← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 154

Sashe 55

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yauma tana gidan su Aishan kasan cewar yau jumma'a ne bayan an sauƙo daga sallan jumma'an ne Man Liman ya iske su a tsakar gida ƙarƙashin bishiyar ceɗiya bisa dukkan alamu suma sallan sukayi.
Cikin girmamawa suka haÉ—a baki wurin ce mishi.
"Baffa sannu da dawowa."
Murmushi yayi tare da miƙa musu ledan cefen da ke hannunshi tare da ce musu.
"Yauwa sannunku tagwayen Baffa, kunyi sallanko?."
Murmushi sukayi tare da gyaÉ—a mishi kai alamun eh.
Man Liman dattijone me karamcin gaske,
Har ya wuce sai kuma ya juyo ya kalli Zaleeha cikin fullanci yace.
"Zaleehatu taho ki ɗan rubuta min wani abu, ke kuma Aisha wonke allon ƙarfen can ki miƙo min."
Da sauri sukace to tare da miƙewa.
A hankali Zaleeha ta shiga sashin baffa,
kan taburma ta sameshi bisa farin buzunshi, gefenshi ya nuna mata tare da cewa.
"Zauna nan wasiƙa zaki rubuta min zuwa ga sarkin numan, dan arnan garin sun samu a gaba."
Cikin ganin girman dottijon tace to.
Kana ya gaya mata duk abinda zata rubuta, ta rubuta mishi sannan ya kira wani É—anshi ya kaiwa É—an aikensu takardar.
Har ta yunƙura zata tashi sai kuma ta koma ta zauna jin yace.
"A a zauna Zaleehatu ban gama da keba."
Murmushi tayi tare da cewa.
"To". Gyara zamanshi yayi da kyau ya fuskanceta kana a hankali yace.
"Zaleeha."
jin yadda ya kirata yasa ta amsa a nitse, cikin kulawa yace.
"In na tambayeki wani abu zaki gaya min gaskiya, kuma. Sannan ban miki shisshigi bako?."
Da sauri ta jujjuya kanta tare da cewa.
"In sha Allah zan gaya maka iya gskyar da na sani. Kuma ka tambayeni duk abin da kakeso dan ka isa katambayenin."
Gyaran murya yayi tare da cewa.
"Ke Æ´ar wanne garine?."
Cikin nitsuwa tace.
"Baffa ni bagombiyace."
Kai ya gyaÉ—a cikin gamsuwa kana yace.
"Me sunan mahaifinki?."
a take idanunta suka cika da hawaye, murya na rawa tace.
"Sunan babana Malam Bashir Sulaiman Dukku."
Fuska cike da al'ajabi Man Liman yace.
"ikon Allah Malam Bashiru ne mahaifinki?".
cin mmki tace.
"Baffa ka sanshi ne?".
Kai ya jujjuya mata tare da cewa.
"Eh to ba a zahiri na sanshiba ina dai jin azuzzukan shi, a radio, shiyasa bai zama ɓoyeyyen mutunba".
Sai kuma ya gyara zama tare da zuba mata ido cikin kula yace.
"To amman meyasaki daga tambayar sunashi kika fara zubda hawaye?, kuma meya kawoki nan cikin arna kika zauna Zaleehatu gaya min meyasa?."
Hannunta tasa ta share hawayenta dake zuba tanajisa kamar matsayin Babanta mahaifi, cikin rawar murya ta bashi labarin duk abinda ya faru na sanadin gudowanta har kwana a gardin da takeyi bata ɓoye mishiba, ta ƙara da cewa.
"Ina so in koma in je in bawa Baba malam haƙuri inyi mishi biyayya kan zaɓin dayamin amman ji nake bazan iyaba gani nake kamar in na koma zan mutu, nasan babana da ƴan uwana duk sunyi fushi dani".
Nisawa yayi tare da gyara zama cikin kula yace.
"Ae bazaki komaba Zaleehatu sabida kafa akayi anan matuƙar ba'a karya sihirin dake jikinki ba, haka bazaki iya yiwa mahaifinki biyayya, kuma dolene yasa kikayi ta gudun ɗakinki kina kwana cikin ciyawayi, domin an miki turen sihiri a ƙarƙashin gadonki, muddin ba'a karya sihirinba ɗakin zaike miki duhu zaina baki tsoro, kuma sihirin da akayi miki kin maganshi a mafarki sai in kin manta ne koda yake an rufe bakinma bazaki iya faɗiwa ko abinda kikeji ba, nima kaina yau tsawon wata uku kenan ina miki tofi cikin abincin da ake mishi shiyasa kika samu damar min bayani da izinin Allah."
Shiru tayi cikin sanyi tace.
"Baffa bana son mijin da aka haÉ—ani dashi wanda nacema ya taimakenin nan shine nakeso."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Kada ki damu, dukkan wani farin cikinki yana ƙarƙashin inuwar mijin da aka aura miki, na nemi al'farma kada ki sake cewa bakya son mijinki, kuma kada ki sake cewa akwai wanda kikeso bayanshi kisa a ranki shine ya taimakeki kuma dashi aka haɗaki, sai kici gaba da yiwa shi wancan ɗin addu'ar Allah ya azirtashi da mafificiyar al'janna Allah ya taimakeshi fiye da yadda ya taimakeki, Allah yasa soyayyarshi a zuciyar maƙiyanshi soyayya ta rinjaƴi ƙiyayyarsa a zuƙatan makusan tansa wlh in kin masa haka kin gama mishi komai sannan in kin yiwa mahaifinki biyayya zaki samu dukkan salama. Kiyi min wannan al'ƙawarin ni kuwa daga yawau zan fara baki addu'oi insha Allah zaki rabu da duk wani sihiri kuma zaki koma ɗakinki."
Cikin jin sanyin da tunda ta gudo bataji ba tace.
"To baffa in sha Allah zanyi ta mishi addu'a, ngd da taimako."
Murmushi yayi kana a hankali yace.
"Akwai wacce ke zuga mahaifiyarki, kuma ta asirce mahaifiyarki ne, da bata isa ta mata musuba,duk abinda tasata ko bata so sai tayi, amman ina karya abin jikinki itama abinda ke jikinta zai karye domin sunan ALLAH a duk inda take zaije ya sameta".
Ganin tayi shiru ne ya sashi É—an sahir tawa tare da cewa.
"Ko Mamanki bata da yar uwa da suke tare".
A hankali ta gyaÉ—a mishi kai tare da.
"Tana dasu É—aya musul mace É—aya kuwa arniya ce".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ba Shatuba ai ita hasken addini na jikinta da zuciyarta, ita É—ayar dai domin ita burinta Mamanku daku yaranta duk kuyi ridda ku koma addininsu, to kuma ya rigada Allah ya tsareku kana mahaifinku a tsaye yake a kanku kun kuma samu cikakkiyar tarbiya."
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Akwai kuma ƙawayenki cikinsu wacca kikafi so ɗin ita ke cin dunduniyarki, amman da zaran kin samu waraka da abinda akayi miki, keda kanki zakiji bakya son mu'amala da ita".
Cikin mutuwan jiki tace.
"Baffa ina son komawa gida".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Zaki koma in sha Allah, yanzu zamu fara addu'oi tsawon sati biyu, daga randa zamu fara miki rubutu kina sha kuma duk mafarkin da kikayi ki sanarmin".
Kai ta gyaÉ—a alamar to.
Hahira sukayi sosai da Baffa'n, nan ta ƙara faiyace mishi irin yanayin da takejin kanta aciki, wanda sau da yawa tanajin son komawa gida aranta, amma saita najin kaman kafata agarin akayi, cikin son kwantar mata da hankali Baffa'n yace.
"Insha Allah zai taimaka mata da wasu addu'o'i wanda zatana sha, da kuma wanda zata nayi."
Nan dai tayi masa godiya sosai, dan ita kanta tanajin son komawa gida acikin ranta.

Bayan wasu ƴan kwanaki ne kuma Baffan yasa, Aisha tayi ƙiranta, nan yabata wani ruwan addu'a yace tana sha tana shafawa jikinta.

Sai kuma haɗin ayatushshifa da ganyen magarya guda bakwai, da kuma zam-zam, yace tana amfani dasu, ƙara jaddada mata yawan yin azkar da kuma zama da al'wala yayi, nan dai tayi masa godiya sosai.
Cikin ikon Allah kuwa yau kwananta biyu da fara amfani da maganin, sannan kuma tanajin sauƙin wasu abubuwan.
Gashi daren jiya ne Adda Maryam taƙirata awaya, sosai kuma tayi mata nasiha, mai ratsa jiki, wanda kalamanta suka ƙara sanyawa taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi.

A gefen Solomon da matarsa kuwa zaman Zaleeha a gidansu yasa hasken addinin musulunci yana ratsa zuƙatansu, suna ganin daraja da kimar addinin musulunci fiye da nasu addinin har an kai matin da yanzu sun fara watsi da addininsu dan sai ayi lahadi uku basuje majami'arsuba, zuwa yanzu Zaleeha kuwa tana tallata musu addinin dayi musu tayi su shiga domin shine hanyar tsira, kana tana ƙyautata musu sosai da kuɗin dake hannunta irin kyautatawar da musulunci ya umarci musulmi yayiwa ahlul kitab dan da kyautata zasu ƙaunaci addinin su san addinine mai sauƙi da tausayawa, to zuwa yanzu dai Zaleeha na zaton musuluntar su Solomon da elizabet a ko wanne lokoci.

Kwanci tashi babu wuya, inda yanzu cikin Ameena yakai wata bakwai, sosai kuma yayi girma, dan kuwa zuwa yanzu daƙyar ma take iya taka ƙafafunta, dan sun kumbura sosai, saikace me haihuwa yau ko gobe, wannan daliline yasa ta ɗauki hutu awajen aikinsu, Ummi ne ke bata kulawa sosai.
Ɓangaren Adda Maryam ma kuwa yanzu cikinta nada wata shida itama, saidai girman cikin nata baikai na Ameena ba.

Yau tunsafe da ta tashi takejin wani irin matsanancin ciwon mara, haka takejin bayanta ya riƙe ƙam, gashi ƙafarta ta sake kumburi, da ƙyar dai take iya takawa, haka ta lallaɓa ta nufi ɓangaren Ummi tana zuwa kuwa ta iskesu zaune afalo, zama tayi itama tana cije laɓɓanta, ganin haka yasa Ummi da kanta ta haɗa mata emptyn shayi me zafi ta bata tace tasha.
Tana sha kuwa tariƙe bayanta da takejinsa kaman zai ɓalle, Ummi da Raliya ne sukayo kanta, abu kaman wasa fa saiga naƙuda ya tashiwa Ameena gadan gadan, nan Ummi ta ka mata, inda ita da Raliya suka sanyata amota,
hankalinsa Saifuddeen a tashe ya shiga motar yana tsoron abinda zai sami É—anshi tunda yasan cikin bai kai haihuwa ba.
Ahmad ne yayi driving ɗinsu zuwa Medical center, suna zuwa kuwa abokan aikinta suka karɓeta hannu bibbiyu nan aka wuce da ita labour room.
Jigum-jigum haka su Ummi sukayi suna mejiran sakamako, hankalin Ummi atashe yake sosai, musamman da likitotin suka tabbatar musu da cewa haihuwace Ameenan zatayi, ma'ana É—an abakwaini zaizo.

Da shigar da Ameena labour room ko 40 minute ba a rufa ba, wata nurse ta fito inda take sanar musu da cewa. "Ameenan ta haihu ta haifi ɗa namiji, kuma daga ita har yaron dukansu suna cikin ƙoshin lafiya."
Wannan magana ita tasanya dariya ya wanzu akan fuskokin su Ummi, Saifuddeen kuwa hamdala yayi tare da É—aga hannunsa sama ya godewa Allah.
Nan Ummi tashiga ƙiran ƴan uwa da abokan arziki tana sanar musu, ana fito da Ameena zuwa ɗakin hutu kuwa, nurse ɗin tace zasu iya shiga.
Suna shiga ɗakin wata nurse ta miƙowa Ummi yaron, hawayene suka cika idanun Ummi abayyane tace.
"Alhamdulillah, masha Allah."
Saboda tsananin kaman Saifuddeen É—inta da ta hango akan fuskar yaron, gashi yaron kamar ba bakwaini ba, dan yana da girmansa, tsabar fari kuwa har saida yayi wani jaja-jaja.
Miƙawa Saifuddeen tayi ya amshi yaron yana mejin tarin ƙaunarsa acikin ransa, rumgume yaron yayi aƙirjinsa yana murmushi, bayan yayi wa yaron huɗuba da ƙiran sallah acikin kunnensa.
Nan dai Su Adda Rahama da Raliya suka amshi yaron suma suna yabawa da irin kyautar da Allah yayi musu.
Chapter 55 · 0% Book details