Sashe 10
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ahmad ne yabi bayan Ishaq da ya shiga bedroom É—in Saifuddeen, akan gado suka sameshi, yana zaune kana abokinshi Aziz Wanda ya kasance babban SS shima yana zaune gefenshi duk sun zubawa laptop É—in idanu bisa dukkan alamu wani abun Saifuddeen ke nuna mishi, kana da alamun tashin hankali a fuskarsu.
Ahmad ne ya kalleshi da kyau kana ya zauna kan durowar gefen gadon,
ganin hakanne yasa Saifuddeen gyara zamanshi kana ya jingina bayanshi da kan allon gadon. Wayarshi ya É—auka text ya turawa Umminshi cewa yana jin yunwa kuma ya gaji.
yana turawa ya ajiye wayar sannan ya ɗan miƙawa ishaq hannu suka yi irin gausuwarsu sanna ya kuma kalli Ahmad daketa mishi kallon tuhuma.
Da Sallama Ummi da Adda Rahma suka shigo falonshi dake cike da abokanshi gaisawa sukayi sannan suka wuce cikin uwar É—akan,
yana ganin Umminshi ya ɗan kwaɓe fuska tare tanƙwashe kanshi bisa kafaɗunshi yayi rau-rau da manyan idanunshi da suke cike da tashin hankali da tarin gajiya,
da sauri Ummi ta zauna gefenshi,
murmushin jin daɗi yayi tare da raɓawa jikinta,
hannnta tasa kan goshinsa sai kuma tayi saurin sunkuyiwa ta leƙa fuskarsa tare da cewa.
"Meke damunka?." rumtse idonsa yayi da ƙarfi, sanna ya buɗesu,
Adda Rahma kuwa murmushi kawai taketayi a ranta take cewa.
"Hmmm shaleleln Ummi wannan ɗan shagwaɓan inaga randa duk ya kusanci matarma sai anyi jinya biyu mutun sam shi baya son wahala abu kaɗan sai yazo yayi ta narkewa Umminshi yana shogoɓa."
a fili kuwa ajiye kulolin abincin da suka kawo mishi tayi tare da zama ƙasa kan carpet ta kamo hannunshi alamun tausasawa,
sai kuma ta ɗan leƙo fuskar wayarshi da yake nunawa Ummi inda ya rubuta,
"Ummi sacemin ita akeson ayi, meyasa? me tayi musu? wayake shirya sacemin matata ranar da za'a kawo min ita gidana? me nayi musu?."
cikin kaÉ—uwa da tsoro Rahma ta mike tsaye tare da cewa.
"Su waye ne Saifuddeen meyasa zasu saceta?."
Ummi kuwa wani irin fargabane da tsoro ya rufeta jiki a mace ta kalli Ahmad da ishaq da Aziz ta musu bayanin abinda ya rubuta mata sosai Ishaq da Ahmad suka shiga ruÉ—ani Aziz kuwa kai ya jinjina tare da cewa.
"To ai da sauƙi tunda mun gano shirinsu,
tun a zuwa ɗaurin aure Saifuddeen ya gano akwai baƙin ayarin motocin da suka shiga sahunmu kana ya ɗauki numbers ɗin motocin ya kuma bi diddigin inda aka sai motocin ashema a kamfanin Salisu ne, to yanzu bincike yazo mana da sauƙi dan Salisu ya bamu komai na masayin motocin harma da number wayarsa, shine ya bawa Saifuddeen damar bibibiyar kiran wayar dama motsinsu munji shirinsu na son sace Zaleeha."
wasu siraran hawayenesu ka zubowa Ummi murya a raunace tace .
"Aziz ku nemo hukuma a lamarin."
kai Saifuddeen ya jujjuya mata alamun a a,
shi kuwa aziz gyara zama yayi tare da cewa.
"Uhmmm Ummi kenan to ai su kansu Hukumar Saifuddeen ne idonsu, tunda duk wani tantirin daya gagaresu gane inda yake Saifuddeen suke miƙawa aikin bin diddiginshi ta na'ura mai ƙwoƙwalwa yake gano musu komai, to yake binciko tantiran da basu shafeshi bama bare wannan dake son sace mishi amarya, yanzu haka ya tsara komai ya kuma haɗe kiran wayar waɗancan da wayata, yanzu haka hatta motar da ya saya dan ɗauko amaryarshi suma sun sayi irinta, dan su samu damar sacetan, rashin sanin Saifuddeen yana ɗaya daga cikin tawagar UPSC, ne ya sasuyin wannan gangancin."
Adda Rahma kam gaba ɗaya hankaƙinta ya tashi, sai dai ganin yadda Saifuddeen ke basu ƙarfin guiwa yasa hankalinsu ya ɗan konta, Adda Rahman ne ta kalli Aziz tare da cewa.
"Wacce tawaga ce kuma UPSC?."
Cikin fidda nufashi yace.
"Ma'ana tawagar Union public service commission! sai dai sirrance yake musu aikin, ƙarƙashin jagorancin DSS."
Jinjina kai Adda Rahma tayi dan ta fahimci sirri Saifuddeen ke yi wanda ba'a cika son mutane su saniba, duk da sunsan yana tare da DSS amman basuyi zaton matsayin aikinshi ya kai nan ba.
nan suka É—an sashi yaci abinci sannan suka fita suka tafi.
Ƙarfe 4 dai-dai kamar yanda al'adan gombawa takasance da yamma suke ɗauko aure kuma hakan ya samu asaline tun lokacin da ƙungiyar ƴan kalare suka fare da sace amare in za'a kaisu gidajen aurensu da dare shiyasa aka dawo da al'adar garin kai amarya gidanta da yamma ido na ganin idop.
Hakan yasa gaba É—aya abokan saifuddeen sun shirya tsab don zuwa É—auko amaryarsu, motoci ne masu uban yawa suka tanada don zuwa É—auko auren, tuni su Ahmad, Ishaq, Salisu, Wareesu, Saminu, Mudassir, Jabeer, Hisham, ibrahim, Rabi'u, Aziz, Aryan, Gaddafi,duk sun kammala komai, kowa yasanja shiga irin ta alfarma.
Ahankali Saifuddeen yake tuƙa kekensa, har ya ƙaraso harabar gidan, sanye yake da ɗanyar shadda blue mai masifar kyau, sai shinning take yayi kyau matuƙa, saidai awannna karon baisanya gareba, hasalima rigar half jumper ce, su Adda Rahama da suka fito don zuwa ɗauko aure tana ganin ƙaninnata taƙarasa garesa da sauri, yanaganinta ya sakar mata murmushi tare da shagwaɓe mata fuska kaman wanda zaiyi kuka, murmushi Adda Rahama tayi tare da ƙarasowa ta shafa gefen fuskarsa, cike da ƙaunarsa tace.
"To sakalallen Ummi na farko yanda naga ka shagwaɓe fuskarnan so kake kace kagaji ko? ehem ai duk wata shagwaɓa Hayatuddeen awajenka ya koyota."
Murmushin daya bayyana fararen haƙwaransa yayi tare da ɗan lumshe idanunsa, hannunta ya kama inda ya ɗaura adai-dai saitin heart ɗinsa, dariya me haɗe da murmushi tayi, cikin jin daɗi ta dubesa inda tace.
"Kamar yanda kake cikin farinciki Saifuddeen haka muma muke, farincikinmu nayau bazai misaltuba angon Zaleeha!."
Yanzunkam dariya sosai Saifuddeen ɗin keyi saidai babu sauti, sosai maganan addan nasa tafaranta ransa, ganin yanda yake dariya yasa Adda Rahama lumshe idanunta tana mejin daɗi acikin ranta, ita da kanta takoma bayansa inda ahankali take ɗan tura kekennasa, harsuka ƙarasa gaban wata hamshaƙiyar ƙatuwar mercedess benz 2019 mai azabar kyau da tsada, sabuwace dal sai shinning take tana ɗauke ido, shida kansa ya shiga motar kamar yanda ya saba, inda Ahmad ya naɗe kekensa ya tura masa cikin both, nanfa kowa yashiga mota, inda ƴan ɗauko amarya ma suka shiga tasu motar, ajere haka motoci ashirin da shidan ke tafiyan gwano akan babban titin, kasancewar Gombe akwai manyan tituna sannan kokusa babu ƙazanta akan gaba ɗaya titunansu, cikin motoci ashirin da shidan nan tsakiyarsu ta Saifuddeen take wanda cikintane za a ɗauko amarya.
Tunda ta kwanta bacci ba ita ta tashiba sai 3:40 cikin ikon Allah kuwa jikinnata yayi sauƙi sosai don koda tatashi babu abun da takeji, don taɗan samu kuzari ajikinta, still Aunty Lubna da Maryam da Aunty Shatu ne suka tsaya kaida fata inda sukaga tasake sabon wanka, to fa yanzukam meckup aka tsantsara afuskartata ta musamman, kayan da tasa kuwa ya banbanta dana ɗazu, duk da kasancewarsu duka dogin riguna ne, saidai wannan na wani tsadadden shadda lace ne me matsifar kyau, shima ɗindai akwai ratsin ja ajikinsa, sosai yayi bala'in yi mata kyau, ɗauri ɗankwali aka zizara mata tare da yane mata jiki da babban mayafi, wasu tsadaddun sarka da ɗan kunne aka sanya mata, turare kuwa kusan ma wanka akayi mata dashi, don wani irin masifaffen ƙamshi take.
Gefe kuwa Rashida da Balkeesu ne zaune, balkeesu sai washe haƙoran munafurci take, yayinda take ta saƙa sharri acikin zuciyarta, bakomai yasama tazo ɗaukan auren ba face matsanancin gulma dake cinta tana son taje taga gidan kurma gurgun tunda Mama ta hanasu ganin kayan auren kam.
Cikin nutsuwa tarin motocin suka ƙaraso ƙofar gidan nasu Zaleeha, su Adda Rahama waƴanda sune zasu shiga gidan don fito da amarya suka fiffito, kaitsaye suka nufi cikin gidan.
Shi kuwa Saifuddeen ido ya ɗan lumshe tare da yin murmushi ganin wata benzz irin tasa tazo kusa dashi ta tsaya kana yaga a ƙalla yanzu motocin sun kai talatin banda guda biyar wanda sukazo suka samu a cikin ƙaton harabar gidan duk da girman wurin saida ya tsuke ya musu kaɗan wata motar har tana gogar wata, lips ɗinshi ya ɗan lasa gano harda motocin masu sun sace Zaleeha ne a wurin.
A cikin gida kuwa Aunty Lubna ce ta shiryata tsab inda ta rufe mata fuskarta da mayafin laffaya mai tsananin tsada da ƙyalli dake jikinta, Goggo Maryama ƙanwar Baba malam da Aunty Aisha ƙanwar Mama ce suka kamata harzuwa falon Baba Malam, inda Ya Ahamd, Ya Aminu, Malam Adam harma da Mamy ke zaune, nasiha sosai Baba Malam da yayunnata sukayi mata, inda suka gargaɗeta sosai akan zaman auren nata, nasiha sukayi mata irin mai ratsa zuciya da jiki, nasihace irin wanda ke nutsar da duk wata ƴa mace, saidai kuma ko kaɗan Zaleeha babu abu ɗaya data ɗauka daga cikin nasihartasu, hasalima kukan baƙinciki kawai takeyi, sukuma take suka cika da tausayinta domin kuwa duk atunaninsu nasihar tasuce ta tsumata har take kuka.
Ganin kukan nata yaƙarune yasanya Aunty Aisha da goggonta ƙanwar Baba Malam suka kamata, domin kuwa tuni Maryam itama tasa kukan rabuwa da ƴar uwartata, haka Zaleeha take kuka sosai, yayinda ayanzu take kukan mai dalilai biyu, dalilin farko shine auren ta da aka ɗaura da wanda bataso, dalili na biyu kuwa shine dalilin dake sa ko wacce amarya kuka da zubda ƙolla tanajin bege da kewa da zafin barin gidannasu da zatayi, tabbas tasan zatayi matsanancin kewar yayu da ƴan uwanta, hakanan takejin duk ba daɗi, haka Aunty Lubna da Goggo suka riƙota har zuwa compound ɗin gidan, kuka take sosai, tanamejin tsananin baƙinciki aranta don kuwa kowani taku ɗaya da zatayi zuciyarta tafasa takeyi, yayinda wani irin malolon baƙin ciki ke cika zuciyarta, sosai takejin takaicin kaita gidan Saifuddeen da za'ayi.
Haka suka nufi wajen motocin tare da tarin zugar ƴan rakiyar amarya wanda dama tuntuni su ake jira, Balkisu da Rasheeda ne tafe wanda dama mota ɗaya sukeson shiga da amarya, babuma kamar balkeesu don ita da biyu ma takeson zama kusa da Zaleehan, dan so take taƙara zugata sosae.