← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 154

Sashe 42

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Koda suka shiga cikin rugar sosai Zaleeha taji zuciyarta tayi sanyi, sakamakon ganin yanda jama'ar rugar keta hada hadansu, wanda dukansu musulmai ne kana kuma fulani masu mutunci waɗanda hasken addini ya ratsasu, don da ka kallesu zakaga hasken musulunci agoshinsu, idanu ta lumshe, tare da sauƙe ajiyar zuciya, tabbas akullum tana ƙara godewa Allah daya yita musulma, domin kuwa tabbas duk wani addini da ba na musulunci ba, babu komai acikinsa sai ɓata,
musulunci shi kaÉ—aine haske.
Koda suka ƙarasa gidan nasu Aisha, cikin girmamawa ta gaishe da Innar na Aisha, haka dai suka ɗan gaggaisa da ɗan sauran jama'ar gidan. Nan suka zauna da Aisha'n, suka shiga ɗan taɓa hira.
Sun ɗan jima suna hira ganin cewa la'asar ta kusa ne, yasa Zaleehan miƙewa, nan tace zata tafi, batason yammaci ya mata awaje, Inna Maman Aishan ne, ta bata pure nono cikin wani babban gora, wanda aka zuba zuma acikinsa, Aisha kuwa da kanta ta gasawa Zaleehan naman ƙatuwar Zabuwa, duk yanda Zaleeha taso kin amsa, saida suka sata ta amsa, nan tayi musu godiya sosai, sannan Aisha ta rakota, har kusan wajen rugar, daga haka sukai sallama, inda Aishan tace da Zaleeha sai tazo.

Batayi wani tafiya mai nisa ba ta iso gida, nan ta iske har zuwa wannan lokacin su kawun nata basu dawo ba, É—akinta ta shiga inda ta aje nama da kuma nonon da suka bata.
Fitowa tayi donyin alwalan sallan la'asar, dai-dai nan Elizabet ta shigo cikin gidan, kamar an jefota ba sallama duk tayi wujiga-wujiga da ita, ƙafarnan tata tayi futu-futu, idanunta kuwa sunyi tsuru tsuru, alamun gajiya da wahala ya bayyana ƙarara ajikinta.
Dubanta Zaleeha tayi, kana ta kau da kanta gefe, da taso yi mata sannu da dawowa, amma tunowa cewa Elizabet É—in daga church take, hakan yasa ta fasa, zama tayi akan dakali, tare da jawo Æ´ar butar ta, ta soma al'wala.
Elizabet kuwa kan wani benci dake tsakar gidan ta baje, nan tashiga maida numfashi akai-akai, saikace wacce tayi wasan tsere, amatuƙar gajiye ta ɗago kai ta dubi Zaleeha, wanda ke gudanar da al'wala cikin nutsuwa, ƙura mata idanu Elizabet ɗin tayi, tana me kallon yanda take alwala'n, cikin ranta tace.
"Oo ni Elizabet kalli yanda suke gudanar da ibadansu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da jin daÉ—i, batare da wani hayaniya ba da ife-ife da raye-rayeba."
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da ɗan gantsarewa dan azabar ciwon da ƙugunta yakeyi sabida wuni rawan da suka wuni tiƙawa a majami'ar bautar tasu.
Duban ƙafanta wanda sukayi suntum tayi, hakan kuma ya farune sakamakon tiƙar rawa da tayi a church, don kuwa tun safe suke rawan bahutu, gaba ɗaya ta gaji.
Idon dai ta zubawa Zaleeha tana ganin yadda take gudanar da harkar ibadarta a mutunce.

Ita kuwa Zaleeha, tana alwalanne amma gaba ɗaya kewar da begen gida da danginta da Baba Malam ne ya cika zuciyarta, sosai takejin kewar mahaifin nata, tana matuƙar son Baban nata ƙwarai da gaske, tabbas ta wani ɓangare tanajin son komawa gida, tana so da ƙaunar taga tayiwa mahaifinta biyayya tana son farin cikin shi dana Ya Ahmad koda irin al'ƙawarurrukan da ya mata, tana jin ciwo a ranta ace da aure a kanta a kuma bata gidanta ɗakinta damahaifinta ya umarceta data zauna lokuta da dama tamkar tayi zama tsuntsuwa tayi fiffige ta koma cikin iyayenta tayiwa mahaifinta biyayya, koda ko sanadin rasa masoyin nata zaisa ta rasa ranta.
To amma hakanan takeji kaman anÉ—aure ta da jijiyoyin jikinta, wanda takejin kamar dole akai mata zama anan Numan É—in tanaji a ranta tana son ta koma amman duk sanda ta aiyana haka sai taji kamar a É—aureta ne, a garin, haka dai ta kammala al'walanta kai tsaye ta wuce É—akinta,
a nan tabar Elizabet zaune tana ta faman maida ajiyar zuciya.

Sallah tayi sannan ta jawo goran nonon, nan taÉ—ansha kaÉ—an sosai kuwa taji daÉ—insa, kasancewar bata wani jin yunwa yasa ta ajiye, kan cewar sai zuwa dare taci zabuwan da kuma nono'n....

Gombe State.

Kasancewar yau ya kasance litinin, kuma yaune su Adda Rahama zasu wuce Kaduna, daga nan kuwa Abuja zasu inda zasu É—au lefen agidan Ya Ahmad, sukai zuwa gidansu Ameena.
Ƙarfe 9 dai-dai dukansu suka hallara afalon na Ummi, Adda Rahama, Goggo Dada, Ahmad da kuma Hayatuddeen, sune wanda zasu tafi, tun ƙarfe 8 Raliya ta gama musu break fast, inda sukaci suka ƙoshi, ƙarfe goma dai-dai jirgin dazai kwashesu zuwa Kaduna zai tashi, hakan yasa tuni suka kammala duk wani shirye-shiryensu, ɓangaren Saifuddeen kuwa, yana can part ɗinsa, baimasan wainar da suke toyawa ba.

Kasan cewar lokacin ana tsaka da gyara Airport É—in Abuja shine ya basu damar samun jirgin kaduna kai tsaye.

Raliya da kuma Ummi sune sukai musu rakiya, har zuwa airport, kamar yanda yake arubuce kuwa ƙarfe 10 dai-dai jirgin nasu ya tashi.

Kwata kwata tafiyar mintuna 46 jirgin nasu yayi, ya iso cikin airport ɗin garin Kaduna, koda suka sauƙo daga cikin jirgin nan suka iske Saminu najiransu, wanda shi da kansa yazo ɗaukarsu, sunyi farin ciki sosai da ganin juna, nan ya kwashesu cikin motarsa, suka nufi gidansa.

Adda Rahama na shiga cikin gidan, Raihana ta rungumeta cikin tsananin farin ciki, itama Adda Rahaman rungume Raihanan tayi, don kuwa tayi kewarta, Hayatuddeen ne ya zumɓura baki tare da cewa.
"Wayyo Adda Raihana ni bazaki rungumeni bane, kodai bakiyi kewata bane?."
Dariya Raihana tayi tare dajan kumatunsa, cikin tsokana tace.
"Ƙato dakai ne zan rungume ka, kaikam ai saidai ma nasa maka duka, kancewa ka shigomin gida, ƙato dakai, ai da katsaya daga waje."
Dariya suka sanya su duka, Hayatuddeen kuwa, sake tunzura baki yayi, tare da faÉ—in.
"Ae dama batun yauba nasan Raliya tafiki sona."
Jin haka yasa Adda Raihana'n jawo hannunsa, cikin ƙaunar autan nasu, ta rungumesa, cikin son sanyaya masa zuciya tace.
"Inasonka mana autan Ummi, ai kowa ya soka bayana ne, saboda kai fa yasa na shirya lafiyayyen girki, harma fa ferfesu nayi maka naka kai kaÉ—ai na musamman."
Jin haka yasa Hayatuddeen sakin murmushi mai É—auke da tsananin farinciki.
Cikin jin dadi yace.
"Yesss shiyasa nake ƙara sonki Adda na, saboda koba komai kinfi su matar o'o kirki."
Yaƙare maganar yana me satan kallon Ahmad.
Dariya suka sanya don sarai sun gane dawa yake.
Ahmad kuwa ƙwafa yayi inda yace.
"Zamu koma ne yaro zakayi bayani agabanta."

Nan dai suka zazzauna inda Raihana ta cika musu gabansu da kayan ciye ciye, haÉ—i dasu drinks.
Saida sukaci abincin suka ƙoshi sannan, suka kimtsa don kama hanyar Abuja. Inda Ahmad ya ɗauki ɗayar motar Saminu, wanda ya ɗauki Goggo Dada da kuma Adda Rahama acikinsa, sai kuma Saminu wanda ya ɗauki, Hayatuddeen da kuma Matarsa Raihana.

Kasancewar tsakanin Abuja da kuma Kaduna babu wani nisa, hakan yasa suka isa dai-dai an idar da sallan Azahar.
Kaitsaye unguwar Wuse zone 2 suka nufa, wanda anan gidan Ya Ahmad yake.
Koda suka ƙarasa gidan sun samu tarba me kyau daga wajen Aunty Lubna, sunkuwa ji daɗi ƙwarai, nan tafito musu da kayan auren suka gani, sosai suka yaba, don ƙwarai kayan sunyi kyau.
Kimtsawa itama Aunty Lubna'n tayi, inda cikin motarta su Hayatuddeen suka loda akwatunan.
Kaitsaye suka nufi Asokoro wato gidansu Ameena.

Horn sukayi inda maigadi ya wangale musu gate É—in gidan, suka shigar da motocinsu ciki. Tabbas gidan yayi kyau ba laifi, sannan suma masu kuÉ—i ne.
Wata matashiyar Mata itace ta fito zuwa compound É—in gidan, nan tayiwa su Adda Rahama jagora zuwa cikin gidan, yayinda driver da kuma mai bawa flowers ruwa sune suka shiga jidon akwatunan suna shigarwa zuwa falon gidan.
Koda su Adda Rahama suka ƙarasa zuwa cikin gidan, sun samu tarba mai kyau, cikin karramawa matan da suka samu acikin falon suka tarbesu.
Nan dai suka zauna inda suka gaggaisa.
Take kuwa aka cika musu gaba da kayan shaye shaye.
Bayan sun É—an nutsane.
Adda Rahama ta gabatar musu da kayan, nan suma suka yaba sosai, haka dai suka ɗan taɓa hira cikin mutunta juna.
Koda suka tashi tafiya haka aka cika musu bayan motarsu da kayan ciye ciye.
Nan dai suka rabu cike da ganin mutumcin juna.

Duk wannan wainar da ake toyawa Ameena na kwance aɗaki tayi ƙumus, zuciyarta cike take da ɗanyar farinciki, ji take kaman tafi kowa sa'a aduniya, bazata iya misalta daɗin da takeji ba, tabbas babbar nasarace samun Saifuddeen amatsayin miji.

Su Adda Rahama kuwa, gidan Aunty Lubna suka koma, nan dai suka É—iba mata kayan ciye ciye dana shaye shayen da aka haÉ—osu dashi.
Basuwani jima agidannata ba suka kamo hanyar Kaduna.

Can gidan su Ameena kusa, ƙwarai sun yaba da kayan, kasancewar sanin Ameena ba budurwa bace, hakan yasa basui tunanin dangin Saifuddeen din zasuyi mata wannan karamcin ba.
Koda Momma taƙirawo ta akan cewar tazo taga kayan, koda tagani taji daɗi ƙwarai, don harta farincikinta saida ya kasa ɓoyuwa, Allah kawai take ta godewa acikin ranta.

Can Kaduna kuwa, gaba É—ayansu zaune suke afalon Raihanan, inda suke ta hiransu, Hayatuddeen ne yasaka bowl É—in snacks agaba yanaci kana yana yagan cinyar kaza, sai wani jijjiga kansa yake, yana lashe red lips É—insa, wanda suke shige dana Hamma Saifuddeen É—insa.
Dubansa Adda Rahama tayi, cikin zolaya tace.
"Aikin ka kenan autan Ummi ci, acici kazar birni, niko da ace halittarka mai ƙiba ne, sannan ci nasa ƙiba, tabbas Hayatuddeen da yanzu girman jikinka ya cika falon nan."
Idanunsa ya zazzaro waje.
Cikin shagwaɓa yace.
"Haba Adda saikace Yaya Saminu."
Dundu Raihana takai masa tare da cewa.
"Mijin nawa?."
Dukansu suka sa dariya.
Ahmad kuwa cewa yayi "KaÉ—an ma kika gani indai Hayatuddeen ne."
Shima dariyar yayi kana yace.
"Ya Wareesu fa nake nufi."
Haka dai sukaci gaba da hiransu, har aka ƙirayi sallan magriba.
Saida sukayi sallan Isha kafun suka zauna inda suka sake kafa sabon hira.
Haka dai sukaita hira har kusan goman dare, dagananne kowa ya nemi makwanci, Inda Ahmad da Hayatuddeen suka shiga cikin wani extra É—akin dake cikin falon, Su Adda Rahama, da goggo Dada ma É—aki guda aka basu. Domin kuwa gidan na Saminu akwai yalwatattun É—akuna.
Chapter 42 · 0% Book details