← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 71

Sashe 26

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ameenatu. " Naila ta bata amsa jinjina kai Ammi ta yi "Masha Allah." Sai kuma ta saki murmushi "Ɗago ki kalleni ki daina jin kunya ta, ai yanzu an zama ɗaya." Sai da ta ɗan ja lokaci sannan ya ɗago sai dai ba ta kalli face ɗin Ammi ɗin ba "So faɗamin ya kike? ya zama gidan da kuma baƙunta?" "Lafiya qlu ai yanzu na saba." Wani murmushi Ammi ta yi "Ai ba'a sabawa da gidan nan, duk mace da ta zo haka take faɗa sai dai ba zaka taɓa sabawa ba." Ɗagowa Naila ta yi ta na kallonta cikin rashin fahimta.

"Na san baki gane abun da nake faÉ—a ba, amma shin baki ji abun da yake faruwa da duka matan da Taj din ya aura bane." Wani murmushi Naila ta yi cikin zuciyar tare da faÉ—ar an zo wajen sai kuma ta É—ago kamar mai jin tsoro ta ce "Wallahi na ji kowa ya na ta faÉ—amun, alokacin ina cikin giyar son shi ne, wallahi Ammi ina tsananin son Taj wanda har ban san yanda zan yi ba, alokacin son shi ne ya rinjayi tsoron da nake ji."

Murmushin jin daÉ—i Ammi ta yi sai kuma a hankali ta ce "Ameenatu. " "Na'am Ammi." "Zo nan." Ta ce ta na nuna mata kusa da ita babu musu Naila ta tashi ta koma kusa da Ammi É—in "Ameenatu magana zamu yi woman to woman ki na ji na." GyaÉ—a kai Naila ta yi.

"Kin san aure acikin wannan family ɗin is not easy, gabaɗaya family ɗin nan abirkice yake ke ma kin gani, sannan Taj wani irin murɗaɗɗen mutun ne baka gane masa, sannan aikin da yake yi ya saka yake da tarin maƙiya kai bama shi ba duka family ɗin."

Ɗagowa Naila ta yi a tsorace ta ce "Innalillahi Ammi ya zan yi?" Kama hannunta Ammi ta yi ta riƙe sannan ta ɗago ta kalli Naila ɗin "Na san Tajudden tun ya na ƙaraminsa ya na da taurin kai da kafiya, ya na da wuyar sha'ani, Tajuddeen ya na buƙatar mace wacce zata zauna da shi wacce zata yi understanding ɗinsa, wacce zata yi softening ɗinsa." A hankali Naila ta ce "Ammi ki faɗamun, ina so in taimaki Tajudden, ina so na basa kariya, Ammi ina mugun son Taj ba zan iya jure ganin wani abu ya same shi ba, ina ma iya ba da rayuwa ta akanshi."

Murmushi Ammi ta yi na cin nasara ta ce "Ka da ki damu in dai ki na tare da ni babu abun da zai same ki, ki bani nunberki zamu yi magana anjima." Exchanging number suka yi kafin Naila É—in ta raki Ammi har babba palor in da Abba ke jira sannan ta dawo part É—insu, direct É—akinta ta shige ta na É—a sakin murmushi wanda ita kaÉ—ai ta san ma'anar shi.

10:32pm

Zaune take kan sofa sanye cikin kayan baccin ta as usual ta rufe rabin jikinta da duvet ta na aiki da Tab shi kuma ya na zaune kan gado ya na aiki da laptop ɗinsa shuru ɗakin ya ɗauka baka jin ƙarar komai sai ta AC ɗago kai ya yi ya kalleta ya ce "Maganar me kuka yi ɗazu da wannan matar?" Shuru na wasu mintuna sannan a hankali ta ce "Warning ta bani." Jinjina kai ya yi "Haka take ai."

Dakatawa ta yi sannan ta É—ago ta kalleshi "Suna tunanin ina son ka sosai." Kallonta ya yi da kyau "Me kika faÉ—a mata?" Cikin idanu take kallonshi "Gaskiyar da suka so su ji." Sai kuma a hankali ta ce "Cewa na yi ina iya mutuwa a kanka." Numfashi mai zafi ya fesar "Ka da ki sake cewa haka." ÆŠauke idanunta ta yi "Me yasa, koh waÆ´an nan kalaman basu isa ba?" Zuba mata ido ya yi "Baki da tsoro." ÆŠage kafaÉ—a ta yi "Ina da, sai dai ba su ba." Shuru ya ratsa É—akin kafin ta sake cewa "Ba su san ni bane Taj. "

Daga haka ta mai da hankalinta kan table É—in babu wanda ya sake magana acikin su.

Washegari

Ba tare suka fita ba kowa da motar da sai dai wannan karon driver ne zai ringa kai ta ya na ɗaukota wanda ainihi security ne, ta na dawo wa gida ta tarar da wani abu, wai an ware mata mai aiki wacce zata kama tayata aiki apart din ta tun da ita ta na zuwa aiki, ita dai bata ce ƙala ba sai godiya da ta yi ta na nuna komai ba komai ba, toh me zata ce tun da dai an riga da an yanke hukunci.

Haka rayuwa ta cigaba da kasancewa wasa wasa Naila ta yi 1 month a gidan Tajudden, zata iya cewa yanzu ta san komai na gidan da ma halayen ƴan gidan, don cikin hikima take karantarsu, don ita dama ta ƙware sosai wajen karantar mutane, so ta kwantar da kai sosai ta na karantar su, gefen relationship ɗinta da Taj kuwa it's professional kamar yanda contract ɗinsu yake no intimacy da sauran su, so kowa na tsayawa iyakar sa, babu mai tsallake iyakarsa, idan sun fita cikin mutane zaka ga suna behaving kamar wasu masoyan ƙwarai da baza su iya rayuwa ba tare da juna ba.

Gefen mu'amalar ta da Ammi kuwa komai ya na tafiya smoothly don kuwa Ammi É—in ta yarda da ita sosai, and ita Naila É—in abun da take so kenan, shiyasa ta kwantar da kanta take behaving kamar wacce bata san komai ba sai abun da aka É—ora ta akai.

☆******☆

Zaune take a babban palor saman carpet ita da Ayan suna solving puzzle sai Mami dake zaune kan kujera ta na taɓa wayarta, Sadeek ne ya shigo palorn bakinshi ɗauke da sallama, amsawa suka yi, ya ƙaraso cikin palorn ya na gaida Mami cikin mutuntawa, amsawa ta yi ta na tambayar sa ya iyali, amsawa ya yi da Alhamdulillah ya na ɗan satar kallon Naila dake zaune saman carpet.

A hankali ta ɗago ba tare da ta kalleshi directly ba ta gaida shi amsawa ya yi ya na sake kallonta ya na mamakin me ya kawota gidan kuma, da sauri Ayan ya miƙe ya ƙaraso in da yake cikin ƴar murnar shi, ya gaida shi ya na tambayarsa ina ya baro masa ƙawarsa Sabrin Sadeek ɗin zai yi magana kenan Taj ya shigo cikin palorn, ɗaga kai Naila ta yi ta na sauke idonta kanshi fuskarta ɗauke da murmushi kafin ta miƙe a hankali, ba tare da tunanin komai ba ta ƙarasa in da yake.

Da kallo Sadeek ya bita ya na tunanin ita kuma ina zata tafi haka sai dai ganin ta tsaya gaban Taj ta na sakar masa wani heart melting smile ne ya saka kanshi kawo haske, matar Taj kenan, É—auke idanunsa ya yi daga kallon su ganin Taj É—in ya kama hannunta ya yi masa kiss, shi ma É—in ya na sakin wani irin murmushi da Sadeek É—in ya manta last time da ya ga Taj É—in ya yi murmushi irin haka nan.

Ita kam Mami bata damu ba don koh kallon su bata yi ba don in da sabo ya ci ace ta saba da halin Taj É—in da Naila, don su É—in basa jin kunyar nuna son da suke yi ma juna a gaban ko waye haka suke especially Taj É—in don ita Naila É—in ma sometimes ta na jin kunya shi dai Taj É—in ne sai ahankali.

Ƙarasowa suka yi cikin palorn idanun Taj ɗin akan Sadeek "Man kai ne a gidan mu yau." "Eh wallahi ni ne ya kake ya aiki?" "Alhamdulillah Lafiya qlu ya iyali." "Suna lafiya." Sadeek ɗin ya amsa "Man ga matata na san baku taɓa haɗuwa ba." Sai kuma ya kalli Naila cikin wani kulawa murya a tausashe ya ce "Wife ga abokina kuma stepbrother ɗina Abubakar Sadeek." Jinjina kai Naila ta yi "Eyya Allah sarki ai mun gaisa ɗazu." "Koh?" Taj ɗin ya ce ya na kallon face ɗinta "Eh." Ta ce ta na kallonshi ita ma sweetly in ka gansu zaka ratse son juna suke yi tsakani da Allah.

Sadeek da duk ya bi ya takura a wajen ya yi gyaran murya ya na miƙewa tsaye kallonshi Taj ya yi "Ina zaka je na ga ka miƙe tsaye?" "Zan wuce ne." "Ba Yanzu ka zo ba?" Jinjina kai ya yi "Eh dama na zo ne in gaida Mami sannan in gan ka, since mun daɗe bamu haɗu ba, tun da naga Alhamdulillah Lafiya qlu kake sai in tafi." "Haka ne kuma, toh idan ka je gida in gaida Nanee." "Zata ji." Sadeek ɗin ya ce sannan ya yi sallama da Mami ya fice.

Part ɗinsu suka nufa tare suka shiga har ɗakinsa na ɗan wani lokaci sannan ta fito ta na murmushi ta shiga nata ɗakin, ta na shiga ta maida fuskarta yanda take, ita ta gaji da rayuwa a gidan ace duk abun da mutun ya yi ana kallonsa, koh yanzu don akwai camera a palor ne ya saka ta raki Taj ɗin har ɗaki, cire hijab ɗin jikinta ta yi ta na zama bakin gado wayar ta ce ta ɗauki ƙara, kallon sunan dake yawo akan wayar ta yi, "Ammi." Shi ne abun da aka rubuta ɗan gyara yanayinta ta yi sannan ta yi picking call ɗin.

"Assalamualaikum. " Daga can Ammi ta amsa "Wa Alaikum Salam, Ameenatu ya kike?" Cikin wani irin kwantar da murya da respect ta ce "Alhamdulillah Ammi ya kwana biyu? Ya hidima?" Casually Ammi ta ce "Fine fine komai lafiya qlu." Sannan ta sake cewa "Toh ya Taj yake? Me ake ciki yanzu." ÆŠan numfashi Naila ta sauke "Ammi kin san Taj duk da yanda muke nuna ma juna soyayya, har yanzu ba komai na sa ma sani ba, he is distant kan wasu abubuwan sa."

Ammi ta ce "Kamar ya distant?" "Har yanzu latti yake dawowa, bai ma cika magana irin sosai ɗin nan ba, sannan sometimes sai ya zauna ya yi shuru ban ma sani me yake tunani ba." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke saboda ta sani duk abun da Naila ɗin ta faɗa haka yake, haka Taj ɗin yake "Ƙwarai kuwa na sani haka Taj yake, he never open up shiyasa auren da yake yi fails."
Chapter 26 · 0% Book details