← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 71

Sashe 44

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari
Fitowa ta yi daga ɗakinta sanye cikin doguwar riga marar nauy,  sai hula a kanta,  Taj ya na zaune kan dining me aiki na serving ɗinsa breakfast ƙarasowa ta yi wajen ta tsaya gefen shi ta na ɗukowa ta sakar masa peck a kumatunsa "Goodmorning. " ta ce ta juyo da face ɗinsa ta sakar masa peck a lips ɗinsa sannan ta miƙe ta samu waje ta zauna, kallonta yake confusely saboda hakan sa ta yi sabon abu ne  awajen sa, ɗaure fuska ta yi kamar bata san abun da ta yi ba ta na nuna ma mai aikin abincin da za'a saka mata, bai ma natsu ya ci abincin ba ya tashi ya bar wajen.

Shi ba wawa bane ya san me ya ke yi, kuma ya na kallonta, ya sa ni akwai abun da ya dawo da ita gidan zuba mata ido zai yi ya ga gudun ruwanta, saboda she can't outsmart him never.

Da dare shigowa ta yi ɗakin ta na sanye da riga da wando na bacci masu taushi sai kanta dake sanye da hula, zaune yake kan sofa ya na shan coffee shi ma sanye da nasa kayan bacci na LV navy blue masu kyaun gaske, shuru ta yi ta na kallonsa ta na tunanin yanda zata yi magana duk da Ammi ta ce mata duk abun da ta faɗa masa kai tsaye zai yarda ba tare da gardama ba, ƙarasawa ta yi cikin ɗakin ta na zama kan gado ta yi facing ɗinsa, ƙafarta ɗaya kan ɗaya, fuskarta a haɗe ta ce "Gobe zan fara zuwa office ɗinka, am taking over ur office. "

"Ok." Ya furta ya na kallonta, koh akwai abun da zata ƙara aciki, itama kallon shi take yi na yanda ya yarda da sauri "Shikenan." Ta faɗa ta na hayewa kan gadon ta kwanta sai kuma ta ɗago ta kallesa ta ce "U will sleep on the sofa, Ayan is not sleeping in this room to night. " "Toh." Ya sake cewa da ya saka ta tsaya ta na kallonsa, sai kuma ta koma ta kwanta, kamar yanda ta ce haka ya yi bayan ya gama shan coffee ɗin ya ɗauki pillow da blanket ya kwanta kan sofa.

Washegari tare suka fito, zuwa office ta na sanye cikin suit ta mata milk color ta D&G, ƙafanta sanye da brown heels na dior da hand bag brown shi ma na dior, sai kanta dake sanye da brown and milk vintage scarf mai shegen tsada, face ɗinta sanye da vintage eyeglass baƙi lips gloss kaɗai ta shafa, ta yi kyau sosai suit ɗin ya zauna ajikinta sai ta fito kamar wata boss lady, like all those female CEOs da basa ɗaukan shit, su na fitowa babban palor Mike ya saki baki ya na kallonta ganin yanda ta haɗe fuska wanda koh kallon sa bata yi ba ta saka kai ta fice Taj ya na biye da ita.

Su na fitowa compound É—in gidan ta kalli motan da aka fitar musu, kallon securities dake wajen ta yi ta ce "I don't like this car, change it to Rolls Royce and don't waste my time am already late." Ta faÉ—a ta na kallon brown leather cartier watch dake hannunta, cikin sauri aka canza musu motar zuwa Rolls Royce, buÉ—e musu motar aka yi suka shiga driver ya ja.

A bakin entrance na AGSL suka tsaya wato Abad Global Security and logistics, aka buɗe musu ƙofa suka fito jerawa suka yi suka nufi cikin company ɗin, ita da Taj wanda shi ma ya yi wani irin halakakken kyau cikin suit dinsa coffee brown and milk color, shima ya yi kyau ya na sanye da baƙaƙen glasses ɗinsa, su na shiga ciki, kawai komai ta tsaya kowa ya juyo ya na kallonsu, especially Naila da babu wanda ya taɓa ganin ta zo office ɗin sai yau, and ta yi wani irin legendary shigowa, like yanda gabaɗaya ta ɗauki hankalin wajen, ta kame face ɗinta ta na wani kalan tafiya kamar wata model kamar wacce zata tafi run away na Gucci yah illahi.

Wani kalan aura ne ta shigo da shi, like yanayin tafiyanta yanayin dressing ɗinta da komai ma ya na ɗauke da wani kalan aura, and god daga ita har Taj ɗin su na serving face card, like face card din su ya ɓaci kyau da koma sun tara, ga yanda su na shigowa ƙamshin turaren su ya mamaye wajen, direct wajen elevator suka nufa su biyu kaɗai suka shiga elevator ɗin zuwa floor ɗin da yake, su na isa office din sa secretary ta taso ta buɗe musu office ɗin suka shiga.

Ajiye jakarta ta yi kan table ta na ƙare ma office ɗin kallo, office ɗin ya tsaru iya tsaruwa kamar ƙasar waje ya yi kyau sosai, Taj na zaune kan sofa na office ɗin secretary ɗin ta sake shigowa ta kawo musu coffee ta bama Taj sannan ta bama Naila,  ɗauka ta yi ta ajiye a gefenta, nan secretary ɗin ta shiga karanto ma Taj schedules ɗinsa, naila na gefe ta na kallo har ta ƙare.

A hankali Naila ta ce "come here." Kallonta secretary ɗin ta yi sai kuma ta ƙaraso in da take saboda ta san da ita naila take don babu yanda naila zata cewa mijin ta come here, gaban naila ta tsaya, kallon sama da ƙasa Naila ta shiga yi mata ta ya mutsa fuska ta na cewa "I don't like it." Kallon confusion secretary ɗin ta yi mata "I mean ur dressing,  dress decent idan zaki zo office or don't come again."

Ta ƙarashe ta na tsareta da idanu "Yes ma'am. " secretary ɗin ta amsa da sauri saboda wani irin ƙwarjini da naila ɗin ta yi mata, "Let me see his schedule. " ta ce ta na miƙa hannunta da sauri precious the secretary ta bata tab ɗin hannunta dubawa ta shiga yi, take ta fara cire waƴan da Taj ɗin zai yi meeting da su, da waƴanda bazai yi meeting da su ba ta na faɗa mata ta yi cancelling abun, bayan ta ƙare ba mayar da Tab din ta ce "Make sure kin yi abun da na ce."

"Yes ma." Precious ta ce da sauri ta na ficewa, mai da kallonta kan Taj dake zaune ya na danna waya ta yi "Ka ta shi tafi ka na da meeting. " "Ok." Ya ce ya na miƙewa ya gyara zaman suit ɗinsa ya fice, ita ma ficewa ta yi ta shiga zagayen company ɗin duk da ba ko ina ta je ba saboda company ɗin na da wani irin girma sosai, duk in da ta gifta sai kallonta ake yi ana gaisheta, babu wanda bai santa ba don duk sunga hotunan auren ta da Taj sannan zuwa yanzu labari ya zagaye office ɗin Mrs Tajuddeen Abad ta na a companyn so kowa ya kama kanshi.

Ko da ta dawo already Taj ya dawo ya na zaune kan kujerar sa, ƙarasawa ta yi ta zagaya ta zauna kan table ɗin ta na facing ɗinsa, shafa kanshi ta yi zuwa face ɗinsa "Ka dawo?" Ɗagowa ya yi ya kalleta "Umm." Ya jinjina kansa, jinjina kai ta yi ita ma ta sauka ta zaga ya ta zauna kan kujera ta shiga janyo files dake gabansa ta na dubawa sai wanda ta yi approving sannan zai yi signing haka suka yini acikin office ɗin lokacin ta shi ya yi suka dawo gida.

Washegari ma haka ya faru tare suka tafi wannan karon ma ita ce take zaune kan kujeran shi kuma ya na can zaune kan sofa, a haka Sadeek ya shigo ya iske su ya gaisa da naila ya koma wajen Taj suka gaisa sai mamakin abun da yake faruwa yake yi, dama Sadeek É—in da naila suna shiri tun lokacin da take wajen Ammi don yakan kira ta su gaisa ko bayan da ta dawo wajen Taj É—in, da haka ya yi musu sallama ya tafi sai mamaki yake yi, ku ma duk da haka Taj É—in bai koh damu ba.

Haka suka cigaba da zuwa office din tare wasa wasa komai na Taj sai ya dawo under Naila's control kome zai yi sai ya sanar da ita ita take yanke decision ita take controlling komai, kai hatta da komai na gida da general acc na gidan da duk wanda ya tashi zai yi amfani da shi ya cire kuÉ—i, naila ta saka limit akan shi like komai ita take controlling.

Mom

Zama ta yi kan dining ta na kallon ɗaiɗaikun warmers dake kan dining ɗin "Hauwa." Ta ƙwala ma chef dinsu kira, da sauri Hauwa ta zo "Whats this me nene haka, why is the dining so scanty." Cikin respect Hauwa ta ce "Mrs Naila ne ta ba da umarni ka da abinci ya wuce three dishes. " Wani irin kallon hauwa ɗin mom ta yi "Kamar yah ban gane ba, ita wacece da zata bada umarni acikin gidan nan, tukuna ma yaushe aka yi haka?"

Cikin tsoro Hauwa ta ce "Jiya ne da kika fita da marece ta tara masu aiki hadda securities gabaɗaya ta yi setting new rules." Jinjina kai mom ta yi "And sai kuka yi abun da ta ce with out even informing me, ita wacece da zata yi hakan who is she." "THE WIFE OF THE HOUSE. " Naila da ta shigo dining room ɗin ta faɗa, daga mom har Haulat miƙewa suka yi, mom ta ce "Har wuyan ki ya yi kaurin da zaki zo ki na setting rules acikin gidan nan who are u? waye ya baki dama? who gave u the permission? "

"Nine." Taj da ya shigo dining room ɗin ya faɗa wani irin kallon Taj mom ke yi confusely ta ma kasa ma yana can ta girgiza kanta ta ce "Taj ka kuwa san me kake faɗa? Kai ne fa ka bata dama ta yi meddling da family affairs ɗin mu? Yaushe aka taɓa yin haka?" Cikin ko in kula Taj ya ɗage kafaɗa ya ce "She is my wife and she has the right to do anything da take so, i don't care ko me zata yi as long as it's make har happy. "
Chapter 44 · 0% Book details