← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 154

Sashe 7

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau Baba Malam yace aje ayiwa Amarya Zaleeha jere, saboda haka tun safe Aunty Lubna da kuma Maryam, sai wata Aunty Aseeya wacce take ƙanwar Mamy sai Aunty Shatu suka kimtsa don zuwa yin jeren,   cikin motar Aunty Aseeyan suka shiga, inda aka haɗasu da ƙatuwar motar dake cike da kayan na Zaleeha wanda su Baba Malam ne ya ƙara matasu duk dan wai ta kwantar da hankalinta, daga gefe kuwa musamman Ya Ahmad yayiwa wani babban company magana, wanda suke da ma'aikata wanda suka iya tsara ɗaki, nan yaɗauki hayan ma'aikata guda biyu wanda sune zasu tsarawa Zaleehan ɗakin nata.
Koda suka isa gidan nasu Saifuddeen wanda sosai ya amshi gyaran da akayi masa, Ummi da kanta ta amashesu, inda tayi Musu tarba me kyau, sosai sukaji daɗin hakan, inda Maryam tacika da farin ciki, domin kuwa sosai taji daɗin karamcin Ummin, dan tasan Zaleeha ta dace da uwar miji, sannan tasan Ummi bazata bar ƴar uwartata ta wulaƙanta ba,   Raihana mutan Kd da Adda Rahma matar Dr Ummi tasanya su kaisu zuwa ɓangaren Zaleeha,   koda sukaje part ɗin da Zaleehan zata zauna sosai suka cika da mamakin yanda aka ƙawata part ɗin, sosai part ɗin yayi kyau, anyi masa tsari mai ɗaukar hankali, inda aka ƙawata komai dake cikinsa,  tabbas sun yaba da haɗuwar part ɗin na Zaleeha, sunkuma yarda cewa Saifuddeen masoyine agareta, don ko ba a faɗa musu ba sunsan sosai ya ɓarnatar da dukiyansa wajen ƙawata wajen,    tuni ma'aikatan da Ya Ahmad ya turo suka haɗu da maikatan da Salisu ya ɗauko sun shiga aikinsu na shirya wajen don kuwa har sun gama kimtsa falo,  sabida su biyarne dan haka aikin ke gudu,
sosai falon ya tsaru haɗaɗɗen falone wanda aka ƙawata gaba ɗaya jikin bangon da wani haɗaɗɗen magic paint me tsananin kyau, yayinda aka watsa wasu   haɗaɗɗun royal chairs atsakiyan falon, kujerune ƴan ubansu wanda aka narka kuɗi sosai wajen sayansu, asalin royal ne masu kyau da tsada, inda kalansu suka kasance milk colour and light sky blue sai kuma ratsin golding ash dake jiki,  sosai kujerun sukayi kyau, yayinda aka malale wani lallausan carpet mai taushin gaske a tsakiyan falon, wanda dazaran ka takashi ƙafafunka zasu nutse aciki saboda tsabar laushi,inda shima yake da kalar milk, and sky,   da wasu irin tsadaddun cottings aka ƙawata jikin window da kuma ƙofar falon, kalan cottings ɗin sun kasance ligh blue irin mai hasken nan,  sannan gaba ɗaya cottings ɗin simples suke basu da wani ado, sai ɗan ratsin golding ash kawai dake jikinsu, cotting ne masu azabar kyau da tsada, wanda suka ɗai ma sun isa ƙawata kyawun ɗakin,   can gefe kuwa wani irin ƙaton tv plasma ne wanda saboda tsabar girmansa yasanya ba'a kafasa ajikin bango ba, kan wani haɗaɗɗen table na glass aka ɗaurasa, wanda kalan table ɗin yakasance sky blue, sai kuma adon jikinsa daya kasance golding ash mai walwali,  gefe da gefen tv'n wasu irin haɗaɗɗun flowers aka sanya guda biyu, ƴan madaidaita, inda flowers ɗin suka kasance kowanne da kalansa, ɗaya milk ɗaya kuma sky, sosai haka ya ƙara ƙawata haɗuwan falon, can gefe kaɗan kuwa, rantsatstsen dinning area ne wanda aka ƙawatasa da haɗaɗɗen decoration mai masifar kyau, inda aka shirya wasu haɗaɗɗun royal chairs wanda suke kalan kujerun dake cikin falon saidai kuma yanayin tsarinsu baizo ɗaya ba, tsakiyan kujerun kuwa wani babban table aka sanya me masifar kyau,  gaba ɗaya falon walwali dake sheƙi yake inda yake fidda ƙyallin haɗuwa, sam ba acika shirgi acikin falon ba, komai antsarasa ne cikin nutsuwa da wayewa, sosai su Aunty Lubna ke yaba falon, saboda ko ƴar gwamna sai haka, sosai Yaya ahmad ya kashe maƙudan kuɗaɗe wajen sayan kayan furnitures ɗin, saboda yana matuƙar son Zaleeha taji daɗi ta zauna ɗakinta shiyasa zai iya kashe ko nawane akanta.

Koda suka ƙarasa zuwa bedroom nansuka samu tuni angama shirya komai, inda acikin ɗakin ma aka zuba wani haɗaɗɗen furnitures mai azaban kyau,  don kuwa haɗaɗɗen royal bed mai kalan white and golding aka kafa mata, inda saman kan gadon ya kasance light blue colour,  sosai gadon ya tsaru da ado haɗi da ƙyale ƙyale irin na zamani, yanayin tsarin gadon kaɗai ya isa nusar dakai cewa ba ƙiran Nigeria bane, inda ajikin gadon akayi wasu haɗaɗɗun bedsite masu kyaun gaske,  gefe da gadon kaɗan kuwa wani tangamemen drawer ne wanda aka cika jikinsa da wani irin zanen ado mai masifar kyau haɗi da wani irin mirror glass me matsanancin kyau, kana can gefe kuwa wani haɗaɗɗen dressing mirror ne me kyaun gaske,  sai kuma stool ɗin sa wanda shima aka ƙawata jikinsa da ado mai ɗaukar hankali, again kuma wani dressing mirror ne ɗan madaidaici mai kyau aka aje aɗan gefe kaɗan,   tsananin tsaruwan da ɗakin yayi yasanya gaba ɗayansu suka shagala, tabbas ɗakin Zaleeha ya ƙawatu iya ƙawatuwa ko aturai al'barka,  komai dake cikin ɗakin abun so da burgewane, tabbas idan za a ƙiyasta kuɗin furnitures ɗin a iya ɗakima kaɗai banda parlour kayan sunkai na 4 million,  domin kuwa kayane masu masifar kyaun gaske,  haka suka dinga yaba kayan, koda suka buɗe bathroom kuwa mamakine yakusan kashesu, sosai aka ƙawatasa kamar ba bathroom ba,  inda wajen wanka ma na glass akayi mai masifar kyau wanda shi kaɗai ya isa ɗaukar hankalinka, sannan gefe ga wani haɗaɗɗen jakuzzie wanda aka ƙawatasa sosai, koda suka fito daga ɗakin na Zaleeha ɗayan ɗakin dake gefen nata suka shiga, don dama 2 bedrooms ne acikin falon,  shima sosai aka zuba masa wasu haɗaɗɗun furnitures masu kalan grey, sosai shima ɗakin yayi kyau, fitowa sukayi daga ɗakin inda suka ƙarasa zuwa cikin kitchine ɗin dake cikin falon, hmmmm wani kaya sai amale, anan fa haɗuwar take, komai dake cikin kitchine ɗin light pink and white colour ne,  sosai aka ƙawata kitchine ɗin, inda aka shirya komai na amfani acikinsa tsab,  da wasu zafafan food flask aka ƙawata jeren kitchine ɗin wanda aƙalla kowanni food flask ɗaya yakai 100k wato dubu ɗari, wani kamma harda ɗori, kaya masu kyau da inganci aka zuba acikin kitchine ɗin, tabbas Zaleeha kam anyi mata auren gata, Ya Ahmad da Baba Malam sun kashe mata kuɗi na fitan hankali wai duk dan su faranta mata rai ko sa samu ta zauna ɗakinta tayiwa mijinta biyayya,  haka dai suka dinga zagaya part ɗin suna yabawa da kyawun komai, inda Aunty Lubna ke ɗaukar komai awayarta, saboda haɗuwan kayan ya zarce misali.
A sashin Saifuddeen ma a ranar aka shirya mishi sabbin kayan gadonshi masu masifar kyau, abundai sai wanda ya gani.
Basu sukabar gidansu Saifuddeen ɗinba sai da sukayi sallan la'asar, bayan sun cika cikinsu da daddaɗan girkin Ummi, inda tayi musu haɗaɗɗiyar fried rice wanda yaji chicken, sai kuma kunun aya mai masifar daɗi,  ga kuma dambun kifi wanda yaji kayan ƙamshi, sosai sukaci abincin don yayi musu masifar daɗi, haka sukayi sallama da Ummi cikin girmamawa kana suka kamo hanyar dawowa gida.

Itadai Zaleeha duk wannan wainar da ake toyawa babu idanunta aciki, don tun jiya takulle kanta aɗaki, bata fita koda cikin falo ne, hasalima zazzaɓi ne ke ɗawainiya da ita kwana biyun.
A dare randa akaje akayi mata jeren ne,
tayi mafarkin wai tana É—akinta na gidan Saifuddeen É—in tana zaune kan gadon,
sai ta hango wani ƙaton maciji baƙiƙƙirin dashi yazo bakin ƙofar ɗakin nata yayi zuɗuɗuɗu ya shige ƙarƙashin gadonta, tana ganin har ya gama shiga ta kasa ihi ko neman taimako, saida taga binɗinshi ma ya shigene, sai kawai ta miƙe a guje ta fita daga ɗakin ta bar gidanma baki ɗaya, tanata gudu bata san inda zata jeba sai Mamanta da Bilkeesu da Ruda ta nuna mata bakin kogi, kawai sai ta nufi cikn kogin har ta fara nisa cikin ruwan da zai iya cinyeta sai taga wani farin dottijo bafulatani ya riƙo hannunta sun fita.
To anan ta farka daga baccin kuma sai ta tashi da zazzafan ciwon kai. hakan yasa sam batason hayaniya.

Musamman Mamy ta sa aka ɗauko mata ƙwararriyar mai zanen lalle da kitso don tazanawa Zaleehan, amma haka Zaleeha ta tubure tace sam ita babu wani lalle da za ayi mata, koda taga Mamy ta matsa kawai saita sa kuka, dan dole haka Mamy ta ƙyaleta, duk wani gyaran amarya kuwa dasuka shirya yi mata haka taƙi basu haɗin kai duk wani abun da za'a bata ace tasha ko taci sai ta buɗe musu shafin kuka, bisa dole suka ƙyaleta, itakuwa Zaleeha shawaran Bilkeesu ne ke yawo acikin ƙwaƙwalwarta, don kuwa Balkeesu ce tayi mata huɗuba akan kada ta yarda ta amince da komai na hidiman bikin, aure ne dai tabari a ɗaura idan yaso bayan an ɗaura auren an kaita gidan musakin plan ɗinsu da suka shirya zai soma aiki.

Koda Rashida dasu Aunty Lumbna da Maryam a Mommy matar Malam Adam sukazo mata da zancen walima ƙi tayi fir taƙi yarda akayi ganin zata kunyatasu yasa suka shereta.

Yau takama ranan jumma'a inda gobe take asabar wato ranan ɗaurin aure kenan, sosai su Saifuddeen suka shiga busy fiye dako yaushe,  hidiman ɗaurin auren na gobe kawai suketayi. Ɓangaren su Hayatuddeen da abokansa suma ba'abarsu a baya ba, don musamman suka ɗinka zafafan shaddodi wanda zasuyi fitan bikin dashi, inda Saifuddeen da kansa ya saya kowannensu haɗaɗɗen getzner wanda zasu saka wajen dinner inda kalan kayannasu ya kasance daban dana abokan ango.
Tunda aka fara hidiman bikin har kawo yau Saifuddeen bai nemi Zaleeha ba koda awaya ne, duk wani abu na hidiman biki da  Rashida da Amira ƙanwar Ya Aminu a sauran ƙawayenta naa gari sukeyi don sunbasu haɗin kae sosai, Bilkeesu kuwa sai tsula rashin ɗa'a takeyi.

Adaren na Jumma'a ne zazzaɓi mai zafi ya rufe Zaleeha, haka taƙi sanar da kowa saima ɓoye kanta da tayi inda ta duƙunƙune acikin bargo tana rawan sanyi, fatanta ɗaya shine Allah yasa ma zazzaɓin yazamo sanadin mutuwarta ta huta da baƙin cikin rayuwa.
Chapter 7 · 0% Book details