← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 154

Sashe 96

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Can ɓangaren Saifuddeen kuwa, kwalliya yasha cikin wata haɗaɗɗiyar shadda ƴar mita me kyaun gaske, wacce take da kalan dark greeen, sosai tayi masa kyau, ga kuma hulan zanna bukar daya kafa akansa, wani tsadadden agogo ya ɗaura atsintsiyar hannunsa, sosai yayi kyau, yayinda sajen fuskarsa ta kwanta lub-lub, turare ya fesa, wayansa kaɗai ya ɗauka, sannan ya fice daga cikin ɗakin, bayan yasawa ƙafansa takalma flat shoe irin na maza me tsadan gaske.
Anan compound ɗin gidan ya haɗu da Ahmad wanda ya jiƙu da ƙyau shima cikin shigar shadda milk colour, atare suka wuce masallaci. Zaleeha kuwa koda ta fito daga wankan sama sama taɗan shafa lotion ajikinta, wata haɗaɗɗiyar powder ta shafa akan fuskarta, wanda tayi mata kyau sosai, kajol da kuma lipstick kawai ta shafa, bata wani cika kwalliya akan fuskar tata ba, wani haɗaɗɗen riga da sket na atamfa tasanya ajikinta, sket ɗin irin pieces ɗinnan ne, yayinda rigar kuwa ta kasance fitted, sosai kayan sukai mata kyau, kasancewar atamfar nada kalan ja ajiki, yasa ta yafa wani haɗaɗɗen mayafi me kalan ja, wani ɗan hill ta sanya aƙafanta me masifar kyau, waya da kuma ɗan jakanta ta ɗauka, tayi kyau matuƙa sai faman baza ƙamshi take, kallon kanta taɗanyi amadubi ta numfashi ta ɗan sauƙe ita kanta taga ramarta.
Juyawa tayi cikin nutsuwa, ta fice daga É—akin nata, kai tsaye sashin Ummi ta nufa, zuwa lokacin kuwa har sun dawo daga masallaci.
Saida Numfashinsa yakusan ɗaukewa alokacin daya ganta, tayi masifar kyau, gashi skin ɗinta ya ƙara haske. Ummi ne tayi musu fatan al'khairi da kuma adawo lafiya, sannan suka fita, yana gaba yana me sarrafa wheelchair ɗinsa, ita kuma tana biye dashi abaya.
Haka suka ƙaraso har wajen mota, Sule driver ne ya buɗe musu motar cikin hanzari suka shiga. Anan gidan baya suka zauna.
Cikin nutsuwa kuwa Sule driver ke tafiya dasu, gaba ɗaya daddaɗan ƙamshin turarensu ne ya cika cikin motar, hakan kuwa ya bada wani irin yanayi me daɗi.
Ɗan lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta da jikin kujera, shikuwa Saifuddeen wani aiki yake shiyasa gaba ɗaya hankalinsa nakan wayarsa ƙiran Samsung S20.
Ahaka suka isa gidan Baba Malam ɗin, jin tsayuwar motar ne yasa duk suka ɗago idanunsu, wani ajiyar zuciya Zaleeha ta sauƙe, sannan ta buɗe murfin motar ta fito, Saifuddeen kuwa Sule driver ne ya buɗe masa murfin motar ya fito, bayan ya ware masa wheelchair ɗinsa. Kusan atare suka jera, sashin Baba Malam ɗin suka nufa.
Zaleehan ce tafara tura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
Baba Malam, da kuma su Mamy sai Ya Ahmad da kuma Ya Ameenu ne zaune afalon, can gefe kuwa wasu ayarin mutane ne wanda aƙalla zasu kai su 15, Ciki kuwa hadda Uncle Solomon da kuma matarsa Elizabet, ga kuma Baffa wato baban Aisha.
Cike da mamaki Zaleeha ta ƙaraso cikin falon tana ɗan rarraba idanunta, ganin Baffa yasa tace.
"Laa Baffa kaine agarinmu?"
ɗan murmushi Baffan yayi tare da cewa. "Ƙwarai kuwa ƴata nice." Nan ta durƙusa har ƙasa ta gaishesa, sannan ta gaishe dasu Baba Malam, wannan karon kam har Ya Ameenu ta gaisar kuma ya amsa mata.
Ƙarasowan Saifuddeen cikin falon ne yasa, Baba Malam faɗaɗa fara'ar dake kan fuskarsa, cikin kulawa haɗi da mutuntawa ya tarɓi Saifuddeen ɗin. Cikin girmamawa kuwa Saifuddeen ɗin ya gaishe dasu Baba Malam ɗin, harma da Baffa'n Aisha. Haka Baffan Aisha ya amsa fuska asake yana yabawa da kyau haɗi da kwarjinin yaron. Anutse kuwa Saifuddeen ya gaishe dasu Mamy da kuma Mama.
Fuska asake duka suka amsa masa, Mama kam sai faman sunne kai take, dan kunyar Saifuddeen É—in takeji, uwa uba kuma kwarjinin da yake dashi. Zaleeha kuwa bayan ta gaishe dasu Mama, kusa da Ya Ahmad É—inta taje ta zauna, zuciyarta fari tas, wani irin dadi takeji, musamman ma da take hango fariniki akan fuskar gaba É—aya ahalin nata.
Bayan sun É—an nutsane Baffa keyi mata bayanin cewa.
"Ai su Solomon musulunta sukazo yi, dan zamanta awajensu yasa sunji kwaÉ—ayi da sha'awar addinin musulci, sun kuma gano cewa shine haske dake haskaka rayuwar duk wanda ke cikinsa, saboda haka suma suna so su musulunta, zasu musuluntan ne kuma ba saboda kowa ba, saidan suma su samu dacewa da rahamar Allah, sukuma samu daman É—anÉ—ana ni'ima da kuma baiwar dake cikin musulunci, saidai ance dama komai nada sanadi, to ita ce ta kasance sanadiyar musuluntar su Solomon É—in wanda harda fastonsu suka zo wanda shima zai musulunta, shiyasa basu musulunta tun tana canba dan sunce sai sunar mishi koda suka gaya mishi ko shima yace zai musuluntan."
Wani irin daɗi da farinciki ne suka cika zuciyoyin gaba ɗaya ahalin, wani irin ni'im taccen daɗine ke ratsa zuciyar Baba Malam da kuma Saifuddeen, Allah mai iko yaugashi asanadin Zaleeha mutum ɗai ɗai har goma shabiyar zasu musulunta, tabbas zuwanta garin Numan yazamanto al'khairi, zuciyar Baba Malam ne tayi wani irin haske, take yaji duk wani abu dake ransa ya kau, ƙaunar ƴar tasa ne ya shigesa, har takai ga yanajin kamar ma bata taɓa yi masa wani abu na laifi ba. Saifuddeen ma yaji daɗin haka, take kuwa Baba Malam da kuma Baffa'n, suka shiga bawa su solomon da kuma sauran maƙotansu da suka biyosu dan suma suna son musulunta, kalman shahada, wasu suyi dadai wasu kuma su kwaɓa harsai angyara musu, ahaka dai har dukansu suka musulunta, su Ya Ahmad ne suka ce.
"Allahu Akhbar, haƙiƙa Allah da girma yake, yau gashi Zaleeha ta jawo sanadiyar musuluntan mutane 15, gaskiya wannan abun farinciki ne acikin zuri'arsu dama musulunci baki ɗaya." Haka dai duka zuciyoyinsu suka cika da farinciki da kuma jin daɗi.
Daga nanne Saifuddeen ya basu kuɗi masu yawa, dan su saya ƙaton fili acan garin nasu, sukuma yi ginin masallaci da kuma makaranta, Baba Malam ne yace.
Shi zai ɗauki nauyin ginin masallaci da kuma makarantar, sannan kuma zaiyiwa babban shugaban malaman izala dake can numan ɗin, akan cewa asama musu malamai waƴanda zasu riƙa koyar dasu addini. Ya Ahmad ma take yace zai bada gudumowarsa 1mil.
A nan Man Lima ya nemi keɓawa da Baba Malam ya sanar mishi dukkan abubuwan daya samu a jikin Zaleeha na sihiri,
Tabbas sihiri gsky ne yana kama ɗan adam tunda ya kama fiyeyyen halittama badon gazawar shiba ko tawayar darajarta ba a a sai dan nuna mana cewa zai iya kama mutun, sai dai tasirinsi ƙalilan ne, sosai Baba Malam yayi mamakin wannan al'amari, kana yayiwa Man Liman godiya mai tarin yawa.

Kana anan take ya kira shugaban ƙungiyan izala reshen Adamawa dake cikin numan ya shaida musu abin Al'khairi daya samu,
su kuma sun É—auki niyar koyar dasu dukkan wani abinda ya kasance na addini,
babban farin cikinsu ga masallaci da islamiyar da za'a gina a yankin da da babu hasken musulunci sai warin kafurci dana burkutu da kashin aladu.

Zaleeha kam farin cikinta bazai misaltuba, kayan da tayi budurci dasu kab ta kwashe ta basu, dan ta san basu da wadattun suturu daya dace suke sawa, Mamy ma da Aunty Lubna sun basu kayayyaki da manya-manyan hijabai,
Mama kuwa saida tayi kuka wato Allah yaso wasu da rahma ne yasa ita da kanta ta tura ƴarta can da nufin watsa sunnar manzo sai gashi sanadin haka addini ya samu ƙaruwa.

Sune dai basu tafiba sai bayan sallan al'asar.

Bayan tafiyan sune Baba Malam ke sheidawa Zaleeha batun an É—aura auren Ziyada da Ya Ameenu,
wannan al'amari yasata ƙara nitsuwa da jin tsoron Allah.

Shi kuwa Saifuddeen sallamansu yayi cewa zaije wurin Ishaq, sai bayan magriba zaizo su tafi gida.

Baba Malam kuwa shida kanshi ya É—auki Ziyada da Ya Ameenu da Ayman É—an Adam Maryam ya kaisu gida.
Sosai ya zauna yayi musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya,
gaba ɗayansu kuka sukeyi sabida al'amarin ubangiji ya wuce wasa ko a zato ko a mafarki basu taɓa zatawa kansu zama mata da mijiba inba mutuwaba mai zai raba Adda Maryam da Ya Ameenu har ya aureta.

Bayan tafiyan Baba Malam ne, ya Ameenu ya ari jarumtar dole dan kukan da Ziyada keyi ya tsananta dole ya fara rarrashinta da nuna mata suyi haƙuri ƙaddar suce haka kums kowa da irin tasa.

Sai bayan sallan magrib Saifuddeen ya dawo shida Sule dan É—aukan Zaleeha su koma gida,
nan kuma ya Ahmad yasa dole suka zauna suci abinci ruwa kawai Saifuddeen yasha don yaci abinci a gidansu ishaq ita dai Zaleeha taci da Aunty Lubna tayi haniƙan dan yau tana cikin farin ciki.

Kafin su gama kuwa an kira sallan isha'a dole sukayi salla kafin Zaleeha ta fito suka tafi gida.

A can gidansu Saifuddeen kuwa tun ƙarfe shida Ameena ta dawo aiki,
tayi mmkin ganin Zaleeha bata gidan ita da Adeel, hakama Saifuddeen baya nan,
Hayatuddeen ta samu a falo bayan taje ta gaida Ummi cikin gajiya tace.
"Autan Ummi Ina Adeel da Amminshi?".
ruwan daya kurɓa ya haɗiye tukun kana yace.
"Sunje anguwa".
Murmushi ta É—anyi tare da cewa.
"Ayyah".
Har ta nufi bakin ƙofar fita sai kuma tace.
"Hamma Saifuddeen fa ya fita ne?".
Hankalinshi na kan wayarshi yace.
"Tare suka fita."
Wani irin malolo taji ya daki ƙirjinta wani zazzafan kishi ya taso mata,
sai kuma tayi ƙarfin halin dannewa murya a daburce tace.
"Okay". Kana ta juya ta fita tana yaƙi da zuciyarta da kuma shaiɗan dake son ɓata mata daren yau ɗin bayan jiyama haka ta kwana tana fushi da mijinta ya nuna yanada buƙatar haƙƙinshima ta hanashi still yau kuma shaiɗan naso ingizata a fili tace.
"A'uzubillah menene dan ya fita da marsa kuma da É—ana".
A haka taje tayi wonka tayi al'wala kana tazo ta kabbarta sallan magriba dan lokaci yayi.
Bata tashi bisa sallayanba saida tayi sallan isha kana ta can-canÉ—a ado cikin wani dandatsestsen boyel mai azabar kyau sosai tayi kyau sihirtaccen kyanta ya baiyana.
Chapter 96 · 0% Book details