Sashe 32
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Messages ɗin Ya Ahmad kuwa sunfi 20 wanda da ya tura mata, wanda suke cike da tsantsar lallashi haɗi da ban-baki yake bata, tare dayi mata al'ƙawarurruka da dama akan idan ta dawo zai yi mata, ba irin al'ƙawarin da baiyi mata ba, har cewa yayi da ita.
"Pleess Zaleeha ki dawo gida hankali kowa ya tashi sabida rashinki,
wlh idan kika amince kika dawo gida, to zan sa araba aurenki da Saifuddeen, sannan kuma zan É—aukeki mu koma Abuja, zan sama maki aiki acan."
Koda ta karanta murmushi kawai tayi, sanin cewa hakan abune mai wahala, domin tasan cewa Yayan nata bashi da wani abun da yakeso, sai wanda Baba Malam yakeso, farin cikin Baba Malam shine nasa, tasan cewa bazai taɓa iya raba auren ta da Saifuddeen ba, domin yin hakan zaisa ya faɗa cikin fushin Baba Malam, wanda tasan da Ya Ahmad ɗin da ya faɗa cikin fushin Baba Malam, tasan zai gwammace gwara mutuwarsa.
Haka koda ta karanta text ɗin, ta watsar tare da gogewa, don kuwa sun cika mata inbox da saƙonninsu, ita harma ta gaji a can ƙasan zuciyanta kuwa ji take kamar taita kuka.
Æangaren Ya Habu kuwa, yau yagama shirinsa tsab, inda ya Æ™udurta aransa cewa, yau zai je Doho, wajen Yayar mahaifiyar tasu, wato Aunty Ruda, domin ransa amatuÆ™ar É“ace yake da ita, saboda yasan cewa, duk wani abu da maman tasu keyi, da sanya hannunta, kasancewar kowa yasan cewa, ita É—ince ke zugata akan wasu abubuwa itace ke gurÉ“ata komai na Mamansu.
Ya Ameenu kuwa yanzu damuwar rashin lafiyar matarsa ne ya damesa, don kuwa tun randa Zaleeha ta gudu, Maryam ta kwanta zazzaɓi da ciwon kai, kasancewar bata da wani aiki kullum sai kuka, sosai ɓatan ƴar uwartata ya shiga jikinta, gefe guda kuwa ga Baba Malam daya shiga halin baƙin ciki, kowa ya gansa yasan da cewa yana cikin damuwa, kasancewarsu Yara masu biyayya hakan yasa basa ƙaunar ganin damuwar mahifinsu, uwa uba ga Mama da ta bar gidan, wannan abu na damun Maryam sosai, ganin lokaci ɗaya zuri'arsu naneman watsewa komai ba daɗi ga ɓatan ƴar uwa ga saɓani tsakanin iyayenta ga ɓacin ran mahaifinta damuwa dai ta taru ta cika zuciyar baiwar Allah.
Ƙarfe 10 na safiyar ranan dai-dai Ya Habu ya kama hanyar zuwa Doho.
Zaune yake akan wheelchair ɗinsa mai kalan silver gold, sanye yake da wani army jeans, sai kuma wata farar long sleeve wanda ya nannaɗe hannun rigar zuwa guiwar hannunsa, aƙafansa kuwa, wasu fararen bedroom slippers ne masu kyau, kamar koda yaushe laptop ɗinsa ne, ɗaure akan cinyarsa, sosai ya bata hankalinsa gurin binciken da yakeyi.
Gefensa Ummi ne wanda tayi jigum, duk damuwan ɓatan Zaleeha ya isheta, kusa da ita kuwa Hayatuddeen ne zaune yana ta faman latsa wayarsa, inda ya ɗan kaucewa ganin idanunsu ya matsa can gefe, chatting yake sosai, da wani sabon abokinsa da yayi acikin G.S.U, wanda yakasance department ɗinsu ɗaya, sunan abokin nasa Khamis, sosai Hayatuddeen yasoma shaƙuwa da Khamis, wanda yake kuma Khamis, yaro ne wanda bayajin magana sam, babansa mai kuɗin gaske ne, gidansu yana nan cikin New G.R.A, gaba ɗaya Khamis asangarce yake, kasancewarsa shine ɗa namiji agidansu, hakan yasa gaba ɗaya iyayensa suka sakar masa yarda, tare da bashi daman yin duk abun da yake so, shikuwa Khamis tun da yaga Hayatuddeen, yaji cewar yana sonsa da abota, kasancewar Hayatuddeen ba laifi yana shiga mai kyau da burgewa, sannan yana ɗan chilling ɗinsa, da sabuwar iphone ɗinsa, makaranta kuwa kaisa ake amotar gida sannan driver ya ɗauko sa, shikuwa Khamis jibgegiyar motace ahannunsa, hakan yasa ko zaman school ɗin bayayi, da yazo sai yawo kawai, kamar da wasa kuma suka fara abota da Hayatuddeen wanda gashi kuma zuwa ayanzun abotan nasu ya soma ƙarfi.
Ajiyar zuciya mai Æ™arfi ya sauÆ™e tare da lumshe kyawawan idanunsa, buguun zuciyarsa ne ya É—an sassauta ahankali, hannunsa yasanya inda ya kama Æ™asan haÉ“arsa, numfashi ya sauÆ™e, tare da fesar da wani irin iska mai zafi ta bakinsa,Â
*"NUMAN"* shine abun daya faɗa acikin zuciyarsa, sake duba inda location ɗin ya tsaya, kansa yajinjina tare da ɗan cije laɓɓansa, tabbas tana can Adamawa cikin Numan domin kuwa, haka sakamakon tracker ɗin da yayi ya nuna mishi.
ÆŠan jim yayi tare da lumshe idanunsa,Â
"Tabbas tana can Numan, amma kuma waye nata acan, da zata je ta zauna?."
Tambayar da yayiwa kansa kenan, sanin cewa bashi da amsa yasa shi, sakin ɗan guntun murmushi, wato da zama dashi ne ta gwammace rayuwa a wancan ƙauyen mai cike da yawan ƙabilu arnataku, hmmmm shikuwa zai zuba mata ido ya gani, bakuma zai faɗawa kowa inda take ba, sannan zaiyi duk yanda zaiyi wajen ganin, ya cire Umminsa adamuwa, dan tasanya ɓatan Zaleeha'n, sosai acikin ranta.
Ta gigita mishi Æ´an uwa da abokai gaba É—aya, Ishaq Salisu Warisu Mudassir Aziz hatta Saminu Hishsm, Jabeer, da baya garin duk ta tashi hankalin kowa.
Yasan ko ahaka Allah bazai bar Zaleeha ta zauna cikin farin ciki ba, saboda yasan ta É—auki al'hakin iyayenta, sannan ga igiyar aurensa dake kanta, wanda take ta walagigi dashi.
Wheelchair ɗinsa ya danna inda ya ƙarasa har gaban Umminsa, hannunsa ya ɗaura akan na Ummi'n, cikin kulawa ya karyar da kansa, tare da ɗan marairaice fuska, anutse yayi mata alama, cikin body language cewa.
"Ta daina sa kanta adamuwa, Zaleehan zata dawo nan bada jimawa ba."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe, cikin rauni ta dubeshi, murya asanyaye tace.
"Banajin daɗi Saifuddeen, idan na tuna da cewar sanadiyar aurenka Zaleeha ta gwammace barin iyayenta, yayunta, ƙannenta, aikinta, mahaifanta, da duka danginta, wannan abun shine abun danake ta gudu tun farko, shiyasa naso afasa auren, gashi yanzu an nemeta an rasa, babban tashin hankalina ma, shine bamu da tabbacin cewa ko lafiya take!."
Kansa ya girgizawa Ummin nasa, tare dayi mata alaman cewa.
"Zaleehan tana nan lafiya ƙalau aduk inda take."
Kai kawai Ummi ta jinjina masa don bata iya cewa komai.
Can Doho kuwa, Ya Habu na isa gidan Aunty Ruda yayiwa tsinke, Aunty Ruda na ganinsa ta taɓe baki, don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, first abun da Ya Habu ya fara tambayarta shine.
"Ina suka kai Zaleeha?."
Shewa tayi tare da cewa.
"Ae baku bani ajiyan Zaleeha ba, balle kuce zaku zo nemanta, abu mafi sauƙi ku shiga uwa duniya ku nemeta kawai, tun da kune kuka salwantar da rayuwarta."
Wannan abun shiya ƙara harzuƙa Ya Habu, nan take ransa ya ƙara baci, haka yayiwa Aunty Ruda'n tas, inda ya wanketa soso da sabulu, ya ɗora da cewar.
"Ita ke zuga mamansu akan komai, kuma wallahi su fito da Zaleeha, duk ma inda suka kaita suka ɓoyeta, kuma ta daina zuga musu uwa tana tura mata halinsu na arna ya ƙara da cewa kada tayi zaton basu gane ita ke zuga Mamaba."
Haka yabaro Doho'n ransa amatuƙar ɓace, domin yasan da cewa sunsan inda Zaleehan take faɗa ne kawai bazasuyi ba.
Bayan kwana 5 da dawowan Ya Habu daga Doho, Baba Malam ya kwanta rashin lafiya, inda ciwon hawan jininsa ne ya tashi, nanfa gaba ɗaya ahalin suka sake shiga cikin tashin hankali, ga jikin Maryam ma da yaƙi daɗi, bata da wani zance saina ƙanwarta Zaleeha.
Saifuddeen dake zaune afalon Ummi ne, ya kwantar da kansa ajikin kujera, yanzu labarin rashin lafiyar Baba Malam ya iskesa, hakanne yasa yaji babu daɗi acikin ransa, sam ada baiyi niyar faɗawa kowa inda Zaleehan take ba, yaso barinta ne idan tagaji don kanta zata dawo, amma ayanzu yazama dole ya faɗa, kodan saboda rashin lafiyar Baba Malam ɗin ma.
Computer ɗinsa ya ɗauka, inda yayi rubutu mai ɗan tsawo, sannan ya nunawa Ahmad, bai jirayi Ahmad yagama karanta saƙon ba, ya ciro wayarsa inda ya turawa Ya Ameenu saƙo, wanda ya rubutashi ataƙaice.
Ahmad nagama karanta saƙon ya ɗago ya dubi Saifuddeen, kai Saifuddeen ɗin ya jinjina masa, ajiyar zuciya Ahmad ɗin ya sauƙe, nan yakai dubansa ga Ummi, sai kuma Adda Rahama dake zaune, cikin nutsuwa Ahmad yace.
"Ummi Saifuddeen ya ganno inda Zaleeha take fa."
cikin mamaki Ummi tace.
"Ta ina? Tana ina? ko wani abune ya sameta?."
Kai Ahmad ya girgiza, cikin nutsuwa yace.
"Uhmmm Ummi kenan wato dai kuna ganin kaman Zaleeha ɓata tayi ko, hmmm to wlh Zaleeha ba ɓata tayi ba, guduwa tayi da ƙafafunta, sannan yanzu haka tana can Numan, halan akwai wasu ɓoyayyun ƴan uwanta acanne, wanda tunanin su Ya Ameenu da Habu baije can ba, amma dai yanzu Saifuddeen ya faɗawa Ya Ameenu'n."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayin hamdala acikin ranta, tabbas ta ɗanji sanyi acikin ranta,don dama ɓatan Zaleehan yayi mata tsaye acikin rai, itakuwa Adda Rahma shiru tayi tana meyin wasu nazari, hakanan Zaleehan ta soma sanewa acikin ranta, tabbas ita duk wani wanda baison Saifuddeen, to fa itama bata
ƙaunarsa ko kaɗan. Raihana kuwa da dama can bata wani sake da Zaleeha a rantaba, sai taji ta fice mata a rai haushinta kawai takeji har ita waye da zatace bata son Hammanta me ya rasa dame sauran maza suka fishi haka dai taketa ƙunƙuninta.