← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 154

Sashe 123

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sama da 50 minute ya ɗauka yanajinsa acikin wata duniya ta daban, cikin abun dabai wuce 3 minute ba ya fara sakin wani irin gurnanin nishi, mai ɗauke da wani irin sauti, lokaci ɗaya yaji bayansa na riƙewa, kaman wanda ake buga masa wani abu gaba ɗaya jijiyoyin bayanshi yaji suna ta riƙewa, wani irin nishi me ƙarfi yayi azauce cikin wata irin muryar dake bayyana zallan yanayin da yake ciki, bakinsa na rawa yaƙira sunan "Za....l..eee...haaa...." Murya ararrabe, wani irin jiri ne yazo masa, hakan yasashi faɗawa saman jikinta, inda ya ɗaura bakinsa adai-dai saitin kunnenta, wani irin numfashi me zafi yake fitarwa, komai na jikinsa yayi rauni, lokaci ɗaya wani irin zazzafan zazzaɓi ya dirar masa, harta haƙwaransa saida suka soma rawa suna haɗewa da juna.
Ɗan mirginawa yayi daga kanta, cikin azaban ciwon da kansa yakeyi masa ya zuro da ƙafafunsa ƙasa daga kan gadon.
Baisan tayayane ko kuma yaushe ne ya iya yunƙurin tashi ba, saidai ga mamakinsa samun kansa yayi atsaye tsam da ƙafafunsa, idanunsa wanda sukai ja kaman anzuba masa barkono ya zazzaro waje, yana kallon ƙafafunsa dake rawa kaman wanda aka jona musu shocking, take yaji bayansa na duka kau! kau!! kauuuuuu!!! haka kaman ƙashin bayanshi zai ɓalle, jiri ne ya ɗebesa, take ya zube akan gadon, zazzafan zazzaɓi me tsanani ne yasake hawansa, haka yaji ko kansa bazai iya ɗagawa ba, ga kuma bayansa dake masa azabebben ciwo.
Hannunsa dake rawa ya kai kan fuskar Zaleeha tare da shafawa, ƴar yatsansa yasa adai-dai ƙofar hancinta, jin bata numfashi ne yasashi rumtse idanunsa da ƙarfi, take wasu irin hawaye masu zafi suka silalo daga cikin idanunsa.
Duk bayan second É—aya kuwa bugun zuciyarsa ke tsananta.
Gaba ɗaya ɗan kuzarin da ya rage masa ya tattaro tare da yunƙura ya tashi zaune.
Ƙokarin miƙewa yake kaman yanda yaga yayi ɗazu, amma sai ya kasa, saboda yanda bayansa ya riƙe sosai, awahalce ya jawo wheelchair ɗinsa ya hau, ko zama da kyau bai iya ba, saboda yanda yakejin bayansa na sarawa.
Dishi-dishi yake gani haka ya nufi bathroom, adaddafe ya ƙarasa gaban shower, inda ya sakarwa kansa ruwa. Jikinsa na kakkarwa haka yayi wankan tsarki, tare da alwala, koda ya fito daga toile ɗin baya wani gani sosai, take kuma yaji wani irin fitinannen sanyi na huda kowani ɓulin gashi na jikinsa, yana shiga ko ina a sassan jikinsa, ciwon kai, zazzafan zazzaɓi, da kuma matsanancin ciwon baya sune abun da suka kassara gaba ɗaya kuzarinsa, har kuma yakejin raɗaɗinsu acikin ƙwaƙwalwarsa jiki na rawa ya buɗe firiji ya ɗauki goran ruwa mai sanyi.
Da ƙyar ya iya kai kansa kan gadon kwanciya yayi, abayanta buɗe goran ya watsa mata ruwan amman a banza kuma watsa mata yayi, wani dogon numfashi taja, jin haka ya ajiye goran kan bedside, jiki na rawa ya jawo rigar baccinta ya saka mata a daddafe ya lalubo hijabinta ya rufe mata daga cikinta zuwa ƙasa, kana ya konta tare da jan blanket ya rufa gaba ɗaya jikinsu, wani irin runguma yayiwa Zaleehan wanda da ace tana cikin hayyacinta, da sai tayi kuka, saboda yanda ya maƙalƙaleta sosai jikinsa ke rawan sanyi, haka haƙwaransa ke haɗewa suna kakkarwa, idanunsa ne suka rufe saboda sunyi nauyi sosai.
Ita kuwa Zaleeha daga numfashi É—ayan bata kuma sake waniba bare tasan inda take.
Ahankali cikin ransa yasoma karatun alƙur'ani, wanda tun yanayi azuci, har karatun ya fito fili, wanda ma da ƙyar muryarsa take fita, dan ciwon kan nasa bawai ya ragu bane, gashi bayansa nata ciwo kaman zai ɓalle.
Haka ya dinga karatun al'ƙur'ani, da zaran ya kai ƙarshen sura sai ya kamo wata surar ma ya karanta, shikam ayau bashi ma da bakin da zaiyiwa Allah godiya, tabbas tsarki ya tabbata ga Allah Ubangiji, majin ƙan kowani bawa, me amsa addu'a, me cuta me kuma waraka da yayewa, sarkin da babu kamarsa, mamallakin abun dake fili da ma wanda ke ɓoye.
Sosai yake karantun, tun muryarsa naÉ—an fita har yazamana ko ya motsa bakinsa muryarsa baya fita, saboda yanda kansa ke masifaffen ciwo, ga kuma ciwon bayan nasa daya tsananta,
Wasu irin hawayene suka silalo daga cikin idanunsa, alokacin da yaji ƙiran sallan asuba acikin kunnensa, wanda rabonsa da jin hakan yau sama da shekara 20 kenan, tun yana ɗan shekara 13 rabanso daji da mgna, lokacin Hayatuddeen bai cika shekara uku bama a duniya wani irin kuka ya fashe dashi mai tsuma zuciya, take kuma ya zamo daga kan gadon, durƙushewa yayi ƙasan tiles tare dayin sujjada, ya kuma fashewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya, me zaicewa mahaliccinsa? wani irin godiya zaiyi masa? haƙiƙa bashi da wannan bakin, saida yayi kuka sosai, sannan ya ɗago daga sujjadar, adaddafe ya shiga toilet ya ɗauro alwala yana fito ya zura jallabiya bisa gajeren wondon da ya saka,
sallah raka'a biyu yayi, ko acikin sallan saida yayi kuka sosai, haka da zazzaƙar muryarsa ya dinga yiwa Allah kirari da sunayensa tsarkaka, yana idar da sallan, yaɗan janyo jikinsa ya jingina da bango, hannunsa yakai yaɗan taɓa Zaleeha, gani yayi komai nata asake yake gashi kuma bata numfashi, hawayen tsananin tausayinta da kuma ƙarin ƙaunarta ne suka kwaranyo daga cikin idanunsa, hannunta ya kama ya riƙe gam, haka yakeji kaman ya maida ita cikin jikinsa. Tabbas Zaleeha rayuwarsa ce, itace silan komai na nakasarsa, itace gaba ɗaya duniyarsa kuma yanzuma gashi itace silar warakanshi. Samunta HASKE ne acikin rayuwarsa. Jin ana ƙoƙarin shiga sallan asuba, yasa adaddafe yayi sallan dan bayajin zai iya zuwa masallaci, saboda ko zama me kyau baya iyawa, koda yazo yin sallan ma saida yaɗan jingina, saboda yanda jiri da kuma zazzaɓi me zafi da suka rufeshi ga ƙugunshi da yakeji kamar ya ida gwamɓalewa, idan yayi sujjada kuwa da ƙyar yake iya ɗagowa, saboda yanda bayansa ke riƙewa.
Yana idar da sallan, adaddafe yajawo kekensa ya hau, ko iya jingina bayansa da kyau bayayi, saboda yanda yakeji, haka ya nufi sashin Ummi, yana ganin dishi-dishi a idanunsa. Da ƙyar ma ya iya bude ƙofar falon yashiga, babu kowa afalon, kaitsaye ɗakin Umminsa ya nufa, jikinsa gaba ɗaya ba ƙarfi, hakan yasa ahankali ya ɗan murɗa handle ɗin ƙofar, jin ƙofar arufe gam yasashi, juyawa, ya nufi ɗakin Hayatuddeen yana zuwa kuwa, ya samu ƙofar abuɗe, koda ya shiga ɗakin bai taradda Hayatuddeen ba, da alama baidawo a masallaci ba. Ƙarasawa cikin ɗakin yayi, inda yaɗan zamo daga kan kekensa, akan lallausan gadon Hayatuddeen ɗin ya kwanta, tare da jawo blanket ya rufa ajikinsa, har yanzu jikinsa rawan sanyi yake, saboda tsabar karkarwan da jikinsa keyi kuwa, hatta gadon ma saida ya ɗauka.
Hayatuddeen kuwa tare da Ahmad suka dawo daga masallaci, sai faman zuba hamma yake dan bacci bai ishesa ba.

Kai tsaye ɗakin Ummi suka nufa, Hayatuddeen ne yayi knocking, Ummi wanda idar da sallanta kenan tasowa tayi ta buɗe ƙofan dan tasan bazai wuce suɗin ba, cikin girmamawa Ahmad ya durƙusa ya gaisheta, fuska asake ta amsa masa, Hayatuddeen kuwa cikin gigin bacci ya gaisheta, amsa masa tayi tare daɗan ranƙwashin kansa, murmushi sukayi su duka, sannan Ahmad ya juya ya haura sama, shi kuwa Hayatuddeen juyawa yayi ya nufi ɗakinsa.

Yana shiga kuwa ya ja kofar ya rufe, juyowan da zaiyi ne idanunsa suka sauƙa akan wheelchair ɗin Saifuddeen, da kuma shi kansa Saifuddeen ɗin dake kwance yana ta masassara, har kana iya jiyo hucin numfashinsa daga bakin ƙofar ɗakin. Idanu Hayatuddeen ya zazzaro, atsorace ya ɗan dafe ƙirjinsa, cikin sauri ya juya ya fice daga ɗakin har yanacin tuntuɓe.
"Ummi! Ummi!! Ummmee"
Haka yake ƙiran sunan Ummi da ƙarfi.
Ummi dake zaune aɗaki jin yanda Hayatuddeen ke ƙiranta, yasa taji gabanta ya faɗi haka yasa jiki na rawa ta miƙe ta buɗe ƙofar ɗakin jin yadda Hayatuddeen ke danna mata kira babu ƙaƙƙawautawa, tana saƙo kanta woje shi kuma yana sako kansa ciki haka yasa sukayi kiciɓis a bakin ƙofar.
A birkice Hayatuddeen ya kamo hannunta cikin firgita yace.
"Ummi Hamma Saifuddeen! zo muje kiga Hamma a É—akina baida lfy sai rawan sanyi yakeyi".
A take Ummi taji wani zufa ta karyo mata haka nan taji jikinta na rawa, dan kuwa mafarkin da tayi daren jiya ne ya faɗo mata wai ƙugun Saifuddeen ɗinta ya ida gwambulewa.
Cikin sauri tabi bayan Hayatuddeen.
Ahmad kuwa har ya haura sama jin yadda Hayatuddeen ke ƙiran Ummi a gigicene ya sashi juyowa zai sauko dan hakanan yaji a jikinsa cewa ba lafiya ba.
Chapter 123 · 0% Book details