← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 71

Sashe 27

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rawar murya kamar irin zata yi kuka Naila ta ce "Ammi ina ƙoƙari wallahi Ammi am trying. " Shuru ya ratsa tsakanin su kafin Ammi ta ce "Shin ko ya sanar dake yanda business ɗinsa ke tafiya?" Ɗaga kanta ta yi ta kalli ƙofa duk da ita kaɗai ce cikin ɗakin sannan ta tabbatar da gaske babu camera aciki kamar munafuka ta ce "Bai faɗa mun ba, amma a cikin kwanakin da suka wuce yakan yi waya da dare." "Waya kuma akan me?" "Ban sani ba amma wani lokacin idan ya ganni yakan rage muryar sa."

Shuru sannan Ammi kamar cikin zafi haka ta ce "Ki maida hankalin ki da kyau, Ameenatu, ya kamata ace mace ta sanar abubuwan da mijin ta yake yi." Numfashi ta ja "Tau Ammi." Sai kuma ta ƙara da cewa "Amma Ammi bana tunanin Taj ya na yarda da mutane da sauƙi, idan nace in matsa masa ya na iya ƙin yarda dani. " "Haka ne kuma kin yi gaskiya, toh ki bi abun a hankali, sannan ki faɗa mun duk abun da ya faru. "

Murmushi Naila ta yi na gefen baki don ta gane me Ammi ɗin take nufi sai kuma ta ce "Ammi akwai abun da ya kamata in damu akai?" Ta yi tambayar ne da wata manufa ta daban, numfashi Ammi ta ja "Tajudden ya na da maƙiya da yawa, so kullum cikin haɗari yake ."

Shuru Naila ta yi kafin cikin sanyi ta ce "Zuciyata ba zata iya É—aukar wani abu ya same shi ba." Murmushi Ammi ta yi ganin Naila É—in is so easy to handle, and so easy to fool bata san abun is the other way round bane.

Bayan sun gama waya ta wurgar da wayar kan gado ta na É—an yamutsa fuska, ita ta tsani pretending wallahi, sai kuma ta É—an saki murmushi duk abun da ta faÉ—a ma Ammi gaskiya ta faÉ—a, na Taj É—in bai yarda da mutane ba, he doesn't trust easily, batun waya da dare kuma yanayi, sai dai ba kamar yanda ta ce bane idan ya ganta ya yi shuru, ya na rage murya ne since É—aki É—aya suke kwana baya so ya dameta.

Bata yi ƙarya akan komai ba, sai dai abun da ta faɗa daban abun da Ammi ɗin ta yi understanding dabam, so ita dai ta yi abun da aka ce ta yi wato ta faɗi duk wani motsi na Taj ɗin.

Ɗan kwantawa ta yi kan gadon ta na sauke numfashi, ta na tunanin plan ɗinta na gaba kuma takan wa plan ɗin zai bi, don kuwa ta yi alƙawarin duk sai ta fito da siffar ainihin mutanen da suke tare da su masu fuska biyu, and yanzu akwai aiki sosai a gabanta ba ma kaɗa ba aiki da yawa.

Meemziey's pen
[04/10, 14:43] Amina Khaleel: Mrs Tajuddeen Abad

By

Meemziey

page______1️⃣7️⃣

Murmushi ta yi ta na sauraren abun da Ilham ɗin take faɗa, don waya suke yi da Ilham ɗin wanda sun fi ƙarfin 10mnt suna waya, "Ke wallahi da gaske nake, da na ga bana da lafiya na zaci ciki ne da ni, ai kuwa da sauri na je na yi awo na ji daɗi na gana negative ne wallahi." Cewar Ilham ta cikin wayar girgiza kai Naila ta yi "Ni ban san me yasa kike tsoron ciki ba Ilham haihuwar ki biyu fah." "Lallai Naila ba zan ce komai ba, idan kika yi ciki zaki gane abun da nake nufi."

Taɓe baki Naila ta yi "Ba nan kusa ba kuwa." Wata daria Ilham ta yi "Lallai Naila sannu, idan ma aka bibiya ciki ne dake." "Hmm." Shi ne ka ɗai abun da Naila ɗin ta iya faɗa, "Yah illahi na mance in faɗa miki, na yi mana order na wasu aphrodisiacs masu shegen kyau, babes tested and trusted ne, ban ma daɗe da ƙare anfani da su ba, da zan sake order ne na yi mana order mu biyu kin san yanzu kin shigo layin mu layin masu aure." Ilham ɗin ta faɗa cikin sheƙiyanci.

Ɗan yamutsa fuska Naila ta yi "Toh ni don Allah me zan yi da kayan mata?" Kasa amsa mata Ilham ta yi shuru na wani lokaci sai kuma ta ce "Ni na ma rasa me zance miki Naila, kamar yah me zaki yi da kayan mata? Dama me ake yi da su." "Ba matan aure ke......." Da sauri ta yi shuru sai kuma ta cigaba da cewa "Toh ai ban daɗe da aure ba, har yanzu ban ƙarasa shanye wanda na zo da su ba."

"Ni babu ruwa na idan na aiki miki ki haÉ—a duka biyu ki sha, ki rikita mana Taj Abad sai dai kawai mu ji labarin an baki rabin share na AGSL." Daria Naila ta yi "Pls bari mafarki don wannan mafarki ne." "Ba mu sani ba har sai mun gwada so idan na aiko maki su ki dage ki sha kin ji?" "Na ji." "Ok Babes bari in je Masoyi ya dawo." Daga haka ta katse wayar.

Sauke wayar daga kunne Naila ta yi ta na saukar da ajiyar zuciya sannan ta miƙe ta jawo hijab ta saka ta fice zuwa babban palor.

Ta na ƙarasawa tsakiyar palorn dai dai da wata budurwa na shigowa bayan ta security ne riƙe da ɗan trolley ɗinta, budurwar bata da wani tsayi sannan bata da wani haske ta na da kyau irin nata.

HaÉ—a idanu suka yi da Naila kallom juna suka soma yi kafin Naila ta É—auke idanunta cikin basarwa, bata yi niyar magana ba amma ta É—aure ya ce "Sannu." Ta ce zata wuce budurwar ta ce "Yawwa Amaryar Yah Taj. " Dakatawa Naila ta yi ta É—an juyo ta kalleta, É—an murmushi budurwar ta sakar mata "Ko ba ke bace Dr Ameenatu bazawarar da Yah Taj ya auro?"

Ɗan zuba mata ido Naila ta yi baza ma ka gane yanayinta ba sai kuma ta saki murmushi "Eh haka ne sunan nawa, Dr Ameenatu ba, yes ni ce bazawarar da ya auro." Ta na gama faɗin haka ta juya ta shige kitchen, har ga Allah idan ta ce maganar bata yi mata zafi ba ta yi ƙarya, sai dai abun bai wani irin dame ta sosai ba.

Da kallo budurwar wacce ake kira Haula ta bita ta na mamakin yanda Naila ɗin bata nuna wani reaction ba duk da abun da ta yi mata, ta na cikin tunanin ne Mom ta fito daga part ɗin ta idanunta na sauka kan Haulat ɗin ta wani washe baki cikin jin daɗi take cewa "Oyoyo auta na sannu da zuwa." Rumgume juna suka yi cikin murna "Me ya sa baki faɗamun yau zaki zo ba." Mom ta tambaya bayan sun raba hug ɗin "Kai wallahi da ƙyar Dad ya bari na zo, plus ina so in yi surprising ɗinki."

"Ai kuwa kin yi surprising ɗina." Murmushi ta yi zata yi magana kenan Naila ta fito daga kitchen, "Barka da war haka Mom. " Ta ce ba tare da ta mai da hankali kansu ba, "Ah Ah Naila ga Haulat ku gaisa ƴata ce, Haula baki ga matar Taj bane?" "Na...." "Mun gaisa ai Mom, ta na shigowa cikin gidan nan dani ta fara cin karo." Ta katse Haulat ɗin sannan ta kalli Mom ta mai da idanunta kan Haulat ta ce "Ki huta lafiya ƴar ƙanwa." Daga haka ta yi wucewarta.

Da kallo Haulat ta bita ta na taɓe baki, "Ke dai Mom mu shiga ciki."

8:11pm

Zaune suke palor dukan su ana ɗan taɓa fira kafin masu aiki su gama shirya dinner, kowa na wajen ban da Taj da bai ma shigo gidan ba tun da ya tafi sallar isha'i, so basu haɗu da Haulat ba, ita dai Naila na gefe ita da Ayan su na game a tablet ɗinsa, su na haka Taj ɗin ya shigo palorn sanye cikin wasu kayan Chanel marar nauyi farare.

Ƙarasowa ya yi ya gaida Mami da kuma Mom yayinda su Taufeeq suka gaishesa, ita Haulat sai kallonsa take yi ta na murmushi sai dai da alama bai ganta ba don kuwa cikin jam'i ya amsa sallamarsu gabaɗaya, ganin bai ganta ba ya sa ta ce "Yah Taj. " Ɗagowa ya yi ya na kallon direction da aka kira shi, shuru ya yi ya na tunanin ina ma ya san wannan halittar, sai kuma can ya ce "Oh ya kike?" Yamutsa fuska ta yi ta na shaƙe murya "Lafiya qlu ya Taj har na yi fushi, ace wai Yah Taj ina nan zaune baka koh ganni ba."

"Oh my bad hankalina baya wajen." Ɗan murmushi ta yi "Babu komai, Yah Taj, na yi missing ɗinka baka yi missing ɗina ba?" "Aa." Ya ce kai tsaye kuma wallahi da gaske yake ɗin don shi bai iya kwana kwana ba, ko wani ɓoye ɓoye kwaɓe fuska ta yi cikin basarwa "Yah Taj mana." "Hmm." Kawai ya ce bai sake kula ta ba ya maida hankalinshi kan Ayan dake nuna masa game da suke yi awaya.

Ita kuma Haulat haushi kamar ya kasheta, don wata rana Taj ɗin ya na da ways na disga mutun, ta ya ya za'a yi ya disga ta gaban matarsa, wanda ita matar ta sa bata ma maida hankalin kan abun da suke yi ba duk da kuwa ta na ji, sai dai bata da lokacin wannan rubbish ɗin, su na haka ne mai aiki ta zo ta sanar da su an gama haɗa dining ɗin, duk tashi suka yi suka nufi dining ɗin, Haulat sai wani salo salo take yi hadda cewa ita ce zata yo serving, haka dai suka gama dinner Naila duk ta cika da takaici, su na ƙarewa koh minti biyu bata ƙara ba ta koma part dinta.

Bayan kwana biyu.

Yau da wuri ta dawo daga asibiti, Wanka ta yi ta yi sallar la'asar sannan ta saka doguwar riga marar nauyi da hijab ta wuce kitchen, yau haka kawai take jin sha'awar yin girki, abun da ta daɗe bata yi ba don tun da tazo gidan sau ɗaya ta taɓa yi girgi, kuma koh shi masu aiko ne suka yi rabi, so daga nan bata sake yi ba kuma babu wanda ya takura mata don gidan basu da takura.
Chapter 27 · 0% Book details