Sashe 115
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Saifuddeen kuwa daga gidan nasu, kaitsaye Habu Hashidu Gombe Hausing Estate suka nufa, inda anan ne gidan su Khamis yake, tunda Hayatuddeen ya gansu cikin unguwan yaji gaba ɗaya tsoro ya kamashi, dan baisan me Hamman nasa ke nufi da zuwa unguwar ba, aƙofar gidan su Khamis sule driver yayi parking motar, idanu Hayatuddeen yaɗan zaro, sakamakon ganinsu aƙofar gidan su Khamis, kallon Hamman nasa yayi, saidai ganin yanda ya haɗe fuska, yasa shi yin gum da bakinsa. Sule ne ya buɗewa Saifuddeen ɗin murfin mota ya fito, bayan ya ware masa kekensa. Ganin haka yasa Hayatuddeen ma jiki asanyaye yafito daga cikin motar.
Waya Saifuddeen ɗin yaɗan lallatsa, ko minti biyu ba ayi ba, wani ya fito daga cikin gidan, wanda yake driver'n gidan ne, shi yayi musu iso zuwa cikin gidan, har falon Baban Khamis kuwa suka ƙarasa, inda suka samesa azaune. Cikin kulawa ya tarbesu, bayan ya miƙawa Saifuddeen hannu sunyi musabaha.
Dai-dai nan Khamis ya shigo cikin falon, ganin Hamma Saifuddeen da kuma Hayatuddeen yasa yaji jikinsa yayi sanyi, cikin ɗar-ɗar ya ƙaraso ya zauna.
Duban Baban Khamis ɗin Saifuddeen yayi, cikin mutuntuwa ya miƙa masa wayarsa, wanda ke ɗauke da rubutun text message, wanda kuma gabatar da kansa ne yayi, duk dama Baban Khamis ɗin yasan da zuwansa, dan ya ɗauki numbernsa acikin awayar Khamis, bayan Baban Khamis ɗin ya karanta saƙon, ɗan murmushi yayi tare da sake bawa Saifuddeen din hannu suka gaisa, cikin kulawa yace. "Masha Allah Malam Saifuddeen ina maraba da zuwanka, sannan bama sai ka wahalar da kanka wajen yin rubutu ba, muyi magana ahaka, dan ina fahimtar body language sosai, dan inada aminina shima bayaji baya mgn."
kai Saifuddeen ya jinjina cikin gamsuwa, É—an gyara zamansa yayi, cikin body language É—insa yace.
"Kaman yanda na faɗa maka maganace akan yarannan ke tafe dani, bansan tayaya zaka ɗauki maganar ba, kasancewar nasan idan na faɗa zakayi mamakin jinta, saboda abune da ba zamu taɓa zato ba, Hayatuddeen ƙanina ne na jini, kamar yanda na ɗaukesa kuwa haka na ɗauki Khamis, yanda nakejin zan hukunta Hayatuddeen haka ma zan hukunta Khamis, najima inasa musu ido, ina kuma bibiyan lamuransu,
ada zarginsu nake, sai-dai tun jiya dana karɓi wayoyinsu na gano cewa suna aikata haƙiƙanin abun danake zarginsu dashi, wato neman mata da kuma kallace kallacen bad vedios waƴanda basu dace ba kwata kwata, bai kuma kyautuwa yara musulmai irinsu masu tasowa suna ganiba, wanda ya zama dole atsaya akansu gudun lalacewar tarbiyarsu da rayuwarsu."
Cike da tashin hankalin fahimtar abunda Saifuddeen din ya faÉ—a yasa.
Baban khamis zare hular dake kansa, ya somayi wa fuskarsa fifita, fuskarsa ɗauke da tsananin kaɗuwa da damuwa haɗi da tashin hankali ya dubi Khamis, wanda tuni jikinsa ya fara jiƙewa da gumi, sosai tsoro da rashin gaskiya suka bayyana ƙarara akan fuskarsa,
cikin tashin hankali Baban nasa yace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, ya Allah ka dubemu da idon rahama lallai nasan tabbas kowa da irin jarabawarsa arayuwa, ya Allah kada ka jarabcemu da lalacewar tarbiyar ahlinmu ta hanyar aikata al'fasha ko wanne irine, tunda nake ban taɓa aikata zina ko fasikanci ba, haka ma kuma sam koda ina ƙiruciyata bana kula mata, har izuwa yanzu kuwa na tsare mutumcin kaina,
Khamis kai ɗayane ɗana dana haifa aduniya, hakanne yasa na baka kulawa da duk wani gata, saboda rayuwarka tayi kyau ta inƙamta, yanda kowa zai amfana dakai gaba bawai inai maka gata dan lalata rayuwarkaba, ashe abun da kuke aikatawa kenan, ashe neman mata kakeyi Khamis da ƙananun shekarunka, so kake ka tozartani ko, ban taɓa tunanin haka daga gareka ba Khamis, ashe nuna maka gata, zai iya zama silan lalacewar rayuwarka."
Hawaye ne suka cika idanun Baban Ƙhamis ɗin, wanda hakan yasa gaba ɗaya jikin Khamis yayi sanyi, take shima hawaye suka cika idanunsa, kansa ya ɗan soma jujjuyawa cikin muryarsa da tayi sanyi yace.
"Dan Allah Baba kayi haƙuri, wallahi ni sau ɗaya ne ma na taɓa yin lalata da yarinya ɗayace , kuma ma daganan ban ƙara ba, kuma nan ma yarinyarce take ta bina, bani kuma na nemeta ba, dan Allah Baba kayi haƙuri, Allah bazan sake ba."
Hayatuddeen kuwa can gefe ya koma tuni zufa ya keto masa, narai narai yayi da idanunsa, cikin tsoro yace. "Nikam ma wallahi ban taɓa aikata zina ba, na rantse da allah da Manzonsa ko hannun mace wallahi ban taɓa riƙewa ba, Khamis shima shaidane ban taɓa riƙe hannun wata mace ba wallahi."
tuni hawaye sun cika idanunsa, wani irin tsoro da fargaba haɗi da matsanancin takaicin kansa da kuma nadama ne ya cika zuciyarsa. Kai Baban Khamis ɗin ya jinjina, cike da alhini da kuma tsoron abun da ɗan nasa ke aikatawa, tabbas yasha mamaki ƙwarai, dan ko kaɗan bai taɓa kawo aransa cewa Khamis ɗin na bin mata ba, kuma wai harma zina ya taɓayi, jiyayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen ya taimakesa, da bai ɓoye masa abun da yaran ke aikatawa ba, duk da cewa kuwa harda ƙaninsa aciki, yayi mamakin halin ɗan nasa ƙwarai, saidai kuma amma yasan cewa babu irin jarrabawan da Allah baya bawa bawansa, wasu tasu jarrabawan akaran kansu ne, wasu kuwa akan ƴaƴansu aka jarrabesu, kowa dai da irin nasa, tabbas basai ka kasance fasiƙi ko mazinaci Allah zai jarrabi ƴaƴanka ba, ita jarabawa da ƙaddara Allah kan ɗaurawa duk wanda yaso. Hawayen da suka cika idanunsa yaɗan share, cikin sanyi ya dubi Khamis da Hayatuddeen tare dayi musu alaman su ƙaraso gabansa yanason ganinsu, jiki asanyaye kuwa suka rarrafo kusa dashi, Khamis kam dan tsoro haka yakejin kaman ƙirjinsa zai fito waje. Cikin kulawa haɗi da sanyin jiki yace.
"Da forko dai Khamis nida kaina zan kaika ayimaka Hukuncin Allah kaida yariyar ayi muku bulalin haddi, kana tayi istibira'i, kuma in aura maka ita in ta kasance mai yin tuba na gskya."
Shiru ya É—anyi ganin yadda Khamis keta gyaÉ—a mishi kai alamar to ya yarda, jiki a mace yaci gaba da cewa.
"Ku yarane wanda asannu watarana zaku zama iyaye, shin alokacin da kuka kai munzalin zama iyaye, idan kuka kama Æ´aÆ´anku suna aikata irin abun da kuke aikatawa ayanzu ya zakuji acikin ranku? shin kuna ma da tunanin cewa ayanzune ya kamata ku inganta rayuwarku?
Nasha mamaki ƙwarai Khamis, ace kana matsayin ɗana kake aikata zina, har kana faɗi da bakinka cewa wai sau ɗaya kataɓa yi? kasan girman zina kuwa Khamis? kasan girman laifin zina kuwa? Kasan hukuncin zina kuwa? to wallahi kasani mazinata ko alahira wutarsu daban ne, ko kuma saboda kana ganin kai kaɗaine baka da ƴa baka da ƙanwa, kai kuma Hayatuddeen kana ganin cewa baka da ƙanwa, shiyasa kuke aikata abun da kukeso ko, haƙiƙa idan mu bama ganinku Allah na ganinku, kuma kome kuka aikata na zunubi sai an rubuta muku shi acikin littafinku, sai kuma Allah ya tambayeku akan hakan, kusani jin tsoron Allah shine gaba akan komai, yau idan akace baku da wani ginshiƙi me tsaya muku arayuwa, zakusha wahala, domin wannan halin naku da kuka ɗauko, bazai taɓa bari kucimma nasara arayuwarku ba, musamman ma kai Khamis, wanda wuyanka yayi kauri, har kayi riƙan da zaka iya aikata zina, wallahi wallahi rayuwar mazinaci ko mazinaciya baya al'barka, sannan komai nasu bashi da al'barka, kama daga kan dukiya da duk wani abun da suka mallaka, yanzu Khamis da wani ido kakeso na kalli mahaifiyarka nace mata ɗanta wanda har kusan rasa ranta tayi, wajen ƙoƙarin haihuwarsa mazinaci ne, kanaga akwai wani farinciki ko soyayyarka da zaiyi saura azuciyarta? Sabida gudun lalacewar tarbiyar ka yasa mukaƙi barinka ka tafi karatu ƙasashen turawa, ashe bamu saniba tana ƙasa tana dabo wai sai wanda yaje yayi karatu a ƙasashen woje ke lalacewa ba." Kuka Khamis ya fashe dashi me tsuma zuciya, wanda hakanne yasa Hayatudeen ma fashewa da kuka.
Kai Saifuddeen ya girgiza, cikin takaicin rayuwar da ƙannen nasa suka jefa kansu aciki, ƙazamar rayuwa marar ɓullewa.
Saida sukayi kuka sosai, kafun Baban Khamis É—in yayi musu faÉ—a sosai, tare dayi musu nasiha mai ratsa jiki, wanda yasa atake sukaji duk sun tsani wayoyinsu ma, balle kuma akai ga kallace kallacen batsa da sukeyi.