← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 154

Sashe 5

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Bappa Ali kuwa ƙarfe biyar dai-dai suka kamo hanyan zuwa garin Gombe shida Malam Ashiru, daga cikin abun da Ummi ta faɗa masa, ko ɗaya bai rage ba, haka ya labartawa Malam Ashiru komai, shikansa Malam Ashiru saida yaji zuciyarsa tayi masa ba daɗi, tabbas yasan sharrin ƙiyayya, ƙiyayya bata da daɗi sam, kuma takan rufewa mutum ido, yayi duk abun dayaga dama, musamman ma ga mace da auren mijin da bata so dan haka shima ya yarda baza'ayi wannan aurenba.

Ƙiran sallan Magriba acikin garin Gombe tayi musu, nan suka tsaya sukayi sallah, inda suna idarwa suka nufi gidan Dirankaɗi, wato Baban Ishaq kenan, kasancewar tunkan su taso sunyi masa bayanin komai sun kuma sanar dashi zuwansu, inda shikuma ya ƙira Baba Malam ya shaida masa cewa da anyi sallan Isha za su zo.
Koda suka ƙarasa gidan na Dirankaɗi, anan sukayi sallan Isha, daganan suka wuce zuwa G.R.A wato unguwar su Zaleeha.
Tarba me kyau suka samu daga Baba Malam, inda ya sauƙesu acikin babban falonsa, nan yasa aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye,
hira kaɗan suka ɗan taɓa, kafun Dirankaɗi ya gyara zama inda ya fuskanci Baba Malam, cikin nutsuwa haɗi da halin dattako yashiga labartawa Baba Malam abun dake faruwa, da irin saƙon text message din da Zaleehan ke turawa Saifuddeen wanda suke ɗauke da barazana haɗi da baƙaƙen maganganu, inda ya ɗora da cewa.
"Kayi haƙuri Malam, amatsayinmu na manya masu hankali, baikamata ace mun zuba ido hakan na faruwa ba, haƙiƙa duk auren da akace akwai ƙiyayya acikinsa to mafi al'khairi shine barinsa, tabbas babu wani uba dazai so ɗansa ya rasa iri awannan gida naka mai cike da kamala haɗi da tarbiya, saidai kuma babu yanda zamuyi ɗaukan ƙaddara ya zame mana dole, saboda hakane mukazo baka haƙuri, kayi haƙuri Malam bisa dole munjanye nemawa Saifuddeen auren Zaleeha da mukayi, fatanmu shine Allah ya bawa kowannensu abokan zama nagari!."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da ɗanyin jigum, tabbas Zaleeha nason dasa masa ciwon zuciya, sannan tanason zubar masa da ƙima da kuma mutumcinsa a idanun jama'a, saidai kuma yayi al'ƙawarin bazai taɓa bari hakan ya faru ba, gyara zamansa yayi tare da duban su Baffa Ali, cikin dattako haɗi da tausasa zance yace.
"Babu wani abu dazan faɗa muku face haƙuri, kuyi haƙuri, haƙiƙa nine nan mahaifin Zaleeha, sannan nike da ikon bada aurenta ga koma waye, tuntuni nakuma bada aurenta ga Saifuddeen, kamar yanda Zaleeha take ƴa awajena, hakama Saifuddeen, shi ba iya ɗalibina bane kaɗai, inajinsa kamar jinina, saboda haka kuyi haƙuri, kujanye batunkun fasa auren, Zaleeha ƴatace kuma inada ikon tanƙwarata duk yanda naga dama, kuyi haƙuri ku ɗauka cewa duk waƴannan abubuwan da takeyi yarinta ne kuma zata daina watarana, tabbas nasan yanzu giyar ƙuruciya ne ke ɗibanta, nan gaba kaɗan bazatayi abun da tayi yanzu ba."
ÆŠan jim yayi tare da cigaba da cewa.
"Kuyi haƙuri dan Allah, Amatsayina na Uba agareta na baku haƙuri, kuma kamar yanda kuke sha'awar haɗa zuri'a dani, haka nima nake sha'awar haɗa zuri'a daku, musamman Saifuddeen daba kowani uba bane zaiƙi son zamowarsa suruki agaresa, kamar yanda na faɗa muku tun daga farko babu abun da zan faɗa daya wuce nace kuyi haƙuri insha Allah aurennan ba fashi."
Da sauri Malam Ashiru ya fara jujjuya kai a hankali tare da cewa.
"A a Malam kayi hak'uri abar batun auren nan mu kam mun janye.....!

BY
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Murmushi Baba Malam yayi irin nasu na manya, kana ya ɗanyi jim, haƙiƙa fasa auren Zaleeha bazai rage komai ba face mutuncinsa da kimarshi, mutuƙar kuwa aka fasa auren to tabbas ita da mahaifiyarta sun samu abun da suke so, sam shikuma bazai lamunci hakan ba, gyara zamansa yayi tare da kai dubansa ga su Baffa Ali da Malam Ashiru.
Cikin nutsuwa haÉ—i da kamala yace.
"Haƙiƙa nafahimci me kukeji agame da wannan auren, saidai kada ku manta mu daku ɗin kamar ƴan uwa muke,  dukanmu tsofaffine masu dattako da sanin ya kamata,  amatsayina kuma na mahaifi ga Zaleeha zan ƙirata na zaunar da ita nayi mata nasiha, insha Allah nasan zata fahimta, dan Allah kuyi haƙuri, rashin tunanine kawai irin na yaran zamani!."
Ajiyar zuciya su Baffa Ali suka sauƙe, cikin sanyin murya haɗi da fahimtar Baba Malam ɗin, Baffa Ali yace, "shikenan Malam Basheer babu komai, Allah yasa auren ya zama al'khairi agaresu, Allah kuma ya sawa Zaleeha so da ƙaunar Saifuddeen acikin zuciyarta, don shikam yana sonta sosai, fatan mu shine auren nasu yayi al'barka!."
Da "Ameen Ameen!." suka amsa su dukansu,  inda Baba Malam ya sauƙe ajiyar zuciya, sosai yaji girman na iyayen Saifuddeen ya ƙaru acikin idanunsa, nan suka ɗan tattauna maganganu masu muhimmanci, daga nan kuwa su Baffa Ali sukayiwa Baba Malam ɗin sallama,  har bakin motarsu Baba Malam ya rakosu, inda bai dawo cikin gida ba saida yaga tafiyarsu.
Zama yayi akan ɗaya daga cikin tausassun royal chairs ɗin da suka ƙawata haɗaɗɗen falon nasa, bayansa ya jingina da jikin kujeran tare da lumshe idanunsa,  cikin ransa haka yakejin ba daɗi, tunda yake baitaɓa sanya ranan auren ɗansa ko ƴarsa daga baya kuma akazo da maganar fasawa ba sai akan Zaleeha! duk kuma a dalilin taurin kai irin nata, tabbas Zaleeha tanason sashi yaji kunya a idanun mutanen da suke matuƙar ganin ƙimansa, amma babu komai zaiyi abun tubkar hanci tunda wuri,  wayarsa dake cikin al'jihun rigarsa ya laluɓo inda ya dannawa nombern Mama ƙira, bugu uku ana huɗu Mama ta ɗauki ƙiran, batare daya jira komai daga gareta ba yace.
"Kituromin Zaleeha." kitt ya kashe wayan, don sam baison abun dazai ɓata ransa da daren nan.
Bayan kamar minti shida dai-dai Mama tashigo cikin falon hannunta ɗauke da ɗan madaidaicin tray wanda samansa ke ɗauke da flask da kuma ƙananan cup guda biyu,  bakinta ɗauke da sallama ta ƙaraso cikin falon, inda ta jawo wani babban table dake tsakiyan falon ta kawosa har gaban Baba Malam ɗin, nan ta ɗaura ɗan ƙaramin tray din akan table ɗin,  duban Baba Malam tayi fuska ɗauke da Murmushi tace.
"Barka da hutawa!."
Shima Baba Malam É—in fuskarsa É—auke da murmushi, ya jinjina mata kai alaman ya amsa.

Su Baffa Ali kuwa koda suka isa gidan nasu Saifudden kai tsaye ɓangaren Ummi suka nufa,  zaune suka isketa ababban falon nata, gefenta kuwa Hayatudeen ne wanda keta faman buga game ɗin Drok Stack Ball awayarsa.
ganinsu yasa Hayatuddeen ya gaishesu cikin ladabi, don kuwa hadda Dirankadi akazo,  nan ya miƙe ya haura sama zuwa ɗakinsa.
Ummi kuwa tashi tayi ta kawo musu drinks masu ɗan sanyi,   nan ta zauna suka shiga ɗan gaisawa, musamman da Dirankaɗi wanda suka jima basu haɗu ba.
Bayan sungama gaisawa ne, Dirankaɗi ya gyara zamansa tare da fuskantar Ummi'n, sanin cewa ita ɗin mai yawan haƙuri da sauƙin kai ne yasanyasa tausasa lafuzansa, tayanda zata fahimcesa sosai, ahankali yace.
"Kamar yanda kika buƙata da muje gidan su Zaleeha, munje munkuma sanar musu cewar mun janye batun auren!.".
Ajiyan zuciya sauƙe a hankali tare da cewa.
"Alhamdulillah".
murmushi suka É—anyi, sai kuma Dirankadi ya É—an numfasa tare da cewa.
"Kiyi haƙuri Hajiya..  kisa aranki cewa auren Saifuddeen da Zaleeha haɗine na Allah bawai yin kanmu ba, sannan kada ki manta ance matar mutum kabarinsa, sannan idan Allah Ya nufa cewa Saifuddeen sai ya auri Zaleeha bamu isa hanawa ba."
shiru tayi jiki a mace taci gaba da sauraronshi.
"Tabbas nasan mekikeji nakuma fahimci irin fargaban da kike ciki, ƙwarai kowacce uwa bazata taɓa son wani abu dazai cutar mata da ɗanta ba, nasan kina gujewa Saifuddeen auren Zaleeha ne badon komai ba saidan, kina jin tsoron abunda kaje kazo, da kuma irin tsananin ƙiyayyar da Zaleehan ke nuna masa,  ƙwarai hakan abun tsorone to amma kada ki manta, babu wani abu dazai samu bawa me kyau ko akasinsa,  face dama tuntuni anrubuta acikin littafin ƙaddaransa."
Kai ta gyaÉ—a tare da cewa .
"Haƙƙun".
Cikin jin daÉ—in tana gamsuwa yaci ga da cewa.
"Wani baya taɓa iya cutar da wani harsai Allah Ne ya tsara hakan,  saboda haka inaso ki kwantar da hankalinki, munyi magana ta fahimta da mahaifin yarinyar, mutum ne shi mai tsananin dattako da kamala, kema kinsan hakan tuntuni, ya ƙasƙantar da kansa ya bamu haƙuri, ya haɗamu da Allah cewa kada a fasa auren! yakuma taushemu da lafuzza masu daɗi, saboda haka mu dai mun aminta cewa Saifuddeen zai auri Zaleeha, saboda haka yana ɗaya daga cikin ƙaddaransa, komai zai wuce kuma watarana sai labari, kema inaso
kisa aranki cewa Insha Allah auren Saifuddeen da Zaleeha al'khairine mai tarin yawa, wanda zaisa dukkanmu farinciki anan gaba,   mudai addu'an al'khairi yadace munayi musu ako da yaushe!."

Baffa Aline yaÉ—an nisa tare da amsawa da cewa.
"Ƙwarai kuwa, abun da Dirankaɗi ya faɗa gaskiyace, haƙiƙa dukanmu nan munsan cewa ke uwa ta gari ce,  munsanki da haƙuri Ummi, dan Allah inaso ki ƙara akan nada, ki-kumayi duba da irin tarin soyayyar da Saifuddeen keyiwa yarinyarnan tunfa suna ƙanana, kuma rauninki zaisa Saifuddeen fasa auren nan!."
Chapter 5 · 0% Book details