← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 71

Sashe 4

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu duka babu zagi amma ta ajiye kowa a in da yake bata son wasa ko kaɗan, ta zama wata irin miskilar gaske, har yanzu ƙawancen su lafiya ƙalau yake tafiya da Ilham,  don ita kaɗai ce ma take ganin murmurshin Naila ɗin.

Da haka har suka rubuta JLCE ɗinsu, so ɗan hutun da suka samu ne ana zaune gida ba'a komai, lokacin an bude wani skill acquisition  centre a anguwar sai suka jona ita da Ilham ɗin suna zuwa, in da take koyon ɗinki Ilham din kuma na koyon beadwork, so haka suka yi keeping kansu busy, har aka yi resuming suka koma SS1.

Basu daÉ—e da resuming ba kuma aka yi bikin yaye su a centre din in da aka basu certificate ita kuma ta ci keken É—inki, Ilham kuma kayan beadwork.

Babu yanda kawu bai yi harin keken ɗinkin nan ba akan a saida ita amma taƙi bari ta ce ɗinki za ta yi, farko da gyaran kayan da suka yage ta fara daga baya ne ta fara ɗinki kuma abin ya amsheta, so da shi ne ma take samun kuɗi take biya ma kanta buƙata ba tare da ta turke Kawu ya bata kuɗi ba.

Da haka rayuwa ta yi ta tafiya da daɗi da kuma ba daɗi da wuya da kuma sauƙi har suka kammala secondary school ita da Ilham,  su na karewa ba da jimawa ba aka soma shirye shiryen bikin Ilham din don dama ta na da miji kuma ba ma a ƙasar yake zaune ba, so idan an yi auren barin kasar za su yi, in da zata cigaba da karatunta.

Gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi saboda za su rabu, haddai Ilham din don tafi nunawa ita kuma Naila tafi jin ciwo saboda ita nata azuciya take jimami, haka aka yi ta shagalin buki, aure da sati ɗaya suka bar ƙasar, sai duniyar ta yi ma Naila faɗi wacce take sharing pain tare da ita itama ta tafi ta barta, sai zaka ɗaki ya zame mata aboki, in har ba ɗinki take yi ba toh zaman ɗakin ne 24/7.

Bata taɓa zato ba, bata taɓa tsammani ba, don result ɗinta ya yi kyau sosai haka ma jamb ɗinta, don kafin duk ma a fara hidimar buki, Dad wato mahaifin Ilham ya amshi takardunta, ta na zaune rana daya ya aiko a kirata ta na zuwa ya bata takarda ta tare da yi mata albishir na ta samu admission a university of Abuja.

She was so happy sai godiya take yi ma Dad hawaye sun cika idanunta, murmushi kawai ya yi haka kawai Allah ya dora mishi tausayin Naila din tun ta na karama, ya tuna lokacin da ya fara ganin Naila ɗin,  ranar mai gadi ya bar gate buɗe sai Ilham ta fita, ta na fitowa ta gefen gidan su ta hango wata yarinya duke ta na kuka.

Karasawa ta yi wajen ta sai kallonta take yi sannan ta ce "Me ya sa kike kuka." Dagowa Naila ta yi ta kalleta "Yunwa nake ji tun safe ban ci abinci ba." Ta amsata, ita kuwa Ilham cikin wautar ta ta yara ta ce "Muje gidan mu kici abinci maman mu ta dafa abinci da yawa." Aikuwa naila ta tashi ta bita zuwa gida, so shi ne mafarin ƙawancen su.

Da registration da komai anyi mata makaranta kawai zata fara zuwa, da za ta wuce kuma ya bata kuɗi masu yawa cikin envelope ya ce ta sayi duk abun da take buƙata godiya ta yi masa ta ta tashi ta tafi.

Ta na komawa gida ta sanar da Kawu, don ka da ma ya ce ba'a faÉ—a masa ba, Inna ta ji kishi sosai don har so ta yi a hana Naila É—in amma Naila ta taka mata burki.

Ita ma Fa'iza ta na ganin Naila É—in ta samu admission ta damu Kawu ita ma Uni take son zuwa sai dai lokacin ya wuce don an riga da an gama dauka sai dai ta jira next year.

Ranar da ta fara zuwa makaranta ta na sanye da maroon hijab dogo har kasa, da tambaya ta isa lecture hall É—insu zama ta yi ta na observing komai, babu surutu babu hayaniya ranar ma basu yi lecture ba.

Haka ta dawo gida, da haka ta cigaba da zuwa makaranta, ta na attending lecture abun da ya kai ta shi take yi bata bin wani abokai, wani surutun banza can duk bata yin su, medicine take karatu shi ta saka first choice dinta kuma ta samu da yake ta na da marks masu kyau.

Ta na da wani irin ƙoƙari she is very smart and intelligent, kullum idan ba'a lecture ta na library always minding her business,  koh library ɗin ma acan ƙarshe take zama, can wani lungu don rashin son hayaniyar ta har ta ɓaci wasu ma kallon mai girman kai suke yi mata,wai ta na jin kanta sama.

Yau ma ta na zaune cikin library kamar kullum ta na karatu, ta tattara duka hankalinta kan karatun da take yi, fuskarta a haÉ—e don dama a haÉ—e take kullum don bata cika daria ba.

Daga can gefe da in da take zaune wani saurayine kyakkyawa  yake zaune shima da laptop a gabansa, akai akai yake ɗagowa ya kalleta sai kuma ya sauke kansa, shi ma a kullum idan bai da lecture nan yake zuwa ya zauna, a cikin library ɗin nan ne permanent wajen sa na zama kamar ita.

Kuma kullum ya zo sai ya ganta,  sai ya yi ta mamaki, bai taɓa ganinta da wani ba, friends ko kuma wani abu, numfashi ya sauke ya na jin yau kam ba zai iya hak'uri ba sai ya tafi ya yi mata magana.

Mikewa ya yi tare da laptop dinsa da jakarsa ya nufi in da take, "Assalamualaikum. " Ya yi mata sallama bayan ya karasa, sai da ta dan dauki lokaci sannan ta ce "Wa Alaikum Salam." Ba tare da ta ɗago  ba, da mamaki yake kallonta sai kuma ya shanye mamakinsa ya ce "Ko an yi min izini na zauna anan?"

Shuru na wani lokaci sannan ta ce "Library din na kowa ne." ÆŠan murmushi ya yi ya na jinjina kai, wato ita babu ruwanta, in ya ga dama ya zauna in bai ga dama ba shi a ciki.

Zama ya yi ya na ajiye kayan shi, shuru ya ratsa wajen kafin ya ce "Am...Amm... Sunana Taufeeq Ibrahim, Am studying computer science and engineering, am in my first year, probably my second degree....." Bai ida rufe baki ba ya ga ta miƙe ta na haɗa kayanta ba tare da ta yi masa magana ba ta yi wucewarta.

Da kallo ya bita, cikin mamaki sai kuma ya saki murmushi ya na mai da hankalinsa kan laptop É—insa.

Shikenan daga ranar kullum sai ya in da take ya yi ta yi mata surutu ita kuma ta kyaleshi, ba zata ce masa komai ba kuma shi baya gajiya, dama can Taufeeq baya da problem, ya na da surutu sosai kuma kullum cikin murmushi yake da wuya ka ga ɓacin ranshi, duk abun da take yi masa komai bai ji ya san wata rana dole ta kula shi.

Yau ma suna zaune a library sai surutu yake yi mata idan ya yi aiki a laptop dinsa daya biyu sai ya dago ya kalleta ya na yi ma bayanin abun da yake yi da kuma amfaninshi, duk da bata tankashi ba amma ta na jin abun da yake faÉ—a, har ya faÉ—i wani abu da ya yi caughting attention dinta ta dago ta kallesa, dakatawa ya yi "Mene ne? In dawo baya ne?" Zuba mishi ido kawai ta yi, by yanzu ya riga da ya gane yawancin maganar ta da ido take yin sa hakan ya saka shi fara mata explanation.

GabaÉ—aya sai ta juyo ta na kallonsa shi kuma bayani kawai yake yi mata, bayan ya kare ya ce ya gane ta gyaÉ—a kanta, daga nan ta koma kan abun da take yi, shi dai haka kawai ta na burgeshi rashin hayaniyarta da sauransu.

Keypad ɗin ta dake gefe ta dan kunna ganin lokaci har ya wuce ta miƙe a hankali ta shiga tattara kayanta, ta saka cikin jaka duk ya na kallonta, ganin za ta wuce Ya ce "Wucewa za ki yi ba tare da kin yi min sallama ba?" Cikin wasa ya furta hakan dan dakatawa ta yi "Sai gobe." Ta ce cikin muryarta da bai taɓa ji ba, dole ta kama rowar muryarta coz ta na da wani irin voice mai daɗi.

Murmushi ya yi "Sai gobe friend. " GyaÉ—a kai ta yi ta wuce.

Washegari

Ko da ta karaso ta iske shi zaune, kujera ta ja ta zauna ta fitar da jotter ɗinta,  ai kuwa da sauri ya dauki jotter din ya buɗe sunanta ne a first page wato "AMEENATU EL BASHIR." Cikin bracket aka rubuta "(NAILA)." Zaro ido ya yi "Laa dama Ameenatu ne sunan ki? Sunan Mahaifiyata ne dake ai sai dai na kira ki da Naila ya fi sauƙi. " Ita dai bata ce komai ba, don jira take yi ya kare surutun sa ya bata littafin ta ta yi karatu.

Ganin ta yi shuru bata amsa shi ba ya ajiye mata littafin ta, ya koma kan laptop dinsa ita kuma ta soma karatu, nan wani lokaci ta dago a hankali ta kallesa "Za ka koya mun computer?" Ta ce a hankali, É—agowa ya yi ya kalleta "Na'am. " Shuru ta yi sai kuma ta ce "Laptop, za ka koya min?" Cikin Jin daÉ—i ya ce "Eh idan ki na so, Mom Naila." Kallon shi ta yi, irin Mom Naila kuma, murmushi ya yi "Eh sunan mamana ne dake Ameenatu. " Jinjina kai ta yi.

Tun daga ranar suka zama friends duk da ba wani sake masa take yi ba, din babu mai tsallake iyaka a tsakanin su, da haka har suka yi exam na first semester aka yi hutu suka dawo second semester wasa wasa sai abotar su ta danyi ƙarfi.
Chapter 4 · 0% Book details