba.

Haka gidan nasu ya cigaba da amsan baƙi har kusan dare.
Sai Bayan sallan la'asar Zaleeha ta farka daga nannauyan baccin da take.
Dai-dai lokacin kuwa Adda Rahma da Raleeya suka shigo, da taimakonsu tayi wanka, dan taÉ—anji dama daman jikinta, sai-dai tafiyan natane har yanzu bai dawo dai-dai ba.
Da taimakon Adda Rahama ta koma É—akinta, sallan Azahar da la'asar tayi.sanna Ta kwanta.

Ƙarfe biyar dai-dai Dr Aleeyu yaso daga Abuja kai tsaye gidan su Saifuddeen ɗin ya Adnan ya kawoshi, ya dubashi yayi da kyau kana yayiwa Saifuddeen allurai da kuma magunguna, ba laifi kuma yaɗanji sauƙi.

Bayan sallan isha ne Ya Ahmad da Aunty Lubna suka zo suma dan dubashi da jiki
Chapter 129 · 0% Book details