← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 154

Sashe 75

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tashi Zaleeha tayi ta wuce ɗakinta, kusan rabin cup tasha yoghurt ɗin sannan ta kwanta. Acan falo kuwa Raleeya ce ta gama shirya musu abinci akan dinning area, Ummi ne tace da Hayatuddeen yaje ya ƙira Zaleeha tazo suyi beak, koda yaje ɗakin nan ya isketa tana bacci. Dawowa yayi ya faɗawa Ummi'n, hakan yasa Ummi tasa Raleeya ta ɗeba mata nata break fast ɗin daban.

Saida suka kusa kammala break fast É—in, Ummi ta É—ago kanta ta dubi Saifuddeen wanda yake tsakalan chips yana kaiwa bakinsa, ahankali yake tauna abincin, yanayin komai nasa cikin nutsuwa.
Gyara zama Ummi tayi tare da É—an muskutawa ta kamo hannunsa, É—ago kansa yayi, tare da sakarwa Ummin nasa murmushi.
Itama Ummin murmushi tayi masa, cikin kulawa tace.
"Ka bani key É—in side É—in Zaleeha,"
Fuska ya ɗan kwaɓe tare da mata alamu.
Shiga baisan inda key É—in yakeba".
Kwaffa tayi tare da cewa.
"Uhumm yayi kyau." Fuska ya É—an kele,
tsareshi da ido Ummin tayi tana mai nazartanshi kana tace.
"To Inaso kashirya anjima ka raka Zaleeha ta bawa Baba Malam haƙuri, ko kuma shima car keys ɗin naka duk baka san inda sukeba."
take yanayin fuskarsa ya sanja, kansa ya girgiza, tare da aje spoon ɗin hannunsa. Idanu Ummi ta zuba masa ganin ya mata alamun dan Allah tayi haƙuri, sai kuma yaja wheelchair ɗinsa yayi baya, tare da juyawa yabar wajen baki ɗaya,
da idanu Ummi ta bisa har ya fice daga cikin falon.

Wasa farin girki sannu sannu dai bata hana zuwa sai dai a dadde ba'a jeba

Littafina na kuɗine. in kina buƙata ga number 09097853276 katin mtn zaki turo na ɗari 300 ko kimin transfer ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbpejtt Kai kawai Ummi ta girgiza tare da tashi kaitsaye ta wuce ɗakinta, Hayatuddeen ma dake zaune ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, sam baiso hakan ba, yaso ace Hamman nasa ya amince, saboda shima ya gamsu cewa, da taimakon Hamman nashi ne kaɗai Baba Malam zai iya haƙura ya yafewa Adda Zaleeha'n.
Haka dai suka kammala cin abincin nasu duk jikinsu asanyaye, acan ɓangaren Saifuddeen kuwa yana barin falon nasa, kaitsaye ɓangarensa ya nufa, sauƙa daga kan wheelchair ɗinsa yayi, tare da haurawa saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon ya kwanta, idanunsa ya lumshe yana jin zuciyarsa nayi masa wani iri, maganganun Ummin ne ya dawo cikin tunaninsa, ahankali ya girgiza kansa, cikin zuciyarsa yace.
"Ada ni ba komai bane awajenta, bata ɗaukeni matsayin komai ba, kullum idan akwai wata magana da zai fito abakinta, wanda ta shafeni to baiwuce kalmar ƙiyayya ba, matsalar da ta faɗa ayanzu, shiyasa ta ɗaukeni wani me mahimmanci agareta, ta gudu ne saboda batason aurena, yanzu kuma gashi ta dawo tana zaune aƙarƙashin inuwata, ahaka kuwa shine har da wani neman alfarmarta."
wani murmushi me ciwo yayi tare da girgiza kansa, shiba sakarai bane, ita tayi amanta saboda haka ita kaÉ—ai zata lashe.
Yana gama tunanin ya gyara kwanciyarsa, tare da sake lumshe idanunsa, yana sakin ajiyar zuciya.
Acan ɓangaren Part ɗin Ummi kuwa baccin Zaleeha baiyi wani nisa sosai ba ta farka, Hayatuddeen ne ya kawo mata abinci, haka ya sakata gaba dolen ta saida taci, tana kammalawa kuwa ya miƙo mata ruwa da magungunanta tasha, nan ƙasan carpet ya zauna, ita kuwa tana kwance akan gado, ganin cewa akwai damuwa atattare da itane yasa shi, soma bata labarai wanda yasan dole zasu ɗebe mata kewa, suna zaune ahaka Raleeya ta shigo, akusa da Zaleehan ta zauna, cikin kulawa tace "Aunty Zaleeha ya jikin naki?".
É—an jinjina kanta tayi, asanyaye tace.
"Da sauƙi." Murmushi Raleeya tayi, tare da faɗin.
"Masha Allah, Allah Ya ƙarasa sauƙi."
Da "Ameen" Zaleehan ta amsa, haka dai suka ci gaba da hiransu, Ita dai Zaleeha idanu kawai ta zuba musu, sau dayawa dramer'n Hayatuddeen da Raleeyan na burgeta. Duk dama har yanzu akwai damuwa kwance aƙasan zuciyarta.
Suna ahaka Ummi tashigo cikin É—akin, ganinsu atare ne yasata sakin murmushi, sake gaisheta Zaleehan tayi, ta amsa mata fuska asake, har cikin ranta kuwa taji daÉ—in ganin Zaleehan cikin É—an yanayi me kyau, kallon kayan dake jikin Zaleehan tayi, take wani tunani yazo mata hakan yasa tace da Hayatuddeen yazo zata aikeshi.
Babu musu ko ya tashi yabi bayanta.
Kaitsaye É—akinta suka wuce, nan kan gado ta zauna, tare da jawo jakarta ta zage zip É—in, duban Hayatuddeen tayi, cikin kulawa tace. "Makay zan aike ka ne, ko San Hussain Super Market?".
ta tambayesa da yanayi na É—an tunani, zama yayi akusa da ita, tare da cewa.
"Wani abu za a sayo miki ne?".
"Kaya nakeson kasayowa Zaleeha, kaga dai bata zo da kayanta ba, part É—in ta kuma akulle yake, na kuma ce Hammanku ya bada key yayimin biris, dama daya ba da key É—in sai nasa ko Raleeya ne ta É—ebo mata sauran kayanta." cikin zumuÉ—i Hayatuddeen yace. "Ummi Makay zanje, wallahi dama ina kwaÉ—ayin strowberry cake, kinga kawai sai na shiga Makay shawarma na saya, nasan itama Adda Zaleehan idan na sayo mata zataci." Hararansa Ummi tayi tare da cewa.
"To sarkin kwaÉ—ayi, an faÉ—a maka cewa dama kowa irinka ne, koko ance maka kowa kwaÉ—ayi kawai yasa agaba?."
Murmushi yayi, cikin zaƙuwa yace.
"Hmm Ummi bakisan wacece Adda Zaleeha ba kenan, ai shan zaƙinta ko shazumami sai haka, yanzu kawo kuɗin naje na sayo mata kayan."

Kai kawai Ummi ta girgiza tare da zaro Kuɗin da aƙalla zasu kai 70k, acikin jakanta ta miƙa masa, cikin kulawa tace.
"Kanutsu dan Allah Hayatuddeen, dogayen riguna nakeson kasayo mata masu kyau, ni hankalina ma kwata kwata bai kwanta da aikanka ka ba, dan tunda ka iya mota kuma shikenan ka zama ayawo, dan ma ana zaman makokin nan ne da da Zakariyya zakuje, saboda hankalina zaifi kwanciya, saboda ya fika nutsuwa wani lokaci'n."
ÆŠan bakinsa ya turo gaba, cikin halin sakalcinsa yace. "Yanzu Ummi dan Allah Zakariyya'n ne ya fini nutsuwa." Murmushi Ummi tayi, tana me zuge zip É—in jakarta tace.
"Ni maza yi sauri ka kawomin aikana, sannan kuma katabbatar kayi driving cikin nutsuwa."
Haka yafita daga ɗakin yanata wani shagwaɓa, da turo baki gaba, tuno da cewa zaije ya saya strowberry cake yasan yashi sakin murmushi, haka ya fice daga cikin falon, yana karkaɗa ɗan makullin motar dake hannunsa.

Zaleeha da Raleeya kuwa har yanzu suna tare, hira Raleeya ke tayiwa Zaleeha'n, ahaka har wani sabon bacci ya É—auketa, ganin tayi bacci ne yasa Raleeya sakin murmushi, nan tatashi ta fice daga É—akin dan zuwa kitchine É—aura lunch.

Ummi kuwa ganin fitan Hayautuddeen yasa, ta É—auki wayarta, text ta turawa Saifuddeen akan cewa tana son ganinsa, tana nan zaune kuwa ko mintuna 7 ba acika ba, sai gashi ya shigo cikin É—akin.
Har gaban Ummin ya ƙaraso da kekensa, sai wani shagwaɓe fuska yake, saboda yasan bai wuce maganan Zaleeha Ummin zatayi masa. Ummi kuwa ɗago kai tayi ta dubesa, cikin nutsuwa tace.
"Wai Saifuddeen me kake nufi da Zaleeha ne? tunfa jiya nake binka da ka bani key ɗin ɗakinta amma kaƙi, ko anan kakeso ta zauna mana bayan gacan ɗakinta?" Ɗan kwaɓe fuska yayi, cikin body language ɗinsa yace.
"Nifa Ummi bansan inda key É—in É—akinta yake ba." gane abunda yake nufi yasa Ummi É—an buÉ—e baki, da mamaki tace. "Bakasan inda key É—in yake ba kuma.?"
Kansa ya jinjina alamar "Eh" kuma har ga Allah ya mance inda ya ake key É—in. Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Sannu uban maƙaryata, Saifuddeen yaushe ka fara yimin ƙarya? wato ma sokake kace key ɗin ya ɓata ko? hmmm inace nan da Addarku Rahama ta amshi key ɗin tatafi dashi, ko wata ɗaya baicika ba kaje har gidan ta ka amso, ko kana tunanin banida labari ne? kaga tunkan raina ya ɓaci Saifuddeen ka buɗewa yarinyar nan ɗakinta ta koma tayi zamanta." bakinsa ya turo gaba, sam shi baisoma Ummi tanayi masa maganan Zaleeha'n, ai koma me yafaru itace ta jawo, hakanan saboda ta ɗaukesu sakarkaru saita gudu ta kuma dawo alokacin da take so. Kuma zancen gaskiya harga Allah ya mance in da ya ɓoye key ɗin side ɗinta, amman gashi Ummi gani take ƙarya yayimata abinda bai taɓata kwatanta yimataba.
Hararansa Ummi tayi tare da ɗanyin ƙwafa tace.
"Ayi mutum da taurin kai da riƙo sai kace mutanen farko, wallahi ka tabbatar ka kawomin key ɗinnan tunkan raina ya ɓaci, idan kaƙi kuwa zansa a ɓalla ƙofan da ƙarfi, ta koma ɗaƙinta ta zauna."
Idanunsa yaɗan zaro waje, jin cewa za'a ɓalla ƙofar, tuna cewa ma ƙofar bazata taɓa ɓalluwa bane ya sashi ɗan sakin ajiyar zuciya, hannuwansa ya haɗe waje ɗaya, alaman Ummin tayi haƙuri, kuma shi ya mance inda key ɗin yake ne.
Haranshi tayi sannan tace.
"To batun rakata gidansu ta bawa Babanta haƙurifa ko shima ka mance hanyar gidan ne?".
A hankali ya jujjuya mata kai alamun bai mance ba, sai kuma yayi ƙasa da kanshi.
Ganin cewa bazai biyu ta sauƙi ba yasa Ummi'n, cewa ya tashi yaje kawai.
Yana fita kuwa Ummi tayi ƙwafa tare da cewa. "Ɗan nema zan yi maganinka ne."
Daga haka ta-tashi ta wuce toilet dan É—auro al'walan sallan azahar.
Chapter 75 · 0% Book details