Sashe 21
Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zaleeha kuwa dama gaba ɗaya batayi wani ishashshen bacci ba, dan sanyine awajen sosai, jin motsi alaman cewa yatafi masallaci yasata tashi zaune, cikin sauri ta ɗau bargon haɗi da pillow'n ta, ahanzarce tanufi ƙofar falon nata, dai-dai lokacin Ahmad yafito daga ɓangarensu dan zuwa masallaci, idanunsa ne suka gane masa Zaleeha, fuskarsa ɗauke da ɗan mamaki yabita da kallo, ganin fitowarta daga cikin garden gashi hannunta riƙe da bargo da kuma pillow alamun nan ta kwana kenan yasanyashi girgiza kansa, cikin ransa yace.
"Allah Ya shirya ki, ae dama mai hali baya taɓa fasa halinsa, saidai in ba'a zauna ba kuma dai duk tsaurin wayon amarya to wlh sai ansha manta anci sadaki an suɗe ki dai gama ɓoye-ɓoyenki."
Nan yawuce masallaci.
Itakuwa Zaleeha sam-sam ma bataga Ahmad ɗin ba, kaitsaye ɗakinta ta wuce, cikin hanzari tasoma rage kayan jikinta, ruwan ɗumi ta haɗa inda tayi wanka, tana fitowa daga wankan ta zura wata farar jallabiya mai kyau, hijab tasanya tare da ta da sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayan ba saida tayi azkar, nan ta ɗauko ɗan ƙaramin Qur'aninta tasoma karatu, ba'ita ta rufe Qur'anin ba saida taga gari yaɗan somayin haske,
wasu bedroom slippers masu kyau ta zura aƙafafunta, inda tasake feshe jikinta da turare me daɗin ƙamshi.
Koda tafito daga ɓangaren nasu kai tsaye part ɗin Ummi ta nufa, bakinta ɗauke da sallama haka ta kutsa cikin falon, wanda ke cike da jama'a, Raihana ne da Saminu waƴanda zasu koma Kaduna asafiyar ta yau, saikuma Goggo Dada da Aunty Meena wanda zasu koma Dukku, Aunty Rahama ma yau zata koma, don tunjiya Dr.Adnan keyi mata waya, kan cewar yayi kewarta gashi weekend yana gida shiyasa yace zaizo da safen ya ɗauketa.
Cikin yin ƙasa da kai haɗi da nuna tsantsar ladabi taƙaraso cikin falon, har ƙasa ta durƙusa inda ta gaishe da Ummi, cikin fara'a haɗi da sakin fuska Ummi ta amsa mata gaisuwan nata, tare da miƙo mata hannu ta kamo nata, cikin kulawa Ummi tace.
"Taso kizonan kusa da Umminki yarinyar kirki, kema ai É—iyatace, tunda kika shigo cikin mu kuwa kinzama jininmu."
Tasowa tayi daga inda take tare da ƙarasowa kusa da Ummi,
Ummi ne tajawota inda ta zaunar da ita agefenta, sadda kai ƙasa Zaleeha tayi tana murmushi, hakanan itakam Allah ya samata son matan aranta, sosai take ganin ƙima da kuma darajan Ummi'n, su Raihana ne suka gaishe da Zaleehan, amatsayinsu na ƙannen Saifuddeen, haka ta amsa musu fuska asake, ɗan zamowa ƙasa tayi inda tagaishe da Goggo Dada dakuma Aunty Meena, sai kuma babbar yaya wato Adda Rahama, da kuma Saminu wanda ke zaune gefen Saifuddeen, da fara'a akan fuskarsu duka suka amsa gaisuwar nata, komawa gefen Ummi tayi ta zauna a ƙasan carpet dan tana matuƙar ji da ganin darajar Ummi, shiru tayi yayinda ko kallon inda Saifuddeen yake batayi ba, shikuwa har acikin ransa mamakin irin tsantsar ladabinta ga ƴan uwansa yake, tanason kowa acikin ahalinsa tana mutuntasu da girmamasu, amma wato shine marainin wayonta sam bata ganinsa da gashin ido, murmushi yayi wanda shi kaɗaine yasan ma'anonin murmushin ransa yace.
 tabbas kuwa zanyi maganinta ne, very soon zankashe bakin tsiwan, badai ni ta raina ba?."
hmmm yasha alwashin duk randa ya kamata kuwa zataji ajikinta.
Saminu ne yace da Raihana su hanzarta sutafi, bayason tafiyar da bata safiya ba, saboda alokacinne yakejin karsashi ajikinsa, nan kowa yatashi don yi musu rakiya zuwa compound ɗin gidan, ciki kuwa harda Zaleeha wanda ta kamo hannun Daddy yaron Bappa Ali wato Junior mai sunan Abbandu Saifuddeen kenan, kasancewar yaron kyakkyawane yasanya sosai yashiga ranta, gashi nan da wayonsa irin yaran nanne masu shiga zuciya, haka suka fito compound ɗin gidan inda yaketa zuba mata surutu, itakuwa murmushi kawai take tayi masa, har bakin mota suka rako su Raihanan, nan sukayi sallama da juna, cikin yanayi na tsokana Raihana ta dubeta, tare da cewa.
"Kikulamin da Hammana da kyau da kyau, dan ko ƙuda bama son ya taɓa manashi."
Dariya sukayi gaba É—ayansu,
itakuwa Zaleeha ɗan guntun murmushi tayi, yayinda taji wani malolon abu ya tokare maƙoshinta, cikin zuciyarta tace.
"Lallai kuwa zai mutu, indai nice zan kula dashi!.
Yo ni me haɗina dashi kunamai ma su sauƙa ajikinsa mana ba ƙuda ba ni me yadameni."
Motar su Raihana baigama fita daga gidan ba saiga Dr.Adnan nan shima yazo ɗaukar matarsa, nanfa suka gaisa, inda Zaleeha tagaishesa cikin mutuntawa, Farouq da Adam kuwa sai tsalle suke dan sunga babansu, duk girmansu baigani ba haka yasasu ajikinsa, babu yanda basuyi ba akan cewa Daddy yazo su tafi ba amma yaƙi, waishi ala dole yasamu sabuwar Aunty yace shi Dukkunma bazai komaba, kusan saida yabawa kowa dariya haka suka tafi anata raha.
Daddy kuwa da ƙyar suka iyayi masa wayo yabi iyayen nasa da karatunshi, Ahmad ne yazo da motarsa wanda dama shine zai mayar dasu Goggo Dada gida, lokaci ɗaya fa gaba ɗaya jama'an baƙin biki suka watse gida yayi shiru.
Ummi Raliya da kuma Zaleehan kawai aka bari, dama Saifuddeen yana part É—in Ummi, kasancewar shi baifito rakiyan ba, shikuwa Hayatudden sarkin bacci, yanacan tun dawowansa daga sallan asuba daya koma bacci shine haryanzun baitashi ba.
Direct Zaleeha part É—inta ta koma, inda su Ummi da Raliya suka koma wajen Saifuddeen.
Tana shiga cikin ɗakin nata ta cire hijabin dake jikinta, kan gado ta faɗa tare da ɗan lumshe idanunta, sosai takejin wani sabon bacci naƙoƙarin ɗaukarta.
Can ɓangaren Ummi kuwa, Saifuddeen naganin dawowansu, ya sakawa Ummin nasa shagwaɓa, sanin halinsa na sakalci kaman wani ƙaramin yaro yasanya Ummi da kanta tashiga kitchine inda ta haɗa masa coffee, sosai yaji daɗin haɗin coffee ɗin da Ummin tayi masa, ɗaukan mug ɗin yayi tare da bar musu falon, kai tsaye yanufi sashinsu.
Saifuddeen nafita, Ummi tayi murmushi cikin jin daÉ—i tace.
"Allah kenan maiyin yadda yaso a lokacin da yaso, kafun auren nan kowa yasan cewa yarinyar nan bason auren nan take ba, amma yanzu cikin ƙuduran Allah gashi suna zaune lafiya, kinga ta saki ranta."
Murmushin gefen baki Raliya tayi tare daÉ—an muskutowa, cikin jimamin abun dake damun zuciyarta tun daren jiya tace.
"Hmmmm hakane kam Ummi, amma nikuwa jiya naga abun daya É—auremin kai ya bani mmki, dan nima da fari da naga ta saki ranta naji daÉ—i."
Dubanta Ummi tayi tare da cewa.
"Mene kuma yafaru?."
Gyara zama Raliya tayi tare da cewa.
"Ummi kinsan kuwa cewa jiya awaje cikin garden ta kwana? wallahi Ummi abun yabani mamaki sosai, inata tunanin dalilin da zaisa ta kwana cikin garden, idan har zatana gudunsa haka, meyasa ta amince da aurensa?."
Cikin matsananci mamakin jin maganan da Raliyan ta faɗa Ummi ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya, jiki amace tace.
"Raliya kin tabbatar da abun da kike faÉ—a kuwa?."
Kai Raliya tajinjina tare da cewa.
"Wallahi Ummi da idanuna naganta jiya a garden ta kwana, kuma koda natashi sallan asuba dana leƙa naganta, alokacin tana ƙoƙarin barin wajen, kuma tabbas nasan babu makawa itace dan Abban Farida ma ya ganta dayazo tafiya masallaci."
Ɗan jim Ummi tayi tare dajinjina kanta, take taji zuciyarta tayi mata wani irin ba daɗi, hankali ya tashi fargaba ya cika mata zuciya wato har ƙiyayyar ta kai haka, jiki a mace tace.
"To Allah dai ya kyauta."
Amin Amin Raliya ta amsa jiki a mace.
Haka dai zaman yaci gaba da gudana har tsawon kwanaki, Kullum in gari ya waye Zaleeha na idar da salla zataje ta gaida Ummi a mutunce, lokuta da dam takan samu Saifuddeen a wurin Ummi, amman tsakaninta dashi sai harara da murguɗa baki,
tana son kowa na gidan yayinda suma duk suke matuƙar sonta musamman Raliya da takanje har ɗakin Zaleeha su ɗanyi hira,
dan itacema ta tayata shirya tarin akwatunan kayan aurenta da kimtsa mata duk abinda zata buƙata a durowa, sauran akwatunan suka kaisu ɗaya ɗakin,
Hayatuddeen kuwa dama akwai sabo a tsakaninta haushinta da yaji kan cewa da tayi bata son Hammanshi yanzu babushi tunda yanaga har ta yarda da auren ta zauna lafiya dashi.
tana matuƙar girmama Ummi wanda hakan yasama mata soyayya a idanunsu,
tana mutunta Ahmad a cewanta mai sunan yayanta ne dan Yaya ma take kiranshi tun tana gaidashi yana amsawa a yatsine har dai ya fara É—an sasaautawa.