← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 71

Sashe 19

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi ya sauke, Mata biyu da Allah ya yi ma rasuwa, ɗan da ake bibiyar rayuwarsa, rayuwa da mutun yake zagaye da maƙiya, duk mutun mai hankali zai so ya nisanci kanshi da wannan yarinyar, sai ya fara tunani _idan ma bai aure ta ba, ta riga da ta zama target ɗinsu and ita kanta has already made her mind, she is willing to do it_

A hankali ya ɗago ya kalleta da wani sharp gaze "This marriage won’t be love, It won’t be soft. And it won’t be easy."

Ɗan murmushi ta saki "Good, i don't do easy." Wani iri ya ji, na for the first time he wasn't fighting alone on the battlefield, and that terrified him, becoz if he let her in, ba yaƙin kawai zata canza ba hatta shi ɗin sai ta canza shi.

Numfashin ta ja "But before that, ina son in san tarihi gidan ku, ba sai kun shiga deep ba but something da zai sa in san maƙiyana."

"Baki da matsala da wannan." Cewar Taufeeq.

Meemziey's pen
[04/10, 14:29] Amina Khaleel: Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

page________1️⃣3️⃣

Tsayuwa Taj É—in ya gyara "Kafin ki san mu su waye, ya kamata ki san wani abu
....... Duk macen da ta aure ni mutuwa take yi." Kallon kallo suka shiga yi ita da shi, ya na so ya ga wani reaction a face É—inta amma babu, daria ta yi "Na sani Mr Tajudden, and am ready for it." Jinjina kai ya yi cikin zuciyar shi sai mamakin rashin tsoro irin na Naila yake yi.

Taufeeq ya kalla "Am going ka yi mata bayanin duk abun da take buƙata." "Sure." Taufeeq ɗin ya ce, sannan Taj ya fice, ya na ficewa, Taufeeq ya wani irin kalleta, ɗab yamutsa fuska ta yi "Mene? Mene kake kallona haka?" "Kin san abun da kika saka kan ki ciki? Did u know how dangerous our family is, did u know how dangerous Taj is? Taj ɗin ma first before a kai ga maƙiyansa, did u know how dangerous he is? Kin kuwa san hatsarin da aikin sa yake ɗauke da shi, kin kuwa san mutane masu hatsari ne zagaye da shi, He is the CEO&Chairman of Abad Global Security & Logistics (AGSL) Kin kuwa san me company ɗin nan yake yi? " Tsayawa kawai ta yi ta na kallon shi shi kuma duk ya ruɗe, ko da yake shi kaɗai ya san abun da ya gani tun da ɗan uwan Taj ɗin ne.

Sai kuma ya sake cewa "A multinational firm operating across Africa, the Middle East, and parts of Europe. A wajen mutane AGSL was a high level security and logistics company, and for mutane waÆ´anda suka sani, waÆ´an da suka san ainihin me company É—in yake yi, it was a gatekeeper of power, controlling access to routes, makamai, intelligence, da kuma rayuwa da kanta,abubuwan da wannan company suke yi sun kama da....tsaron manyan Æ´an siyasa da kuma royal families, sannan suna ba da security convoys na wajajen da suke da hatsari, suna transporting sensitive assets, kaman documents, tech, da bullion ya na da contract da government wato gwamnati, embassies, oil and gas companies, da kuma international organisations."

Ya kalleta ya ce "Kin san su waye suke aiki a wannan company ɗin special forces ne wato sojoji na musamman, da kuma intelligence trained wato ma su anfani da ƙwaƙwalwa masu kaifin tunani, sai kuma waƴanda da maganar Tajuddeen kaɗai suke aiki, waƴanda zasu iya bada rayuwar su don Tajuddeen ɗin, suna ba da tsaro ga manya manya kayan gwamnati da za'a fitar da su, su na gadin bakin boarder da kuma manya manyan jirgin ruwa dake ɗauko kayan especially makamai, su na hana human trafficking wato safara mutane, da ma na ƙwayoyi, da ma duk wani rikici na siyasa, kin san auren Taj nawa?" Ya karashe da tambayarta.

Girgiza kai ta yi "Auren Taj biyu, kuma duka kashe su aka yi wato matan sa, ɗayar ta na da ciki aka kashe ta wanda ɗan cikin nata ma ya riga ta mutuwa, ɗayar kuma sai bayan ta haihu sai bayan da ta haifi Ayan, wanda akan hakan ne ana sanin ta na da ciki aka bar ƙasar da ita basu dawo ba har sai da ta haihu amma still aka kasheta, kin san duk me ya jawo hakan?" Girgiza kai ta yi "Saboda ya ce A'a, saboda ya ce Aa, saboda baya amsan cin hanci, saboda ya na tsaye akan gaskiya, ya na fallasa duk wanda yake tunanin he is untouchable that is how our family became haunted, sun san cewa ba za su iya taɓa shi ba sai suka koma kan matanshi ƴaƴan shi da kuma duk wata macen da zaɓe shi, did u know the biggest betrayal da aka yi ma family ɗin mu? Is lokacin da best friend ɗin maman mu ta auri mahaifin mu sannan ta saka mahaifin mu ya saki mahaifiyar mu."

Kallon shi kawai Naila ke yi coz familyn su is so complicated, daria ya yi ganin yanda take kallonshi "Are u surprised, shin kin san waye babban maƙiyin mu a yanzu?" Girgiza kai ta yi "Mahaifin mu ne, our father wanda ya haife mu he is our biggest enemy, ba wai ya na cutar da mu bane, A'a but ya san duk abubuwan dake faruwa da mu, ba zai taɓa protecting ɗin mu ba sannan ba zai taɓa saka hannu wajen cutar da mu ba, our father knows all the dirty works, shi dai abar shi wajen kare business ɗinsa empire ɗin sa, duk abun da muka faɗa sai ki ji ya ce "It's business" shi ya sa Taj yake jin zafin sa babu wanda Taj ya tsani gani kamar Mahaifin mu, koh maganar sa ma baya so ayi, so ki bar cewa gidan mu akwai tarin securities da kuma security cameras don kuwa na kusa da mu da su ake haɗa baki wajen cutar da mu." Ya ce ya na kallon Naila ɗin.

Numfashi ya sauke sannan ya ce "Tell me Ameenatu El Bashir, are u ready for this war? are u still in for this war?" Zuba mishi idanu ta yi "Yes am ready, babu abun da zai saka in yi backing down Taufeeq. " Jinjina kai ya yi "This is a different game, ba irin wanda muka bugawa bane lokacin da muna school." "Na sani." Jinjina kai ya yi "Welcome to the game Ameenatu, welcome to the family." "Thank u." Ta ce fuskarta a É—aure don kuwa ta riga da ta shigo ciki she don't think akwai abin da zai saka ta canza ra'ayinta.

Miƙewa Taufeeq ya yi "mu bar asibitin nan, coz at any time za ki sha mamaki." Gyaɗa kai ta yi ta na kama gashin kanta ta dunƙule shi waje ɗaya, sannan ta nufi in da hand bag ɗinta da sauran tarkacenta suka ajiye, ta ɗauki veil ɗinta ta yi rolling sannan ta dauki bag ɗinta tare da saka takalim ta suka fice, gida ya ajiyeta wanda ta yi mamaki don ko da suka isa gida wasu manyan securities ne ke gadin gidan, ta ko'na securities kawai kake ganin, kallon Taufeeq ta yi daria ya yi "Ai gara ki saba tun yanzu don kuwa kin zama target and daga yanzu duk in da za ki tafi da securities za ki tafi, ka da ki manta kin kusa zama Mrs Tajuddeen Abad. " Jinjina kai kawai ta yi ta sauka ta shige cikin gidan shi kuma ya ja mota ya bar wajen.

Ko da ta shiga cikin gida ta iske su Kawu hankali tashe, tambayar ta suka shiga yi koh ta san me yasa securities suka zagaye gidansu? Ce musu ta yi ba komai ba ne su kwantar da hankalinsu babu abun da ya faru sannan babu wanda ya yi laifi, sun É—an ji dama dama tun da ta san da securities É—in hankalinsu ya É—an kwanta, wucewa part É—inta ta yi ta yi wanka, ta shirya cikin kaya marar nauyi sannan ta kwanta ta huta.

Washegari around 12 Taufeeq ya kirata akan ta shirya an turo mota ta ɗauketa, miƙewa ta yi ta shirya simple shiga ta yi babu wata hayaniya, ta na gama shiri Taufeeq ɗin ya sake kiranta ya ce ta futi ga driver nan ya zo, fitowa ta yi ta na kallon compound ɗin gidan su dake zagaye da securities har yanzu, driver ɗin da kansa ya buɗe mata ƙofa cikin girmamawa, shiga ta yi ya rufe sannan ya zagaya ya ja suka bar wajen, bakin wani luxury restaurant suka tsay, nan ma driver ɗin da kansa ya buɗe mata kofa sannan ya yi leading ɗinta to cikin restaurant ɗin.

Gefen VIP suka nufa in da acan ta samu Taj zaune da menu a hannunsa ya na dubawa "Assalamualaikum. " Ta ce bayan ta karaso sannan ta ja kujera ta zauna "Wa Alaikum Salam. " Ya ce ya na ɗagowa cikin wani class da kuma wayewa, ya yi wani irin kyau cikin lallausan baƙin yadin da yake sanye da shi, wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka san da cewa ba ƙaramin yadi bane, an yi masa wani irin ɗinki na zamani, hannnun sa sanye da Rolex pepsi silver color, ƙafanshi da ya yi crossing kuwa suna sanye cikin baƙaƙen lofers masu kyau da tsada, dressing ɗinsa is simple but yah illahi he is looking so damn rich, everything about him screams, luxury, elegant, mad money, da kuma class, ga wani ƙamshi dake tashi ajikinsa mai shegen daɗi, wanda duk ƙamshin ma ya cika restaurant ɗin gabaɗaya.

Shi ɗin ba fari bane sannan kuma ba baƙi bane, but Allah ya yi masa wani irin skin mai ɗaukan hankali especially da ya kasance skin ɗin nasa na samun kulawa, ya na da tsawo sosai, sannan jikinsa a murɗe yake, jikin sa is built, ya na da faffaɗan ƙirji muscles duk dai abubuwan nan don kuwa ƙirar masu ƙarfi ne da shi, ya na da kyau wani irin kyau mai ɗaukar hankali, manyan fararen idanu pink lips, cikar ƴar gira, dogon hanci, komai ya na da wanda ya yi daidai da face ɗinsa.
Chapter 19 · 0% Book details