← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 154

Sashe 78

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Saifuddden da Ameena kuwa, yau zagewa tayi ta nuna masa soyayya kala kala, babu laifi kuma shima ya biye mata, hakanne kuma yasa kasantuwarsu tayi mata armashi, dan bakaɗan ba takejin daɗin Saifuddeen. Haka ko da suka kwanta bacci tawani rungemesa, ranta kuwa fari ƙal, bata da wani damuwa, saboda kasantuwarsu na yau yasa tanajin kanta kamar wata sarauniya.

Washegari

Yau ya kama Lahadi, inda gobe Monday Amina zata fara zuwa aikin rana.
kuma yaune ake sadakan Uku na rasuwar Adda Maryam, Inda sukejin mutuwar ta dawo musu sabuwa, sosai suka sha kuka har suka godewa Allah, yayinda mafi yawancin mutanen da suka zo musu ta'aziyya duk kowa ya kama gabansa. Haka gidan ya rage daga, su Yaya Ahmad sai kuma Hajja Inna da Goggo maryama, sai kuma su Ziyada da kuma wasu mata guda biyu, wanda suke ƙannen.
Yaya Ameenu ne, wato Zainab da kuma Ubaida, sai wanda suma dukansu matan aure ne, sai Hajja Ma'u mahaifiyarta Ya Ameenu kenan rasuwar ne ya sasu zama anan gidan na Baba Malam, wanda suɗin ma yau zasu tafi, zuwa yanzu babu wani baƙo ko ɗaya da ya rage acikin gidan, iya su yasu ne, haka suka sha kukansu suka ƙoshi, daga ƙarshe sukayiwa Adda Maryam ɗin addu'a da fatan Allah ya raya ɗanta Ayman.

Can gidan su Saifuddeen kuwa, Yau Zaleeha da wuri ta tashi, tana idar da sallah kuwa tawuce É—akin Ummi ta gaisheta, anan ta iske Saifuddeen É—in, koda ta gaishesa, saida ya É—auki kusan second 30 kafun ya jinjina mata kai alaman ya amsa, haka tatashi ta koma É—akinta jikinta duk asanyaye, shikuwa falon Ummi ya koma ya zauna.
Wanka tayi sannan tasaka ɗaya daga cikin riga da sket ɗin da aka sayo mata, ganin kayan ya kamata yasa ta ɗaura hijab akai, murɗa handle ɗin ƙofar tayi tafita, dan tanason fara taya Raleeya aikace aikacen gidan. Tana fitowa falon kuwa anan zaune ta iskesa, sadda kanta ƙasa tayi sannan ta wuce kitchine, Sarai ya ganta amma saiyayi kaman bai ganta ba, saida ta wuce yabi bayanta da kallo, harda wani ɗan lumshe idanunsa.
Tana shiga kitchine ɗin kuwa tasamu Raleeya na firan dankali, amsa tayi ta soma tayata suna ɗan taɓa hiransu.

Ameena ce tashigo cikin falon, ɗauke da Adeel akan kafaɗunta, ganin Saifuddeen zaune afalon Ummin yasa ta sakin murmushi, shima murmushin ya sakar mata, har acikin ransa yaji daɗin ganinta yanzun, dan da itane zaina buga Game ɗinsa, wanda ya tabbata wata rana kuwa zaiyi winning, ƙarasowa cikin falon tayi, tare da ajiye masa Adeel akan cinyarsa, nan ta wuce ɗakin Ummi, koda taje ɗakin na Ummi kuwa cikin ladabi ta gaisheta, fuska asake Ummi ta amsa mata, tare da tambayanta Adeel, murmushi tayi tare da cewa.
"Ummi yana falo suna tare da Abban shi."
Itama Ummin murmushi tayi tare da jinjina kanta, dan tana lazumi ne, batason magana. Miƙewa Ameena tayi ta fice daga ɗakin, Tana fitowa falo Saifuddeen ya miƙo mata hannunsa, cikin jin daɗi ta ɗauke Adeel dake kan cinyarsa tayi, ta ɗaurasa akan kujera, raɓawa kan cinyar Saifuddeen ɗin ta ɗanyi dan taga falon ba kowa kuma tasan Ummi na lazumi ba yanzu zata fitoba, ahankali ya sanya hannuwansa, ya saƙalo waist ɗinta, harshensa yasa inda ya ɗan laso lips ɗinta, idanunta ta ƙura masa bata ko ƙiftawa, ganin haka yasashi ɗan ɗaga mata gira, murmushi tayi tare da sake shigewa jikinsa, fuskarta ya ɗago ya haɗe bakinsu waje ɗaya, jin haka yasa ta kamo laɓɓansa tana tsotsa sosai.
Gaba ɗaya sun shagala, musamman ma Ameena, wanda idan tana shan laɓɓansa takejin kamar tana shan sweeet.
Adeel kuwa sai wutsil wutsil yake, yanason jawo flowern dake gefen kujera, hakanne yasa har yazo bakin kujeran batare da sun ankara ba, Zaleeha ce ta fito daga cikin kitchine ɗin hannunta riƙe da flask, da sauri taja baya sakamakon abun da idanunta suka gane mata, ƙoƙarin komawa cikin kitchine ɗin take, idanunta suka sauƙa akan Adeel wanda saura ƙiris ya faɗo daga kan kujeran, cikin sauri ta ajiye flask ɗin hannunta, da gudu ta ƙarasa inda yake, dai-dai lokacin kuma har ya faɗo daga kan kujeran, saidai kuma bata bari yakai ƙasa ba, tayi saurin zubewa akan guiwowinta ta taro sa, yafaɗa jikinta, wani irin firgitaccen ihu ya saki har kamar zai shiɗe dan yayi masifar tsorita ruggumeshi tayi a jikinta da kyau, hakan yasa ya ƙanƙameta tare da kuma cilla ihu, wanda hakanne ya fargar dasu Saifuddeen, azabure suka juyo suna kallonsu, ɗagosa Zaleeha tayi tare da mannasa aƙirjinta, tana jijjigasa, Idanu Saifuddeen ya zuba mata, ita kuwa Ameena hakanan taji wani iri aranta, kukan Adeel ɗinne yafito da Ummi, daga ɗaki, harta Raleeya ma saida tafito, cikin kulawa da tsananin son yaron Ummi tace. "Lafiya kuwa me ya sameshi."
ta ƙarasa maganar tana shafa kanshi tare da kallon Zaleeha
Cikin damuwa murya a tausashe Zaleeha kamar zatayi kuka tace.
"Faɗowa ya kusayi daga kan ƙujera, inaga shiyasa ya tsorata, gashi yana ta kuka."
ta faÉ—i maganar tana me ci gaba da jijjigasa, saboda sam batason kukan Adeel É—in, tanajin yaron sosai aranta, ganin baiyi shiru bane yasa ta sanya bakinta akunnenshi tana É—an hurawa masa isaka tare da É—an bubbuga bayanshi kana tana jijjigashi, wanda hakanne ya bawa jikinta damar rausaya wa, take kuwa yayi shiru, tare dayin lub ajikinta, jin yayi shiru yasa ta wuce É—akinta dashi.
Har zuwa lokacin kuwa idanun Saifuddeen akanta suke, Ameena kuwa gaba ɗaya ma takasa tantance meke damunta, tausayin ɗanta ne ko baƙin ciki da kishi takasa tantance wanne ne ɗaya, ganin lokaci na ƙurewa yasa ta juya ta fice daga falon dan batason tayi lattin zuwa wajen aiki dan yau ɗin mitin zasuyi da manyan likitoci.
Zaleeha kuwa tana shiga ɗaki, ruwa me ɗan ɗumi ta haɗa, tayiwa Adeel ɗin wanka, Hayatuddeen ne ya shigo cikin ɗakin, hakan yasa tace dashi yaje ya karɓo mata kayan Adeel tasa mai.
Part ɗin Ameenan yaje, ya amso kayan sannan ya kawo mata, tsab ta shirya Adeel ɗin cikin kayansa me kyau, sosai kuwa yaron yayi kyau, haka ta rungumesa aƙirjinta tana ta yi masa wasa.
Ganin alamun bacci yakeji yasa ta É—auki towel ta goyeshi ai tuni yayi bacci.
Saida Ameena ta zo tafiya aiki sannan ta amshe sa, still agaban Zaleehan Saifuddeen ya sake jawo Ameenan yayi mata kiss abayan hannunta kafun ta tafi, Zaleeha kam idan ta kallesu sau É—aya bata yarda ta sake kallonsu, zuwa yanzu ma mamaki suke bata dan ta lura basa gajiya da tsotse, saidai kuma idan ta tuna cewar rashin damuwa ne ke sasu hakan, sai taji matsanancin tausayin kanta.
Tace su kam sunji daÉ—i da basu da damuwar duniya.
Koda tayi break É—aki ta komawa tayi ta kwanta, cikin zuciyarta kuwa fargaba ne, me tarin yawa, saboda batasan ta yaya zata fuskanci Baba Malam ba.
Chapter 78 · 0% Book details