← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 154

Sashe 151

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

By
*GARKUWAR FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: "Inaji a jikina Zaleeha bazaki dawo ki sameni a rayeba, shiyasa na rubuta miki abinda na fahimta dan in ankarar da ke.
Ina fatan ko kin dawo bayan raina zaki saurari abun da zan faÉ—a miki, da kunnen basira, kuma inaso kiyiwa kalamaina kyakkyawar fahimta, ki zauna kiyi nazari akan abun da yake faruwa. *Dan inaga kina tare da wanda kike ta wahalan nema kina tare dashi shi kike nema kuma shi kika gujewa* ina kyautata zaton cewa Saifuddeen shine mutumin daya taimaka miki! saboda bayan kin gudu naje gidan Ummin Saifuddeen, naje munyi magana da'ita, ta bani wani labarin daya bani mamaki, wanda kuma labarin irin makamancin labarin da kika bani ne, time É—in da kika faÉ—amin haÉ—uwarku da Dalla, har wani mutumi ya taimakeki, lokacin din da kika faÉ—amin, lokacin É—in Ummi ta faÉ—amin, tace dukan Saifuddeen akayi da magriba, kuma wasu Æ´an kalarene suka dakesa da time da date duk iri É—ayane.
suma kawai zuwa kawai police ya sanar musu aka ce musu yana medical centre bashi da lafiya kuma ƴan kalare ne suka dashi, to su a lokacin ta ranshi lfyarsa sukeyi basubi ta kan waɗanda sukayi dukanba, daga wannan rashin lafiyanne kuma ya rasa ƙafafunsa, saboda abayansa suka dakesa, wannan shiya jawo masa matsalan rashin tafiya, saboda haka ne nakeji ajikina Saifuddeen shine wanda ya taimakeki, dan tace bada gurguntakan aka haifesa ba, kwata kwata faruwar abun shekara ɗaya ne da ya wuce, kuma da aka kaisa medical centre, Abuja suka tura su, daga Abuja kuwa aka wuce dashi India, sai bayan shekara ɗaya ya dawo, hakanne yasa nake kyautata zaton Saifuddeen shine wanda ya taimakamiki, amma kiyi bincike akan hakan, wata ƙila hakan ya zama gaskiya, amma ina roƙonki koda bai kasance shiɗin bane, kizama maiyi masa biyyaya, Zaleeha ki zauna agidan aurenki da zuciya ɗaya, darajar ƴa mace shine ɗakin mijinta, dan Allah Zaleeha kizama me biyayya ga mijinki da kuma Baba Malam, ki nutsu kicire tunanin wani acikin ranki, ki rungumi mijinki hannu bibbiyu, insha Allah Zaki ga riban hakan naso in sanar miki a waya to in na kiraki bata shiga." Cikin wani irin yanayi Zaleeha tayi wani zazzafan numfashi tare da sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya, da kuma sauƙan wasu irin razanennun hawaye, take taji kanta na jujjuyawa, wasu abubuwane suka shiga dawowa cikin ƙwaƙwalwanta, sai yanzu tunaninta ke ƙoƙarin daidaita, cikin yanayin mamaki da ruɗu da gigicewar tunani tace. "Ziyada Hamma SAIF shine wanda ya taimakeni, tayaya hakan zai kasance?."
Cikin mamaki Ziyada tace.
"Haba dai Adda Zaleeha?".
Kai ta shiga ɗan girgizawa, domin kuwa tashin farko taji zuciyarta na neman gamsuwa da zancen, amma kuma abun tambayar shine wazai tabbatar mata da hakan? idan kuma dagaske shiɗin ne me yasa ya ɓoye mata kansa? Turo ƙofar ɗakin akayi, hakan yasa ta ɗago kanta da sauri, Ya Ameenu ne, cikin kulawa yace.
"Inkin gama kiyi sauri, dan yana jiranki awaje." Kanta ta jinjina, shi kuma ya juya ya fice daga cikin É—akin Ziyada na biye dashi dan yafitota da yayi alamun tazo, ko minti 2 basuyi da fita ba, cikin sauri ta juya ta fita daga É—akin, abakin shigowa cikin É—akin sukayi karo da Ziyada, hannun Ziyadan ta kamo, cikin wani irin yanayin da ta kejin kanta aciki tace.
"Shine Ziyada, inaga da gaske Hamma Saif ne, shine wanda ya taimaka min."
Cikin yanayin mamaki Ziyada tace.
"Shi kuma?." Kai ta jinjina alaman "Eh." dan gaba É—aya tashiga mamaki da ruÉ—u. Sakin Ziyadan tayi, cikin sauri ta nufi waje. Dai-dai lokacin kuwa Saifuddeen sun gama magana da Ya Ameenu, harma ya shiga cikin mota, Sule driver ne ya buÉ—e mata murfin motar ta shiga, bayan tayiwa Ya Ameenu sallama.

Tana shiga kuwa Sule driver yaja motar suka tafi, da sauri ta juyo da fuskarta garesa , akiɗime takai hannunta ta tallafo haɓarsa, juyo da fuskarsa yayi ya zamana suna fuskantar juna, wani irin abune taji yana shiga zuciyarta, cikin muryarta da tayi sanyi, take kuma fidda yanayin da take ciki, tace.
"Hamma Saif wai kaine? kaine wanda ka taɓa taimakona? ka tuna fuskata Hamma Saif, please kafaɗamin, kaine wanda ka taimakeni lokacin da yaran Dalla suka so cutar dani?, kafaɗamin Hamma Saif dan Allah ka tabbatar min da hasashena ka tuna a bakin A.A ALIYU." Idanu ya zuba mata naɗan wasu daƙiƙu, lokaci ɗaya ya saki wani irin murmushi me tsayawa azuciya, bayajin zai iya amsa mata wannan tambayan ayanzu, ba kuma bazai faɗa mata bane, kawai dai yafi so ne ya koyar da ita zazzafan soyayyarsa, amatsayinsa na kurma kuma gurgu, duk dama dai ayanzu yasan ta zurma cikin kogin sonsa.

Ganin ya kawar da kansa gefe, yasa ta kamo hannayensa, tare da zubawa gefen fuskarsa ido, wani irin sabon yanayi takeji na ratsa zuciyarta, ahankali ta matsa jikinsa, kan kafaɗarsa ta ɗaura kanta tare da lumshe idanunta, har yanzu jin abun take wani iri, sai-dai murmushin da taga ya mata, ya matuƙar sata a ruɗani.
Ahaka har suka isa baice da ita komai ba, Sule driver na gama parking ɗin motar, ya fito, ware wheelchair din saifuddeen ɗin yayi, cikin nutsuwa ya buɗe murfin motar ya fito, anutse ya hau kekensa ya wuce cikin gidan, da sauri Zaleeha ta rufa masa baya, cikin sassanyar muryarta take ƙiran sunansa, sam bai tsaya ba balle har tayi tunanin zai juyo ya kalleta, sun kawo dai-dai bedroom ɗinsa ne cikin sauri ya shige tare da jawo ƙofar ya rufe, hakanne yasa bata samu daman shiga ba, fuska ta kwaɓe tare da ɗan karyar da wuyanta gefe, a bayyane tace.
"Me yasa bazaka amsa min tambayoyina ba Hamma Saif why?." asanyaye ta juya ta fice daga cikin falon. Shikuwa yana shiga cikin ɗakin nasa ya saki wani irin murmushi, dariya ya ɗanyi me sauti, cikin tsantsar nishaɗin daya samu kansa yace. "Kina yarinya ƙarama amma bakya iya gane mutane to in kin tsufa kuma wato wata ranama cewa zakiyi ni ba mijinki bane ki sani uku".
daga haka kayan jikinsa ya É—an rage sannan ya wuce toilet.

Zaleeha kuwa daga sashin nasa part din Ummi ta wuce, rashin ganin kowa acikin falon yasa taɗan ɗaga murya, tana ƙiran sunan Ummi'n, jin shiru babu amsa ne yasa ta nufi ɗakin Hayatuddeen kasancewar ta jiyo muryar Hayatuddeen ɗin yana ce mata.
"Ummi ta shiga wonka".
kana taga ƙofar ɗakin nasa abuɗe, ahankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Shi kuwa Hayatuddeen zaune yake akan sofa, yayinda ya baje hotunan Abbansu da Ya Nuruddee da Saifuddeen tun kafin ya samu matsalar tsayuwa, kasan cewar in Ummi taga hotunan tana kukane yasa suka ɓoyesu, yanzuma begen ganin mahaifinsu da babban yayansune yasa ya fito dasu.
Hotunan Saifuddeen ne agabansa yana kallo, wanda kuma yayi hotunan ne tunkafun yasamu nakashewar ƙafafunsa, hankalinsa ya ɗanyi nisa shiyasa baiji sallaman nata ba, Ahankali ta ƙaraso cikin ɗakin, tare da baza idanunta akan hotunan dake gaban Hayatuddeen ɗin, wani irin bugawa taji zuciyarta tayi, alokacin da ta sauƙe idanunta kan wani hoton Saifuddeen wanda yake tsaye akan ƙafafunsa shidasu Ahmad dasu Salisu Ishaq yana murmushi, ga fuskarnan tasa fayau ta bayyana, babu wani cikar ƙasumba asamanta, saɓanin yanzu da saje yayi mata ƙawanya, hannunta dake rawa tasa ta ɗauko hoton, gaba ɗaya jikinta ɓari yake, bakinta na rawa tace. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Hayatuddeen waye wannan?."
jin muryanta yasashi É—ago kai, murmushi yayi yana É—an kaÉ—a kai yace.
"Kaman yaya waye wannan kina nufin baki ganeshi bane?." Cikin ruÉ—ani tace. "Please Hayatuddeen kafaÉ—amin waye shi, karkacemin shine Hamma Saif kuma na kasa gane shine dan zan jawa kaina Allah ya isa, ka cemin wanine daban ba Hamma ba."
Cikin yanayin mamaki yaÉ—an shafi sumar kansa, shaye da mamaki yace.
"Ikon Allah yau kuma Hamma Saif ɗinne baki gane ba, to ki wanke idanunki wannan ba kowa bane face Hamma Saif, nasan kinyi mamakine saboda kin ganshi tsaye kan ƙafafunsa, lokacin bai samu matsalan spinal cord injury bane shiyasa." Durƙushewa tayi akan ƙafafunta, murya na rawa tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, wallahi shine, shine mutumin daya taimakeni Hayatuddeen Hamma Saif ne, shi ya ceceni daga hannun ƴan iskan da suka so tarwatsamin rayuwata, shine wanda ya zamemin Garkuwa alokacin da babu me iya taimakona, shi ne wanda ya zama makari kuma madubin dubawata, da ace alokacin babu shi, da yanzu rayuwata wani babin take fuskanta ba wannan ba, Wallahi Hamma Saif ne Hayatuddeen, shi nake ta nema tsawon shekaru Wlh Hamma Saif ne!!!." Ta ƙarishe mgnar da ƙarfi Baki Hayatuddeen ya buɗe yana kallonta, shikam cike yake da mamakin Zaleehan, dan kalamanta sun ɗaure masa kai.
Dai-dai lokacin Ummi ta shigo cikin ɗakin da sauri, kasancewar fitowarta falo kenan, taji tashin maganganun Zaleeha'n, Zaleeha kuwa ganin Ummi yasa ta ƙarasa gabanta cikin sauri, tuni hawaye sun kwaranyo daga cikin idanunta, hannuwan Ummin ta kamo tana jijjiga kai tace.
"Shi ne Ummi Hamma Saifuddeen ne, wallahi da gaske shi ne! Gskyan ADDA MARYAM tayi gsky."
Da mamaki Ummi ke kallonta, cikin rashin gane inda maganganun Zaleehan suka dosa tace.
"Bangane me kike faÉ—a ba Zaleeha, shi ne wa?". Ganin Ummin kaman bazata fahimceta ba, yasa cikin sauri ta nufi hanyar fita daga É—akin, baki buÉ—e Ummi ta bita da kallon mamaki.

Hayatuddeen kuwa zuwa yanzu ya fahimci abun da Zaleehan ke nufi, dan baya taɓa mantawa sun taɓa taɗin da Zakariyya, wani irin dariya yayi, tare da shafa sumar kanshi, cikin matsanancin farinciki yace.
"Yess dama ashe akan mune aketa wannan badaƙalar, wannan shine rashin sani yafi dare duhu, mu ake so kuma mu ake gudu, batare da ansani ba."
Dariya yayi sosai, hakanne yasa Ummi da Raleeya wanda ta shigo yanzu, suka zuba masa ido, cikin ƙufula Ummi tace.
"Wai kam lafiyanka, kaketa dariya?." gyara zamansa yayi, cikin zumuÉ—i ya labartawa su Ummi duk abun daya sani.
Ai kam su Ummi sosai suka shiga mamaki, sun kuma yi farinciki sosai, tabbas sun yarda cewa Allah Babu yanda baya abunsa.
Raleeya kuwa cewa tayi. "Lallaima Aunty Zaleeha ashe dama duk wannan guje gujen naki, akan Hamma ne batare da kinsani ba." ita kuwa Zaleeha tana fita part ɗinsa ta nufa da gudu, dai-dai ta kawo bakin ƙofar shiga falon nasa, shima ya bude zai fito.
Chapter 151 · 0% Book details