Sashe 43
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari da safe kuwa, Raihana lafiyayyen break fast ta shirya musu, inda suka cika cikinsu, nan kuma suka soma shirye-shiryen tafiya, don yau ɗinma jirgin ƙarfe 10 zasu bi zuwa Gombe.
Saminu ne ya kaisu airport wanan karon hadda Raihana tayi musu rakiya.
Basu bar airport É—in ba kuwa saida suka ga tashin jirginsu, sannan suka dawo gida.
Ƙarfe sha ɗayan rana acikin garin Gombe tayi musu, inda Sule driver yazo da babbar motar Saifuddeen har airport ya kwashesu zuwa gida.
Afalon Ummi suka baje, wanda nan suka samu Saifuddeen zaune akan wheellchair dinsa, yana shan yogo fruit wanda Ummi ta haɗa masa, yayinda tasashi agaba sai tarairayarsa takeyi kamar wani ƙaramin yaro, shikuwa dama aikinsa ne shagwaɓa hakan yasa ya narke mata.
Sam abun baya bawa su Adda Rahama mamaki, saboda sun san ƙaunar dake tsakanin Ummi da kuma Saifuddeen mai ƙarfi ce.
Nan dai suka shiga labartawa Ummi, irin tarban mutumcin da suka samu daga wajen dangin Amina.
Jin suna ta yaba kirkin dangin su Ameenan yasanya Saifuddeen kauda fuska, nan yamaida hankalinsa ga tv, don bama yason fahimtar mai suke faÉ—a.
Anan dai Adda Rahama tayi sallan La'asar kafun Dr Adnan yazo ya É—auketa.
Goggo Dada ma ɗakin Ummi ta wuce don hutawa, shi kuwa Hayatuddeen sama ya haura, yana shiga ɗakinsa ya jawo wayarsa, data ya kunna sannan yashiga cikin Whatsapp ɗinsa. Nan ya iske saƙon Ameena. Inda tace.
"Hey ƙanina." Ganin tana online yasashi sakin murmushi, nan yayi mata reply da cewa.
"Sannu me wayo, wato kinma fara ƙirana da ƙaninki ko, saboda kinsan kinyi nasara, zaki auri handsome ɗin Hammana."
Ameena dake kwance ganin saƙon Hayatuddeen din yasa ta saki murmushi, harda dariya. Cikin kulawa tace.
"Dama na faÉ—a maka ae watarana insha Allah zan zama auntynka saboda haka biyayya dole."
Koda Hayatuddeen yagama karanta saƙon dariya sosai yayi, nan dai ya tsaya suka ɗan taɓa hira da Ameenan, daga ƙarshe ganin ta sauƙa online, yasashi maida hankalinsa wajen chatting da abokansa.
Yau kwana Uku kenan dakai lefen Ameena, har zuwa yau kuwa ko da sau ɗaya ne Saifuddeen bai taɓa tura mata saƙo ba, harkokin gabansa ma yake, yayinda ya watsar da batun auren acikin ransa. Inda yanzu auren ya kama saura kwana takwas kacal, domin dasa lokacin auren zuwa yanzu anci kwana shida acikin kwanakin bikin.
Adda Rahama da kanta taƙirayi Ummi inda tace ta tambayi Saifuddeen, ko yayi mgna da Ameena'n, sai alokacinne ma Ummi ta farga.
Aikuwa tana aje wayan, ta dubi Hayatuddeen dake kwance akan doguwar kujera yana chat.
Cikin kulawa tace.
"Hayatuddeen ƙiramin Hamma'n ka."
Take kuwa ya miƙe, inda ya nufi part ɗin Hamman nashi.
Koda yaje afalo ya iskesa, zaune akan wheellchair, inda yake sanye da dogon wando da kuma wata farar t shirt, laptop ɗinsa ne agabansa yana ta faman dannawa yana ta murmushin ganin amsar saƙon da ya kai kwana goma da turawa Zaleeha shi da numbarsa ta sirri in da ya nuna mata shi saurayine kuma yana sonta, to bata duba saƙonba sai shekaran jiya, bata kulashiba kuma sai yanzu da ya sake ce mata.
"Hello my love". Koda ta buɗe saƙon sai yaga ta turo mishi amsa.
"Wa iyazubillahi, kai wanne irin mutunne da zaka rasa wanda zaka so da bibiya sai matar aure, nayi block naka tun randa naga saƙonka sai kuma naga ka kuma min mgna ban san kai waye bane dake iya sarrafa na'urar da ba tasaba, na haɗaka da Allah da Manzonsa kada ka sake yimin mgna ni matar aurece, kaji tsoron Allah ka rabu dani!".
Murmushi yaketayi yana mai-maita karanta saƙonta, yasan dole tayi mmkin cewar tayi blocking nashi kuma taga ya sake mata mgna. A ranshi yake cewa.
"Baki san cewa nike sarrafa wayarki ba."
Saƙon Ummin Hayatuddeen yasanar masa, sannan ya juya ya fita.
Bai wani ɓata lokaci ba, ya nufi ɓangaren Ummin nasa bayan ya rufe system ɗin nashi.
Tana nan zaune akan kujera, tana ganinsa taɗan sanja yanayin fuskarta, sarai tasanshi dayaga murmushi akan fuskartata, to tabbas tasan zai ɗauki maganar da zata faɗa masa amazaunin wasa kuma zai samu damar shigar da ƙorafinshi.
Dubansa Ummin tayi bayan ya ƙaraso gabanta.
Cikin kulawa tace.
"Daga ranan dana baka number'n Ameena kawo yau sau nawa katura mata saƙo?."
Gane abun da ta faɗa yasashi kwaɓe fuska, tabbas yasan dama watarana za'ayi haka.
Ganin yanda ya kwaɓe fuska yasa Ummi cewa.
"Au baka tura mata saƙon ba kenan?."
Kansa ya jinjina alaman "Eh." danshi dama kwata-kwata bai iya ƙarya ba, sannan kuma koda wasa baya yiwa Umminsa ƙarya.
Duban sa Ummi tayi tare da cewa.
"To lallai katabbatar da yau katura mata saƙo, ko ka manta cewa aurenta zakayi ne?."
Fuska ya sake kwaɓewa, tare da ɗan ciza kyawawan laɓɓansa, shikam yaga takansa da wannan liƙaƙƙen auren, hakanan an tilastashi auren wata mayyar yarinya, gashi tun ma bata shigo cikin gidan nasu ba, Umminsa ta fara takura masa akanta.
"Kajini dae kam ko?."
Ummi ta katse masa tunanin da yake.
Kansa ya jinjina mata alaman yaji.
Daga haka Ummi batace dashi komai ba, ta juya inda ta wuce É—akinta, idanunsa yaÉ—an lumshe tare da buÉ—esu alokaci guda, kallonsa ya mayar ga Hayatuddeen wanda gaba É—aya hankalinsa nakan wayarsa, sai murmushi yake yi, da'alama wani abun yake.
Ƙura masa idanu yna ƴan wasu mintuna Saifuddeen yayi, kana ya girgiza kansa, cikin nutsuwa ya tura kekensa inda yabar falon.
Bayan yadawo Sallan Isha ne, yaje part É—in Ummin coffee ya amso tare da dawowa part É—insa, wayarsa ya É—auka inda ya shiga cikin Whatsapp chat É—insa.
Contact ɗinsa yabi inda ya laluɓo numbern Ameenan, da yayi seven ɗinta da sunan *Ta'annabi* a cewarsa wai sadaka za'a kawo misho ita shiyasa ya raɗa mata sunan Ta'annabi.
ido ya ɗan zuwa no tata wanda hoton ta nema akan profile picture ɗinta. View ɗin hoton yayi, inda ya ƙurawa hoton ido.
Sosai tayi kyau a hoton don tasha adone cikin wani jan lace, sannan fuskartan nan tayi fayau, don tana murmushi ne aka ɗauketa hoton, taɓe baki yayi tare da maganar zuci, mayya ko me ya tuno kuma sai yayi murmushi sannan ya rubuta mata saƙo kamar haka.
"Slm".
Ameena wanda kusan always tana online, kwance take akan gado, kamar da wasa kuwa taga numbern Saifuddeen É—in yayi mata magana, azabure tatashi ta zauna, cikin zumuÉ—i tace.
"Wayyo Allah ni daɗi kasheni, nakarɓi numbern ka wajen Hayatuddeen inason yi maka magana, sai gashi kai ka rigani."
Cikin sauri ta amsa masa da.
"Wslm".
harma da ƙarin tambayarsa.
"Ya gida."
Yana karanta saƙon nata, yaƙara taɓe laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace.
"Su mazari, daga magana sai amsa babu É—an jan aji kamar ba maceba."
ÆŠan jim yayi, cikin rashin sabo ya rubuta.
"Ykk." Sannan ya tura mata.
Lumshe idanu Ameena tayi tsabar daÉ—i, cikin mamaki tace.
"Wai yau ni Ameena Saifuddeen ke tambaya ya nake?."
Cikin sauri tayi typing.... "Lafiya ƙalau ya aiki, yasu Ummi?."
Saida yayi kusan 3 minute bai buɗe saƙon ba, kafun daga bisani ya buɗe.
Koda ya karanta ataƙaice yace.
"Lfy." Ya amsa ataƙaice.
Sanan ya kuma rubuta.
"Meyasa kika amincewa Aurena, bayan kinsan da cewa, ni kurma ne, sannan kuma bana iya tafiya?."
Ganin tambayar tasa yasa Ameena sakin murmushi, abayyane tace.
"Kaiɗin nakeso Saifudeen ina matuƙar sonka, inasonka fiye ma da yanda nakeson komai."
Arubuce kuwa cewa tayi.
"Nakasa Ba Kasawa Bace, inasonka aduk yanda kake, sannan kuma zan zauna dakai ahaka, aurenka kuma ba kasawa bace."
Koda ya karanta saƙon idanunsa ya lumshe tare dayin shiru, kamar zaice wani abu kuma, ataƙaice ya rubuta.
"Okay saida safe jekiyi bacci."
Daga haka ya kashe data'n sa, tare da aje wayan gaba É—aya.
Inda ya haurawa saman gado ya kwanta.
A ranshi yake cewa.
"Hmmmm kina dai da abin da kikeso a jikina, fitinanniya kawai mai idon cin maza."
Ameena kuwa ganin ya sauƙa online yasa ta lumshe idanunta, daɗi da farin ciki su suka cika zuciyarta, haka tayita juyi akan gadon, wani irin shauƙinsa ne ke damunta, da haka tayi bacci.
Tabbas akullum kwanaki ƙarewa suke, haka kuma lokaci na shuɗewa, akwana atashi asaran me rai, yau dai ya kama saura kwana uku kacal bikin Ameena da Saifuddeen.
Inda daga ɓangare biyu na gidajen duk shirye shiryen bikin suke.
Babu ma kamar gidansu Ameena, inda Ameena'n ke karɓan gyara na musamman, sosai ake mata gyaran jiki, hakan yasa fatarta tayi fresh.
Æangaren gidansu Saifuddeen kuwa, su Ummi ne kaÉ—ai ke kiÉ—a da rawansu, Saifuddeen iyakacinsa ido, tunkuwa ranan da yayiwa Ameenan magana ta Whatsapp baisake bi ta kanta ba.
Zaune suke su dukansu Afalon Ummi, nan Ahmad ya shigo inda yake ƙara sanar dasu batun tashinsu don dama ya kammala gidansa tuntuni, Nan fa Saifuddeen ya kafe kan cewar Ahmad ɗin babu inda zaije, ae tunda ya saka baki ake ƙoƙarin yi masa auren dole dolensa kuwa ya zauna agidan.
Duk kuwa yanda Ahmad yaso Saifuddeen da Ummi su barshi ya koma gidansa sun ƙiya.
Nandai Saifuddeen yace Hayatuddeen ya dawo ƙasa, su kuma Ahmad ɗin su koma sama.
Hakan kuwa akayi, inda aka gyara duka ɓangare biyun, Raliya ta tattaro kayanta suka dawo sama.
Hayatuddeen kuwa ƙasa ya dawo.
Can ɓangaren su Ahmad ɗin kuwa aka gyarawa Amarya Ameena.
Sannu-sannu bata hana zuwa saide adaÉ—e ba'a je ba.
Rana kuwa bata ƙarya.
Yau yakasance Alhamis, inda gobe Jumma'a É—aurin auren Saifuddeen da Ameena.
Acan Abuja yau Ameena ta gudanar da walima, inda aka yi wa'azi mai ratsa jiki, sosai kuwa waliman ya ƙawatar, don Ahmad dakansa ya tura mata kuɗi a account ɗinta, inda yace tayi duk wani hidima da takeso. Kana kuma yaune akaiwa Amarya jere, domin kuwa Babanta da kansa yayiwa kamfanin masu saida furnitures magana, ta online suka sai kayan, wanda Ameenan da kanta ta zaɓi kalan da takeso.
Ma'aikatan kamfanin kuwa suda kansu suka zo har gidan su Saifuddeen É—in suka jera mata kayanta, sosai kuma yayi kyau.
Washegari.
Jumma'a.
Ranan yau takasance jumma'a, wanda kuma ayau É—inne za'a É—aura Auren Saifuddeen da kuma Ameena.
Tun safe kuwa Saifuddeen yaƙi fitowa, inda ya ce bashi da lafiya, sanin cewa Ameenan ba budurwa bace, kana kuma ba agari za'ai ɗaurin auren ba, yasa sam su Bappa Ali basu matsa masa ba.