← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 71

Sashe 64

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kallon gate É—in saif ya yi, sannan ya kalli Taj "Me kake yi a Haddad Estate?" Waiwaya wa ya yi ya kalli motar sa "I came to see someone." Jinjina kai saif ya yi "Waye?" Murmushi Taj ya yi "Actually am looking for Mr El Bashir Haddad. "

Ɗan zaro ido Saif ya yi "Ka ce Abba kake nema, yanzu mu ƙarasa ciki, i will call and check idan ya na gida." Jinjina kai taj ya yi ya juya ya koma cikin motar shi, shi kuwa saif ya yi ma securities magana sannan ya koma motar shi ya ta da suka shiga Haddad estate ɗin, tun cikin mota saif din yake kiran uncle El Bashir but line busy, so kai tsaye gidan su ya nufa da taj ɗin saboda ka da ya kai ma uncle El Bashir bako har gida azo uncle ɗin bai nan gara ya kai su wajen ummi su gaisa kafin El Bashir ya ɗauki wayar.

Gafen naila kuwa faɗuwar gabanta tsananta ya yi ta na tunanin me zata je ta iske a cikin gidan haddad,  yaya Haddad's ɗin zasu amshe ta, da haka suke ratsa babban titin haddad estate ɗin don kuwa kusan round about biyu ne aciki sannan wajen ya na da girma da kuma faɗi da kyau fiyeda tsammani.

Sannan daga ganin tsarin gine ginen dake cikin estate ɗin zaka san an zuba dukiya wajen ƙera gidan da haka har suka ƙarasa bakin gate ɗin wani gida, cikin jerin gidaje kusan shida dake cikin estate ɗin gidan babba ne sosai tun daga waje, wangale musu gate aka yi saif ya shiga sannan su ma suka shiga.

Saif ɗin ne ya fara fitowa daga tasa motar, taj kuwa sai da ya ɗan kwantar ma da Naila hankali sannan ya fito, ƙarasowa saif ya yi wajen shi ya na cewa ya kira uncle El Bashir ɗin bai dauka ba, wanda El Bashir ɗin yaya ne ga mahaifin saif ɗin, shi ya sa yake ce masa uncle, Naila ce ta karaso in da suke wanda Saif na ɗago kansa suka haɗa ido wani irin dasƙarewa ya yi a wajen ya na nuna ta da hannu ya ma kasa magana sai kallonta yake yi.

Duk kallon reaction É—inshi daga taj har naila ke yi, wanda su na haka wani mutum dattijo haka ya buÉ—o kofar gate É—in gidan ya shigo, ya na sanye da kaya na alfarma sai dai duk a rikice yake, shi ma ya na ganin naila É—in ya dakata cak ya na kallonta cikin rikicewar da ta fi ta É—azu, jikinshi na rawa, da mamaki daga naila har taj suke kallon su saboda wannan reaction haka kamar an ga dodo, saboda shi mutumin kallon tsoro mamaki da al'ajabi yake yi mata.

Wanda basu gama tantance meke faruwaba aka sake buɗo ƙofar gate wata budurwa ta shigo ita ma a rikice, face dinta ya yi ja sosai, in ka ganta ta na da kyau sosai, da kuma blue eyes, ta na ƙarasowa in da suke bata kalli kowa ba sai gaban wannan mutumin ta tsaya ta na watsa masa papers ɗin hannunta ta shiga magana cikin yare ƴan ƙasar da su taj basu wani fahimta ba, sai dai da yake ta na haɗawa da turanci abun da suka yi grabbing kawai shi ne lokacin da take faɗar "Tell me it's a lie."

A tsawace take yi masa maganar wanda mutumin in dai a haife ne ya haifeta, haka take yi ta magana a tsawace da ƙarfi har mutanen da suke cikin gida suka fito, wata mata da alama mahaifiyar Saif ce sai kuma wani saurayi wanda da alama ɗan uwansa ne, abun nata kamar bama cikin hankalinta take ba don kama rigarsa ta yi ta na jijjiga shi wanda hakan ya ɓatawa ɗan uwan saif ɗin rai wanda ake kira kareem ya ƙaraso in da take bai yi wata wata ba ya karaso in da suke ya fisge hannunta daga rigar sa ya na wanke mata fuska da mari.

Hakan ya saka ta yi baya ta na faɗuwa ƙasa ɗagowa ta yi a zafafe zata miƙe idanunta suka haɗa ido da naila, cak ta tsaya ta zuba ma naila ido suka shiga kallon kallo, ita ma mamaki ne akan fuskarta sosai, dafe ƙirjinta naila ta yi ta na jin wani irin kuka na son ta so mata da alama attack zata samu.

Kawai wannan yarinya kamar mahaukaciya ta miƙe ta nufi wannan mutumin ta na magana kamar ta zare sai dai bata jin abunda take cewa, da sauri saif ya kama wannan yarinyar ya na riƙe ta, ita kuma sai fisge fisge take yi na a bari ta tafi in da wannan mutumin yake.

Meemziey's pen
[04/10, 21:48] Amina Khaleel: Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

Page_________ 3️⃣4️⃣

Da sauri Taj ya riƙe Naila wacce ta soma kuka sosai ta na sake dafe  saitin zuciyarta, sai kallon yanda saif yake kokawar riƙe wannan budurwar suke yi.

Kareem wato ɗan uwan saif  ya ɗuka ya ɗauki paper ɗin da wannan budurwar wacce ake ce ma malak ta watsar ya na karantawa, takardar DNA ce, babu abun da ya gane sai 99.999 matched, which ana nufin duk waƴan da aka yi ma DNA din suna da alaƙa,  koh ɗa da uba koh ƴa da uba, so bai gane ba don ba'a rubuta sunayen waƴan da aka yi ma gwajin na.

Hakan ya saka shi cewa "Wai ke wace paper ce wannan." Cak ta dakata da fisge fisgen da take ta kasa kuka dama bata kuka bata iya yin kuka, ta juya ta kalli saif gabaÉ—aya a ruÉ—e take ta ce "Ai ba mu da haÉ—i da shi koh? Shi ba babana bane, shi ba mahafin na bane? Bamu haÉ—a komai da shi ba." Shi ma saif É—in duk arikice yake akan yanda take behaving ya ce "Waye shi? Waye shi mahaifin ki?" "El Bashir Haddad El Bashir Haddad El Bashir Haddad. " ta maimaita har sau uku.

Tsitt wajen ya ɗauka kowa na kallonta hadda shi wannan mutumin, naila ma kallonta ta yi jin takira sunan wanda aka ce shi ne mahaifin ta wato El Bashir Haddad,  wani irin rumtse ido wannan mutumin ya yi, ya na jin wani yanayi tattare da shi.

A hankali naila ta fita daga cikin jikin Taj ta ƙaraso in da Malak take bakinta na rawa ta ce "Me me kike cewa, waye mahaifin ki?" Da yake ta ji wasu abubuwan da suke faɗa saboda su na haɗawa da turanci, ɗagowa Malak ta yi ta kalleta fuskar Naila ɗin bata yi kama da surgery aka yi mata ba, wannan natural face ce, sai yanzu ta gane ta riga da ta ɗago komai "Ahankali ta ce "El Bashir Haddad. " Nuna wannan mutumin naila ta yi ta ce "Wancan wancan shi ne El Bashir Haddad?"

Duk da halin da Malak  ke ciki sai da ta yi murmushi "Eh shi ne, baban ki ne kema koh?" Jinjina kai naila ta yi hawaye na taruwa A idonta "Eh babana ne, shi ne aka ce babana, shi nazo nema anan gidan." Duk mutanen dake wajen kallon naila, kowa na sonya haɗa kan zaren amma ya kasa banda Taj da shi ya san El Bashir baban matar shi ne.

Wajen shuru ya yi kamar an yi mutuwa, kawai suka ji Malak ta fashe da daria, daria fah, daria sosai ta na fitowa daga jikin saif, ta ja baya ta na nuna naila ta ce "El Bashir baban ki ne, nima baba na ne, sai dai abun da ban sani ba shi ne tare muka fito, koh kuma kowa uwarsa daban, don fuskokin mu iri ɗaya ne, wait  ka da in ruɗar da ku, na taɓa yin surgery na canza fuska." Sai ta sake nuna Naila "Amma kafin in yi surgery i have the same face as u komai iri ɗa....."

Da sauri malak ta dafe ƙirjinta sakamakon wani sharp ciwo da ta ji ya ratsa ƙirjinta,  bata taɓa jin irin shi ba kuma ta san halin da take ciki ne ya jawo mata haka, dafe ƙirjinta ya yi dai dai da ita ma Naila ta dafe nata ƙirjin kawai sai ta fashe da kuka saboda ita ma irin ciwon ta ji a ƙirjinta,  mutane sai kallon ikon allah suke yi, da sauri taj ya karaso in da naila take ya na rungumeta, baya baya malak ta shiga yi kamar ƙyeptawar idanu, idanunta suka gano mata wani sniper can saman wani gini ya saita bingidarsa in da suke a hankali ta kalli direction ɗin da yake nunawa, bata ma sani ba, bata ma san ya aka yi ba sai ganin kanta ta yi gaban Naila ta na tare naila ɗin kawai lokaci ɗaya bullet ɗin ya sameta a ciki.

Wani kalan kuwa Naila ta saki saboda jinin da ya watso mata a jiki da sauri ta tare Malak din kafin ta kai kasa suka faÉ—i kasa gabaÉ—ayan su, Naila ta saka hannu ta na dafe in da aka harbi malak É—in ta na É—ago hannun ta ta ga jini kawai ta tafi luuuuuu ta faÉ—i ita ma, da sauri daga taj har Saif suka karasa in da suke.

Saif ya kamo Malak Taj ya kamo naila, "Innalillahi wa'inna illahi raji'un. " kawai Saif dama wanda ke wajen yake faɗa kawai ya shiga kiran sunanta "Malak, malak malak." Ita kuma sai kallon shi take yi hawaye na gangarowa daga idanunta, bakinta ma jini yake fiddawa, da sauri ummi wato mahaifiyar saif ta karaso wajen wanda ita khair ƙanwar saif kenan take ta suma saboda jinin da ta gani, shi kuwa El Bashir wasu hawayen ne masu zafi suka zubo masa saboda a karo na ba adadi ya sake cutar da jininshi.

Tsoro yake ji ya na jin tsoro ya na jin wani irin mugun tsoro a ce a wannan lokacin bata da rai ace bata rayu ba saboda idan haka ta faru bai san a ina zai saka kanshi ba.
Chapter 64 · 0% Book details