Sashe 25
Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ɗan murmushi matar ta yi ta na cewa "Ai da baki wahalar da kanki ba, daga gida muka fito, na ce bari in zo in ga Amaryar Mr Taj da yake ba mu nan ko da aka yi bikin." Jinjina kai Naila ta yi "Eyyah Allah sarki da yake bikin ya zo a ƙurarren lokaci." "Hmmm kuma haka ne." Cewar matar sai kuma ta sake cewa "Sunana Hassana, za ki iya kira na da Nanee, ni matar friend ɗin Taj ne wato Sadeek za'a iya cewa ma ƴan uwa ne." Gyaɗa kai Naila ta yi "Allah sarki Nanee, ni kuma sunana Ameenatu. " Murmushi Nanee ta yi "Ai na san ki don mun taɓa haɗuwa dake a asibiti lokacin da Ayan bai da Lafiya. "
Zaro ido Naila ta yi "Really ni ban ma sani ba kin san yanayin aikin mu a rana ka na haɗuwa da mutane kala kala ba lallai bane ka gane kowa." "Kuma haka ne." Nan dai suka cigaba da fira sama sama ba'a wani daɗe ba Nanee ta ce zata tafi, har parking lot Naila ta rakata sannan ta dawo cikin gida ta na shigowa ta sauke ajiyar zuciya ta na yamutsa fuska, haka take ji kamar an cire mata ƙaya don a takure take lokacin da Nanee ta na nan.
6:22pm
Cup ɗin da ta gama anfani da shi take wankewa bayan ta ƙare ta ajiye cup ɗin a muhallinsa sannan ta fito daga kitchen ɗin dai dai ya na shigowa palorn dawowar shi kenan daga aiki, ɗan dakatawa ta yi ta na ɗan juyawa cike da hikima ta na kare jikinta saboda ba wata rigar kirki ce ajikin nata ba, vest ce sai wani dogon wando mai ɗan faɗi marar nauyi ajikinta, ita bata ma zaci zai dawo yanzu ba tun da ta a kwanakin sai bayan isha yake dawowa "Barka da zuwa." Ta ce ta na kallon gefe, bai amsa ba sai takowa da ya shiga yi zuwa in da take.
Dab da ita ya tsaya ya na kallonta, sannan a hankali ya cire jacket din suit dake jikinsa ya na ɗora mata ajiki riƙe jacket din ta yi ba tare da ta ɗago ba, a hankali ƙasa ƙasa ya ce "Ki daina fitowa haka akwai cameras acikin palorn." Ya ce sannan ya ja baya, Ɗagowa ta yi ta kalleshi, jinjina mata kai ya yi, zata yi magana ya ɗora yatsanshi saman lip ɗinta ya na girgirza mata kai.
Fasa magana ta yi hakan ya saka shi juyawa ya nufi hanyar É—akin shi da kallo ta bishi sannan ta sake bin palorn da kallo, no wonder take jin wani iri duk lokacin da ta zauna palor É—in shi yasa bata fiye zama ba.
Komawa É—akinta ta yi sai tunani take yi, sai kuma ta shiga kallon É—akin nata haka kawai bata ma yarda da É—akin ba, wa ya sani ko a kwai hidden camera anan É—in.
10:30pm
A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama a bakinta, zaune ta gansa saman gado ya na aiki da laptop amsa sallamar ya yi ba tare da ya ɗago ba, ƙarasawa ta yi cikin ɗakin ta na ajiye wayarta da Tab ɗinta sannan ta nufi closet ɗinsa bata daɗe ba ta fito riƙe da duvet da kuma pillow zama ta yi kan kujerar ta na rufe rabin jikinta da duvet ɗin ta ɗauki tab ɗinta ta shiga aiki da ita.
Shuru É—akin ya É—auka can ta ji ya ce "Ba ni na saka camera É—in ba." ÆŠagowa ta yi "Ban tambaya ba ai." Jinjina kai ya yi "Amma na san ki na so ki tambaya É—in." Ajiye Tab É—in ta yi gefe ta na kallonsa da kyau ta ce "Ka san da camera É—in me ya sa baka cire ba?" Shi ma kallonta ya yi "Saboda ina so su ga kamar cewa har yanzu su É—in suke juya ni." "Shi ya sa ka ce mu kama kwana É—aki É—aya." "Eh atleast nan É—in babu camera."
Wani kallo ta yi masa da ya saka ya saki murmushi "Ka da ki damu É—akin ki ma babu camera." Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta ce "Ya aka yi ka sani?" "Kafin ki shigo gidannan sai da na duba da kyau na ga babu camera É—in, kin ga ba zan so wani ya ga sirri na ba." ÆŠauke kanta ta yi "Da ina da ina ke da camera a part É—in nan." "Ko ina ban da É—akin ki da É—aki na." Jinjina kai ta yi kafin ta ce "Ranar Monday zan koma bakin aiki na." "Ok Allah ya kai mu." "Ameen." Ta amsa ta na É—aukar Tab É—inta ta cigaba da abin da take yi shi ma bakin aikin shi ya koma.
☆***********☆
Kamar yanda ta ce ranar Monday ta koma aiki wanda tare suka fita sai da suka ajiyeta a asibiti sannan suka wuce office, ranar ta yi busy sosai saboda ta daÉ—e bata zo asibiti ba so ta na da patients da yawa.
Da marece bayan ta gama aiki tare suka koma gida da Taj wanda ya biyo ya É—auketa.
Fitowa suka yi daga mota suka nufi cikin gida dukan su kallo ɗaya zaka yi musu ka san a gajiye suka, ya na saka ƙafarsa cikin palorn ya ji kansa ya yi masa wani irin nauyi zuciyarsa na rufewa nan take saboda muryar wanda ya ji, a hankali ya sauke idanunsa kan mahaifinsa da kuma matar sa da suke zaune kan doguwar kujera.
Ƙarasawa ya yi cikin palorn ya ɗauke hanya zai nufi part ɗinsu ba tare da ya ce ƙala ba, duk da Mami da Mom su na palorn amma bai jin zai iya magana.
Shigowa Naila ta yi ta na karantar yanayin wajen wani irin energy ke tashi awajen daga gani ba za'a kwashe lafiya ba, ita kam ƙarasowa ta yi ta gaida su Mami da ma baƙin dake wajen, duk amsawa suka yi, cikin kulawa mahaifin Taj ɗin ya amsa ya na tambayarta ya take, haka ma matar mahaifinsa sai wani kallon Naila ɗin take yi.
"Tajudden baka ga mahafin ka bane?" Ya ji muryar Mami cak ya tsaya ya na rumtse idanunsa, bai so Mami ta yi magana ba, don kuwa idan har ta yi magana ba zai iya kauce wa maganar ta ba, a hankali ya juyo ya kalleta idanunsa sun kaɗa sun yi ja "Mami ina yini, Mom ina yini." Sai kuma ya yi shuru ya na tunanin yanda gaiswar da zai yi ma mahaifinsa zata fito daga bakinsa, da ƙyar kamar ana yanka halshensa ya ce "Barka da zuwa Mr Abad, Barka da zuwa Mrs Abad."
Murmushi matar dake kusa da mahaifinsa ta yi "Yawwa Tajuddeen ya kake? Ya Amarci?" Jinjina kai kawai ya yi, Shi dai dattijon sai kallon Taj yake yi ya wani zuba masa ido sai kuma a hankali ya ce "Tajudden ban san ka raina ni ba sai yanzu, aure ka yi ba tare da ka sanar da ni ba." A hankali Matar mahaifinsa wacce suka kira da Ammi ta miƙe ta kalli Naila dake zaune kan carpet ta ce "Daughter na muje muyi magana mana." Ɗagowa Naila ta yi ta kalleta sai kuma ahankali ta kalli Mami jinjina mata kai Mami.
Hakan ya sa ta miƙe a hankali murmushi Ammi ta yi "Muje part ɗinku koh." Gyaɗa kai Naila ɗin ta yi ta na wani ɗuƙar da kanta kamar ta ƙwarai suka nufi part dinsu.
Harara Mom ta sakar ma Mami "Kefa Yaya haka kike watarana me yasa kika ce ta tafi." Miƙewa Mami ta yi ta kalli Abba da Taj sannan ta kalli Mom ta ce "Ki ƙyalesu kawai, idan mutun yana da halin ƙwarai babu yanda za'a a canza tunaninshi." Daga haka ta nufi hanyar part ɗinta harara Mom ta sakar ma Abba sannan ita ma ta yi nata ɗakin.
Sai ya rage daga Abba sai Taj a plorn "Mr Abad me ya kawo ka gidan mu." Taj ɗin ya faɗa kai tsaye murmushi Abba ya yi "Nan ɗin ma gida na ne, koh ka manta kai ɗin ɗana ne ina da iko da kai da kuma abun da kake da." Girgiza kai Taj ya yi ya na sakin murmushi mai ciwo "Kuma haka ne na manta, mutane sun yi gaskiya duk wanda ya haife ka ya ƙwareka."
Ya ce ya na juyawa zai wuce Abba ya ce "Tajudden me yasa ka yi aure a wannan lokacin? Baka jin tsoron abun da ya faru da matanka ya sake faruwa...." "Mr Abad!!!" Taj ya ce da ɗan ƙarfi ya juyo gabaɗaya ya na kallon Abba ɗin ya ce "Ka daina, ka daina Mr Abad stop pretending like u care, stop it, it doesn't suit u ka daina saka baki cikin al amarin gidan mu pls, we don't need u, bama buƙatar kulawarka, ka na iya zuwa ka ga sauran ƴaƴan ka ban hanaka ba, and su suka ji suna iyawa da kai, amma ni bana son alaƙar dake tsakanina da kai i know ba zan taɓa iya cire jininka dake cikin jikina ba but atleat ka daina damuwa ta." Ya na gama faɗar haka ya juya ya fice daga palorn don mai ma jin zai iya shiga part ɗinsa ya haɗu da waccan matar.
Gefen su Naila kuwa su na shiga part ɗinta Ammi ta zauna kan kujera wucewa kitchen Naila ta yi ta ɗauko mata drinks da ruwa ta kawo mata, "Yawwa ƴar Albarka thank u so much." Zama kan kujerar dake facing ta Ammi ta yi ta duƙar da kanta kamar irin ta na jin kunya ɗin nan, ita kuma Ammi sai ƙarema palorn kallo take yi sai kuma ta kalli Naila ɗin "Menene ma sunan ki?"