← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 154

Sashe 51

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummi kuwa murmushi take, dan tagama fahimtan komai, tabbas tasan cewa Saifuddeen baison wahala ko kaɗan, wannan dalilin shiyasa ma wata ƙila zazzaɓi ya sauƙar masa.
Yana gama shan maltina'n Raliya ta kawo masa, haÉ—aÉ—É—en fruit salad wanda yaji madara.
Balaifi ya É—an sha, ya kuma ji daÉ—in bakinsa.
Dubansa Ummi tayi cikin kulawa tace.
"Kasamu kayi wanka, kuje asibiti likita ya dubaka, ko kuma ma zan ƙira Dr Adnan kawai yazo ya dubamin kai agida."
Tana gama faɗan haka ta miƙe tsaye, nan ta fice daga cikin ɗakin,  kana Raliya ma ta rufa mata baya.
Ahmad ma binsu yayi, Hayatuddeen kuwa hannun Hamman nasa ya kamo, cikin kulawa yace.
"Sannu My lovely Hamma Allah yabaka lafiya."
Kai Saifuddeen ya jinjina masa alaman "Ameen."
Nan Hayatuddeen ɗin ya miƙe yafice daga cikin ɗakin.

Ajiyar zuciya Ameena ta sauƙe, tare da takowa taƙaraso kusa dashi, zama tayi agab dashi, cikin kulawa ta kamo hannunsa,  fuskarsa ta shafa tare da cewa.
"Ya jikin naka?"
Kansa yaÉ—an jinjina mata, alaman.
"Dasauƙi"  tare da ɗan mako hannunta yayi kissing bayan hannun, sannan ya janye fuskarsa  baya.
Jawo wheelchair É—insa yayi ya hau, ahankali ya tura kansa zuwa toilet.

Ajiyar zuciya Ameena ta sauƙe, hartayi tunanin binsa cikin toilet ɗin kuma saita fasa,   nan dai tayi kwance akan gadon, lumshe idanunta tayi, tana me tuno moment dinsu na daren jiya, hannunta takai kan mararta, asanyaye tace.
"Ya Allah kasa adaren jiya nasamu rabo daga Saifuddeen, tabbas kuwa da sainafi kowa farinciki, domin samun iri daga Saifuddeen babban abun al'fahari ne,  sannan kuma zan zama kamar zara acikin taurari, dan haihuwa da Saifuddeen babban nasara ce, ya Allah kabani ɗa ko ƴa me kama dashi."
Cikin farin ciki ta amsawa kanta da "Ameen."

Saifuddeen kuwa balaifi yaÉ—anji dama, sake wanka yayi tare dayin brush, nan yafito jikinsa duk danshin ruwa, harzuwa lokacin Ameena na kwance, kasancewar wani É—an bacci-bacci ne ke fusgarta.
Tsane jikinsa yayi, inda ya shirya kansa cikin wasu lafiyayyun riga da wando ƴan kanti masu tsadar gaske, sosai yayi kyau cikin kayan,  wankan turare yayiwa jikinsa,  wasu baƙaƙen toms yasanya aƙafansa, masu kamar combat, gashin kansa sai ƙyalli yake, wayansa ya ɗauka, nan yaƙaraso jikin gadon, ahankali yaɗan leƙa fuskar Ameena, gani yayi ma baccinta take cikin kwanciyar hankali.
Kansa ya jinjina tare da yin É—an murmushi cikin zuciyarsa yace.
"Badole kiyi bacci ba, tun da dai daren jiya kinsamu ɗan bawan Allah kin gurza."  
tura kekensa yayi inda ya fice daga cikin É—akin.

Cikin nutsuwa ya nufi part ɗin Ummin nasa, koda Ummi tagansa taji daɗi sosai, duk da cewa zazzaɓin baisakesa duka ba amma dai yaɗanji sauƙi, kwanciya yayi afalon, Ahmad dake zaune afalon ne ya matso kusa dashi.
Duban Saifuddeen ɗin yayi cikin ƙasa da murya yace.
"Ango kasha mai, to yaya yakaji auren da daÉ—i ko?"
Cikin takaici Saifuddeen ya É—auki pillow'n kujera ya gwaÉ—awa Ahmad É—in, dariya Ahmad yayi, tare da cewa.
"Daga faɗan gaskiya kawai, ai kuwa dai wannan amarya taka jaruma ce, saboda haka ka ƙara riƙeta da kyau, kaikuma saika tsaya adubaka,  saboda dai yanzu kam kafita sahun saurayi kadawo bazawari!."
Cikin tsokana Ahmad ya ƙare maganar, sanin cewa ya hasala Saifuddeen ɗinne yasashi matsawa gefen cikin sauri, dan yasan yanzu Saifuddeen ɗin zaikai masa duka.
Saifuddeen kuwa sosai ya ƙulu, hakan yasa yadinga cije laɓɓansa, yana hararan Ahmad, Ahmad kuwa mezaiyi inba dariya ba.
Suna haka Dr Adnan ya iso, dan Ummi taƙirasa, inda tasanar dashi matsalan Saifuddeen ɗin.
Sosai Dr Adnan din yayi checking dinsa, ganin komai lafiya yasashi, rubutawa Saifuddeen ɗin magunguna, nan ya miƙawa Ahmad yace "Yaje pharmacy ya sayo."  
bakomai yasa masa zazzaɓin ba kuwa face, yanayin daya samu kansa aciki wanda bai taɓa ba, hasali kuma hakan yafarune bawai don bashida lafiya ba,  ko wasu masu lafiyan sukan samu kansu cikin irin condition ɗin da Saifuddeen yasamu kansa,  musamman idan hakan yazama shine farkon fara sex ɗinsu, sannan hakan na faruwa idan Namiji yaɗauki tsawon lokaci yanajin sha'awa, sannan kuma bai samu yayi sex ba, to aduk lokacin da yayi sex da mace, yana zubar da sperm zazzaɓi  me zafi zai iya rufesa, wanda kuma zai iya sauƙa akowani lokaci.
Nan dai Dr Adnan yayi masa fatan sauƙi daga, haka yayiwa Ummi sallama ya tafi.
Cikin mintuna kaÉ—an kuwa Ahmad ya kawo maganin, shida kansa ya bawa Saifuddeen din magungunan yasha.

Haka dai Saifuddeen ya ƙare, gaba ɗaya wunin yau  a part ɗin  Ummin sa, ba laifi kuma yaji sauƙin jikinnasa sosai.           

Can cikin Gombe State University kuwa Hayatuddeen ne ke zaune acikin class, inda gaba ɗaya fiye da rabin ɗaliban ajin nasu ke waje, kasancewar sun ƙarƙare lecture ɗinsu na wannan ranan,   can ƙarshen benci yaje ya takure kansa, wayarsa ƙirar iphone 8+ ne ahanunsa, yayinda ya saƙala earpiece akunnensa,  gaba ɗaya yaba da hankali haɗi da nutsuwarsa ga wayarsa, da dukkan alama wani abu yake kallo wanda ya ɗauke masa hankali.           
Khamis dake tsaye akansa tun ɗazu batare da, Hayatuddeen din  yasan da zuwansa ba ne yasaki dariya, azabure Hayatuddeen ya ɗago kansa, ganin Khamis yasashi, sakin wata irin ajiyar zuciya me ƙarfi, aɗan hasale yace. 
"Mcheeww wallahi Khamis kai banza ne ji ka tsoratani."     
Murmushi Khamis yayi tare da zama agefen Hayatuddeen ɗin, hannu yasa ya dafa kafaɗan sa, dubansa yayi tare da cewa.   
"Kai wallahi tsoronka yayi yawa, menene to acikin BF da har ma sai ka ɓuya kake kallonsa, hmmm yaro inzakasha giya kasha ta dubu, kaine har yanzu kanka bai gama wayewa ba, har yanzu fa baka iya ko riƙe hannun mace, iya iskancinka ya ƙare a waya, daga anyi magana kace kai bazaka iya ba, mufa yanzu mune manyan gobe, yanzu ne ya kamata ace munci ƙuruciyar mu, mun shana, sannan muyi abun da mukeso." 
         
Iska Hayatuddeen ya fesar ta bakinsa,  girgiza kansa yayi tare da   cewa.                  
"Bazan iyaba Khamis, ni sam bazan taɓa iya aikata haka ba, insha Allah har duniya ta tashi bazan taɓa yarda nakusanci zina ba, kasan girman zunubin wanda ya aikata zina kuwa Khamis?  hmmm nikam dai ba ruwana, iskancina a iyaka waya ya tsaya kamar yanda ka faɗa da farko, amma taɓa jikin wata mace, wanda ba muharamma ta ba gaskiya bazan iya ba."     
Hararansa Khamis yayi tare da cewa. 
"Shiyasa nace bazaka taɓa wayewa ba, yanzu mene amfanin kallon BF matuƙar bazakanemi inda zaka gusar da sha'awan ka ba? hmmm nidai wallahi shanawa ma yanzu na fara ehe."     
Murmushi kawai Hayatuddeen yayi tare da playing vedio'n sa ya cigaba da kallo, yana mejin wani irin abu acikin jikinsa, sau dayawa yakanji kamar ya daina kallo, amma kuma zama da Khamis yasa kallon BF ya zame masa tamkar wani kallon film, yayi sabo da ganin BF sosai, saboda haka koda yace zai daina sai yaji ya kasa, duk da cewa yasan kallon BF din ba kyau, amma sosai idan yana kallo yakejin kansa cikin wani irin shauƙi, saboda  yanajin cewa shima yanzu yazama saurayi shekara 20 da yake dasu, sunsa yanajin kansa kaman ɗan 30 years.
Shida kansa yasan da taraiyar sa da su Imran tafi mishi daɗi da al'khairi to abin ta kaicin Imran F.C.E yake Sulaiman kuma da Isma'il Kashere University suke. Zakariyya kuma da yake nan cikin G.S.U ɗin sai kuma ya kasance Department ɗinsu ba ɗayaba, tofa wannan dalilin ne ya rabashi da tsoffin abokansa a makaranta ya haɗashi da wannan ɗan banzan khamis ɗin mai ƙafafu kamar faskaren wawa.

Wannan yana É—aya daga cikin illar abokai, dole iyaye mu lura da abokan yaranmu muddin sun fara tasawa.
Zakiyi shekara 14 kina bawa ɗanki/ƴarki tarbiya mai inƙanci to. Tofa daga shekara 15 zuwa 18 akai ashirin zaki fara yaƙi da gasa da abokanshi da zasu fara bashi tasu tarbiyar da in kinyi sakaci da addu'a dasa ido cikin awa ɗaya zasu kore taki tarbiyar nan su ɗaura tasu, shike nan sunyi nasara a kanki sun cuci rayuwar yaronki damake kanki, hattara garemu iyaye mu kula...!

Tashi tsaye Khamis yayi tare da cewa. 
  "Saika tayi ae, kazauna nan a haka kada ka nemi ƙarin wayewa akan wanda kake dashi, ni kaga ma tafiyata, saboda yau ƙarfe 7 dai-dai muna da wani show me zafi a night club, nasan ma idan nace kazo ba zuwa zakayi ba."                  
Kai Hayatuddeen ya jinjina tare da cewa.       
"Saimun haɗe gobe, danni ma nasan driver ya kusa zuwa ɗauka na,  aje night club lafiya amman banda ni kam, bazanci amanar hamma da Ummynmu ba."       
Dukan wasa Khamis ya kai masa, sannan ya juya ya fice daga cikin class ɗin.                 
Bawani jimawa shima Hayatuddeen ɗin, sule driver yazo ya ɗaukeshi.                           

Ƙarfe takwas na dare dai-dai  yadawo daga masallaci, kaitsaye part ɗinsa ya wuce, kasancewar akwai wani aikin sirri wanda zai gabatar, domin ansashi binciken wani riƙaƙƙen ɗan fashi, wanda ya addabi mutane, sannan kuma har zuwa yau ankasa gano inda yake, saboda hakane ma aka danƙawa Saifuddeen ɗin ragamar case ɗin ahanunnsa, kasancewar sun san ya ƙware wajen iya computer, da computer kaɗai zai iya gano musu inda mutumin yake.          
Yana  shiga ɗaki kayan jikinsa ya soma ragewa, inda ya zauna daga shi sai 3 guater da kuma farar singlet, laptop ɗinsa ya jawo tare da sanyata  gaba, nan ya maida gaba ɗaya hankalinsa ga aikin da yakeyi.             
Chapter 51 · 0% Book details