← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 154

Sashe 2

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani irin Murmushi Ahmad yayi still hawayenshi na kwaranya, kai ya jinjina ganin Zaleeha na rarrafe tamkar yarinya k'arama a hankali ta isa gaban Baba Malam hannu ta had'e wuri d'aya cikin yanayin neman gafara, murya na rawa jikinta na kar-kar-wa numfashinta na ficewa ba komawa,
cikin shak'k'k'iyar murya a disashe tace.
"Na amince Baba Malam na yarda ayi auren ka aura min Saifuddeen d'in na amince. Ka yafe min Babana ka gafarta min ka rufa min asiri kada in hallaka sabida fushinka na amince ayi auren na yarda."
Da sauri Maryam da Ziyada suka ruggumeta.
Ahmad da Habu kuwa ruggume juna sukayi,
Mamy kuwa kamo hannun Baba Malam d'in tayi ta nufi side d'inshi dashi, shi kuwa ba musu ya bita. Ahmad da Habu sukabi bayansu,
Aunty Lubna kuwa kamo hannun Zaleeha tayi ta nufi Side d'in Mamy kana Ziyada da Maryam sukabi bayansu.

Zahira kuwa da sauri tabi bayan Mama.

A gidan Saifuddeen kuwa, Ummi ce zaune a parlournta ita da.
Su Bappa Ali da Malam Ashiru.
Cikin nitsuwa tayi musu bayanin dalilin nemansu da tayi ta k'ara da cewa.
"Hankali na ya tashi tun zuwansu na forko, yarinyar ta nuna bata son auren da Saifuddeen ta gaggaya musu bak'ak'en maganganun da suka gigitasu suka tayar musu hankali, anan Ahmad ya dawo yana kuka cur-cur da hawayenshi dan wulak'ancin da tayi musu ita da aminanta.
basu b'oye min komai ba, sai dai shi Saifuddeen baiso su sanar min ba sabida tsananin son yarinyar yakeyi ita kuwa bata sonshi ina tsoron kada tazo ta cutarmin shi."
Ta k'arishe maganar cikin yanayin tsantsar karaya da tsoro.
Bappa Ali ne ya gyara zama tare da fuskantarta da kyau kana yace.
"To yanzu me kike so ayi?."
Nannauyan ajiyan zuciya ta sauk'e tare da cewa.
"Ni dai auren ya fita raina, ku kira Saifuddeen ku taushi zuciyarshi ya rabu da yarinyar ya janye batun auren, kana kuje ku sanarwa iyayenta cewa an fasa batun auren tunda yarinya bata so gwara a bari kawai, magnin bari kadama a soma."
Baba Ashiru ne ya katseta da cewa.
"A,a sam bamu da hujjar janye batun auren nan, da girmanmu da mutuncinsu munje munyi magana gemu da gemu sannan dan zancen baya muce zamuje muce mun fasa auren. Sannan keda kankifa kika ce mana Saifuddeen yana son yarinyar matuk'a gaya."
Cikin sanyi ta girgiza kai tare da cewa.
"Ba zancen bayan kadai bane. Ko shekaran jiya Hayatuddeen yaje gidan kakarsu wurin Abokinshi k'aninta ya sameta can tanata kuka, wai ita bata son auren gurgu kurma. Tayi al'washin in dai aka aura mata shi zata kashe kanta.
Kuma jiya ma dasu Saifuddeen d'in sukaje nanma ta ciccimusu nutunci sun dawo nan suna mgnar basu san na jisu ba."
A hankali Bappa Ali yace.
"Ba komai! In sha Allah babu abinda zai faru sai al'khairi! Ke dai kiyi ta addu'a kin san addu'ar uwa karb'eb'b'iyace domin bata da hijabi,
Tunda kin sani mun sani Saifuddeen yana sonta tofa mu bisu da addu'a.
in har bata so ai iyayenta zata sanarwa kuma in bata sonshi baza bashi izinin turamu ba."
kasake tayi tana jinsu, suna bata k'arfin guiwa, cikin kula Malam Ashiru yace.
"Kinga fa du-du-du kwana biyar ne ya rage bikin ta yaya zamu fito da wata matsala ta b'angarenmu, muyi hak'uri in har bata so d'in su sa fito da matsalar."
Kai ta jinjina tare da cewa.
"To tunda kunce haka ba matsala, amman ni naso Saifuddeen ya nemi matar aure a cikin tarin matan dake bibiyarsa da soyayyarsu. Amman ba komai Allah yasa hakan shine mafi alkairi."
Amin Amin sukace baki d'aya, kana sukace to su zasu koma dukku.
nan suka sallemi juna suka tafi.

A can gidansu Zaleeha kuwa, shiru gidan ya koma kamar gidan zaman makoki, kowa da abinda ke ransa, su Ahmad da Mamy da Maryam dai sunyi ta magiya da rok'on Baba malam da bashi hak'uri. Har saida suka ga alamun ya samu sassaucin tashin hankalin da yake ciki.

Bayan anyi sallan isha ne. Malam Adam da Ya Aminu suka shigo gidan a jere.
Kai tsaye parlour Baba Malam suka nufa,
Bayan sun gaisa ne ya musu bayanin abinda ya faru.
kwaffa ya Aminu yayi dan tabbas da yana nan to da tuni ya karya Zaleeha.
Shi kuwa Malam Adam kai ya jinjina cikin tsananin mmki da tsoron yaran zamani yace.
"Aminu je ka kirawo min Zaleehan."
To yace kana ya mik'e ya nufi part d'in Mama.

Ita kuwa Zaleeha zuwa yanzu dai tayi kuka har hawayenta sun kafe.
Da kyar Aunty Lubna da Maryam suka sata tayi wonka kana tayi salla, sannan suka bata magani ta sha, domin tuni wuyanta ya kumbura haka fuskarta ,gaba d'aya jikinta ciwo da tsami yake mata duk farar fatar nan tayi jazir ga tsami da yankan da tayiwa kanta yayi duk da anyi mata dressing.
Rumtse idanunta tayi lokacin data rab'a jikin Ya Ahmad da yanzu ya shigo, wasu zafafan hawaye ne masu k'una suka kwaranyo mata.
sosai ta zama abar tausayi dan duka iya duka Habu ya jibga mata gashi ita da kanta can ƙasan zuciyanta take jin zafin abinda ta aikatawa mahaifinta.
cikin sanyin murya da tausayawa tare da lallashi Ahmad yace.
"Zaleeha!." bata amsa ba sai wasu sabbin hawaye ne suka fara sintiri a fuskarta.
Lubna ce tasa tafin hannunta ta share mata hawayen, yayinda Maryam ma idanunta sukayi rau-rau alamun zasu zubdo kwalla,
muryar Ya Ahmad d'in nasune ya katse musu shirun nasu.
"Dan Allah Zaleeha na rok'eki da girman Allah kiyi biyayya ga umarnin mahaifinmu, kiyi koyi da Maryam, ki kare mana mutunci da martaba da darajar gidanmu dana mahaifinmu."
A hankali ta bud'i baki cikin disashewar murya tace.
"Ya Ahmad bana sonshi wallahi na tsaneshi ji nakeyi kamar zan mutu in na tunoshi."
kanta ya shafa tare da cewa.
"Zaki soshi, zaki daina jin komai, in kin rabu da aljanin dake jikinki. Ni nasan Zaleeha tana son farin cikin Babanmu."
Shiru tayi dan ta fahimci ya Ahmad dai ya maidata mai aljanu so bazai tab'a fahimtar matsalarta ba,
shi kuwa d'agota yayi suka fuskanci juna cikin tausaya mata yacee.
"Dan Allah Zaleeha kiyi biyayya ga auran da Baba Malam zai miki ki zauna d'akinki, nayi miki al'k'awarin zan miki duk wani abu da kikeso a duniya matuk'ar baifi k'arfina ba, kuma bai sab'awa shariya ba,
ki gaya min duk abinda kikeso zan miki shi k'anwata, ni dai fatana a miki auren ki zauna lfy da mijinki."
cikin zubda hawaye tace.
"Ka saya min sabuwar mota, motocina su zama biyu."
da sauri Maryam tace.
"Ai yanzuma motocinki biyu ne, ai kayan aurenma da motarki sabuwa fil Saifuddeen ya had'o miki."
Ido ta rumtse da k'arfi dan wani d'aci da takaicin jin sunanshi da Maryam ta kira cikin had'e fuska tace.
"Bana son wannar, abin gori abin dangin miji".
murmushi Ya Ahmad yayi tare da cewa.
"Zan saya miki k'anwata sabuwa fil zan saya miki, motocinki su zama uku."
sosai taji dad'in amincewar da yayi zai saya mata mota,
ganin taji dad'i yasasu jin dad'i suma.
Ahmad ne ya rik'o hannunta tare da cewa.
"Da me kuma kike so?."
cikin jin dad'i tace.
"Sabuwar system." cikin jin dad'i fa da ganin yarintarta yace.
"Kin samu."
kayan d'aki kuma wanne iri kikeso."
jim ta d'anyi tare da cewa.
"Ko wannema." a tunaninta me zata ce a kan kayan d'aki abinda ko sun kashe kud'i sun mata bazata soshiba.
haka fa sukayi ta lallab'ata.

Ya Aminu kuwa yana isa parlour Mama ya samu, Habu cikin had'e fuska yace.
"Ina Zaleeha tazo, Baba malam na kira."
"Tana part d'in Mamy."
"Je ka kira min ita."
to yace kana suka nufi parlour Mamy,
daga bakin k'ofa ya tsaya tare da cewa.
"Ke Zaleeha maza ki zo, Baba Malam na kira."
jin muryar habu yayi masifar razanata, da sauri ta mik'e ta nufi parlour.
Ahmad d'inne yabi bayanta.
ganin Ya Aminu da Ya Habu a parlour'n ya k'ara firgitata.
nur-nur tayi gaba sana suka bita a baya,
tana tafe tana d'ingisa k'afarta.
har suka isa parlour.
kana Ahmad na biye dasu a baya,
A hankali ta isa gaban Baba Malam d'in jiki na rawa ta durk'usa ganin yadda ya Aminu ke watsa mata harara yasa tayi maza tayi k'asa da kanta, murya na rawa tace.
"Baba Malam gani."
shiru yayi yana k'are mata kallo,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi,
Malam Adam ne ya kalleta tare da gyara murya wanda sai lokacin ta ganshi,
cikin rawan murya tace.
"Daddy ina wuni." ido ya lumshe tare da cewa.
"Lafiya lau Zaleeha."
daga nan sukayi shiru na tsawon 55 seconds sannan Malam Adam ya kira Zaleeha wacce tsoro ya hanata salama.
"Na'am". A hankali ya fara magana.
"Naji abinda kikayi, da kuma abinda kike Al'washin yi na cewa zaki kashe kanki ko?." shiru babu mgna sai wata zazzafar zufa data keto mata,
"To yanzu gaya min cikin mutun biyu da kika sa suka turo mana iyayensu wa kike so?."
kai ta jujjuya alamun babu.
Cikin fad'a Aminu yace.
"To uban wa yasa zaki had'a mana kayan mutun biyu, kin san aurenki saura kwana biyar meyasa zakisa Abdussalam turo iyayenshi." da sauri tace.
"Bani bace nace su kawo kayansu bafa."
a hatsale Habu yace.
"Waye to." cikin tsoro tace.
"Mama ce."
shiru sukayi sai Baba Malam ne yace.
"Uhummm". Malam Adam kuwa yace.
"To yanzu dai gwara mu zare hannunmu a kanki, gwara mahaifin naku ya tafi ya barku kiyi duk yadda kika ga dama ko."
cikin raunin murya tace.
"Dan Allah, Baba Malam kayi hak'uri na tuba, ku gafarceni,
Kayi hak'uri kada ka tafi, na yarda ayi auran."
cikin jin dad'i Malam Adam yace.
"Allah ya miki al'barka, tashi kije."
jiki na rawa ta mik'e ta tafi.
daga nan suka ci gaba da tattaunawa.
Nan Baba Malam ya bawa Habu umarnin cewa gobe da safe ya kwashe kayan su Abdussalam ya mayar musu.

Ita kuwa Zaleeha d'akinta ta wuce,
kana ta d'auki wayarta.
10:15 pm ta gani,
zuciyarta cike da bak'in ciki ta kwanta,
text tayi ta rubutawa da mugayen kalamai tana tura mishi har kashi uku,
sannan ta kira Bilkeesu ta gaya mata duk abinda ya faru,
nan bilkeesun tace.
Tana zuwa gobe dan mgnar bazata yiwu a waya ba.
Chapter 2 · 0% Book details