← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 146 OF 154

Sashe 146

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 3 min read

ɗago kanta, kansa yaɗan jinjina cikin kulawa yace. "Sannu ko, ya jikin naki?." Kanta taɗan jinjina masa alaman da sauƙi, ɗan ƙaramin jakan dake hannunsa ya ajiye, yana ƙoƙarin saka hand clobes ahannunss yace. "Ina da ina ke miki ciwo?." awahalce taɗan karyar da wuyanta, murya asanyaye tace. "Amai da jiri nakeji, sai kuma tashin zuciya da zazzaɓi, gashi bakina duk ba daɗi". Idanu yaɗan zuba mata, lokaci guda kuma sai ya ɗan saki murmushi, bargon da take rufe dashi yaɗan yaye, hannunta ya kamo tare ɗa ɗaura mata wani abu kaman igiya, ganin ya fito da allura ne yasata rumtse idanunta da ƙarfi tare dasa hannu ta riƙo hannun Hamma Saif ɗin. Jininta yaja sannan yayi mata wata allura, wanda yasan zata ɗan taimaka mata, dai-dai lokacin Ummi da Raleeya suka shigo cikin ɗakin, amutumce suka gaisa da Dr.Adnan ɗin, nan yace musu zai koma asibiti dan yanaso ya gwada jininta daya ɗiba, "to" sukace sannan ya fita. Ummi ne ta ƙaraso jikin gadon, kan Zaleehan ta shafa, cikin kulawa tace. "Ayya Zaleeha sannu kinji, ya jikin naki?." Jin muryan Ummi ya sa ta buɗe idanunta ashagwaɓe tace. "Da sauƙi, amma Ummi jiri fa nakeji kuma har da amai". dagajin yanayin maganan nata kasan ba iya zafin ciwo bane, harda zallan shagwaɓa ne da raki. Sake shafa kanta Ummi tayi cikin kulawa tace. "Sannu ko, zaki samu sauƙi insha Allah." Raleeya ne tayi mata ya jiki, jinjina mata kai tayi alaman da sauƙi. Zama sukayi awajenta suna ƙara shagwaɓata da kuma tattalinta, Saifuddeen ma kasa barin ɗakin yayi, idanunsa kawai ya zuba mata, ita kuwa kasancewar alluran da Dr.Adnan yayi mata nada ƙarfi, hakan yasa wani irin bacci me nauyi ya ɗauketa. Ba'awani ɗau lokaci sosai ba Dr.Adnan ya dawo, fuskarsa cike take da wani irin annuri haɗi da zallan farinciki, ahankali ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo, ganin yanda yake sakin murmushi hannunsa riƙe da wata farar takarda yasa suka zuba masa ido, Saifuddeen ne ya fara cewa. "Lafiya kuwa Dr. me yake damunta?." Ƙarasowa cikin ɗakin yayi tare da miƙawa Saifuddeen ɗin hannu, alaman su gaisa, da ɗan mamaki Saifuddeen ya basa hannunsa, cikin bayyana farinciki Dr Adnan yace. "Congrats Bro, Zaleeha na ɗauke da cikinka almost 2 to 3 month." Tamkar shigar shock haka duka sukaji maganan acikin kunnensu, Jikin Saifuddeen ne ya soma ɓari, cikin matsanancin mamaki, jin abun yayi kaman al'amara, duk da yasan cewa shiɗin baida matsalan rashin haihuwa, amma hakanan yakejin batun cikin Zaleehan kaman amafarki, Allah mabuwayi me yin yadda yaso a lokacin da yaso, yau gashi Zaleeha macen da zuciyarsa ke tsananin so da muradi, tana ɗauke da cikinsa, zamewa yayi daga kan wheelchair ɗinsa yayiwa Allah sujjada, dan nuna godiya da kuma tsantsar farincikinsa. Ummi da Raleeya kuwa ba abun da suke cewa sai. "Alhamdulillah Masha Allah." Cike da matsanancin farinciki, Ummi ta dubi Zaleeha, wanda ita bata ma san meyake gudana ba, dan baccinta ya ɗanyi nisa, Murmushi me ɗauke da farinciki tayi, cikin jin daɗi tace. "Allah sarki Zaleeha yarinyar kirki, Allah Ya miki albarka, ya kuma sauƙeki lafiya". Sai alokacin Saifuddeen ya ɗago daga sujjadan da yayi, kan wheelchair ɗinsa ya hau, sannan ya ƙaraso jikin gadon, wani irin farinciki ne bayyane akan fuskarsa, rungume Ummin sa yayi ƙam, tamkar wani ƙaramin yaro, cikin kasa ɓoye farincikinsa yace. "Alhamdulillah, Ummi na kinga Allah me iko ko, yabani kyauta me mahimmanci alokacin da ba zata ba, Ummi ki taɓa zuciyata kiji, har wani tsalle take saboda tsabar farinciki." murmushin jin daɗi Ummi tayi, cikin kulawa tace. "Nasan kana cikin farinciki Babana, kuma muɗinma hakane muna cikin farin cikin." Ɗan janye jikinsa daga na Ummi'n yayi, inda ya ƙurawa Zaleeha mayun idanunsa, cute face ɗinta yake kallo, wanda tayi fayau da ita, lokaci ɗaya har taɗan rame. Wani sabon zazzafar soyayyarta da ƙaunarta ne ke ratsa duk jikinsa, haka yakeji kaman ya jawota ya rungumeta.
Chapter 146 · 0% Book details