Sashe 77
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi kuwa Saifuddeen yana gama karanta saƙon Ummin sake lumshe idanunsa yayi, zuciyarsa duk ba daɗi. Cikin sanyi ya rubuta cewa.
_"Kiyi haƙuri Ummi banso na ɓata ranki ba, shikenan naji na amince zan rakata, amma dan Allah Ummi kiyi haƙuri zuwa gobe idan anyi sadakan uku saina kaita kafin nan mutane sun ɗan ragu a gidan nasu"_
Murmishin farinciki da samun nasara Ummi tayi, bayan ta gama karanta text message É—in daya turo mata, nan tace dashi.
"Allah ya kaimu goben." Sai alokacin ya É—anji sanyi acikin ransa, saboda yasan zuwa yanzu, zuciyar Ummin nasa zata É—anyi sanyi.
Can ɓangaren Zaleeha kuwa kuka tasha sosai har taji babu daɗi, dan kanta haka ta share hawayenta saboda koma menene tasan ita ta jawa kanta, ko ahaka suka barta ma, tasan sunyi mata gata tunda suka bata muhallin zama, abun da ƴan uwa da mahaifinta suka kasa yi mata kenan saboda fushin da sukeyi da ita.
Ganin kukan bazai kaita ba yasa ta tashi ta wuce toilet tare da wanko fuskarta wanda tayi ja sosai saboda kukan da tayi, fitowarta daga toilet ɗin kuwa yayi dai-dai da shigowar Ummi cikin ɗakin, ganin fuskar Zaleehan da kuma idanunta sunyi luhu luhu, yasa Ummi kamo hannunta suka zauna anan bakin gado. Cikin kulawa Ummi tace. "Kuka kikayi ko?" Sadda kanta ƙasa tayi, saboda bazata iya musawa Ummi'n ba, kanta Ummi ta shafa, tare da cewa.
"Ki kwantar da hankalinki kinji, Insha Allah gobe Hammanku zai kaiki kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, kuma Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, ki daina kukan nan kinji!."
Ummi tafaɗi maganar cikin lallashi, jin cewa Hamma Saifuddeen ɗin ya yarda zai kaita yasa taji wani irin farinciki ya lulluɓe Zuciyarta, hakanne yasa ta faɗa jikin Ummi ta saki kuka. Rarrashinta Ummin ta somayi tare da sanya hannu tana shafa bayan Zaleeha'n, cikin kukan tace.
"Nagode sosai Ummi, haƙiƙa kin zame min uwa, nagode sosai..."
saurin rufe mata baki Ummi tayi, cikin kulawa tace.
"Kamar Æ´a haka na É—aukeki Zaleeha, saboda haka bama saikin min godiya ba, duk wani burina bai wuce farincikin ku, Allah Ubangiji ya muku al'barka, ungo wannan kayan É—azun Hayatuddeen ya sayo miki su."
Ummi ta faɗi maganar tana me miƙawa Zaleehan ƙatuwar ledan dake hannunta.
Amsar ledan tayi cikin farinciki tace.
"Nagode sosai Ummi." har cikin ranta taji daɗin kayan, saboda itama kayan jikin nata sun isheta, yau kwanansu biyu kenan ajikinta, abunda tunda take aduniyarta bata taɓayi ba kenan, dama haka rayuwa take tana juyawa da abubuwa kala-kala, wai ita Zaleeha me yawan ado da kwalliya uwa uba ƙwalisa, itace ke sanye da kaya ɗaya ajikinta har tsawon kwanaki biyu, bacin da arana ɗaya saita sanja kaya kusan kala uku, amma yau gashi komai ya juya mata, damuwa ya mata yawa, wani lokacin har takan manta wasu abubuwan da suka shafeta.
Ummi kuwa tashi tayi inda da kanta ta shiga toilet ta haɗawa Zaleehan ruwan wanka me ɗumi, cikin kulawa Ummi tace da Zaleehan ta shiga tayi wanka, babu musu kuwa ta shiga rage kayan jikinta, ganin haka yasa Ummi fita daga cikin ɗakin, tare da jawo mata ƙofa.
Jikinta aɗan sanyaye haka tayi wankan, ba laifi kuwa taɗanji damuwarta ta ragu, nan cikin kayan da Ummin ta kawo mata ta zaɓo wata doguwar abaya gown me kyau ta sanya, sam damuwar da take ciki kuwa bai hana zallan kyawunta fitowa ba, gashi rigar ta amshi jikinta tayi mata ɗas, mayafin doguwar rigar ta yafa, sannan cikin yanayin sanyi ta fito zuwa falo.
Nan ta iske Raleeya da Hayatuddeen zaune, Raleeya karatun littafin hausa take, shikuwa Hayatuddeen game ya haÉ—a yakeyi.
Yana ganinta ya É—an waro idanunsa, tare da cewa.
"Wow Adda Zaleehan mu kinyi kyau, yeah ashe dai niɗin gwanine wajen iya zaɓen kaya." Murmushi tayi masa, tare da zama anan kusa da Raleeya.
Duban Raleeya tayi cikin kulawa tace.
"Sister sannu da gida." cikin sakin fuska Raleeya tace.
"Yauwa sannu my kyakkyawar Auntyn mu, halan wannan kwalliyan duk na hamma ne" Raleeya ta ƙare maganar cikin yanayi naɗan tsokana, murmushi Zaleehan tayi wanda har saida fararen haƙwaranta suka bayyana, nan ta sadda kanta ƙasa tana tunanin. Uhum Hammanku kam ko kallo ban isheshiba ba ai. Hayatuddeen kuwa tashi yayi ya wuce ɗakinsa, mintuna kaɗan sai gashi ya dawo da leda ahannunsa, nan kan cinyarta ya ajiye mata, cikin kulawa yace. "Aunty roasted fish ne da cake, please kici kinji, nasan kinaso." murmushi tayi tare da cewa.
"Nagode auta." Dukansu murmushi sukayi sannan suka shiga ɗan taɓa hira, ita dai haryanzu akwai damuwa kwance aƙasan zuciyarta, hakanne ma yasa maganarta bai wuce.
"Eh, ko A'a ba".
Suna nan azaune Ummi ta fito ta samesu, zama tayi acikinsu, itane ma take ƙoƙarin jan Zaleehan da hira.
Saifuddeen ne ke tura wheelchair ɗinsa, yana son ƙarasawa part ɗin Ummi, dai-dai lokaci Ameena wanda dawowarta daga aiki kenan ta shigo cikin gidan, ganin Saifuddeen ɗin yasa ta ƙaraso da sauri tana sakar masa murmushi, shiɗinma murmushin ya sakar mata, tare da miƙa hannu ya karɓi Adeel dake rungume akafaɗanta. Ɗan ranƙwafowa tayi tayi mishi kiss a forehead ɗinsa, cikin kulawa tace. "Nayi kewarka Mijina." murmushinsa me kyau yayi mata, tare dayi mata alaman cewa shima haka, nan ta riƙe saman wheelchair ɗin nasa, tana turasa shikuwa yana riƙe da Adeel haka suka nufi part ɗin Ummi.
Ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga bakin Ameena ɗauke da sallama, hakanne yasa gaba ɗayansu suka ɗago kai suka kallesu, Ummi ne ta fara amsa sallaman, kafun suma suka amsa, kallo ɗaya Zaleeha tayi musu ta duƙar da kanta ƙasa, cikin kulawa Ummi tace. "Mutanen asibiti kun dawo."
Murmushi Ameena tayi, wanda ganin Zaleeha cikin shiga me kyau yasa duk taji zuciyarta ba daɗi, ɗan durƙusawa tayi tare da cewa.
"Ummi barka da gida." Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Yauwa Ameena ya wajen aikin naki?" tana murmushi ta amsa da lafiya lau, Raleeya da Hayatuddeen ne sukayi mata sannu da dawowa, baki awashe haka ta amsa musu, duk dama dai aranta sam bataji dadin ganin Zaleeha ba, gashi kuma Zaleehan tayi kyau sosai, ÆŠago kai Zaleeha tayi tare da É—an kallon Ameena'n, cikin sanyin murya tace.
"Ummu Adeel barka da dawowa."
Cakwai haka Ameena taji muryan Zaleehan acikin kunnuwanta, take kuwa taji kaman an watsa mata ruwan zafi ajikinta, wani irin haushin Zaleehan ne ya cika mata zuciya, amma ganin idon su Ummi yasa ta ɗanyi yaƙe tare da cewa.
"Yauwa Sannu." Ɗan ɗago kai Zaleeha tayi ta saci kallon Adeel dake kan cinyar Saifuddeen, Gani tayi Adeel ɗin na kallonta, hakan yasa ta sakar masa murmushi wanda har saida dimples ɗinta suka lotsa, shima yaron murmushi yake ta mata yana wangale mata haƙora tare da mutsu-mutsu har yana zamowa tare da miƙo mata hannu alamun ta ɗaya shi.
Cikin dariya Hayatuddeen yace.
"Aunty Zaleeha ke yakeyiwa hakafa".
murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Ae wannan ɗan naku saiku yaron ba dai ƙirniya ba abinda ya iya".
Murmushi sukayi baki É—aya su.
Ita kuwa tashi tayi daga zaunen da take, gaba ɗaya ta gama mantawa cewar ma yaron akan cinyar Saifuddeen ɗin yaƙe, ƙarasawa tayi tare da ɗan ranƙwafawa tasa hannu zata ɗauki Adeel ɗin, daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya daki hancinta, cikin tsautsayi kuwa hannunta ya gogi nasa, wani irin shock sukaji su duka biyun, ahankali ta ɗauki Adeel ɗin, sannan ta ɗagashi sama tana sakar masa murmushi,
baki ya wangale mata harda tsalle shi, Allah ya sani tana son Adeel har cikin ranta kuma shima yaro yana sonta.
Baki buɗe Ameena ke kallonsu, kishi kuwa haka takeji kaman zai fasa ƙirjinta, ƙwarai tazo iya wuya, dan kasantuwar Zaleeha akusa da Saifuddeen ɗin baƙaramin dacewarsu ta gani ba.
Ummi kuwa jin wayarta dake cikin ɗaki na ƙara yasa tatashi ta bar musu falon, Raleeya ma miƙewa tayi ta haura sama.
Nan falon ya rage daga Hayatuddeen, Zaleeha, sai su Saifuddeen ɗin, Zaleeha kuwa rungume Adeel ɗin tayi tana yi masa wasa, Saifuddeen kuwa ahankali yake ɗan satan kallon Zaleeha'n, saboda tayi masa kyau sosai, duk da kasancewar ma ya lura cewa idanunta aɗan kumbure suke kuma gaba ɗaya yanayin rayuwarta ta sauya ta zama mai sanyi, hakan yasa shi jin wani abu na tausayi acikin ransa. Ameena kuwa ganin cewa Saifuddeen ɗin na ɗan satan kallon Zaleehan ƙasa-ƙasa ne, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, wani irin matsanancin kishi ne ya taso mata, amma saita dake, cikin kirsa ta tashi ta dawo kusa da Saifuddeen ɗin, ɗan durƙusawa tayi tare da tallafo haɓarsa cikin son nunawa Zaleeha matsayinta tace. "Mijina Mekakeso na kawo maka kasha?" Shikuwa sanin cewa Zaleeha na falon, yasashi jawo hannun Ameenan kusa dashi, kissing ɗinta yayi, tare da nunata da hannunsa, alaman ita yake so, wani irin daɗi haɗi da farinciki ne suka cika zuciyar Ameena, wani irin fari tayi da idanunta, da ɗan ƙarfi yanda ta tabbatar cewa Zaleehan zataji tace.
"Indai nice kasameni." Saman Wheelchair É—insa ta kama, tare da juya akalan keken suka fice daga cikin falon, sai sakin wani shu'umin murmushi takeyi.
Duk da cewa duk abun da sukeyi tana jinsu, amma gaba ɗaya hankalinta ba akansu yake ba, sam kuma bataji wani abu na ɓacin rai dangane da hakan ba, gaba ɗaya ma ita hankalinta naga wajen yiwa Adeel wasa,
sai dai tana jin zuciyarta na riƙe da abinda sukayi.
Hayatuddeen kuwa sosai hakan da Ameenan tayi yasa yaji ba daɗi, saboda ya fahimci cewa, Ameenan so take ta ƙuntatawa Zaleeha, amma ganin cewa Zaleehan bata damu ba, yasashi girgiza kansa kawai ya ci gaba da game ɗinsa.
Ameena kuwa suna isa part ɗinsu, cikin mazari tasoma ƙoƙarin rage musu kayan jikinsu, jin ranta take fari ƙal, saboda hakane ma zata gwadawa Saifuddeen ɗin soyayya kala-kala, tayanda sai tasa ya manta da wata Zaleeha.
Afalon Ummi kuwa saida aka ƙira sallan Magriba, kafun Ummi ta karɓi Adeel,
inda tace da Zaleeha taje tayi sallah.
Koda ta idar da sallan kuwa bata tashi akan sallayan ba sai da aka idar da sallan isha, daganan bata ƙara leƙa waje ba, kifi da kuma cake ɗin da Hayatuddeen ya bata shi taɗan ci, sannan ta kwanta, take kuwa bacci ya ɗauketa.