← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 154

Sashe 22

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Har yau kuma a woje take kwana cikin gardin,
wannan abun shine yasa Ahmad yake matuƙar jin baƙin cikinta,
shi kuwa Saifuddeen  da fari baisan bata kwana a ɗakintaba dan baya shiga kuma da safe yana ganinta a wurin Umminshi,
To tun shekaran jiya daya dare ya ankara da bata É—akin, ya dudduba ko ina na cikin part É—in nata babu ita ba dalilinta, falonshi ya koma wayarshi ya É—auka tare da yin mgnar zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana yau kwana biyu kenan bata kwana a nan."
Kanshi ya É—an jingina da jikin kujerarsa tare daci gaba da mgnar zuci.
"To waya sanima ko ta daÉ—e da barin kwana a nan."
sai kuma yayi ajiyan zuciya tare da cewa.
"ko dai part É—in Ummi take kwana? kai Anya kuwa Ummi zata barta ta kwana a side É—inta,
to ko dai part É—in Raliya take kwana."
Text ya rubutawa Ahmad,
"Kayi bacci ne?."
Ahmad da ke zaune a falo shida Raliyya suna mgnar Zaleeha dan hango wucewarta da sukayi,
murya a sanyaye Raliya tace.
"To wai ko dai Hamma Saifuddeen bai san bata kwana a É—akinba?."
Ajiyan zuciya Ahmad ya sauƙe tare da cewa,
"Ina zaton bai saniba, kinfa san shi da miskilanci, in kuwa yasan bata kwana a cikin to yasan inda take kwanan shiyasa bai kulataba ai jiki magayi."
da sauri ya ɗago wayarshi ganin saƙon Saifuddeen ne ya sashi cewa.
"To ina ga dai bai san bata kwana cikiba sai yanzu dan ga text É—inshi wai nayi bacci ne."
ido Raliya ta zuba fuskar wayarshi tana ganin amsar da yake rubuta mishi.
"A a banyi bacci ba, lfy dai ko?."
jim kaɗan sai ga wani saƙon.
"To lafiya dai zance,amman Zaleeha na wurinku ne?."
murmushi Ahmad yayi tare da cewa Raliya,
"Hmmm zanyi mgnin yarinyar nan."
sai kuma ya rubuta mishi amsa.
"A a Zaleeha kuwa, bata nan."
a take sai ga wani saƙon.
"Kasa Raliya ta dudduba nan wurinku, taje Side É—in Ummi ma ta duba ko tana can."
yana gama karan tawa yace.
"Lafiya dai kam ko?."
tsaki Saifuddeen ya É—an ja kana ya rubuta mishi,
"Nima ban saniba lafiya ko ba lfy ba, ina dai zargin yarinyar bata kwana a gidan nan, dan tun shekaran jiya na lura babu motsinta, sannan yanzu na dudduba ko ina bata ciki side É—in."
cikin nuna fargaba Ahmad yace.
"Innalillahi, to ina take zuwa ta kwana, gani nan fitowa."
sai ya kuma miƙe ya kalli Raliya tare da cewa,
"Maza kije side É—in Ummi ki gaya mata, ana neman Zaleeha ki kuma ce karta nuna tasan inda take kwana zanyi mgninta."
to tace tare da juyawa ta nufi side É—in Ummi,
kana shi kuma Ahmad ya nufi ƙofar falon Zaleehan nan yayi kicibis da Saifuddeen daya fito,
"To wai ina ta shigane, mufa mun dudduba wurinmu babu ita."
kai ya jujjuya mishi alamun shimafa ya dudduba wurinsu babu ita.
dai-dai lokacin kuma Ummi da Raliya suka iso, nan fa suka haÉ—u suka nuna basu san inda takeba.
ita kuwa Zaleeha tun fitowan su Ahmad ta buÉ—e ido,
jin ita ake nema yasa ta zame a hankali ta konta a ƙasan kujerar fulawi ke zagaye da ita.
Ahmad kuwa yana hangota hakan ya sashi cewa.
"Hmmmm zaki gane kurenki."
wayarshi ya zaro lallatsata yayi ya nemo number Ya Aminu,
ya kirashi kana ya kara wayar a kunnenshi.

Can cikin bacci Ya Ameenu yaji wayarshi nata suwa,
a hankali ya É—an zare Maryam daga jikinshi,
hannu yasa ya ɗauki wayar time ya duba ƙarfe ɗaya na dare.
"Ahmad kuma a daren nan lfy kuwa?."
sosai yaji fargaba ,kar dai Zaleeha nacan na tarfa musu rashin É—a'a, jiki na rawa ya amsa kiran cikin sauri yace.
"Salamu alaikum ,Ahmad lfy kuwa?."
cikin nuna tashin hankali yace.
"Ya Ameenu Zaleeha ce bamu ganiba mun nemata ko ina a gidan babu ita ba dalilinta,
kuma Saifuddeen yace tun shekaran jiya bata kwana a side É—insu,
to sai yayi tunanin wai ko side ɗinmu take shigowa ta ɓuya ko na Ummi,
to shine yanzu ya sanarmana zatonsho tana wurinmu,mun duba kab gidan bata, nan shine nace bari in kiraka ko ta dawo gidane?."
cikin kaɗuwa Ya Ameenu ya miƙe tare da cewa.
"Zaleehan to ina take zuwa?."
a taƙaice Ahmad yace.
"To ko tana gida ne?." rai a ɓace Ameenu yace.
"Kai anya kuwa sam bata gida, to ina take zuwa ta kwana, yi haƙuri bari in kira Baba malam."
to Ahmad yace kana ya katse kiran sannan ya gaya.musu yadda sukayi da Yayanta Ameenu,
kana yace su shiga ciki kafin Ameenun ya kirashi.

Shi kuwa Ya Ameenu wani irin tashin hankali ne da ɓacin raine mai tsanani ya rufeshi to ina Zaleeha take zuwa ta kwana ina take tafiya ta bar ɗakin mijinta me haka yake nufi?
kiran Baba Malam yayi bawan Allah yana zaune bisa sallaya yana karatun qur'an kiran Ameenu ya shigo wayarshi,
har wayar ta katse bai ɗaukaba duk da yaga Aminune so yake yaje ƙarshen surar Arrahaman da yake karantawa,
yayinda wani fargaba ya rufeshi lfy kuwa kira da tsakiyar daren nan.
Yana zuwa ƙarshen surar kira na uku na shiga wayar, da hamzari ya amsa kiran,
"Barka da dare Baba Malam kayi haƙuri na tada kai daga bacci."
Ameenu ya faÉ—a a ladabce,
murya a É—an harÉ—e Baba Malam yace.
"Ameenu lfy kuwa meke faruwa?."
cikin sanyi Ya Ameenu yayi mishi bayanin da Ahmaɗ yayi mishi, ya ƙara da cewa.
"Ko dai ta taho gida ne?."
lumshe ido Baba Malam yayi yana jin wani irin suya da zuciyarshi keyi me Zaleeha ke nufi zubda mishi mutunci da kima  a idanun mutane ko?
a hankali ya cewa Ameenu.
"Ameenu bana zaton tana cikin gidana ,bazata zo nanba, amman dai bari in bincika."
to Aminun yace kana y katse kiran.
shi kuwa Baba Malam fitowa yayi da kanshi yayi tabin luggu da saƙo na gidan ya duba ko ina kab babu ita, koda ya titse Mama da tambayar ina Zaleeha ke zuwa ta kwana,
rantse-rantse tayi ta mishi akan ita bata san ina Zaleeha ke zuwa ta kwanaba.
a daren Ameenu ya kira goggonsu Maryama da duk inda suke zaton zataje ko ina sai ace musu bata zoba.

Wannan abu yayi matuƙar tada hankalin Baba Malam ya Ameenu kuwa ji yake in yaga Zaleeha zai kusan karta,
dole ya kira Ahmad yace,
wlh bata wurinsu amman tunda da safe tana dawowa zai zo ya sameta, har É—akinta.

Da  wannan kowa ya koma ɗakinshi, Ahmad kuwa ranshi ƙal yasan Zaleeha zata gane kurenta.

Washe gari kamar yadda ta saba, suna tafiya masallaci ta koma ɗakinta wonka tayi da ruwan ɗumi wai ko tsamin cizon sauro da  jikinta keyi zai ragu, wanka da al'wala tayi,
kana ta fito tazo tayi salla koda ta idar  azkar tayi sanan ta miƙe ta kimtsa jikinta cikin wata doguwar rigar mai ɗan karen.kyau wanda duk na kayan aurene, da mayafinshi ta yane kanta ,kana ta nufi sashin Ummi.
a falo ta samesu, dukansu, cikin nitsuwa ta isa gaban Ummi dake mata murmushi tare da cewa.
"Gari ya waye ko É—iyata?."
murmushi tayi tare da rusunawa gaban Ummi cikin ladabi da sanyin lafazi tace.
"Ummi Ina kwana?."
cikin kula Ummi tace.
"Lafiya lau ya  baƙunta?."
kai a sunkuye tace,
"Alhamdulillahi."
"Masha Allah." cewar Ummi kenan
Hayatuddeen ne ya gaidata ta amsa fuska a sake, kana ta kalli,
Ahmad dake zaune kusa da Saifuddeen bisa alamu lissafi sukeyi,
cikin sanyin sauti tace.
"Yaya ina kwana?."
a taƙaice yace.
"Lafiya lau." daga nan kuma sai ta miƙe tare da cewa Ummi .
"Raliya na kitchen  ko?."
cikin jin daÉ—i Ummi tace.
"A a tana sashinta yau wai kanta ke ciwo."
a hankali tace,
"Ayyah ban saniba Allah ya bata lfy."
Amin Amin Ummi tace,
Kana sai ta É—an rusuno tare da cewa,
"To Ummi bari in shiga kitchen, me zan  haɗa  mana breakfast?."
sosai Ummi take jin daÉ—in yadda take sakewa da Raliya su shiga kitchen tare, gashi yanzu har tana shiga ita É—aya ma tayi musu girki.
cikin kula Ummi tace.
"Bari inzo mushiga tare to."
da sauri tace .
"A a Ummi ki bari zan iya ki huta."
sai kuma ta kalli Hayatuddeen daketa murmushi tace,
"Zo muje kitchen ka tayani hira."
da sauri ya miƙe yabi bayanta, yana cewa.
"Yauwa muje ki min dege-dege."
da ido Ummi ta bisu har suka shiga kitchen É—in.
Chapter 22 · 0% Book details