← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 71

Sashe 55

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taj da abun ya fara isar shi ya ce "Sadeek, lets talk this out meke damun ka what is wrong with u?" Nuna kan shi ya yi "Ni, Taj kai kake damuna, i want u,i want i want ur life, i want to be u, i want to be Tajuddeen Abad." Ya faɗa a tsawace gabaɗaya tsayawa aka yi ana kallonshi everywhere is silent,  shi fah faɗan shi da taj yake yi he is so obsessed with taj da duk abun da ya shafi taj, he seriously want to be Tajuddeen Abad which ba zai taɓa zama ba har ya mutu.

Ya cigaba da cewa "Ko me ya taso kai everything taj taj taj duk in da na shiga sai na ji sunan taj, idan naje gida sabrinta ce Ayan's dad, idan ina wajen aiki taj, ko ina taj taj taj Tajuddeen Abad, i hate hearing that name bana son sunan its irritate me, it pisses me off." Sai ya girgiza kansa a hankali ya furta
"Because every time I hear it, I remember that no matter what I do…" Ya nuna Taj "I am still behind you, ba zan taɓa kamo ƙafar ka ba."

Kallonshi kawai suke yi, sadeek ya cigaba da cewa "That's why I wanted to be you, Duk abinda kake da shi…."

“I want it, Duk abinda ka yi…..sai na yi,Business? I'll do it, Money? I'll get it, Respect? I'll earn it."ya ɗan yi shuru idanunsa na sauka kan naila "Family…" ya mai da kallon shi kan taj "I'll take it." "That is why na ɗauke duka matan ka." Kamar saukar aradu haka maganar ta sauka akan kunnuwansu, wannan karon Mom ce ta yi magana "Me kake nufi da ka ɗauke su." Wani irin kallonta ya yi ya na sakin daria "Da farko ba haka naso in yi ba, amma kun san me wai ni zasu nuna ma ba sa  iya cutar Taj ba, sai na saka a a kashe su."

Gabaɗaya mutanen wajen are in total shock da sauri taj dake rungume da ayan ta miƙe tare da ɗaukar shi ta nufi part ɗin Mami don bata ma son Ayan ya ji wannan mugun abun, sadeek ya cigaba da cewa "Da ta farkon da ta biyun duka nina kashe su, don me zasu so taj har haka don me suka yarda dashi don me ba zasu iya cutar da shi ba, sai ni kuma suka ban haushi na kawar dasu." Ya sake sakin wani daria "Babu wani maƙiya babu wani Mr sidi duk ni ne am the mastermind behind all that happened right from the beginning, nine sanadi, koh Ammi da ta haɗa baki da Mr sidi da kuma Alhj Rabi'u bata san ni na turosu wajen ta ba, she thought ta na da wayo bata san ɗanta outsmart her ba."

GabaÉ—aya mutanen wajen kasa magana suka yi, Ammi da asirinta ya fara tonuwa tsurewa ta yi awajen ganin kowa ya kallota and É—anta na cikin ta ne yake tona mata asiri, ai kuwa da sauri ta ce "Bani kaÉ—ai bace ba ni kaÉ—ai na yi aikin ba hadda Asiya (Mom)." Da sauri Mom ta zaro ta na cewa "Ke Khadija ka da ki yi min sharri." Wani kallo ammi ta yi mata "Babu wani sharri ki faÉ—i gaskiya, kome ya faru tare muka yi hadda auren Ibrahim (Abba)da na yi." Kam bala'i yanzu kallon tsakanin su mom da Ammi abun ya koma.

Shi ma Abba kallon su kawai yake yi, Sadeek daria kawai ya yi ya na girgirza kansa don kuwa ya san komai, babu abun da bai sani ba har yanda aka yi auren, Naila da ta dawo wajen don ta bar ayan a nan part din Mami wanda sai da ta saka shi bacci sannan ta fito, ta ji ana wannan maganar ita ma dai ta san wasu daga cikin abubuwan tun ba yau ba tun lokacin da ta koma gidan ammi sa zama ta na jin every conversation É—in da suke yi ita da mom a lokacin har ta ma yi recording É—in wasu.

Taj da yake jin kansa kamar ya buga ya ɗago ya kalli Ammi Mom sannan ya kalli sadeek, ya san mom bata son su tun ada can but bai san zata iya aikata wani abun ba, why why hadda ita , Naila na ƙarasowa wajen sadeek ya ɗaga kafafu zai isa in da take da sauri ta ja baya ta na komawa in da taj yake ta na ɓoyewa bayanshi, dakatawa sadeek ya yi ya ɗan girgiza kai "When  I first saw u, kawai burgeni kike yi, but bayan taj ya aure ki na ji i can never let u live with him, ba zan taɓa bari ku zauna tare ba, bantaɓa tsanar mutun at the same time ina sonshi ba kamar ke, i hate u becoz u see taj for him,  ba a matsayin Tajuddeen abad kike kallon sa ba, kina kallon sa ne as mutun kamar ke, and i want u becoz taj wants u, I was very happy da na ji auren ku is contract,  but kin san me ya ban haushi."

Ya ce ya na batun binta har bayan taj ɗin da sauri ta sake riƙe taj coz da gaske tsoron sadeek ɗin taje yi, "Ur relationship start  becoming more and more and more intimate,  why will u allow him to touch u, why?" Ya karashe a tsawace "Ina son in mallake ki becoz kina matar taj, da in bar ma taj ke gara na kashe ki kamar yanda na kashe sauran, gara na kashe ki, sai na kashe ki." Kawai ya shiga kuwace kuwace, ya na daga murya kamar mahaukaci ya na.

Da sauri Taj ya sake rungume naila ɗin ya na janyewa, tare da ɗaga murya ya shiga kiran securities ai kuwa sai gashi sun shigo, nan aka kakkama sadeek din kafin Taj ya kira waya nan take ya ce ya na buƙatar ƴan sanda, Mom sai zare ido take yi ita da ammi, saboda sun ji an kira yan sanda, su na tsoron a kama su,  Nanee kuwa kuka take yi coz ita kaɗai ta san me take ji, abubuwa sun taru akanta sun yi mata yawa.

Ana haka jami'an tsaro suka iso nan aka yi arresting Sadeek ɗin, dama Taufeeq ya yi recording duk abun da ya faru so sai ya bama yan sandan suka tafi da shi, sai bayan an wuce da sadeek ne Mami da hankalinta ya kasa kwanciya ta kalli, Mom da Ammi ta ce "Asiya da Khadija me sadeek ke nufi da maganar da ya yi akan u are behind everything. " Wani kalan miyau Mom ta haɗiye da ƙyar.

Sai kuma ta saki daria ta ce "A'a Anty Zainab a bar maganar kawai." Ammi dake ma mom wani kallo ta ce "Babu wani barin maganar da za'a yi baki da gaskiya Asiya kuma baki taɓa son zainab ba ni shaida ce." Kallon su su duka Mami ta yi sannan ta ce "Ku taso mu je part ɗina wannan maganar ba ta nan bace." Ta faɗa ganin su Yara a wajen, sai da Mom da Ammi suka harari juna sannan suka nufi part din Mami hadda Abba dake wajen.

Bayan sun wuce ne, Naila ta nufi in da nanee take ta tada ita suka wuce part É—in Taj shi kuma Taj shi sa su mike da Taufeeq station suka nufa, gefen naila kuwa bayan sun shiga part din, nasiha ta soma yi mata ta na bata baki da sauran su ta na lallashinta har hankalin nanee É—in ya kwanta duk da ba duka ba.

Gefen su Mami kuwa turke su Mom ta yi akan abun da suke nufi wanda babu yanda Mom ta iya dole ta faÉ—a musu komai.

So yanzu bari mu ɗan taɓo labarin asalin su Mami

Da Asiya wato Mom da Zainab wato Mami, uban su ɗaya amma uwa kowa da tashi, ma'ana ƴaƴan kishiyoyi ne, Mahaifiyar Mami ita ce amarya, ita kuma Mahaifiyar Mom ita ce uwar gida, mahaifiyar Mom na da ƴaƴa uku namiji ɗaya mata biyu,  ita kuma mahaifiyar Mami ita kaɗai ta haifa, sunan mahaifin su Malam Yusuf haka ake kiran sa ko acikin anguwa.

Dangin su mahaifiyar Mami su na da kuÉ—i sosai don kuwa ikon allah ne da rabo kawai ya saka mahaifiyar Mami auren Malam yusuf don kuwa shi É—in ba mai kuÉ—i bane sai dai ya na da rufin asiri, Mami ta bama Mom kusan wata huÉ—u so Mami ce yaya, and Mom gabaÉ—aya É—akin su Mami ta taso, sometimes har É—auka ake yi uwar su É—aya da Mom, tsakanin mahaifiyar Mami da mom su na shiri duk da dai ba'a rasa irin faÉ—a haka na kishiyoyi da ake yi but su na jituwa.

Tun asali Mom mace ce mai son kanta sosai she is very greedy sai dai bata cika nunawa ba but in ka lura da halinta da kyau zaka ga haka, tun farko ba wai don ta na son Mami ko kuma maman Mami bane ta koma ɗakin su Mami, aa ta koma ne saboda dangin mahaifiyar Mami su na da kuɗi, kuma suna son su mami ɗin, don kuwa suturar da Mami ke sakawa ko a lokacin ba gaskiya bane, komai na ƴan gayu na ya yi yake sakawa, shiyasa Mom ta tattara kayan ta ta koma ɗakin su Mami da yake mahaifiyar Mami bata da problem sai ta riƙe ta hannu biyu biyu.

Sai ya zamana ko me zata yi ma Mami ɗin tare da mom ake yi musu,  so har dangin su Mami ɗin idan suka tashi sai su kama yin komai kala biyu da na Mami da na Mom, lokacin duniya na zaune ƙalau ba'a ɗauki komai da zafi ba, so da haka ne ita wata irin shaƙuwa ta shiga tsakani Mami da mom, komai tare suke yi.

Ita kuma Khadija wato Ammi, gidan su ammi na kusa da gidan su Mami ne su tare suka taso acikin anguwa, islamiya da boko ɗaya suka yi shiyasa suka zama ƙawaye da Mami da Ammi ɗin, duk da ammi da mom basu shiri saboda mom gani take yi kamar ammi zata ƙwace mata Mami shiyasa suke yawan faɗa saboda bata son Ammi na raɓar mami.
Chapter 55 · 0% Book details