← Book details Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 154

Sashe 69

Nakasa Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubansa Ummi tayi tare da cewa.
"Lafiyanka kuwa Saifuddeen, akan me zaka koreta?"
Rumtse idanunsa yayi tare da girgizawa Ummin nasa kai, alaman cewa bayason ganin Zaleehan. Kukan daya zo mata ne takasa dannewa, hakan yasa ta sakeshi da tsananin ƙarfi a hankali jiki na rawa ta shiga takowa, tana ƙarasowa gaban Ummi.
Ganin halin da take cikine yasa Ummi miƙo mata hannu alamun tazo.
ai kuwa ganin haka yasa da sassarfa ta ƙaraso gaban Ummi cikin kuka ta zube akan guiwowinta, tare da ɗaura kanta akan cinyar Ummin, nan ta saki wani irin gigitaccen kuka, mai ratsa zuciya, da kuma ban tausayi, Shiru sukayi gaba ɗayansu falon sai sautin kukan Zaleeha'n ne kawai ke tashi, wanda hakanne ya sanya gaba ɗaya jikin su Adda Rahama Ahmad Raliya yayi sanyi, Kuka take kamar ranta zai fita, cikin kukan tare da sarƙaƙƙiyar muryarta wanda bata fita sosai tace.
"Na shiga uku Ummi Baba Malam yayi fushi dani, naje gidansa ya koreni, yace baya ko son ganina, Ummi kowa baya sona, kowa guduna yake, Ummi ya zanyi, yazanyi da rayuwata, Ƴar uwata tatafi ta barni, Babana kuma yana fushi dani, duka ƴan uwana suna fushi dani, ina zansa rayuwata, Ina ma da ace mutuwa ni ta ɗauka ba Adda Maryam ba, ina ma ace mutuwa zata ɗaukeni!!!." ta ƙare maganar tana sakin wani irin gigitaccen kuka, harda shiɗewa.
Jin abun da Zaleeha'n ke faɗa ne yasa Ummi taji idanunta sun kawo ƙwalla, wani irin tausayin Zaleehan ne ya kamata,
Cikin wani irin yanayi Numfashin Zaleehan ya sarƙe aƙirjinta,
Ummi ne tasanya hannu ta ɗan ɗagota, hakan kuwa yayi dai-dai da ɗaukewar numfashinta, take ta tafi luuuu ta faɗi ƙasa summamiya.
Hankalin Ummi da su Adda Rahama ne yayi wani irin masifaffen tashi, da sauri sukayo kanta.
Ganin Haka yasa Saifuddeen rumtse idanunsa, wanda lokaci guda sukayi ja, bayajin zai iya cigaba da zama acikin falon baya jin zuciyarshi nada ƙarfi da taurin da zata juri ganin halin da Zaleeha ke cikiba, hakan yasa ya danna madannin kekensa, batare dasu Ummi sun farga ba ya fice daga cikin falon.

Littafin nan na ƙuɗine

By
*GARKUWAN FULANI*
10/4/20, 7:04 PM - Mmn Khalid: Sbpejddwl Cikin tsananin ruÉ—ani da firgici Ummi ta É—ago kanta, ta kalli Raliya, cikin sauri tace.
"Raliya bani ruwa na yayyafa mata maza-maza bani da sauri-sauri, kiyi sauri mana."
Cikin sauri jiki na rawa Raliya ta nufi, fridge ɗin dake cikin falon, goran ruwa ta ɗauko, saboda tsabar sauri kuwa har tana haɗawa da tuntuɓe. Ummi ne ta karɓi goran ruwan, jiki na rawa ta ɓalle murfin tare da zuba ruwan ahannunta, ta watsa a fuskar Zaleeha, ko motsi batayi ba bare su saka ran farfaɗowanta, ganin haka yasa Ummi sake watsa mata wani ruwan, nan ma shiru, babu alaman cewa numfashinta zai dawo jikinta, hakanne yasa arikice Ummi ta ɗago da kanta ta kalli Adda Rahama, wanda itama gaba ɗaya ta gama tsorata da sha'anin Zaleehan, sake ɗebo ruwan Ummi tayi akaro na uku ta watsa da ƙarfi akan fuskar Zaleeha'n, minti ɗaya kacal taja wani irin ajiyar zuciya me ƙarfin gaske, wanda hakanne yasa Ummi dasu Adda Rahama wanda suke amugun tsorace suka sauƙe wasu tagwayen ajiyar zuciya masu nauyi.
Batare da ta buɗe idanunta ba, sheshsheƙan kukanta ya soma tashi, kanta dake matuƙar sarawa da wani irin matsanancin ciwo ta shiga jujjuyawa tare dasa hannu ta riƙe kan, lokaci guda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, hannu Ummi tasa ta tallafota, cikin kulawa tashiga shafa bayanta,
jinta ajikin Ummi yasa tasake jin wani irin fitinannen kukan tausayawa rayuwarta ya taso mata, hakan yasa ƙam ta rungume Ummin tana kuka sosai, kuka take mai tsananin zafi da gigita, kukane irin mai ɗauke da tsananin dana sani, haɗi da zallan na dama, kukane me ɗauke da zallan baƙincikin rayuwa, haka zalika kukane dake bayyana, gaskiyar abun dake cikin rai da zuciyarta, sannan kuma yake bayyana zallan tashin hankalinta.

Cikin matsanancin tausayinta Adda Rahama ta miƙe tsaye, kaitsaye gaban fridge ta nufa, goran ruwa me ɗan sanyi ta ɗauko, hannu tasa taɗan dafa kafaɗan Zaleeha'n, wanda har yanzu take nan a jikin Ummi, kuka take sosai kamar ranta zai fita. Asanyaye Adda Rahama tace.
"Kukan ya isa haka Zaleeha, dubi yanda jikinki duk ya ɗauki zafi jau, zakije kisawa kanki wani ciwon, kisha ruwa ko abun zai ɗanyi miki sauƙi."

Kai Ummi ta jinjina cike da tausayin Zaleehan ta karɓi goran ruwan, ɗago Zaleehan tayi tare da cewa.
"Karɓi ruwa kisha Zaleeha nasan zakiji sanyi acikin rai da zuciyarki, sannan kada ki manta kuka baya maganin komai, ki ya waita yin addu'a, hakan zaisa kiji sanyi acikin ranki, yanzu dai kidaina wannan kukan, karɓi ruwa kisha kinji." Kanta ta shiga girgizawa, take kuma numfashinta ya soma wani irin fusga kaman zai ɗauke, sosai jikinta ke ɓari, kukan ta shigayi kaman zata shiɗe, gefe guda kuwa ga wani irin masifaffen ciwon kai da yasa takejin kaman kanta zai rabe gida biyu.
Ganin haka ne yasa Ummi ta kamo kafaɗunta, soma jijjigata tayi, hankali amatuƙar tashe tace.
"Kinutsu Zaleeha, ki dawo cikin hayyacinki, kidaina wannan kukan, Insha Allahu Baba Malam zai yafe miki, dan Allah ki daina wannnan kukan kinji."
Ummi tafaɗi maganar, hawayen tausayin Zaleehan na sauƙa daga cikin idonta, sosai take matsanancin jin tausayin Zaleeha'n, ganin haka ne yasa Raleeya komawa gefe itama ta fashe da wani irin kuka, sosai takejin tausayin Zaleeha'n, saboda ba' a iya matar ɗan uwa kaɗai ta ɗauki Zaleehan ba, tana jintane kamar ƴar uwarta ta jini. Kana tasan zafi da ƙuna da ciwo da ƙuncin zuciyar da mutun keji lokacin daya rasa ɗan uwanshi, domin har yau in begen Ya Nuruddeen ɗinsu ya dawo musu kuka sukeyi koda hotonsa suka gani, shiyasa takeji tausayi Zaleeha.
Gaba ɗaya falon ya ɗauki shiru babu abun da ke tashi, sai sheshsheƙan kukan Raliya dana Zaleeha, wanda kuma takeyinsa cikin fitar hayyaci, duban Raleeya Ummi tayi, cikin sanyin murya tace.
"Haba Raleeya ya kukeso inyine kunsan bana son kukanku, madadin ki lallasarmin ita sai kema ki tasata gaba kuna kuka ya kukeso inyi.
Maza tashi ki haÉ—o mata tea me kauri tasha, dan nasan duk yau bataci komai ba."
Miƙewa tsaye Raleeya tayi tare da share hawayen dake kan fuskarta, kai tsaye ta wuce kitchine don haɗawa Zaleehan tea kaman yanda Ummi ta buƙata.

Ummi kuwa hannun Zaleehan ta kamo, tare da miƙar da ita, kaitsaye ta jata zuwa bedroom ɗinta, Adda Rahama wanda itama gaba ɗaya zuciyarta ta gama karyewa, ta rufa musu baya.
Akan gado Ummi ta zaunar da Zaleeha'n, tare da kamo hannuwanta, ta riƙe, cikin halin tausayawa tace.
"Kuka bashida amfani, sannan kuma baya magance damuwa, ki riƙa faɗin kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, insha Allah zakiji sauƙi acikin zuciyarki."
Cikin sheshsheƙan kuka ta jinjina kanta, ahankali ta soma motsa laɓɓanta wanda sukayi mata nauyi, so take ta furta kalman, amma harshenta rawa yake, kamar yanda duka ilahirin jikinta ke rawa.
Ganin haka ne yasa Ummi soma faÉ—in kalman abakinta, take kuwa ta amsa, nan ta jingina kanta da cinyar Ummi tana faÉ—in 'Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."
tana magananne cikin matsanancin kuka da rawan murya.
Dai-dai nan Raleeya ta shigo hannunta É—auke da cup É—in tea.

Hannu Ummi tasa ta amshi cup É—in, É—an É—ago Zaleehan tayi, cikin kulawa tace.
"Tashi kisha kinji, nasan ayanda kike É—innan, koda kika je gidan nakuma bakici komai ba."
Cikin kuka ta girgiza kanta, don batajin akwai wani abu aduniya da take buƙata, batajin cewa zata iya sanya wani abu abakinta yayi mata daɗi, matuƙar kuwa Baba Malam bai yefe mata ba, yafiyar Baba Malam shi kawai take buƙata ayanzu da yafiyar wandake matsayin mijinta.
Cikin muryarta dake rawa haɗi da sarƙewa tace. "Ummi bazan iya shaba, banason komai, bana sha'awar komai ayanzu idan ba yafiyar Baba Malam ba, dan Allah Ummi ki roƙeshi ya yafemin."

Hawayene suka kuma cika idanun Ummi, amma saita shanye su, sam bata bari sun fito kowa ya gani ba, sake tallafo Zaleehan tayi, cikin sanyi, da lalllami tace.
"Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, ki kwantar da hankalinki kinji, yanzu kiyi haƙuri kisha ko kaɗanne, kinga shima zai taimaka sosai wajen ɗan baki ƙarfin jiki, gashi kuma naji jikin naki ma ya ɗauki zafi jau kamar wuta, buɗe baki kisha ko kurɓi biyune, yafi ace bakici komai ba." Ummi ta ƙare maganar cikin kulawa.
Haƙiƙa Ummi nada matuƙar daraja da ƙima a idanunta, saboda haka batajin akowani yanayi take ciki zata iya yi mata musu, ganin ta buɗe baki ne, yasa Ummi da kanta ta shiga bata tea ɗin abaki, kurɓan farko da tayi haka taji tea ɗin kaman an surkashi da maɗaci, sam babu wani ɗanɗano acikinsa, wanda kuma ta tabbatar cewa rashin ɗanɗanon daga bakinta ne, bawai daga tea ɗin ba, kurɓa uku kawai tayiwa shayin ta kauda kanta gefe, cikin sanyin murya hawaye na zuba tace.
"Ummi na ƙoshi".
Gyada mata kai Ummi tayi, ita kuma zamewa tayi ta kwanta luf akan gadon Ummi, cikin sanyi take faɗin kalman "Innalillahi wa'inna Ilaihirraju'un." tana faɗi kana tana sakin sheshsheƙan kuka, Ummi kuwa ahankali take shafa lallausar sumar kanta, wanda gaba ɗaya ya baje akan pillow'n da ta ɗaura kanta akai, ko mintuna goma ba'a rufa ba kuwa bacci ya ɗauketa, wanda dagani kasan na dole ne, don ko acikin bacci'n sheshsheƙan kuka kawai take saki.

Jigum haka Ummi da Adda Rahama suka zauna, tare da sakata gaba, sosai sukejin tausayinta, lokaci ɗaya gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta, idanunta sun kumbura kamar wanda ta shekara guda tana kuka, wani abun mamakin da suka gani kuwa, shine har yanzu bacci take, amma kuma hawaye ne kebin gefen fuskarta, kamar ruwa, sai faman sakin sheshsheƙa take, ita dai Ummi al'amarin Zaleeha na matuƙar bata tausayi, sannan kuma zuciyarta me raunice.
Chapter 69 · 0% Book details