Sashe 37
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sallama Hayatuddeen ya shigo cikin falon Ummi, ganin su azaune ga kuma Hammansa daya haɗe fuska, yasan yashi ƙarasowa cikin falon, jakar makaranta da kuma littatafan dake hannunsa ya watsa akan kujera, zama yayi daɓas akan sofa, tare da miƙe ƙafafunsa, cikin shagwaɓa haɗi da kasala ya ɗago indo ya dubi Ummi, asangarce yace.
"Ummi am so tired, ƙafana bayana kaina idona kunennena ɗuwawuna kai ko'ina ɗina ma ciwo suke min!."
Murmushi Ummi tayi, tare da cewa.
"To sannu auta na, ae dai ku kam gaba É—ayan ku haka kuke, abu kaÉ—an ke gajiyar daku, sai kace ba gwaraza ba."
Sake shagwaɓe fuska yayi, cikin salon sakalci yace.
"Wallahi Ummi makaranta ba daÉ—i, duk acika ku da lectures, yau fa ko É—an hutu bamu samu ba."
Ƙare maganar yayi yana me ɗago kansa, inda ya kalli Saifuddeen, wanda ya haɗe fuska, inda ya kawar da kansa gefe, da'alamu cewa ba ya cikin yanayi me daɗi, cikin kulawa haɗi da faɗuwar gaba, asanyaye Hayatuddeen ɗin yace.
"Hamma!."
Kasancewar Saifuddeen ɗin ya juyar da fuskarsa, zuwa wani ɓangare na daban hakan yasa baiji ƙiran da Hayatuddeen ɗin yayi masa ba, don dama sai yana kallon ka ne, sannan yake karantar abun da kake faɗa, ta hanyar kallon yanayin motsin bakinka shiyasa yake da yawan kallon ammanfa ga wanda yake son ya gane abinda zai faɗa.
Ganin Hamman nasa baisan da cewa yanayi ba, hakan yasa ya taso da sauri ya, ƙarasowa gaban Hamman shi hannunshi ya ɗaura a akan kafaɗan Hamman nasa, ahankali Saifuddeen ya ɗago da kansa, duban Hayatuddeen ɗin yayi, sai kuma ya kau da kansa gefe.
Hakanne yasa jikin Hayatuddeen yayi sanyi sosai.
A take kuma yaji gabansa ya faɗi, ƙirjinsa ne ya shiga duka, cikin zuciyarsa yace.
"Nashiga uku badai Hamma na yasamu labarin cewa, yau na fita amakaranta, na bi Khamis muntafi yawo ba?."
Cikin ɗari-ɗari da fargaba ya kalli Ummi, wanda ke ƙoƙarin tashi, don komawa ɗaki, da sauri ya rufa mata baya, jin mutum abayanta yasata juyowa, kafe Hayatuddeen ɗin tayi da ido, tare da cewa.
"Lafiyanka ƙalau kuwa kake biye dani, sai kace wani ƙaramin jariri, kodai ka aikata wani rashin gaskiya ne?."
Ummi tafaɗa tana me ƙare masa kallo, don tsab tasan yaranta, da zaran sunyi wani abun da ba dai-dai ba, takan saurin ganewa, ko daga halin rashin nutsuwa da zata gansu aciki, kamar dai yadda ta fara zargin yanayin canji nitsuwar Hayatuddeen.
Ƙifi-ƙifi Hayatuddeen ɗin yayi da idanunshi tare da cewa.
"A'a babu abun danayi, kawai dai naga ran Hamma Saifuddeen ne kamar aɓace yake."
Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Hmm rabu da Hammanku, gata ake son a mishi shi kuma wai baya so."
Da sauri yace.
"Ummi wanne irin gatane?."
murmushi tayi tare da cewa.
"Wai fushi yake don ance masa ya ƙara aure, shine yake ta faman haɗa rai sai kace wanda akace yayi wani abun, wanda ba dai-dai ba."
Cikin zaro ido Hayatuddeen yace.
"Haaah Ummi to kuce ni inyi auren mana, tunda shi baya son gatan ni kuyi mini."
Cikin mamaki da al'ajabi da zazzaro ido Ummi tayi kana tayi kasake tana kallonshi da nazartanshi.
Shi kuwa da sauri ya dawo nitsuwarsa gudun karta ramfoshi.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Hayatuddeen ya sauƙe, ya godewa Allah da yasa, ba asirinsa bane ya tonu, domin yasan tabbas idan Hamman nasa, ya gane irin abubuwan da yake yi, to fa kashinsa ya bushe, yasan sai anrabasa da duk wani abu nasa najin daɗi.
Gyara tsayuwarsa yayi tare da cewa.
"To Ummi me yasa zai ƙara aure, yaushe ma yayi auren?."
Harara Ummi ta watsa masa, tare da cewa.
"To kai mekasani acikin aure da kake tsoma baki cikin abun da babu ruwanka?."
Kanshi ya jujjuya tare da cewa.
"Wallahi ba abinda na sani, kawai a auro mishi mai sonshi tunda hegiyar nan taƙi zama."
haÉ—e fuska Ummi tayi tare da cewa.
"Hayatu baka da kunya fa ba yayarka bace kake ce mata hegiya, to a kul wlh kada in sake jin ka zagarmin ƴata dan mu dai Zaleeha bata ƙi muba bata mana wani laifiba ita dai auren ne da bata so."
Murmushi yayi tare da É—an shafa kansa yace.
"Afwan ya Ummi bazan sakeba, nima nasan Zaleeha na sonmu amman dai ina jin haushinta in na tuno wai bata son Hamma nane yasa ta gudu."
ya ƙarishe mgnar tare da, juyawa ya inda ya fice daga cikin ɗaki, a falo ya samu Adda Rahama, har yanzun Saifuddeen na zaune afalon,  komawa kan sofa yayi ya zauna, inda ya matso kusa da Adda Rahama wanda kecin abinci, dubansa Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Bafa zanci dakai ahaka ba, jeka wanko hannunka."
Ɗan shagwaɓe fuska yayi tare da cewa.
"Dan Allah Adda Rahama, muyi karɓe-karɓe, don nagaji, dama kafun na zauna ne kikace na wanko hannun nawa."
Kai Adda Rahama ta girgiza tare da cewa.
"Allah ya shiryeka, sarkin lalaci kawai, da ace kai mace ne, tabbas da anyi uwar son jiki."
Murmushi kawai yayi tare da amsan spoon ɗin dake hannunta, haka suka shigayin karɓe-karɓe, idan tayi loma guda, ta bashi spoon ɗin shima yayi, duk wai saboda tsananin ganda, ɗauko spoon kaɗai ya gagaresa.
Ummi ce tafito É—aga cikin É—aki, hannunta É—auke da wayarta, duban Saifuddeen tayi tare da cewa.
"Bappa Ali ne ya ƙira."
ÆŠago kai Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Akan maganan auren ne ko?."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa, koda na faɗa masa cewa, babu wacce ayanzu Saifuddeen ɗin keso, cewa yayi wannan ba uzuri bane, za'a ne mamasa ko acikin dangi."
Idanu Saifuddeen yaÉ—an zaro waje, kasancewar yana kallon Ummin nasa, hakanne yasa ya fahimci me take faÉ—a.
Murmushi Adda Rahama tayi, É—an satan kallon Saifuddeen É—in tayi, cikin kulawa tace.
"Hakan ma yayi, tun da dai shi yace bashida zaɓi."
Hayatuddeen ne ya É—ago kai tare da duban Ummi, cikin nutsuwa yace.
"Acikin dangi kuma tab, nikam dai banso Hamma ya yi auren dangi, to idan ma hakane ae ga nan Amina da Asma'u, duk suna sonshi, musamman ma Ameena, dake bala'in sonsa ae sai ya zaɓi ɗaya acikin su ko?."
ÆŠan jim Ummi tayi, nan kuma tasaki murmushi, cikin gamsuwa da kalaman Hayatuddeen tace.
"Tabbas, ka ga kuwa ni na manta ma da batun Ameena, gaskiya yarinyar akwai hankali, sannan kuma tana da kirki sosai, don ko lokacin da yake jinya a Hospiatal ɗin Abuja, ta kula dashi sosai, gaskiya na yaba da hankalinta sosai tana son Babana."
Duban Ummi Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Okay wannan nurse É—in ba, gaskiya nima yarinyar ta kwanta min arai, sai-dai kuma wacece Asma'u, don ban shaida ta ba."
Carab Hayatuddeen yayi inda yace.
"Wata jarumar film ne, kinma santa ae, wannan Asma'u Ahmad Matawalle wanda take rawa da waƙa, tauraronta yana haskawa sosai."
Idanu Adda Rahama ta É—an zaro tare da cewa.
"Mai rawa da waƙa kuma? chab awani gidan? gaskiya a'a, Ameenan dai tayi, don ƴar gidan mutumci ce da dukkan alama, kuma Saifuddeen da yawan kishi ai bazai iya aurenta ba."
Cikin gamsuwa Ummi tace.
"Tabbas nima Ameenan tafi kwanciya min arai, don dai ita Asma'un kam sam batayi ba, don idan ma muka zaɓeta bamusan da wanne ita kuma zata zo ba, duba da irin lalurar da yake fama da ita ma, sam baidace ya auri wata ƴar nanaye ba, wanda suka saba cuɗanya da maza, ko yaushe suna cakuɗe da maza awaje guda ga Saifudden da ɗan karen kishi, balallai ma yasamu ingantacciyar kulawa daga gareta ba, Ameena ɗin dai ita muka zaɓa."
Nan Adda Rahama ta jinjina kai cikin gamsuwa.
Shikuwa Saifuddeen daya duƙar da kanshi kasa, sai alokacin ya ɗago, kasancewar bai kallesu ba, hakan yasa baiji mai suka tattauna ba.
Madanannin wheellchair É—insa ya danna, kai tsaye yanufi hanyar barin falon, don yagaji so yake yaÉ—an je ya kwanta ya huta.
Yana fita Ummi ta dubi Hayatuddeen wanda keta aikin zubawa cikinsa abinci, cikin kulawa Ummi tace.
"Hayatuddeen bani wayarka."
Adaburce ya ɗago kansa, kasancewar yakai loman abinci bakinsa, hakanne ya sakashi ƙwarewa, take tari ya sarƙesa, da mamaki Ummi ke kallonsa, yayinda Adda Rahama kuma keyi masa sannu, botle water ta miƙo masa, nan ya amsa haɗe da kafa bakin goran abakinsa, saida yasha sosai kafun yaji ya samu relief,  cikin kulawa Ummi tace.
"Sannu, haba kaima sai cikawa cikin ka abinci kake babu ko tsayawa, tayaya bazaka ƙware ba, bacin abincin ba guduwa zaiyi ba, kana abu kamar mara gsky."
Shiru yayi tare da ƙoƙarin neman hanyar barin falon.
Dubansa Ummi tayi tare da cewa.
"Ina kuma zakaje? bacewa nayi kabani wayarka na É—au number'n Ameena ba."
Jin haka yasashi sauƙe gagarumar ajiyar zuciya, zaro wayar daga cikin al'jihun wandonsa yayi, nan yashiga contact ɗinsa, inda ya laluɓo number'n Ameena'n, nan ya miƙawa Ummin nasa.
Tsab Ummi ta kwafe number'n Ameena'n, inda ta sanya awayanta, kana ta miƙa masa wayarsa, haka ya wuce sama sumu-sumu, daganinsa kasan bashida wadataccen gaskiya.
Nan Adda Rahama da Ummi suka ci gaba da tattaunawa akan sabon auren da za'a ƙarawa Saifuddeen ɗin, sai ayanzu ne suma suke ganin cancantar yin hakan, saboda Zaleeha ta gujesa, tana ganin cewar shi nakasashshe ne, yayinda su gani sukeyi dan shi nakasasshene yasa ta gujeshi sannan babu wata mace wanda zata iya zama dashi, hakan yasa dole ne ma su Aura masa Ameena, tun da dai ita tana son shi, sun tabbatar da cewa kuma zata kula dashi. Sun ɗan taɓa hira kafun Adda Rahama ta tafi, Ummi kuma ta nufi ɗaki ta kwanta, bayan taƙira Bappa Ali ta sanar masa zaɓin da tayiwa Saifuddeen ɗin, sosai shima Baffa Ali'n yayi na'am da batun, nan take yaƙirayi Baba Malam ya sanar masa, da batun, sosai Baba Malam yaji daɗi, don kuwa ko ba komai hakan da sukayi sun karramasa.