← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 154

Sashe 18

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Balkeesu kuwa baki tasake tana ƙarewa Raihanan kallo, gaba ɗayama hankalinta yatafi ga tsadadden zanin dake jikin Raihana'n, domin kuwa babban Chiganvy ne ɗan ubansu.
Murmushi Raihana tayi tare da duban Zaleeha cikin kulawa tace.
"Idan babu damuwa muna buƙatarki afalo, za'a ɗanyi muku buɗan kai ne!."
Dammm haka Zaleeha taji ƙirjinta ya doka, sam batason abun dazai ƙara haɗata dashi, musamman idan ta tuna da abun daya shiga tsakaninsu jiya saitaji kanta kamar zai buga gaba ɗaya tsoro lamarinshi ke bata.
Cikin baƙinciki da takaici Balkeesu tace.
"Mezai hanamu zuwa kuwa, ai zamuzo yanzun nan." tafaɗa tana me miƙewa tsaye dan samawa Zaleeha mayafi, ɗan murmushi Raihana tayi tare da cewa.
"Badamuwa, ai bama sai kunzo ku dukanku ba, itaɗin dai kawai muke buƙata!."
ta ƙarishe mgnar cikin yatsina fuska dan sam ita da Bilkeesu bata konta mataba, Zaleehan kanta a fakaice take sonta tunda ance bata son Hammanta ita kuwa duk wanda yace baison Hamma Saifuddeen ɗinta itama bazata sotaba.
Ƙasake Balkeesu tayi tare da watsawa Raihana harara ƙasa-ƙasa, tabbas maganace afakaice Raihanan ta faɗa mata, amma dai koma menene ta rantse saitaje anyi buɗan kan da'ita.
Wani tsantsareren mayafi laffaya Zaleeha ta yafa aduka jikinta inda ya sauƙo ya rufe har fuskarta, wani flat shoe kalan yadin jikinta ta sanya aƙafafunta,  Raihana da kanta taƙara fesa mata turare nan Balkeesu uwar gulma tariƙe Zaleehan, Raihana na gaba sukuma suna biye da ita abaya haka suka nufi cikin gidan.

Sunanan zaune afalo suna ɗan taɓa hira, daddaɗan ƙamshin daya ziyarci hancinsa shiyafara sanar masa da zuwanta, juyawan dazaiyi kuwa ya hangota cikin wani light orrange ɗin mayafin laffaya mai tsananin kyaun gaske, sai walwali da sheƙi yake, Raihana da kanta ta kamo Zaleehan, inda ta zaunar da ita akan kujeran dake facing na Saifuddeen ɗin, tsulum Balkeesu daketa faman ƙarewa falon kallo tazo ta zauna akusa da ita, sosai Balkeesu tasha mamakin haɗuwan falon, wanda kuma yake mallakin Ummi, sam abubuwan mutanen suna shammatan ta, kwata-kwata bata taɓa tunanin yawan arzikinsu har yakai haka ba, duk abun da sukayi takan ɗauka, ƙaryane kawai da fafa, wani abun kuwa takanyi tunanin sunayinshi ne kawai don su mallaki Zaleehan, saidai kuma tunaninta ya fara sauyawa ne tun lokacin da aka kawo Zaleehan gidan,  yanzu kam tagama yarda cewa suɗin masu arziki ne, duba da irin kuɗin da aka kashe wajen ƙawatawa Ummin nasu falonta, uwa uba ga ƴan uwan Saifuddeen ɗin da ako yaushe suke cikin sutura mai kyau, da shiga ta al'farma domin kab cikinsu babu wacce take sanye da ƙasa da  kayan dubu ashirin, saima yayi sama, kowa kagani acikinsu masha Allah, Gaba ɗayansu cikin jindaɗi da rufin asiri suke rayuwarsu gasu kyawawane ajin forko, duban Adda Rahama wanda ke sanye da wani jan leshi mai shegen tsada tayi, taɓe baki tayi, cikin ranta tace "Ƴan iska, kowa kagani cikin farinciki yake, badai Saifuddeen shine farincikin ku ba, hmmm ai na gano lagonsa, rashin Zaleeha shine baƙin cikinsa, kukuma baƙin cikinsa shine tashin hankalinku, to kuwa kushiryawa tashin hankali, don wallahi al'ƙawari nayi sai nasa Zaleeha tasa ya saketa saki mafi muni kafin insata ta gudu daga gidannan."
  ƙasa-ƙasa tayi ƙwafa, tare da cigaba da ƙare musu kallo.
ita kuwa Zaleeha shiru tayi kanta a sunkuye ta cikin mayafin ta zubawa ƙafafun Saifuddeen ido, wanda suke ƙal-ƙal kana daga ganinsu zasuyi tsananin laushi da taushi kodan hakan bazai rasa nasaba da rashin takawarsuba daga ganin fatar tiɓis zatayishi laushi, yatsunshi ta zurawa ido tana kallonsu tamkar ka taɓasu jini ya tsallo kan faratun yatsun nashi ta maida idanunta ganinsu ƙal-ƙal yasata ɗan kauda idonta, a ranta take tajjudin yawan tsabta na wannan nakasasshen aljanin yakeda shi sabida ita fa tana alaƙanta kyan Saifuddeen da iska, takalmanshi dake gefe ta kalla wanda suke na Gucci a tsiwace cikin ranta tace,
"Hmmmm gurgu kafi mai ƙafa iya shege, shi komai nashi mai tsada, wannan da lafiyarsa lau, alla'anɗi iya ƙasaitar da zai zuba.
Shi kuwa Saifuddeen kota kanta baibiba hira yake da abokanshi.
Bilkeesu kuwa sam bata tsinke da al'amarin nasu ba saida taga yanda Ummi da kuma Goggo Dada ke yiwa Saifuddeen ɗin ɓarin kuɗi, sosai suka zuba masa kuɗi, inda Aunty Meenat ma tazuba masa nata, nanfa kuma suka dawo kan Zaleeha,  Goggo Dada ne tasa Raliya ta buɗe mata mayafin, nanfa suka shiga zuba mata kuɗi itama, sosai suka zuba mata nairori, Ummi ne ta dubi Raliya inda tace taje ɗaki akwai wani gift da ta ajiye akan gado ta ɗauko mata, babu ɓata lokaci kuwa saiga Raliya ta dawo, hannunta ɗauke da wani ƙaton gift wanda aka masa ado da pink flowers, sosai yayi kyau, hannun Zaleeha Ummi takamo inda ta sanya mata babban gift ɗin cikin nutsuwa tace.
"Wannan tukuici ne agareki na zamantowa matar É—ana da kikayi, Allah Ubangiji yayiwa rayuwar aurenku al'barka, sannan yabaku zuri'a ta gari tare da zaman lafiya mai É—orewa."
Gaba É—aya jama'an wajen suka amsa da Ameen, saidai banda Zaleeha, sai kanta data sunkuyar alamun jin kunya, kana tanata wasa da yatsun hannunta.
Sosai Ummi taji ƙaunar ƴarinyar a ranta komai da nitsuwa da kunya take yinshi.
Balkeesu kuwa da ƙarfi tafaɗi Ameen ɗin, wanda hakan kuwa da biyu tayishi, sam bataso sugane cewa itaɗin munafukace, don tafuskanci cewa kamar, Raihana ta ganota.
Haka suka gamayi musu buɗan kaiɗin cikin nuna ƙauna, Balkeesu ne tajata suka koma part ɗinta bayan duk an haɗa mata kuɗin.
Su kuwa su Saifuddeen anan falon Ummin sukaci gaba da zama.

Suna shiga cikin ɗaki, Balkeesu wanda jikinta ke mazari ta amshi gift ɗin, hannunta har rawa yake wajen ƙoƙarin buɗewa.
Zaleeha kuwa mayafin dake jikinta ta yaye, cikin ƙunan zuciya tayi wurgi da mayafin, faɗawa kan gado tayi tare da lumshe idanunta, sam batajin tsanar kowa dake cikin gidan saishi kaɗai haka nan taji tana so duk mutanen gidan sabida ta lura sunada karamci da mutunci kuma sunfi ƙarfi tijara koda da ƙwayar zarrane a wurinta.

Ihun da Balkeesu tayi shiyasanya Zaleehan É—agowa da sauri ta dubi Balkeesun, cikin yanayin mamaki haÉ—i da firgita Balkeesu tace.
"Gold, Zaleeha Gold ne fa aciki da kuma turaruka masu tsada ga kuÉ—in duk ke akabarwa."
Wani haÉ—aÉ—É—en kwalban turare Balkeesun ta zaro tare da cewa.
"Zaleeha kinkuwa san kuÉ—in wannan turaren?, oh my God ashe waÆ´annan mutanen masu kuÉ—ine sosai har haka!!."
Wani dan ƙareren agogo da sarƙan gold Balkeesun ta ciro, wanda aka ƙawata gidansu da wani farin glass, cike da mamaki tace.
"Lallai kuwa mutanen nan sunshiryawa auren nan, what a surprise." 
Kallon sarƙa da agogon Zaleeha tayi, wanda lokaci ɗaya sukayi bala'in yi mata kyau, amma ayanda takejin zuciyarta yasa bata  nuna ba, maida kanta jikin pillow kawai tayi tare da lumshe idanunta, abun daya dameta shine aranta ita kuɗinsu baya gabanta.
Balkeesu kuwa kaman Zararriya haka ta dinga yaba kayan, saida tagaji don kanta sannan tayi shiru, nan kumafa zuciyar hassadan nata ta motsa, take taji wani danƙareren baƙin ciki ya cika zuciyarta, inama da ace itace tasamu wannan kayan more rayuwa haka? wai ma shin maiyasa ita rayuwa bata zuwar mata da garaɓasa haka? lallaima dole ne taraba Zaleeha da wannan gidan, idan bahaka ba tanaji tanagani zasu maida Zaleeha millionaire girl, ita tananan zaune Zaleeha zata shiga cikin sahun manyan mata, wanda kokaɗan kuwa ita bata fatan haka, dole ne ma taƙara zuga Zaleeha akan batun a sakin kafin guduwarta, don kuwa ayau ɗin ta hango irin tsananin soyayyar da dangin Saifuddeen ɗin keyi masa, tabbas ayanda tafahimta ayanda suke masifar sonsa, to zasu iya ɓatawa da duk wani wanda ya ɓata masa, dakuwa zasu tsani Zaleeha da tafi kowa murna.
Saboda tsananin ƙyashi da hassadan dayaci Balkeesu kasa cigaba da zama agidan tayi, lokaci guda tayiwa Zaleehan Sallama inda takoma gida, zuciyarta cike da saƙe-saƙe kala-kala.

Tun wannan fitowan da Zaleeha tayi na zuwa buɗan kai, daganan bata sake fitowa ko falo ba, abincin da aka kawo mata ma har ɗaki, Raliya takawo mata ta ajiye, sam kasa cin abincin tayi, Zaheera ce taci inda tacika cikinta, itakam babu abun daya shallaketa, tanajin daɗin zaman gidan, babu wani takura, dagaci sai kallo, dama ita tanan tafi kauri, aiki ko na misƙala zarratinne basonshi take ba, wannan dalilin ma yana ɗaya daga cikin abun dayasa ta ƙi komawa gida, domin tasan da zaran takoma tofa aiki za'aita sakata kamar jaka, itakuwa sam bason hakan take ba, ga shi Ziyada ba zama take ba, always tana gidan Hajja ga Zaleeha dake yawan yin wasu aiyukan kuma an aurarta.

Saifuddeen kuwa gaba É—aya wunin yau dasu Ishaq yayisa, don sosai suka zauna don É—ebe masa kewa, kasancewar acikinsu babu wanda baisan matsayin auren Saifuddeen da Zaleehan ba, kowa yasan baso takeyi ba, dan haka nan suka wuni sai dare suka tattafi.

Koda Yadawo sallan Isha, kai tsaye falonsa ya wuce, koda yazo falonta ko ƙofar ɗakinta bai kalla ba, dan shima yau ƴan jan ajinnasa suna kusa, duk dacewa yana da buƙatar jinta ajikinsa, amma dole haka zai daure, dan yasan koda yaje ma tofa faɗa zasuyi, shikuwa bayanzu yakeson yafara gwada mata ƴar ƙarfi ba.
Koda yashiga haɗaɗɗen bedroom ɗinsa wanka yayi, inda ya kimtsa kansa cikin kayan baccinsa, kwanciya yayi tare da jawo laptop ɗinsa, nan yayi ƴan danne danne, a hankali ya zubawa system ɗin ido, yana kallon motar nan da yasa Hayatuddeen ya liƙa mata na'ura tana tafe har gidan da ta shiga,

yaga matasan baki ɗaya sai kuma duk sukayi cikin gidan hakanne ya hanashi damar ganin abinda ke faruwa a cikin gidan. bincike yaci gaba da yi akan gidan da matasan har saida ya samu iya abinda zai samu to amman har yanzu babu ƙwaƙran laifin da za'a kamasu dumu-dumu a ciki haka dai ya haɗa abinda ya samu,
kafun daga bisani bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Chapter 18 · 0% Book details