Sashe 88
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Washe gari.
kamar yanda ta faÉ—a jiya, yau awajen Zaleeha tabar Adeel, bayan ta aje madara da duk kuma wani abun daya kamata da za'a bashi.
Sosai Zaleeha taji daɗin barin Adeel ɗin awajenta, haka ta saɓasa akafaɗanta tanayi masa wasa, cikin ikon Allah kuwa ko kuka baiyi ba. Da rana ne kuwa Hayatuddeen yaje ya kwaso su Zakariyya, Isma'il, Imran, Sulaiman, Zaleeha taji daɗin zuwansu ƙwarai, nan falon Ummi suka baje, haka suka kafe kai da fata wai dole ita zata shiga kitchine tayi musu ferfesu, acewarsu wajenta suka zo ba wajen Ummi ko Adda Raleeya ba, haka dole ta sauƙe Adeel ta shiga kitchine ɗin, cikin ƴan mintuna ƙalilan kuwa ta dafa musu indomie, da kuma ferfesun naman kaji, nan tsakiyan falon suka zauna su kaci, gaba ɗaya surutunsu ya cika gidan, haka sukayi wa Ummi kaca-kaca da falo. Sunjima sosai agidan dan sai wajen bayan sallan la'asar kafun suka tafi.
Ameena kuwa yau ƙarfe 5 ta dawo, koda ta dawo kuwa bata karɓi Adeel ba, yana nan awajen Zaleeha, saima da akayi sallan magriba ne ta karɓeshi ta bashi nono.
*Bayan Kwana É—aya*
Sannu ahankali haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda acikin kwanaki biyun nan kullum sai Ameena tabarwa Zaleeha Adeel, awajenta yake wuni harta dawo daga wajen aiki. Hakanne yasanya shaƙuwa me ƙarfi ta shiga tsakanin Adeel ɗin da kuma Zaleeha tana jin yaron har cikin ranta.
Saifuddeen ne zaune kan wheelchair ɗinsa, wayarsa ya jawo sannan ya turawa Raleeya, text akan taƙira Hayatuddeen suzo tare yana son ganinsu, kasancewar yau Hayatuddeen ɗin baida lecture'n safe shiyasa baije school ba.
Suna shigowa cikin part ɗin nasa ya miƙowa Hayatuddeen key tare da cewa.
"Karɓi key ɗin part ɗin Zaleeha ne."
cikin yanayin zumuɗi Hayatuddeen yace. "Nakai mata." Hararansa Saifuddeen ɗin yayi, cikin body language ɗinsa yace. "To sarkin azarɓaɓi bahaka nakeson cewa ba."
Ɗan zumɓura baki Hayatuddeen ɗin yayi, cikin shagwaɓa yace.
"To me za ayi dashi."
Duban Raleeya Saifuddeen É—in yayi, cikin body language É—insa yayi mata alaman cewa.
"Su shiga ɓangaren Zaleehan, suɗanyi share share."
Murmushi Raleeyan tayi, har acikin ranta taji daɗi, saboda hakan alama ne dake nuna cewa Zaleehan ta kusa dawowa ɓangarenta, jan hannun Hayatuddeen tayi suka wuce sashin Zaleehan, shikuwa Saifuddeen laptop ɗinsa ya ɗauka ya cigaba da aikinsa.
Raleeya da Hayatuddeen kuwa suna shiga sashin Zaleehan, suka soma ƴan share share da goge goge, kafun awa biyu tuni sun tsab tace ko ina sun gyara komai, haka falon yadawo sabo fil sai sheƙi yake, inda suka fesa turaren air feshener,
suna tsaka da aikin ne Ahmad ya ƙira Raleeya dan tun ɗazu ya dawo baiganta ba, ya kuma sauƙo har ƙasa bai ganta ba.
Nan take sanar masa cewa tana ɓangaren Zaleeha Hamma Saifuddeen yaɗan sasu suyi mata share-share da gyare-gyare.
Ƙwafa Ahmad yayi tare da cewa.
"Lalle ma Saifuddeen so yake ya maidamin da mata baiwa ko? yarasa wazai sa yayiwa Zaleehan share-share sai ke, zanyi maganinsa ne badai yayi mata biyu ba yaseen zamu ƙaura." Dariya Raleeya tayi sannan ta kashe wayan, nan dai suka kammala komai suka fice daga sashin.
Washe gari ne Goggo Dada taturowa Saifuddeen saƙon godiya, da kuma fatan al'khairi kala-kala, dan sosai taji daɗin kyautar nasa.
Nan yake ce mata. "Bakomai, Goggo Dada ai kema uwace agareni kuma uba".
ananne ma yake ce mata.
"Lafiya ko batazo tayi ta'aziyyan rasuwar Adda Maryam ba".
cewa tayi.
"Itama tana tason zuwa to amma Allah ne baiyi ba."
take kuwa yace washe gari zai turo sule driver ya É—aukota, haka dai tayi ta masa godiya, daga nan sukayi sallama . Murmushi yayi bayan ya aje wayar, cikin zuciyarsa yace.
"Awannan karon Goggo Dada dake zanyi amfani wajen dawo da Zaleeha ɗakinta, tun alokacin da Ummi ta bini akan na bada key ɗin ɗakinta ban nemeshiba, yanzu kuwa dana ga key ɗin bani da wani ƙarfin guiwan da zan iya tunkaran Ummi nace mata ga key ɗin ɗakin Zaleeha, amma yanzu tunda dai zakizo nasan lokacin dawowan Zaleeha ɗakinta yayi, zanyi komai asauƙaƙe tayanda Ummi bazata zargeni ba."
Haka dai yayita saƙawa da kuncewa, sosai ƙudurinsa ke ƙara ƙarfafa acikin zuciyarsa.
Kaman yanda ya faÉ—a kuwa washe gari yasa Sule driver yaje har Dukku ya É—auko Goggo Dada'n, Raleeya ne ta rakata gidan su Zaleehan tayi musu ta'azziyya, daga nan kuma suka dawo gida.
Yauma kamar kullum Zaleehan ne tayi musu girkin abincin dare, kusan atare sukaci abincin, koda suka kammala cin abincin, nan cikin falon ta koma ta zauna akan sofa tare da tanƙwashe ƙafafunta, sama sama take ɗan kallon tv, ahaka taɗan jingina kanta da jikin kujeran falon, bacci takeji sosai, saidai sanin cewa Goggo Dada na cikin ɗakin nata yasa bata shiga ta kwanta ba, saboda kallon suruka takewa Goggo Dada'n.