← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 71

Sashe 51

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma Mami ta kasa ta tsare ta hana taj ɗin zuwa kusa da naila, da naila din ta farka part ɗin ta ta mayar da ita,  sosai Mami ke jin haushin Taj ɗin, saboda ɓarnar da ya yi seriously ba karamin ciwo Naila ta ji ba, abu sai kace ba matar shi ba sannan wai aure kusan shekara babu abun da ya shiga tsakanin shi da matar shi, how comes me ya saka suka yi hakan, toh dama zaman me suke yi a gidan, oh dama they are just putting on a show, ai jira take yi ita ma Naila ɗin ta ji sauƙi ta turke su su dukan su.

Naila
Ita har kunya take ji yanda Mami ke kula da ita, yanzu Mami ta san komai duk abun da ya faru tsakaninta da Taj yah Allah wani irin kunya take ji sosai, ga shi Mami ɗin bata wani bata face ba, sai dai duk wani kulawa ta na samu, and ta na lure da yanda taj da Mami ɗin suke faɗa, Mom da Haulat har sun gaji sun dai na tambayar me yasa Mami ta ɗauko Naila daga part ɗinta,  sosai Naila ke samu kulawa ta ji sauƙi sosai sai dai, bata warke a wajen nan ba har yanzu ta na nan ta na jin boni, ita ma ɗin sosai take fushi da Taj ɗin na abun da ya yi mata, jira kawai take yi ta warke su yi settling score duk da dai ya riga da ya ƙwareta.

**********
Nanee
Tsaye take cikin closet dinsa ta na gyara masa kayan shi, sun shirya amma ba kamar da ba, don har yanzu ta na jin haushin shi, amma ya ya zata yi tun da mijinta ne, kuma ta san naila ɗin ba zai sameta ba tun da Taj ba sakinta zai yi ba, so duk maitar sadeek ɗin dai dole ya yi haƙuri, tun da mace dai ba ta auren maza biyu balle ace sadeek din will be the second husband,  ba kamar namiji bane da zai iya auren mace har huɗu.

A hankali ta buɗe glass sliding door na wardrobe ɗin ta na jera kaya mistakenly hannun ta ya taɓa wani abu dake wajen kawai kayan suka janye wata ƙofa ta buɗe, dakatawa ta yi tsoro na kamata, coz bata yi tsammanin ƙofa a wajen ba, daurewa ta yi ta shuga wajen wanda saura kaɗan zuciyarta ta buga ta mutu awajen, wani ɗaki ne mai ɗauke da desktops kusan biyar, and bangon ɗakin cike yake da hotunan Naila Taj da kuma Ayan, sai hotunan matan Taj ɗin sa suka rasu,  no gabaɗaya ɗakin cike yake da hotunan Abad family.

Wanda hoton naila sun fi yawa aciki gasu nan zube wasu bata ma san an yi mata su ba alamar da gaske dai stalking É—inta yake yi.

Rawa jikinta ya ɗauka ta na jin kafafuwanta ba zasu iya ɗaukarta ba hakan ya saka ta sulale a ƙasan wajen, hawaye na taruwa a idonta, wani baƙin ciki da fushi tare da ƙunar zuciya suka taso mata nan da nan, har wani ɗaci ɗaci take ji a bakinta saboda haka, yawunta na ƙafewa a wajen, Sadeek has become more and more and more obsessed with Taj da family ɗinsa gabaɗaya, wani kalan level of obsession ne haka?

"Innalillahi wa'inna illahi raji'un. " Shi ne kawai abun da take yi ta maimaitawa hankalin ta na sake tashi kukan ta na sake tsananta jikinta ya na sake ɗaukar rawa, me sadeek yake so ya mai da rayuwar shi, ya na tunaninta koh? Ya na tunaninta sa ita da Sabrin ko kuwa he is busy stalking and obsessed with other people,  Hasbunallahu wani'imal wakeel, ta daɗe zaune awajen don bata ma san iya adadin da ta ɗauka ba sannan ta miƙe ta ƙarasa kusa da table ɗin ta kwaso hotunan abun da hannunta ke iya ɗauka sannan ta fice ta na jin zuciyarta na yi mata nauyi sosai.

Da haka ta lallaɓa ta koma ɗakinta.

**********
Bayan sati É—aya
Naila ta ji sauƙi sosai ta warke saboda kulawar da take samu wajen Mami, kullum suna tare da Taslim anan part ɗin, and Mami ta riƙe ta anan part ɗinta ta hanata komawa part ɗin Taj, jira kawai take yi Naila ɗin ta ji sauƙi don kuwa a kwai case a gidan, so take yi ta turke daga naila ɗin har Taj especially taj ɗon don kuwa shi ne mai laifi.

Taj kam shi kaɗai yake zama a part ɗinsa don har Ayan ɗin shi ma ya gudu ya dawo part din Mami in da Ummin shi take wato Naila, wacce ta daina zuwa aiki ta ɗauki hutu saboda lafiyar da bata da, ita ma wani irin kunyar Mami take yi sai allah allah take yi ka da mami ta yi mata magana coz bata san ta in da zata fara ba, shi ma taj ɗin ya san ƙyalesa kawai Mami ta yi for now, but ya san dole sai ta yi masa magana.

Su mom da haulat sun yi gulmar me naila ke yi a part É—in Mami har sun gaji saboda ba su gane komai ba, hadda tambayar taslim ita ma ta ce bata san me Naila É—in ke yi apart É—in ba.

Around 2pm ta na zaune ta na danna wayar ta, taslim bata nan ta yi tafiya ta tafi auren ƙawarta da za'a yi a lagos, so ita kaɗai ce ayau, ta na dannan waya, sai dai hankalinta baya wajen kwata kwata, gabaɗaya wani iri take ji, hakan ya saka ta kashe wayar tare da ajiyeta gefe, sai yanzu ta tuna Ayan bai dawo daga school ba, ƙarfe ɗaya ya kamata ace ya dawo but ga shi har ƙarfe biyu bai dawo ba, miƙewa ta yi ta na jan hijab ɗinta tafita, daga ita sai wayarta a hannu.

A baban palor ya fito ta na tafiya, bata ma ga alamar Ayan ɗin ha dawo ba, hakan ya saka ta fice gabaɗaya daga palorn zuwa waje, ta na fita securities dake wajen suka taso, sai gai da ta suke yi, amswa ta yi ta na tambayar su ina driver ɗin Ayan yake, da sauri suka ta fi suka kira mata shi,  da yake shi ma security ne, bayan ta amsa gaisuwar shi tambaya ta farko da ta yi masa shi ne "Ina Ayan?" Shuru ya yi ya na ɗan kame kame kafin ya ce "Na je in ɗauko shi, ban ganshi ba wai an zo ɗaukar shi."

Wani kalan faɗuwa gabanta ya yi ta ɗago ta na kallonshi bata san lokacin da ta ce "Saboda kai daƙiƙi ne da ka dawo baka iya sanar da kowa ba, are u mad?" Ta karashe a hasale coz yanda take ji a jikinta kamar something is not right, wani rawa jikinshi ya ɗauka, ita gabaɗaya ranta ya soma ɓaci, ta ce "Wa aka ce ya zo ɗaukar shi a school?" Girgiza kai driver ɗin ya yi "Ma wallahi ban....." "To hell with baka sani ba, don't f*cking tell me baka sani ba." Ta faɗa a kausashe, sannan ta ɗaga wayarta ta shiga neman number Taj, ta yi dialing.

Ringing biyu cikin na uku ya ɗauka, "Assalam Alaikum." Ta faɗa daga can cikin calm voice ɗinsa, "Wa Alaikum salam." Ta amsa, shuru ya yi saboda yanda ya ji muryar ta, bai ida tunani ba ya ji ta ce "Ka ɗauko Ayan daga school ne?" "Na'am?" Ta faɗa ta sigar tambaya kamar bai ji abun da ta ce ba, "Ayan na wajen ka ne?" Girgiza kai ya yi kamar ta na ganinshi "A'a baya waje na, driver bai ɗauko shi bane?" Numfashi ta sauke "No bai ɗauko shi, wai ya tafi school ɗin aka ce masa an zo ɗaukar sa." 

Shuru ya yi ya na jin hankalinsa na son tashi, but ya danne ya ce "Ina Taufeeq? Mike fah? baya wajen su?" Girgiza kai ta yi "Ban sani ba, ban tambaye su ba, ka kira Taufeeq i will talk to mike ya na gida." "Ok do so, will get back to u in five minutes. " ya faɗa sannan suka katse wayar,  hararan driver ɗin ta yi sannan ta ce "Ka tafi but ka jira kirana." Daga haka ta juya ta shige ciki, part ɗin mike ta nufa direct sai addu'a take yi Allah ya sa ba abun da take tunani bane.

Har ga allah tsoro take ji, ta san komai ya zo ƙarshe,  but ba duka ba har yanzu akwai sirrukan da ba'a tono ba, there is more and more abubuwa da ba'a sami ba, no bata son abun nan ya fara ka Ayan coz bata jin zata iya ɗauka, iya tsakani da allah take son Ayan ko ba don ta na auren mahaifin sa ba, ya na bata tausayi coz tun ya na karami ya fara experiencing pain, no she cant even think about wani abu ya samu Ayan.

Har ta isa kofar dakin mike bata sani ba, wanda dai dai fitowar mike daga ɗakinsa "Hey  cousin In_law me ya kawo ki nan or did u miss me?" Ya faɗa ya na sakin murmushi, ɗan juya idanunta ta yi "Plss enough with the joke where is Ayan?" Zaro ido ya yi "What did u mean by where is Ayan? Nah he is not here." "Have u seen him ance an je ɗaukar sa daga school and it wasn't the driver or Taj so i thought its u." Gyara tsayuwar shi ya yi ya na zama serious coz he knows how the family is.
Chapter 51 · 0% Book details