← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 71

Sashe 9

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta furta "Idan ka dake ni za ka yi dana sani, da na sani na har abada." "Are u threatening me." Girgiza kai ta yi "Aa ina faÉ—a maka abun da zai faru ne."

Sai ta matso kusa da shi dab da shi ta ce "Yanzu baka jin daɗi koh? Ba ka jin daɗin duka da kake yi? Na ga da u find pleasure in doing it." Sai kuma ta saki murmushi ta kai bakinta saitin kunnesa murya ƙasa ƙasa ta ce "Hakan ya na nufin ka fara loosing control, Sannan maza kamar ku sun tsani hakan."

Cikin confusion yake kallonta gabaɗaya ta hargitsa masa ƙwaƙwalwa, dukawa ta yi ta shiga kwashe abincin da ya zube Allah ya so plate ɗin bai fashe ba "Ba ri in ɗebo maka wani abincin, ka san fushi ya na saka mutane su fita hayyacin su, yunwa kuma tafi saka haka." Daga haka ta juya ta koma kitchen wani abinci ta ɗebo mishi ta ajiye kan table tare da ruwa da drink kamar yanda ta saba, sannan ta dauko kayan shara ta shiga share wajen da ta ɓata ya na tsaye ya na kallonta ya kasa komai.

Bayan kwana biyu, a hankali ta shigo ɗakinshi ya na zaune kan sofa ya na danna waya "Me kika zo yi nan." Ya ce ya na ajiye wayarsa, Zama ta yi kan side drawer ɗinsa riƙe da wasu paper a hannunta "Magana na zo muyi." "Ta me?" Ya tambaya "Ta duk abun da ke faruwa."

Ya daɗe ya na kallonta sannan ya ce "Ina jin ki." Miƙewa ta yi ta karaso in da yake ta ajiye papers ɗin a gabansa, paper farko da aka rubuta divorce agreement wanda ya fito ɓaro ɓaro daga shi kuma ba'a rubuta komai ba sai paper ta biyu ita ma wata agreement ce, daria ya kwashe da ita bayan ya gama karantawa ya mike ya na kallonta "Ina ganin kin haukace, ka da ki manta ban fanshi kuɗin sadaki na ba."

Murmushi ta yi "Wannan ba matsala ta ba ce." Hannun ya É—aga zai daketa ta É—ora hannu kan lips É—inta ta ce "Shhhhhh." Dakatawa ya yi, a hankali ta ce "Baka ji ba?" Cikin rashin fahimta ya ce "Me ne?" A hankali ta soma tafiya zuwa wata flower da aka yi kwalliya da ita cikin É—akin ta É—auko camerar dake lake da flower É—in wanda bama za ka gane camera bace ta dawo ta ajiye gabanshi.

Ɗauka ya yi ya na dubawa "Camera." Ya ce cike da mamaki, jinjina kai ta yi ta zauna kan sofa ɗin da yake tashi ta ce "Ka ga ni gidan nan cike yake da irin cameras ɗin nan tun ranar da na sako ƙafata a ciki, kuma ni da kai na na saka su."

Sai kuma ta mike ta shiga yawo cikin dakin shi kuwa sai kallonta yake yi "Ka ga ni duk abun da ya faru a gidan da duka na da kake yi da komai ma har Æ´an mata da samarin da kake kawowa duk ta É—auka, me zai faru idan waÆ´an nan videos É—in suka fita? ko kuma in ce me zai faru da siyasar mahaifin ka?"

Sai kuma ta juyo ta kalleshi "Ka duba what'sapp É—in ka na turo maka sample Idan ka na ganin wasa ne, zan tafi in kwanta amma ka sani ba ni kaÉ—ai nake da wannan videos É—in ba a akwai wanda yake da su, kuma ko da wasa wani abu ya same ni na ba da umarni a saki videos É—in, shawara ta rage naka." Daga haka ta fice.

Wani zufa ne ya shiga tsatsafo mishi hankalinshi ya yi wani irin tashi, ya sani da videos ɗin sun fita tashi ta ƙare, daren ranar ko iya runtsawa bai yi ba, dama ance TSORO na ɗaya daga cikin abun da ke hana mutane bacci, toh shi ne abun da ya faru da shi, especially da abun ya haɗe da ta shin hankali.

meemziey's pen
[02/10, 07:37] Amina Khaleel: https://www.arewapen.com/chapter?id=6ab666b35f6cf14541213029

Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

Page________7️⃣

Washegari da safe ta na zaune cikin ɗaki ya yi knocking yes ta amsa hakan ya saka shi buɗe ƙofar ya shigo, kallon shi ta yi duk ya yi zuru zuru kamar bai ma runtsa ba tun jiya, fukarshi da idanunshi sun kumbura, bai kalleta ba fuskar shi na kallon gefe ya ce "Ki kira lawyer ɗin ki, zan kira nawa su zo nan ayi agreement ɗin." "Tau." Ta ce ta na gyaɗa kai, ficewa ya yi, ta bi shi da kallo ta na sakin murmushi.

2:45pm

Zaune suke a palor Bilal, ita, lawyer É—in ta da Taufeeq ya dauko mata sai lawyer din shi, nan aka yi agreement É—in komai, ya rubuta mata saki uku dinta complete, sannan ya yi signing papers É—in da ta bashi ita ma ta yi signing na shi da aka shirya akan ta yi alkawarin ba zata yi saki waÆ´an nan videos É—in ba, sannan kuma babu ita babu shi ko a hanya suka haÉ—u ka da su nuna sun san juna.

Da haka aka kare komai suma lawyers É—in suka yi signing bayan sun yi signing sun wuce, ta mike ta shiga dakinta ta sako hijab, bata dauki komai ba sai handbag ta fito, sai da ta tsaya ta kalleshi sannan ta ce "Ala khairan." Ta na sakin murmushi daga haka ta fice.

Yau wata É—aya da sati É—aya da aurensu,
Kamar yanda ta ce ne zama agidan Bilal will be educational, ko ba komai she study him and yanzu she understands his brain, ta gane abun da ya sa yake jin pleasure a lokacin da yake duka koh abusing mutun, it's becoz he feels powerful, saboda ya na ganin ya na da iko, ya na so mutane su yi ta jin tsoron shi, kuma shi ne abu na farko da ta fara ruguwa FEAR wato TSORO, da farko ta nuna ta na jin tsoron shi daga baya kuma ta daina.

Abun da ya rikitar da shi kenan, yanda duk lokacin da ya daketa, bata bashi hakuri, bata kuka, sannan bata nuna tsoro, hasalima koh emotion bata nunawa, sai ya fara tunanin me ya sa take haka, me ya sa take daban cikin waƴan da ya yi ma haka, na biyu kuma lokacin da yake buƙatar ta yi shuru lokacin take magana cikin ruwan sanyi babu hayaniya babu tashin hankali.

Sannan lokacin da yake buƙatar ta yi magana sai dai ta yi shuru ta zuba masa idanunta masu kaifi, kamar yanda ta ce ne she will be an understanding and submissive wife, ta hanyar da bai taɓa zata ba, haka kuwa aka yi, lallai she is submissive in a different way da ta ruguza rayuwar shi, babu duka babu zagi sai salient punishment.

A duk lokacin da ta nuna komai ba komai ba ne in ya daketa, rikitacciyar ƙwaƙwalwar sake rikice wa take yi, saboda dama ya na shaye shaye so abun definitely ya rikitar da shi, so da wannan ne ta yi amfani ta yi reversing tsoron zuwa gare shi sai ya zamana ya na shakkarta ya na tsoronta, ba zai iya dukanta ba saboda duk lokacin da ya ɗaga hannun da niyar dukanta zata kafe shi ne da idanunta, so hakan na saka shi shakkar dukanta, sai ta zama ita ce in control yanzu ya yin da ya yi loosing power.

Ta yi amfani da psychological destruction ta yi destroying ɗinsa, sannan kuma ta yi manipulating tunaninshi, wanda ko a yanzu bayan sun rabu abun zai tsaya daram a ƙwaƙwalwar sa, wato shakkarta, kuma koh ganinta ya yi a hanya sai ya tuna da abun, he ruined her, she studied him, he abused her, she survived him, that's the logic.

A bakin ƙofar gidan su taxi ta ajiyeta, buɗe kofar gidan ta yi ta shiga da sallama, babu kowa tsakiyar gidan hakan ya sa ta nufi ciki, palor ta shiga karema kallo wanda aka gyara shi aka saka masa wasu sabbin furnitures, yanzu kam ya yi makari don kuwa da duk yanda aka gyara shi haka zaka ganshi kamar bola.

Ta na tsakar palorn inna ta fito daga ɗakin ta kawu na biye da ita, turus suka tsaya su na kallonta kawu ya ce "Ameenatu ya dai me kika zo yi a gidan nan?" Ya bai taɓa manta maganar da ta faɗa masa kafin a wuce da ita gidan Bilal ɗin "Ba zan taɓa dawowa gidan nan ba sai ranar da aure na da Bilal ya ƙare." Kuma tabbas idan ta fadi maganar dole sai ta yi hakan, sai dai bai taɓa tunanin abun nan kusa ba.

Bata yi magana ba sai buɗe jakarta sa ta yi ta dauko masa takardar sakinta ta miƙa masa, ya na amsa ta wuce shi zuwa ɗakin su na da.

Ta na shiga Kawu ya shigo "Ke me nake gani haka? Sakin ki ya yi ? Me kika yi masa da ya sake ki?" Shuru ta yi ta kyaleshi "Au ba za ki yi magana ba dake nake fah, me kika yi masa haka ya dalla miki zunzurutun saki har guda uku." Nan dai ya yi ta bambami in da yake shiga ba ta nan yake fita ba hadda cewa sai ta bar masa gidan sa, mene ne menene.

Ita dai ta na jin shi koh kallon shi bata yi ba har ya kare ya fice, ita mamaki ma kawu yake bata wai me ta yi ma Bilal ba ma me Bilal É—in ya yi mata don ya san halin Bilal É—in.

Bayan wata biyu.

Babu idda saman kanta don babu abun da ya shiga tsakaninta da Bilal ɗin so she is free, haka ta cigaba da zuwa makaranta har suka yi jarabawa Zango ƙarshe wanda zata kai su wani aji, sun koma normal yanda suke da Taufeeq, lafiya qlu abotar su ke tafiya.

9:30pm
Chapter 9 · 0% Book details