Sashe 119
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ahankali ya buɗe ƙofar toilet ɗin yafito, sanye yake da white bathrobe, yayinda gaba ɗaya jikinsa ke ɗauke da danshin ruwa, da dukkan alama wanka yayi, ɗan tsayawa yayi, yana kallon ta fuskarsa cike da mamakin ganinta acikin ɗakinsa a ransa yace.
"Uhum yarinya kin kawo kanki".
Ita kuwa Zaleeha jin kaman motsin mutum abayanta, yasa tayi saurin juyowa, idanunsu ne suka sarƙe acikin na juna, da sauri taɗan ja da baya, tare da turo bakinta gaba, idanunsa ya ƙura mata, tare dayi mata alama kan in boddy language cewa.
"Wayace kishigo min É—akinna?."
sake turo baki gaba tayi, ashagwaɓe tace.
"To ni ba Ummi bace, tace na kawo maka coffee."
tsumammun idanunsa yaɗan lumshe, tare da sakin wani irin killer smile, ahankali yaɗan soma turo kekensa zuwa gareta, ganin haka yasa da sauri ta ajiye tray ɗin, tare da juyawa ta nufi hanyar barin ɗaƙin, cikin azama ya rigata ƙarasawa bakin ƙofar ɗakin ganin guduwa takeda niyar yi, hannu ta ɗaura akan handle din ƙofar, dai-dai lokacin shikuwa ya sanya hannunsa ya kare ƙofar, ta yanda bazata iya buɗewa ba.
Idanu taÉ—an zaro waje cikin mamaki tace.
"To miye haka, nidai ka matsamin nafita, ai dama coffee akace na kawo maka, to kuma baga can coffee É—in na ajiye maka ba."
tafaɗi maganar tana kakkarya ƴan yatsun hannunta tare da sunkuyar da kanta. Rikitattun idanunsa ya watsa mata, wanda har saida taji, tsikar jikinta sun mimmiƙe.
ÆŠan rolling idanunsa yayi, tare dayi mata alaman cewa.
"Ai tunda kika shigo ba zaki fita ba."
Idanunta ta zaro, tare da ɗan murguɗa masa ƙaramin bakinta, asakalce tace.
"Dan Allah nidai kabarni na fita kaji."
ɗan karyar da wuyansa yayi, tare da girgiza mata kai, alaman yaƙi ɗin.
Hannunsa yasa inda ya murzawa ƙofar key, tare da zare key ɗin yasa a aljihunsa, ganin haka yasa ta kwaɓe fuska, take idanunta sukayi rau-rau dasu.
Ɗan janye jikinsa baya yayi, tare da ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinsa, cikin nutsuwa ya ɗauko body lotion ɗinsa yana shafawa. Idanu ta zuba masa, sai faman tattaune lips dinta take, zuciyarta kuwa duka yake da ƙarfi, ganin cewa yama manta da ita, hidimansa kawai yakeyi, yasa ta ƙaraso har gabansa, ahankali ta shiga ɗan bubbuga ƙafanta, asakalce tace. "Dan Allah ni dai kabuɗemin ƙofa na fita, bacci nakeji."
ÆŠago idanunsa yayi ya kalleta, tare dayi mata nuni da gadonsa alaman ga gado nan ta kwanta. Fari tayi da idanunta, tare da cewa.
"Nidai bazan kwanta akan wannan gadon ba, ai nima ina da nawa, nidai ka buÉ—emin naje na kwanta a É—akina."
Murmushin gefen baki yayi, tare da mata alamar.
"Ai ni ba'a shiga É—akina, a fita ba'a kwanaba, haka kuma É—akina yanada dokoki".
Cikin sanyin murya tace.
"Ni dai É—akina zan koma in kwana".
A ranshi yace.
"Eye yanzu dai kin yarda nan gidanki ne wato harda wani a É—akinki zaki kwana, to saura in tabbatar miki ni mijinki ne kuma nan É—akin mijinkine.
Ba tare daya kulataba, ya ƙarasa gaban drawer ɗinsa, wani 3quater mai taushi ya ciro, ganin yana shirin zare bathrobe ɗin jikinsa agabanta ne, yasa tayi saurin kawar da kanta gefe tare da rumtse idanunta. Shikuwa babu wani ɗar ya cire bathrobe ɗin, tare da zura tattausan wondon ɗin ajikinsa. Body spray ɗinsa ya fesa, sannan ya ƙara gudun AC'n ɗakin,
Wayarshi dake kan mirror ya ɗauka, juyowa yayi ya kalleta, da sauri ta janye idonta dan ganin yadda ya haɗe mata fuska, rubutu yayi a wayarshi kana ya miƙa mata, ba musu ta karɓa ta fara karanta abinda ya rubuta mata.
"Ki shiga bathroom kije kiyi al'wala kizo, dan ni ba'a kwana É—akina saida al'wala".
Miƙa mishi wayar tayi cikin sanyi tace.
"Inada al'wala, sweet kawai nasha".
alama ya mata taje ta kurkure bakinta to.
tura baki tayi da niyar zatayi mgna sai kuma tayi shiru ganin ya É—aga mata hannun kana ya mata nuni da hanyar bathroom É—in nashi.
Sumai-sumai ta wuce jiki a mace,
koda ta shiga tsayuwa tayi tana kallon tsari da zubin bayan gidan nashi, cikin sanyi tace.
"Son kai komai nashi yafi namu kyau".
Ta ƙarishe mgnar tare da kurkure bakinta kana ta juya ta fito.
Ido ta É—an zuba mishi ganinshi sanye da wani farin jallabiya kana yana bisa sallaya ga kuma wani sallayan a gefenshi,
kai ta jujjuya ganin yana nuna mata kan sallayan,
cikin mmki tace.
"Ai ni nayi sallan isha'a na tun É—azu kuma nayi shafa'i da wittirinama".
Fuska ya tsuke babu alamar wasa ya miƙa mata wayarshi daya rubuta mata.
"Na sani ai, ko ce miki akayi ni ɗin banyi sallan isha'a ɗin bane? Kizo Nafila zamuyi, in roƙa miki Allah ya shiryeki ya rabaki da guje-guje nan da kokenki na tsoro dan karki sake guduwa da kuka".
Wani irin bugawa taji ƙirjinta yayi dan ta fara tsinkewa da manufarsa, cikin sanyi da ɗan tsoro tace.
"ÆŠan guntun rigar bacci a jikina fa".
Kai ya gyaɗa mata tare da mata alamun ai hijabin jikinta ƙatone mai kauri kuma gashi har ƙasa".
Babu damar wani musu dole ta matso gefenshi a hankali ta ajiye sweet É—inta gefen kulan dake kan bedside sannan ta dai-dai-ta tsayuwar ta kan sallayar,
shi ya limanceta sukayi nafila raka'a biyu.
Koda suka idar juyowa yayi ya fuskanceta hannunshi ya É—aura bisa kanta ya kama goshinta cikin ransa yayi addu'o'in kana, ya saketa,
haka nan taji jikinta yana rawa kar-kar, shiyasa tana jin ya saketa ta yunƙura zata miƙe,
da sauri ya kamo hannunta ya maida ita ta zauna gab dashi,
cikin yin rau-rau da ido tace.
"bacci nakeji".
Bai kulata ba, sai hannunshi yasa ya sauƙo da wannan kular, da Adda Rahma ta sa mishi gasasshiyar zabuwar nan, ya ajiye kulan a gabanta, sannan ya buɗe ɗan madaidaicin firijin dake gefenshi, goran madarar nan ya fitar ya ajiye gabanta,
Zuwa yanzu lamarinshi ya fara sata shakku,
wani irin ƙamshine taji ya ziyarci ƙofofin hancinta sanda ya buɗe kular, a fakaice ta kalli dangwaleliyar zabuwar da tasha gashin tukunya mai ɗan karen kyan gani da daɗin ɗanɗano, to Zaleeha dai dama uwar kwalamace, bata san cewa kazar ci inciki bane, kazar bashi kanaci kaima ɗin za'a tsotseka,
tura mata kular yayi gabanta tare da mata alaman taci.
Kai ta É—an jujjuya duk da yawunta da taji ya tsinke, cikin rauni tace.
"Na ƙoshi".
Kici-kici yayi da fuska cikin bada umarni ya mata alamu.
"Maza taci, shi ba'a kwana É—akinshi da yunwa".
Sosai yayi mata kwarjini, kana ta kuma tuno al'khairin da taiwa Baba Malam na cewa zatabi umarninsh,a hankali tasa hannu ta ɗan yagi kaɗan daga jikin ƙunɗun zabuwar dai-dai irin farin tsokar nan tibis taji tsokar sai nason mai da takeyi,
ido ya zuba mata ganin bata kai hannunta bakinta ba,
hannunshin yasa ya kamo natan ya É—agashi ya kai matashi kan bakinta,
kana ya mata alamu da idonshi cewa ta buÉ—e bakinta,
Rau-rau tayi da idonta kana a hankali ta buÉ—e bakinta tasa tsokar namar,
wani irin tsinkewa yawunta yayi sabida yadda É—anÉ—anon naman zabuwar ya ratsa mata jijiyoyin bakinta, a hankali ta fara sarrafa naman,
shi kuwa Hamma Saif sake kamo hannunta yayi ya maidashi cikin kularar, kana ta kuma yago gutsuren naman, still ya kuma kai mata hannun bakinta,
haka yai ta mata saida ta cinye rabin tsokar ƙungun, kana ya barta sabida taƙi sake yarda ta buɗe bakinta tunda tace mishi ta ƙoshi.
Rufe kular yayi kana ya tureshi gefe,
goran madarar ya buÉ—e wacce tayi sanyi kalau, rabinshi yasha, sannan ya kai mata bakin goran bakinta,
tana buƙatan abu mai ruwa-ruwa tunda taci maiƙo shiyasa ba musu ta buɗe baki ta.
Tasha mai É—an yawa dan taji garÉ—in madarar da zuma sai ya tuna mata zamanta a numan.
janye kanta tayi tare da yin gyatsa cikin sanyi tace.
"Na ƙoshi, zanyi bacci".
Rolling idonshi yayi tare da nuna mata hanyan bayan gida alamun taje ta wonke hannunta, dan shi bai taɓaba ko loma ɗaya.
A hankali ta miƙe ta nufi bayan gidan da wonko hannun nata.
Shi kuwa Hamma Saif ninke sallayoyin yayi ya ajiyesu wurin zamansu, kana ya ɓare sweet ɗin nan mai ɗan karen ƙamshi ya afashi a bakinshi, kana yaje gaban mirror ya kuma fesa turare sannan ya nufo jikin gadonshi da yafi kamanni da gadajen sarauta ko kuma na indiyawa dai-dai lokacin kuma ta fito daga bayan gidan.