← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 154

Sashe 94

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amina kuwa tana shiga É—akinta bakin gado ta zauna tanajin tana son danne zazzafan kishinta kenan yanzu yauma a É—akin Zaleeha zai kwana,
kwanciya tayi tare da kife kanta bisa pillow ta saki nannauyan numfashi.
Ita dai ALLAH ya sani da Saifuddeen zai saki Zaleeha wlh da tanaso da kuma tafi kowa jin daÉ—i.
ɗago kanta tayi ta ɗauki woyarta jin alamun saƙo ya shigo mata.
buɗe saƙon tayi ganin sunan Abban Adeel hannu tasa ta share hawayenta lokacin data karanta abinda ya turo mata.
"Kin tafi kinje kin fara kukan ko?."
Da sauri ta tura mishi amsa.
"A a wonkafa zanyi".
ajiyan zuciya ta sauƙe sanda taga saƙonshi.
"Kin tabbata ba kuka kikeyi ba?".
Da sauri tace.
"Eh."
"Yauwa Ummu Adeel haka nake son ji,kinji ko kada in sake ganin kina min kukan da babu dalili,in laifi nayi miki ki gaya min banfi ƙarfin in baki haƙuri ba".
Wannan text É—in yayi masifar sata jin daÉ—in, sai kuma shaiÉ—an ya kisa mata.
"Ke sokuwa kika san me yake gaya mata ita kuma?".
Take ta kife kanta taci gaba tubka da worwora amman tana mai yiwa kanta faÉ—an ta zauna lfy da mijinta da abokiyar zamanta.

A can falon Ummi kuwa, yana gama text É—in da yakeyi ya fice ya nufi side dinshi dan zaije yayi shirin bacci.

Ita kuwa Zaleeha bacci takeji sosai to amman tsoro tafiya da Adeel takeji tana son tafiya dashi tana kuma tsoro sabida kada Abbanshi yaje karɓanshi ya mata tijara irin ta jiya shiyasa take shirin kontar dashi a nan ta gudu ta barwa Raliya shi, ai in bata tafi da ɗanshiba bazai bitaba.

Raliya ce ta miƙe tare dayi musu saida safe ta haura sama,
Ummi ce da yanzun ta fito tare da Raliya ta kalli Zaleeha dake ƙoƙarin kontar da Adeel tace.
"A a Zaleeha har yanzu kina nanne, dare yayi ai sha É—aya saurafa, tashi ki É—auki coffee É—in Babana ki kai mishi".
Da ƙarfi taji cikinta yayi wani ƙugi,wannan shine anyi gudun gara an tadda zago,
amman ba halin yiwa Ummi musu bare gardama,
a hankali ta miƙe goya Adeel tayi sannan ta ɗauki tray ɗin da aka shiryawa Hamma Saif ɗin coffee ɗin shi,
jiki a mace tayi musu saida safe ta juna ta nufi side É—insu.

A hankali ta tura ƙofar falonshi ta shiga da sallama, cikin nitsuwa take taku ta shiga falon nashi da bata taɓa gangancin shigaba,
ganin ba kowa yasa tayi sauri-sauri gudu-gudu ta ajiye mishi tray É—in bisa dinnin table É—in shi,
ta juya ta fita da sassarfa kamar wacce za'a kama ko tsarin falon bata gama ganinba.

Shi kuwa Saifuddeen tuni yayi wonka shi ya shirya cikin wasu tattausan riga da wondo na bacci masu kalar sarararin samaniya, ya fesa turare yayi ras dashi sai ƙamshi yakeyi.

Daga falonshi kai tsaye É—akin Ameena ya nufa.

A kan gado ya hangota tana zaune tasa kanta cikin guiwowinsa bisa alamu tunani takeyi,
jin motsinshi ne yasata É—an É—agowa ta kalleshi,
sai kuma ta meda kanta ƙasa da alamun bata son ganinshi ne ko haushinshine ma takeji bata dai son ta gaza danne kishinta ne.
shi kam lamarin Ameena ya tsaya mishi a rai don ya rasa me zai mata ta saki ranta,
a hankali ya iso bakin gadon hannunshi ya miƙa mata alamun tazo,
cikin jin haushin sa dan gani take ai duk abinda yakeyi mata zaiyiwa Zaleeha, hararanshi ta É—anyi cikin son danne kishinta tace.
"Dan Allah ka fitarmin a É—aki ka tafi can wurin maikai saida safe".
Kanshi ya jinjina mata kana ya zuba mata ido.
Da sauri ta sauƙo kan gadon jiyo muryar Zaleeha na sallama a falon ta.
Hannunta tasa ta share hawayenta tare da fitowa,
cikin kirsa take kallon Zaleeha sama da ƙasa,
murmushin da bai kai zuci ba tayi jin Zaleeha na cewa.
"Ga Adeel kar ya tashi dare-dare yayi ta kuka".
Motsowa tayi jikin Zaleeha da ta É—an sunkuya ta kunce abun goyon, cikin kirsa tace.
"Ae kam ya iya rigama kamar na Abbanshi,shima gaya can a É—aki yanata min rigama, nace inji da É—anka inji da kai".
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Saida safe".
Harara ta mannawa Zaleeha tare da cewa.
"Allah ya bamu al'khairi".

Amin Amin Zaleeha tace tare da ficewa ta koma side É—inta.

Kai tsaye bathroom ta shiga,wonka tayi soso da sabulu kana tazo ta kimtsa cikin tattausan rigan baccinta mai tsawo har guiwa.

Kasancewar tana tsoron duhune yasa ta bar wuta É—akin a kunne,
konciya tayi bisa gadonta tare da jawo borgo ta shiga ciki ta konta tayi lib tana sauƙe numfashi dan tana tare da gajiya.

Ita kuwa Ameena tana komawa cikin bedroom É—inta gado ta hau cikin jin ba daÉ—i ta juyo ta kalli Saifuddeen baki ta tura tare da cewa.
"To sai ka tafi ai tunda ga É—ana an dawo min dashi sai kuje can kuci juna".
Zuwa yanzu dariya Ameena ke bashi dan fushinta mara daliline,
dan haka juyawa kawai yayi ya fita.

Falonshin ya shiga nan ya samu coffee É—inshi, shida kanshi ya haÉ—awa kanshi dai-dai misalin abinda zai sha, saida ya sha sannan ya É—an zaro wayarshi a saman lips É—inshi yace.
"Shabiyu harda kwata".

Lumshe yayi lokacin daya nufi side É—in zali a ranshi yace.
"Itama tanada haƙƙi a kaina dole in san ya ta kwana ya ta tashi.

A hankali yake sarrafa kekenshin har ya isa bakin ƙofar ɗakinta mamaki yayi ganin yadda ta bar wutan ɗakin a kunne, cikin nitsuwa ya tura ƙofar ya shiga,
ita kuwa Zaleeha bacci ya É—an fara fizgarta shiyasa bata san da shigowanshi ba,
a hankali ya isa bakin gadon.
Da sauri Zaleeha ta buɗe idanunta jin mitsin mutun wuƙi-wuƙi tayi da idanunta ganin shine, da sauri, ta ɗan matsa gefe cikin tsoronshi da muryar bacci tace.
"Menene? Nifa na maida Adeel wurin Mamanahi,baya wurina! Kuma na kai maka coffee É—inka falonka!".
ta ƙarashi magar cikin tanayin rau-rau da idanunta, dan ita batama san lokacin data meda Adeel yana ɗakin Ameena ba.
Baki shine ya ɗan taɓe tare da buɗa kafaɗu shi kana ya mata alama.
"To an ce miki Adeel nazo karɓane? Ko dai bani da enci da damar shiga ɗakin ne sai kin bani izini ne?".
Ya ƙarashi maganar cikin alamun tambaya.
Kai ta karyar bisa kafaÉ—a cikin sanyi tace mishi.
"A a".
Kanshi ya jinjina tare da mata alamun.
"To naza kwana a É—akin nan É—inne".
A take sai ga hawaye shar-shar a fuskarta cikin rauni da sanyin ta tace.
"To shike".
Sai kuma ya zuba mata ido ganin ta ɗauki pillow ta sauƙo daga kan gadon da alamun zata fita ne.
Da sauri yasa hannunshin ya fizgota kana ya ajiyeta kan gadon a gaban shi, ya zama suna fuskantar juna,
cikin yarensu ya mata magana.
"Ok yanzunma can cikin garding É—in zaki koma ki kwana ne?".
Kai ta jujjuya mishi kamar ƙaramar yarinya murya can ƙasa tace.
"A a".
Cikin tsareta da ido yace.
"To ina zakije ki kwana? Sannan ni kurane da in na shigo kike gudana gaba É—aya jikinki na rawa".
Ya ƙarshe magar da mata alama da kyau yadda zata gane.
A hankali tace mishi.
"A a". Tare kuma da girgiza kai alamar a a yadda zai gane.
Cikin bada ubarni da yaransa yace mata.
"To hau ki kwana". Ba musu ta haura kan gadon ta dugungune wuri É—aya.
Cikin kula yake kallon yadda gaba É—aya jikinta ke karkarwa, a hankali yake mata misali da cewa.
"Nifa babu abinda zan miki,ki nitsu ki konta kiyi baccinki, sai da safe".
Kai ta gyaɗa mishi tare da sauƙe nannauyan ajiyan zuciya.
Shiru yayi yana ƙare mata kallo gaba ɗaya ta rame, fuskarta tayi fiyau, kuma har yanzu akwai damu da jimamin rashin ƴar uwarta.
Da wannan tunanin ya juya ya fita bayan ya kashe mata wutan ɗakin, sabida bata cikin yanayi mai daɗin da zata iya fahimta ko jin daɗi wani abun da zaiyi mata shiyasa bari dai ya ɗaga mata ƙafa.

Washe gari da, kuwa ranar Ameena zata karɓi Saifuddeen domin ya gama kwanakin shi biyu na ɗakin Zaleeha.

Da yamma Ummi na zaune a ɗakinta tana kwaɓa lallen gargajiya da takeso tasa a daren yau ɗin Zaleeha ta shigo gefenta ta zauna,
cikin nitsuwa ta gaidata,
ganin tayi shirune yasa Ummi cewa.
"Kinyi shiru Zaleeha me kikeso?".
Cikin sanyin yanayin da rayuwarta ta dawo ciki tace.
"Uhum Ummi dama gobene za'ayi sadaka bakwai É—in Adda Maryam, kuma ina son zuwa Ummi a gayawa Hamma Saif mana dama ina son zuwane in na samu".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To Zaleeha ni zan tamɓayan miki,keda mijinki kije ki tambaye shi da kanki kinji ko karkiyi haka".
Cikin nitsuwa ta gyaɗa kanta alamar to kana ta miƙe ta fita,
binta da ido Ummi tayi a fili tace.
"Uhmmm Saifuddeen ya sawa yarinyar nan tsoronshi, da shakkarsa ban san meyasaba, yarinya duk ta zama shiru-shiru abar tausayi".

Ita kuwa Zaleeha yau tunda safema bata kuma ganin Hamma Saif É—in ba, dan yau tunda safe ya tafi Office É—insu na SS.
Dan sun samu wani bayani kan Dalla ya kusa dawowa.

To ta dai sa a ranta zata daure ta tambaye shi koda zai gwatsaletan ne.

Gab da magriba ta fito daga falon Ummi kenan tana ruggume da Adeel tazo gab bakin kofar shiga side ɗinsune tayi kiciɓis dashi.
yayinda Ameena kuwa tana falon Ummin dan yanzu ta dawo
Chapter 94 · 0% Book details