← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 154

Sashe 50

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana cikin gabatar da sallan Ameena tatashi, tasha mamakin ganinsa, dan kuwa tasan baya sallah agida,  nan dai ta wuce toilet ta ɗauro alwala, can gefe ta shumfuɗa sallayanta sannan ta tada nata sallan.             
Saifuddeen kuwa yana idarwa, addu'a kawai ya shafa,  ataƙaice yayi azkar tare da ɗan jan jikinsa ya sake hayewa saman gado,  dan zazzaɓin ƙara hawa jikinsa yake, ko ina na jikinsa ya ɗau zafi jau, kamar wanda ake hura masa wuta, sake  duƙunƙunewa yayi acikin blanket, lokaci ɗaya ya fara masassara.              
Koda Ameena ta idar da salla, cikin sanyi ta dubeshi,   tashi daga kan sallayan tayi nan taƙaraso zuwa jikin gadon.      
Cikin kulawa tasanya hannu inda taɗan taɓa forehead ɗinsa, jin jikinsa da zafi yasa taɗan waro idanunta waje.    
Cikin yanayin tausayinsa tace. 
  "Sannu baka da lafiya ne?"                        Idanunsa ya lumshe batare daya amsa mata ba, saboda sam baya son damuwa, cikin zuciyarsa kuwa cewa yayi.
"Kuji shegen iyayi, koma mene bake kika jawomin ba, ina zaman zamana kinzo kin tsotseni, jarababbiya kawai, saboda kin zuƙeni ne ae yasa duk zazzaɓin ya hau jikina,  hakanan ina matsayin saurayi, kinzo cikin mintuna kaɗan kin maidani ɗan ƙaramin bazawari."                 
Ganin yayi shiru ne yasa Ameena cikin tausayawa  ta gyara masa blanket ɗin, nan ta kashe AC'n da sanyinsa keta busawa,   asanyaye tace. 
  "Allah ya ƙara sauƙi."     
Nan tashiga kimtsa ɗakin nasa, tana kammalawa kuwa ta kunna burner, inda ta zuba turaren wuta mai daɗin ƙamshi, take kuwa ɗakin ko ina ya cika da ƙamshi.     
Fita tayi daga ɗakin nasa, kai tsaye ta koma nata ɗakin, wanka tayi  tare da kimtsa kanta cikin riga da sket na atamfa, kana ta yane jikinta da mayafi, flat shoe tasanya, kai tsaye ta nufi ɓangaren Ummi dan zuwa gaisheta, kamar yanda ta saba akowacce rana.

Saifuddeen kuwa, bacci ne ya ɗaukesa, don dama daren jiya baiwani samu isashshen bacci ba.              

Itakuwa Ameena koda ta ƙarasa ɓangaren Ummi, yau bata iske Ummin a falo ba, saidai ta taradda Raliya wanda ke ƙoƙarin kimtsa falon, kasancewar daren jiya anan Hayatuddeen ya ƙare hirarsa da ciye ciyensa, gaba ɗaya yayi fatali da filullukan kujerun falon, ya watsar su aƙasa, sannan ga ledodin sweet wanda yasha ya zubar acikin falon.
     Gaisawa sukayi da Raliyan sannan ta nufi ɗakin Ummi. 
Tsayawa tayi ajikin ƙofar tare dayin knocking,  Ummi dake zaune akan gado, jin ana buga ƙofar, yasa ta bada izinin shigowa,  ahankali Ameenan ta tura ƙofar ɗakin ta shiga.  
Ganin Ameena yasa Ummi sakin murmushi. 
Ƙarasowa cikin ɗakin Ameena tayi, anutse ta durƙusa, cikin ladabi ta gaishe da Ummi'n, nan Ummi ta amsa mata fuska asake, tana murmushi kamar kullum.   
Ganin kaya akan gadon Ummi'n, wanda da dukkan alama kayan gugane, yasa Ameenan tashi, cikin nutsuwa ta shiga jerawa Ummi kayan acikin drawer, sosai Ummi kuwa taji daɗin hakan, dan dama tana ƙoƙarin jera kayan kenan Ameenan ta shigo.   Haka Ameena ta gama jera  kayan tsab, inda suke ɗan taɓa hira kaɗan kaɗan da Ummi'n, tana kammalawa kuwa ta sharewa Ummi ɗakin nata, duk da cewa ma ɗakin fes yake, bai wani buƙatan shara, don kuwa Ummi sam batason ƙazanta, kusan awajenta ma Saifuddeen ya gaji ƙamshi da kuma yawan tsabta da ƙyanƙyami.      Koda ta gama  falo ta dawo, bayan tasamu sanya al'barka daga bakin  Ummi'n,  ganin Raliya  a kitchine yasa tayi  kitchine ɗin itama, nan  tashiga tayata aikin breakfast ɗin da takeyi, inda suke hira sosai.          
Koda suka kammala kuwa akan dinning suka jere komai, lokacin kusan ƙarfe 8 na safiya kenan, Ahmad ne ya shigo cikin falon, dai-dai lokacin kuma Ummi ta fito daga ɗakinta. 
   Cikin girmamawa Ahmad ya gaidata,  cikin kulawa, da kuma nuna ƙauna ta amsa masa.
Sosai tayi mamakin rashin ganin Saifuddeen a falon, dan kuwa tasan dayaje sallan asuba ya dawo, ita yake fara zuwa ya gaisar, amma saigashi yau bashi babu alamansa, abun dayaso ɗaga mata hankali kenan, dan tasan cewa idan Saifuddeen nada lafiya bazai taɓa kai warhaka baizo ya gaisheta ba, kuma kullum, koda yaushe, a irin wannan lokacin zaka sameshi cikin falon nata zaune.
Duban Ameena tayi cikin kulawa tace.
"Ameena waini kuwa yau ina Saifuddeen, anya kuwa yana lafiya?."
Kai Ameena ta sadda ƙasa, cikin sanyi tace.
"Yana ɗakinsa, tun safe yake kwance, zazzaɓi ke damunsa."

Cikin matsanancin damuwa Ummi tace.
"Subahanallah, zazzaɓi kuma, to yasha magani ne?."
Kai Ameena ta girgiza alaman.
"A'a"
Ahmad dake zaune ne yace.
"Nima nayi mamaki dan yau banganshi cikin masallaci ba, kenan ko sallan asuba bai samu yaje ba."
Kai Ameena ta jinjina alaman.  "Eh."
Cikin yanayin sanyi haÉ—i da tausayawa Ummi tace.
"Nidai nasan cewa hakanan Saifuddeen bazai taɓa kaiwa har iwar haka, batare da yazo ya ganni ba, rashin lafiya ce kaɗai zata ɓoyeshi, muje yanzu ki kaini sashin naku na duba shi."
Nan Ahmad da Raliya sukace suma zasu, Hayatuddeen da fitowarsa kenan, jin cewa zazzaɓi na damun hammansa yasa yaji gaba ɗaya hankalinsa ya tashi.
Nan suka bi Ameena zuwa part É—in nasu.

Haryanzu kwance yake acikin blanket, dan kuwa zazzaɓin nasa bai ragu ba, saidai kuma ya farka daga ɗan baccin daya ɗaukesa.
Ahankali Ameena ta tura ƙofar ɗakin, kasancewar itace agaba.
Nan su Ummi suka rufa mata baya.
Ganinsa nannaɗe cikin bargo yasa Ummi ƙarasowa cikin sauri, hannu tasa taɗan ɗage blanket ɗin, hannunta takai ta taɓa goshinsa, jin an taɓa goshinsa ya sashi ɗan buɗe idanunsa kaɗan, dan duk atunaninsa mayyarsan ce Ameena. 
Ganin Ummi yasa shi ware idanunsa, tare daɗan yunƙurawa ya tashi ya zauna.
Cikin kulawa Ummi tace.
"Sannu Saifuddeen."
Kansa ya jinjina mata amatuƙar shagwaɓe, yana me kallon su Ahmad dake tsaye.
KafaÉ—ansa Ummi taÉ—an kama, cikin kulawa haÉ—e da tausayinsa tace.
"Sannu meke damunka ne?."
Sake shagwaɓe mata fuska yayi, cikin zuciyarsa yace.
"Bakune kuka matsa sai na auri wannan Ameenan ba, gashinan jiya duk ta tsotseni, ta rabani da samartaka na, ji yanda take wani wuƙi-wuƙi da ido, ko kunyana ma bataji." 
  a bayyane kuwa hannun Ummin nasa ya kamo, ya ɗaura akan wuyansa.
Nan Ummi taji jikin nasa zafi jau, cikin tausayawa ta dubesa, murya asanyaye tace.
"Zazzaɓine ke damunka ko, sannu, yanzu me kakeson ci, idan kaci sai kuwuce asibiti da Ahmad, dan nasan bakasha magani ba."
Kwaɓe fuska yayi tare da kamo hannun Ummin nasa ya sanya acikin nasa, idanunsa yaɗan lumshe, gane abun da yake nufi yasa Ummin riƙe hannunsa ɗaya cikin kulawa tace.
"Bayan zazzaɓin kuma saime ke damunka!."
haka take lallaɓasa kamar wani ɗan yaro.
Shikuwa kansa ya ɗaura akan kafaɗanta, inda yasa hannunsa ɗaya ya nuna mata waist ɗinsa ta baya, alaman bayan zazzaɓin nan ke masa ciwo, sannan kuma ya nuna mata jikinsa, alamun cewa gaba ɗaya jikin nasa ma ciwo yake masa.
Ɗan jim Ummi tayi tare da ƙuresa da ido, hakanan zuciyarta ta bata wani abu, ɓoyayyen murmushi ta sake, take wani irin daɗi ya cika zuciyarta, hannunta tasanya cikin gashin kansa, cikin yanayin kulawa tace.  
"Fine boy ɗina sannu ko, zakaji sauƙi insha Allah, sannan ciwon jikinma zai daina, yanzu faɗamin mekakeson ci, zan dafa ma da kaina."

Baki Ameena ta buɗe tana kallon Ummi da Saifuddeen ɗin, tunda take aduniya bata taɓa ganin ƙauna irin tasu ba, wannan salon ƙaunar tasu daban take, musamman idan akayi dubi da irin yanda Ummi ke shagwaɓa Saifuddeen, shikuwa indai yana gaban Umminsa jinsa yake kamar yaro ɗan shekara 3, saboda haka duk wata irin shagwaɓa ta duniya da taɓara ya iyata.
Ahmad  da Raliya kuwa murmushi kawai sukayi, dan sunsaba da ganin zallan shagwaɓan Saifuddeen da kuma yanda Ummi ke biye masa, Hayatuddeen kam waje yanema ya zauna.

Sake narkewa Ummin nasa yayi, asakalce ya kuma ƙara ɗaura kansa akan kafaɗanta, sai wani ɗan yamutsa fuska yakeyi, saikace wanda shi yayi aikin.
Kansa Ummi ke shafawa, duban Raliya tayi kana tace.
"Raliya haÉ—o masa tea, da kuma chips, idan yaci sai su wuce asibiti"

Hannun Ummin nasa ya kamo tare da girgiza kansa, cikin body language É—insa, yace.
"Fruit salad da maltina kawai yake da buƙata."
Dubansa Ummi tayi tare da sakin murmushi, nan tace da Raliya takawo masa maltina'n, idan yaso saita koma ta haÉ—o masa fruit salad É—in.
Hakan kuwa akayi, maltina meɗan sanyi Raliya ta kawo masa,  Ummi dakanta ta ɓalle masa murfin maltina'n, ahankali yakai bakinsa tare daɗan lumshe idanunsa,  cikin ransa yace.
"Idan kuwa nasha naji ƙarfi ajikina, ya tabbata cewa wannan Ameenan ba sperm kaɗai ta zuga ajikina ba harda jinina."

Ɗago idon da zaiyi kuwa karab sukai ido huɗu da Ameena wanda ta ƙura masa ido, itakam sosai duk wani acting ɗin da zaiyi yake burgeta, yanzu ma haka ji take inama da ace ita yakeyiwa shagwaɓan nan ba Ummyn shiba aima itace matarsa itace ta dace da irin wannan abin da yakeyi.
ÆŠauke idanunsa daga kallonta yayi, cikin ransa yace.
"Wallahi gudunki zannayi, hakanan da ƙuruciyata  bazan amince ki maidani tsoho ba, daga zuwa ɗaya har kinsani rashin lafiya, next kuwa inaga ko tashi bazan iya ba, da wani idanunki awajen ai kin san dai bani da lfy."
Yaƙare zancen zucin yana ɗan hararan gefenta.

Ahmad kuwa duk abun da Saifuddeen din keyi yana lure dashi, hakanan yasaki wani irin dariya, wanda yasa Saifuddeen É—in watsa masa harara, cikin ransa yace.
"Ehem dole kayi dariya ae, tunda kafahimci cewa mayyar da kuka haɗani da ita, tun ba'ayi nisa ba tafara tsotseni." 
  Idanu Ahmad ya kashe masa alaman, yane?  laɓɓa SAIFUDDEEN ɗin ya ciza, tare da jinjina kai, alaman zasu haɗu ne.
Chapter 50 · 0% Book details