Sashe 117
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Acan gida kuwa, gaba É—ayansu zaune suke afalon Ummi, Zaleeha wanda gama girkinsu yasa taje tayi wanka, wani sabuwar shiga ta sanja, inda tasha kyau cikin wata tighty gown sky blue me kyau, sosai tayi, kyau yayinda ta tubke gashinta ta bar jelanshi sake , hakan yasa ta zama kamar wata ba india.
Zaune take agefen Raleeya yayinda taÉ—an jingina kanta da kafaÉ—an Raleeyan daketa kitse mata jelan gashin yana kuma koncewa sabida santsinshi kuma ba iya kitson tayiba,
sai kuma Adeel dake gefenta yana ta wasan sa,
shigowarsu cikin falonne yasa taɗan yunƙura tare da matse jikinta waje ɗaya, kasancewar babu mayafi akusa da ita, sam kuma batayi tunanin dawowarsa yanzu ba. Ƙarasowa cikin falon yayi,
Ameena dake zaune ne ta sakar masa murmushi, shima murmushin yayi mata tare da lumshe mata ido, cikin nutsuwa ta miƙe ta ƙarasa gaban fridge inda ta ɗauko masa lemo maisanyi, karɓa yayi yaɗan sha, sannan ya juya ya ya karɓi kulan zabuwarshi da madararshi dake hannun Hayatuddeen kana ya juya ya koma part ɗinsa, dan yanaso yaɗan watsa ruwa.
Raleeya kuwa kitchine ta shiga, inda ta haɗo musu fruit salad wanda ta cika madara acikinsa, Kaɗan Ameena tasha dan ita haka take kayan fruits basu wani dame ta ba kayan zaƙima duka bai dameta ba.
Zaleeha kam dama abincinta ne, saboda haka sosai tasha, ɗago idanu tayi ta kalli Hayatuddeen wanda gaba ɗaya yazama wani silently dashi, da duk kan alama akwai abun dake damunshi, hakanan taji duk ba daɗi, saboda tasa aranta damuwar Hayatuddeen damuwarta ne, tashi tayi daga zaunen da take, tare da ƙarasawa kan kujeran da yake zaune, zama tayi gefenshi, cikin kulawa tace.
"Sweet bro me yake damunka? ko baka da lafiga ne autanmu?." ÆŠan É—agowa yayi ya kalleta, asanyaye ya jingina kansa da da jikin kujera.
Yana jin yadda ƙirjinsa ke bugawa, wani irin tsoro yakeji, yasan idan Hamma ya faɗawa Ummi halin da yake ciki, zatayi fushi dashi sosai, shi kuma tsoron hakan yakeji, gashi kuma yaga Hamman nasa ma, bawai ya sake dashi bane, ganin yanda ya marairaice fuska yasa Zaleehan ɗan gyara zama ta fuskanceshi da kyau, ahankali ta miƙa masa cup ɗin fruit salad din dake hannunta, babu musu kuwa ya amsa ya sha, cokali huɗu kawai, ta ɗan hararesa tare da cewa.
"To ya isheka haka malam, dan naga alaman idan na biyeka zaka shanyemin."
Dariya sukayi gaba ɗayansu, miƙewa tayi, tare da ɗaukan Adeel, ɗayan hannunta kuwa bowl ɗin fruit salad ɗinta ne, wanda bata gama shanyewa ba, zata je ta sanya acikin fridge. Kaitsaye part ɗinta ta nufa, nan cikin firdge ta sanya bowl ɗin fruit ɗin, sannan ta ajiye Adeel akan gado, jin anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba ne, yasa taje ta ɗauro al'wala, koda ta fito daga toilet ɗin sallaya ta shumfuɗa tare da tada sallah.
Tana idarwa kuwa taji anayi mata knocking ƙofa, tana buɗewa kuwa ta ga Ameena ce tsaye cikin shirinta na zuwa wajen aiki.
ÆŠan faÉ—aÉ—a murmushin kan fuskarta tayi tare da cewa. "Ummu Adeel har kin shirya."
Murmushi itama Ameenan tayi tare da cewa.
"Eh wallahi, kinsan idan na tsaya saina makara, ni kuma banason makara wallahi sam, ina Adeel É—in yake sarkin son jiki, yazo na goyashi".
Murmushi Zaleeha tayi, tare da komawa cikin ɗakin ta ɗauko Adeel ɗin, miƙawa Ameenan shi tayi, tare da cewa "Gashinan ai sai wasan sa yake tayi abinsa."
Karɓansa Ameenan tayi tare da goyasa, sai wutsil-wutsil yake wai shi adole wajen Amminsa zai zauna, har bakin ƙofa Zaleehan ta rako Ameena, tare dayi mata adawo lafiya, da "Ameen." ta amsa, sannan ta juya ta koma ciki.
Zama tayi akan sallayan tana ɗan addu'o'i, tana nan azaune kuwa har aka ƙira sallan isha.
Tana idar da sallan kuwa ta wuce sashin Ummi, nan kan dining ta taradda Saifuddeen, da kuma Hayatuddeen ɗin azaune, sai kuma Ahmad, shigowarta yayi dai-dai da fitowar Ummi daga ɗaki, ƙarasowa tayi cikin girmamawa tayiwa Ummin
"Barka da dare." fuska asake Ummi ta amsa mata, sannan suka zauna akan dinning table É—in.
Raleeya ne tayi seving ɗinsu, nan suka fara cin abincin cikin nutsuwa. Bata wani ci abincin mai yawa ba, dan ta ƙosa da irin kallon da Saifuddeen ɗin keyi mata, gaba ɗaya jinta take wani iri, kuma dama bawai yunwa takeji ba, dan tasha fruit salad, kuma shi kaɗai ma ya ƙosar da ita, miƙewa tsaye tayi tana goge bakinta, dubanta Ummi tayi tare da cewa. "Zaleeha ya kika tashi, badai kin ƙoshi ba." Kanta ta jinjina tare da cewa.
"Eh Ummi naƙoshi sosai, kinsan ɗazu munsha fruit salad, kuma ma inaso ne naɗanyi aiki a system ɗina."
Kai Ummi ta jinjina cike da gamsuwa tace.
"To masha Allah, ayi aiki lafiya, Allah ya tashemu lafiya."
da "Ameen" ta amsa, , cikin kulawa tace.
"My Autan Ummi good night da safe zamuyi magana kaji."
Kansa ya jinjina mata yana murmushi, duban Raleeya da Ahmad tayi, tare dayi musu saida safe, fuska asake duka suka amsa mata, sannan ta fice daga cikin falon, kaitsaye É—akinta ta wuce.
Su kuwa cikin nutsuwa suka kammala cin abincinsu, Hayatuddeen ne ya soma ƙoƙarin tashi tsaye, hannunsa Ummi ta kamo tare da zaunar dashi, ɗago idanunsa da sukayi rau-rau dasu yayi ya kalli Ummi'n, wanda tun ɗazu kunyan kallonta yake, idanu Ummi ta zuba masa, tare da ɗan watsa masa harara, cikin bayyanar masa da ɓacin ranta dan shi baida nitsuwar Saifuddeen shiyasa bata mishi irin Hukuncin da takewa Saifuddeen wanda shi da idoma yakan ɗimauce in tana hukuntashi da kallon tuhuma, to shi autanta yafi gane zahirin zance yafi gane yaren faɗa, cikin haɗe fuska tace.
"Koma ka zauna, Hayatuddeen, wato abun da kake aikatawa kenan ko?, kai atunaninka cewa idanunmu ba akan ka su ba ne, hmmm najima ina zarginka da aikata rashin gaskiya da kuma abun da bai dace ba Hayatuddeen, musamman ma ga yanda bakaso ko wayarka aɗauka, wato shine wannan rayuwar daka zaɓawa kanka Hayatuddeen kana ganin me kyauce? ko irin tarbiyan dana baka kenan?."
Hawayene suka cika idanunsa, sosai jikinsa yayi sanyi, ahankali yaÉ—an shiga girgiza mata kai alaman "A'a." cikin muryan kuka yace.
"Dan Allah kiyi haƙuri Ummi, wallahi bazan sake ba, kuma hakan ba halina bane, bansan me ya ruɗeni ba Ummi, bansan meyasa nake aikata haka ba, bayan kuma nasan da cewa babu kyau, nasan nabiyewa sharrin zuciya da kuma na aboki, amma bazan ƙara ba, wallahi dama Khamis ne ya koya min, kuma nayi miki rantsuwa Ummi, Wallahi ko hannun mace ban taɓa riƙewa ba, tsoro nakeji Ummi, idan keda Hamma kukayi fushi dani, wallahi rayuwata watsewa zatayi, bazan iya jure fushinku ba Ummi, dan Allah kuyi haƙuri."
Fashewa yayi da wani irin kuka, mai É—auke da zallan nadama haÉ—i da danasani.
Kai kawai Ummi ta girgiza cikin sanyi tace. "Bansan yaushe kazama haka ba Hayatuddeen, a iya sanina dakai babu ruwanka da duk irin waƴannan abubuwan na banza, saboda ban koyar daku hakan ba, nasan giyar samartaka ne ke ɗibanka daga kai har Khamis ɗin, kunajin cewa kuma kun tasa, kun fara zama samari, shiyasa kuke ƙoƙarin gurɓata rayuwarku amaimakon gyarata, bahaka na tarbiyantar dakai ba, wannan ɗabi'ar kuma ba irin ta cikin gidan nan bane, na lura kuma barinka da waya da mukayi ne, duk ya jawo hakan insha Allah kuma, daga yau kadaina riƙe babbar waya har abadan kenan, domin da mummunar rawa gwamma ƙin tashi." kuka ya sake fashewa dashi, har acikin ransa yayi danasani da kuma nadama.
Ganin yanda yake kuka sosai ne, yasa Ummi kwantar da murya, cikin nutsuwa ta shigayi masa nasiha mai ratsa jiki, tana gamawa kuwa Ahmad da Saifuddeen harma da Raleeya suka ɗaura nasu, sosai jikinsa yayi, sanyi haka ya dinga sakin sheshsheƙan kuka, tare dayi musu rantsuwa kan cewar bazai sake ba. Nan dai sukayi masa faɗa sosai. Ummi ne ta fara tashi ta wuce ɗakinta, saboda akwai abun da zatayi aciki, Saifuddeen ne nabiyun tashi, saida safe yayiwa su Ahmad sannan ya fice daga cikin falon.
Hayatuddeen kuwa cikin falon ya koma, ya zauna tare da kunna tv, tashar MBC Action ya kamo, inda ya samu suna haska film É—in MULAN, sanin cewa yaga tallen film É—in a net, ya sashi maida hankalinsa ga tv'n yana kallo duk hankalinshi na kan tv.
Ganin haka ne yasa Ahmad sanya hannu ya jawo Raleeya jikinsa, ɗan shagwaɓe masa tayi, akasalance tace.
"Nifa Allah ko Habibi jikina ciwo yake." Murmushi yayi, tare da sanya hannu ya shafi kyakkyawar fuskarta, harshensa yasanya inda yaɗan lashi lips ɗinta, cikin mayen sonta yace. "Muje maza namiki maganin gajiya my kyakkyawar matata." Yana gama faɗan haka, ya ɗagata sama, ƙoƙarin zillewa take amma yaƙi bata daman hakan, haka suka haura sama, yana ɗauke da ita kaman ƴar ƙaramar baby. Hayatuddeen kuwa baisan ma me sukeyi ba, dan gaba ɗaya hankalinsa naga tv. Acan part ɗin Zaleeha kuwa fitowarta daga wanka kenan, towel ta sanya inda taɗan goge ruwan dake jikinta, wani fitinannen body lotion mai ƙamshin gaske ta shafa ajikinta, tare da bin kowani lungu da saƙo na jikinta da daddaɗan turare.
Wata irin fitinanniyar sleep gown ta sanya ajikinta, wanda gaba ɗayanta net ne, sannan an ƙawata gabanta da wasu igiyoyi, sosai rigar tayi mata kyau, yayinda kuma ta bayyana komai na jikinta, gaba ɗaya shape ɗin jikinta a bayyane yake, kasancewar rigar nada breast cup hakan yasa, bata sa brezia ba, wanda hakan yasa shatin pink nipples ɗinta suka bayyana acikin rigar. Wani perfumed ta fesa lungu da saƙo na jikinta tare da yin parking dogon gashinta, atsakiyan kanta.
Tayi kyau sosai,
A hankali ts hayewa saman gado, tare da jawo laptop É—inta, wayarta ta shiga É—an duddubawa, tunowa cewar ta manta shi a falon Ummi yasa taÉ—an dafe goshinta tare da cewa.
"Mitsee wlh na gaji". tsai kuma ta tashi tare da zaro wani ƙaton hijab daga cikin drawer'nta, sanya hijab ɗin tayi, tare da zura wani bedroom slipper aƙafanta, har zata fita kuma sai idanunta suka sauƙa akan sweet ɗin da ta ciro acikin firij wanda har sun zama dutsen ƙanƙara, guda uku ta ɗauka sweet ɗin masu ƙamshin strowberry, ɗaya ta ɓarewa ta jefa a bakinta, kana ta riƙe biyu a hannunta tanajin sanyi su na ratsata, niyarta inma ta shanye ɗayan kafin ta dawo ga biyu a hannu, handle din ƙofar ta murɗa sannan ta fice daga cikin ɗakin, kaitsaye sashin Ummi ta nufa.