Sashe 71
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Jin sauƙar Muryar Hayatuddeen acikin kunnuwanta yasa, ta juyo da sauri, ganin shine kuwa yasa ta zare jikinta daga na Ummi, faɗawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi, tare da sakin kukan da yafi wanda tayi abaya ciwo, dan jin Hayatuddeen takeyi tamkar Zakariyya. Shima Hayatuddeen ɗin kukane ya ƙwace masa, cikin kukan nata tace. "Hayatuddeen ya zanyi Baba Malam yayi fushi dani, haka Ya Ahmad ma da Aunty Lubna duk sunyi fushi dani, babu wani wanda yake saurara ta, basason ko ganina akusa dasu, Mamy ma fushi take dani, gashi Ya Ameenu ya zama abun tausayi, Adda Maryam ta tafi ta barmu."
Ɗagowa daga jikinsa tayi tare da kamo hannayensa, cikin kuka taci gaba da cewa. "Baba Malam yace kar na sake zuwa gidansa, hatta Ziyada ƙanwata ma fushi take dani, Zakariyya ma nasan adole yake kulani, Hayatuddeen ya zanyi? ina zansa rayuwata? kowa baya sona, kowa guduna yake, babu wasu wanda ke rarrashina sai su Ummi, inajin kamar zuciyata zata fashe, duk wani majinginan danake tinƙaho dashi ya ruguje, rayuwata tayi mini zafi, har inajin gwamma mutuwa ta da rayuwata." taƙare maganar tana me sake komawa ta raɓa jikinsa ta riƙesa ƙam, kuka kuwa yinshi take harda majina.
Duk yanda yaso shanye kukansa kasawa yayi, hakan yasa ya sake rungumeta ya fashe da kuka, saida yayi kuka sosai sannan ahankali ya shiga shafa bayanta, cikin sanyin murya yace. "Kiyi haƙuri kinji Adda Zaleeha, ki daina kuka, idan duka mutanen duniya zasu ƙiki, ni da Zakariyya bazamu taɓa kinki ba, kiyi shiru kinji, nasan Baba Malam yayi fushi, amma zai yafe miki."
Kai Ummi ta jinjina cikin son kwantar mata da hankali tace.
"Ƙwarai kuwa Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, yanzu dai ki samu kici abincin kinji." Cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Ummi bazan iya ci ba, ko tea É—in É—azu dana sha haka najisa kaman maÉ—aci, gaba É—aya kaman yanda zuciyata take babu É—anÉ—ano acikinta, haka bakina ma, banajin daÉ—in komai."
cikin tausayawa Ummi tace.
"To akawo miki fresh milk kisha ko kaÉ—anne?"
Batason yawaita yin musu da Ummi hakan yasa ta É—an gyaÉ—a kanta, dai-dai lokacin kuwa Raleeya ta shigo, nan Ummi tace da ita, ta kawowa Zaleehan fresh milk.
Babu ɓata lokaci kuwa takawo fresh milk ɗin me sanyi.
Karɓan cup ɗin Hayatuddeen yayi, cike da tausayinta yace. "Adda Zaleeha, ki tashi kisha kinji."
bazata iya janye jikinta daga garesa ba, saboda tanajin ya zame mata kamar majingina, hakan yasa ahankali taɗan ɗago kanta dake masifar sarawa, cikin kulawa Hayatuddeen ya shiga bata fresh milk ɗin abakinta, sam kwata kwata batajin daɗi ko ɗanɗano abakinta, jima take kamar magani take sha, kurɓo huɗu kawai tayi ta janye bakinta daga jikin ƙofin, har yanzu sheshsheƙan kuka take, gashi jikinta ya sake ɗaukan zafi sosai, komawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi ta kwanta, tana ta faman fusgar numfashinta dake neman ƙwace wa. Ummi, Adda Rahama, Raleeya, har zuwa kan Hayatuddeen babu wanda ya gusa da ga kusa da ita, wani irin kulawa haɗi da tattali na musamman suke bata, sosai suke faɗa mata kalaman dazai kwantar mata da hankali..
Suna nan azaune har aka ƙirayi sallan la'asar, Ummi ne tace da Adda Rahama da kuma Raliya su shiga kitchine su ɗaura abinci, kasancewar tunda akayi rasuwa'n kullum sai sunkai abinci gidan su Zaleeha.
Nandai Hayatuddeen ma ya tashi ya wuce massallaci, itama Zaleehan sallah tayi, nan kan carpet ta kwanta tana masassara saboda zazzafan zazzaɓin ya soma cin ƙarfinta.
Su Adda Rahama kuwa suna kammala girkin, nan cikin wasu manyan food flask suka juye abincin.
Kamar kullum dama Hayatuddeen da Raleeya ne ke kai abincin, to yau ɗin ma dai hakanne, ta kasance dan sune suka kai abincin, Hayatuddeen ne ke driving, kasancewar yanzu hannunsa yaɗan faɗa wajen iya tuƙin mota, saboda Khamis na koya masa tuƙin time to time, babu laifi kuma yaɗan iya.
Koda suka ƙarasa gidan su Zaleehan bayan sun sake yi musu gaisuwa, Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zakariyya da Imran ƙanin Ishaq wanda da Babansu yazo, zagawa sukayi wajen da babu yalwar mutane. ɗan karyar da wuya Hayatuddeen yayi, cikin sanyi haɗi da damuwar dake bayyane akan fuskarsa yace. "Zakariyya Adda Zaleeha taje gida bata da lafiya sosai, gaba ɗaya jikinta zafi kaman wuta, har suma tayi, dan Allah abawa Baba Malam haƙuri ya yafe mata, tana cikin matsanancin damuwa, kuka yazama tamkar abinci agareta."
Idanun Zakariyya ne suka cicciko da ƙwallan tausayin ƴar uwartasa, ɗan lumshe idanunsa yayi, yana mejin tausayinsu su dukansu, tabbas yasan akwai ƙauna me zafi atsakaninsu, wanda koda ace babu auren Hamma Saifuddeen akan Zaleeha, idan Hayatuddeen yaganta cikin damuwa zai ji ƙanta, kuma gashi nan damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa, sunyi imani cewa duk wani damuwan ɗayansu nasune su duka.
Cikin sanyi yasa hannu ya share hawayensa, muryarsa asanyaye yace. "Hayatuddeen nima bansan ya zanyi ba, Baba Malam yace. Bayason sake ganinta, yana fushi da ita sosai, kuma ta basa haƙuri ma yaƙi haƙura."
Sosai jikin Hayatuddeen da Imran yayi sanyi, dole da addu'a kawai zasu taya ta, dan basu da wani zaɓin daya wuce hakan.
Fitowar Adda Raleeya daga cikin gidan ne, yasa sukayi shiru da zancen, ƙarasowa wajen da su Zakariyyan suke tayi, ganinta yasa Hayatuddeen duban Zakariyya murya asanyaye yace.
"Mu zamu wuce."
Har bakin mota Zakariyya da Imran suka rakasu, saida yaga tafiyarsu sannan suka komawa cikin gida, zuciyarsa gaba É—aya ba dadi, sosai tausayin Zaleehan ke damunsa.
Koda su Hayatuddeen suka koma gida kuwa kai tsaye ɗakin Ummi suka wuce. Har yanzun Zaleeha na duƙunƙune waje ɗaya, gefenta Ummi da Adda Rahama ne zaune.
Ƙarasowa cikin ɗakin Hayatuddeen yayi tare da zama akusa da ita, hannunta ya kamo, hakan yasa ta ɗago ta dubeshi da idanunta wanda sukai jajur, murmushi yaɗan ƙaƙalo akan fuskarsa, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha kukan ki ya kusa ƙarewa Insha Allah, Baba Malam zai yafe miki nan bada jimawa ba, kuma Ya Ahmad ma da kansa yace agaisheki."
Zabura tayi tare da matsowa gab dashi, idanunta ta zuba masa, kansa ya jinjina mata alaman dagaske yake, idanunta ta lumshe, take kuma wasu sabin hawaye suka zubo mata, matsawa kusa dashi tayi tare da ɗaura kanta akan kafaɗansa, hannunsa ta riƙe ƙam tana sauƙe ajiyar zuciya.
Ganin haka yasa su Ummi sakin ajiyar zuciya suma, dan gaba É—ayansu burinsu bai wuce ganinta cikin nutsuwa ba.