← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 154

Sashe 114

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washe gari kuwa tun ƙiran sallan asuban fari ya buɗe idanunsa, ɗan jim yayi tare da zubamawa Zaleeha kyawawan idanunsa, wanda take baccinta cikin nutsuwa da kuma kwanciyar hankali, gaba ɗaya ta wani shigewa jikinsa. Ɗan murmushi yayi tare da lumshe idanunsa, ahankali yaɗan zareta daga jikinsa,
yunƙura yayi inda ya tashi zaune, wheelchair ɗinsa ya jawo, saida ya hau sannan yakai hannunsa jikin Zaleehan yaɗan taɓa ta, kasancewar bata da nauyin bacci, hakan yasa asakalce ta ɗan buɗe idanunta, ƙaramin bakinta ta turo gaba, tare da kwaɓe fuska, kansa kawai ya girgiza, cikin body language ɗinsa yace.
"Sarkin bacci, wato kinsamu jiki na me daɗi, shine harda wani narkemin da maƙalemi harda minshari kikeyi ko, to sai kitashi kiyi sallah." Ya ƙare yanayin maganar tasa yana me ɗan yi mata hararan wasa, kana ya juya yafice daga cikin ɗakin.
Ganin fitansa yasa ta sake shagwaɓe fuska, cikin sakalci tace. "Nima ai dai jikina me daɗi ne ehe, kuma kaima ai kasan hakan, tunda saida ka riƙeni sannan ka iya bacci."
Cike da kasala ta sauƙo daga kan gadon, kaitsaye toilet ta wuce, wanka tayi sannan ta ɗauro alwala. Ɓangaren Saifuddeen ma hakance ta kasance, dan yana fita daga ɗakin nata, kaitsaye ɗakinsa ya wuce, wanka yayi sannan yayi alwala, wata brown ɗin jallabiya ya sanya, sannan ya fice zuwa masallaci.

Zaleeha kuwa koda ta idar da sallah, karatun Alkur'ani taɗan taɓa kaɗan, sannan ta miƙe, sama sama ta shafa mai ajikinta, sannan tabi ko ina na jikinta da body spray me daɗin ƙamshi, wani lallausan yadi tasanya ajikinta, wanda yaji ɗinkin riga da sket pencil, sosai kayan yayi mata kyau, kana kuma ya fitar da shape ɗin jikinta, kasancewar yadin mai kalan shuɗi da kuma ratsin pink, hakan yasa farar fatarta ya bayyana sosai, simple meckup tayi akan fuskarta, sannan ta kafa ɗaurin ɗan kwali wanda yayi matuƙar zama akanta sosai, wani ɗan siririn vail mai kalan pink ta yafa daga kanta zuwa ƙirjinta, tayi kyau sosai, ita kanta da ta ga kanta acikin madubi saida ta saki murmushi. Wayarta kawai ta ɗauka sannan ta nufi sashin Ummi.
Kasancewar ta ɗan makara wajen fitowa yasa ta tarar har Raleeya ta shiga kitchine, tamaci kusan rabin aikin, inda gefe guda kuma Ameena ke taya ta, suna ɗan taɓa hiransu,
cikinsu ta shiga tare da kama musu aikin, Ameena ce ta dubeta cikin kulawa tace. "Masha Allah Auntyn Adeel kinga yanda kikayi kyau kuwa."
Murmushi tayi wanda har saida dimple ɗinta suka ɗan lotsa, cikin zazzaƙan muryarta tace. "Nagode sosai." Murmushi sukayi dukansu, nan suka ci gaba da aikin, cikin mintuna kaɗan suka kammala break fast ɗin, Zaleeha da Raleeya ne suka jere duka abincin akan dinning area, inda Ameena kuwa ta dawo cikin falon ta zauna nan kusa da Ummi da kuma Ahmad suna hira, Adeel dake hannun Ahmad kuwa sai wasan sa yake. Tsaye take tana ƙara gyara dinning area'n, ƙamshin turarensa da tajine yasata ɗan ɗago kanta, karab kuwa idanunsu suka faɗa cikin na juna, sosai yasha kyau cikin bugaggigar shaddan dake jikinsa, mai kalan shuɗi, wato kalan kayan Zaleeha'n kenan, yayi kyau matuƙa, fuskarsa sai ƙyalli take, kanta taɗan kawar gefe tare da turo bakinta gaba, cikin zuciyarta tace.
"Kujisa dai har da wani sa irin kayana, ko wa yace masa yasama oho, thank god ma saida nasa kafun yasa, da sai ace na kwaikwayeshi."
Ta ƙare maganar zucin nata tana ɗan jujjuya bakinta.
Wani irin murmushi yayi tare daÉ—an lumshe idanunsa, kana ya buÉ—esu alokaci guda, yajima yana zargin cewa zuciyoyinsu da jininsu haÉ—e suke awaje guda, baikuma gaskata hakan ba, sai ayanzu da gaba É—aya tunani da kuma hankalinsa sun sanar dashi abun da take faÉ—i acikin zuciyarta.
Ƙura mata ido yayi, itakuwa ɗan ɗago kai tayi, ganin cewa har yanzu kallonta yake, yasa afakaice taɗan murguɗa masa baki.
Dariya ne yaso kamasa, wanda hakan yasa duk hankalin su Ummi ya dawo kansa, shikuwa yanayin yanda tayi da bakin nata ne yayi matuƙar burgesa, murmushin daya bayyana fararen haƙwaransa yayi, tare da ɗan hararan da taɓe baki sam baisan cewa hankalin su Ummi na kansu ba, su Ummi da Ameena kuwa ganin inda Saifuddeen ɗin ke kallo, yasa suma ɗan juyawa, ganin cewa Zaleeha yake kallo yasa Ameena yin ƙasa da kanta, cikin ranta tasoma ambaton sunan Allah, saboda wani abu da taji acikin ranta, Ummi kuwa girgiza kai kawai tayi tana murmushi. Miƙewa tayi tare da cewa.
"To maza kutashi muje muyi break, kunsan yau jumma'a, kana zaune saidai kaga lokaci ya tafi."
Babu musu haka dukansu suka ƙarasa kan dinning ɗin, Hayatuddeen sai fama suɗe baki yake. Zaleehan ce tayi seving ɗinsu, sannan itama tayi seving ɗin kanta. Haka sukai break fast ɗin cikin nutsuwa, har suka kammala, Ita da Raleeya ne suka kwashe kayan suka kai kitchine, sannan suka tsabdace dinning area'n, Saifuddeen ne yace Hayatuddeen ya taso yana so ya rakasa wani waje.
Hakanan yaji gabansa yaɗan faɗi, amma sai ya dake, miƙewa yayi, ya bi bayan Hamman nasa, wanda tuntuni yayi gaba.

Ameena kuwa miƙewa tayi, cikin yanayi naɗan gajiya tace. "Ummi zan shiga naɗan kwanta, wallahi nagaji sosai, ahakan ma waidan guduwa nayi lokacin tashina baiyi ba, dana zauna kam da ni dana dawo sai 8 to 9." Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ai ma kuna ƙoƙari Ameena, night duty ai akwai wahala, jeki kwanta abunki kawo Adeel ɗin sai ariƙe mikishi, kinsan idan kika tafi dashi ma, hanaki bacci zaiyi wannan yaron naku da rigimarsa." Cikin jin daɗin kulawar Ummin gareta ta miƙowa Ummin Adeel, sannan ta wuce sashinta, dan har wani dishi-dishi take gani a idanunta, saboda rashin samun wadataccen bacci.

Su Zaleeha kuwa anan falon Ummin suka zauna, inda ta karɓi Adeel tanayi masa wasa, hira sukayi sosai kafun Ummi ma ta tashi ta wuce ɗaki.
Chapter 114 · 0% Book details