← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 71

Sashe 2

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wucewa ta yi in da ake tara wanke wanke tashiga wankin su cikin sanyi wanda yake shiga har cikin ƙashinta, bayan ta ƙare ta yi shara sannan ta wuce kitchen ta hura wuta, duka ayyukan da take yi sunfi ƙarfin ta nesa ba kusa ba amma ita ke yin su tun bata iya ba har ta iya, da duka da zagi da komai kuma bai hana idan ta ƙare a daketa ɗin ko da ta yi shi da kyau, duka ya zama kamar routin ɗinta na kullum kullum, anan cikin kitchen din ta yi zamanta ta na shan ɗumin wutar da ta kunna.

Sai da haske ya fito sosai sannan Inna ta buɗe ƙofar ta kallo ɗaya ta yi mata, ya sa da sauri ta miƙe ta wuce ciki ta dauko kayan fitsarinta, ta shiga dauraye su sannan ta shanya, bayan ta ƙare ta shiga aikin gyaran palor wanda ko da an gyara shi ba wani kyau zai yi ba duba da yanda kujerun suka yi wata irin dauɗa sannan duk sun lalace, cikin sauri take yin komai saboda ta na so ta tafi makaranta.

Sai da ta share tass ta gyara sannan ta wuce ta yi wanka ta shirya sai sauri take yi, bata ma nemi abincin safe ba don ta san babu wanda zai bata ta fice daga gidan, ta na fita dai dai wata mota na pakawa bakin kofar gidan, da sauri ta nufi motar ta buɗe baya ta shiga, yariyar dake gaban motar wacce za su yi sa'a ɗaya ana ce mata Ilham ta juyo ta kalleta "NAILA, ai na za ci ko da zamu zo baki shirya ba." Ɗan murmushi Naila ta yi cikin muryarta mai sanyi ta ce "Sauri na yi ka da na ɓata lokaci. " "Kin yi assignment?" Ilham ta tambaye ta, zaro ido ta yi ta na girgiza kai "Ban yi ba wallahi."

"Dauko littafin ki ki kwashe nawa." Ilham ta ce ya na buɗe jakarta ta dauko littafin ta ta bama Naila, amsa ta yi cikin sauri ta shiga kwashe assignment ɗin, Allah ya taimake ta kafin su isa ta ƙare.

A bakin gate driver ya ajiye su, suka shiga ciki, private school ce take zuwa, wanda mahaifin Ilham ne da kansa ya sakata a makarantar ganin ta na ƙawar ƴar sa sannan bata zuwa makaranta don Kawu bai sakata a makaranta ba.

Mahaifin Ilham É—in shike daukar nauyin karatunta, komai ya saya ma Ilham É—in sai ya saya ma Naila in dai harakan makaranta ne don ajinsu su É—aya, shi ya sakata both islamiya da boko kuma makarantar da Ilham É—in ke zuwa, sannan ya na ba Ilham kudin break ta bata, sannan food flask din naila na makaranta ya na gidan su ilham din ita ke wuto mata da shi, wani son Naila din Allah ya dora ma Ilham, ko a gida take magana É—aya biyu Naila, kuma iyayenta basu kyamaci Naila É—in ba.

Ya kan yi musu kaya iri É—aya especially lokacin sallah don kawu Usman kwata kwata bai damu da Naila É—in ba, kamar dole ta zamar masa zama da take yi agidan.

Karfe biyu bayan an tashi daga makaranta driver ya zo ya dauke su, sai da aka ajiyeta a gida sannan su Ilham suka wuce don layin su É—aya gida biyu ne a tsakanin su.

Ana ajiye su direct wucewa ta yi cikin gida ta wuce dakinsu lokacin su Faiza basu kai ga dawowa ba don da kafa suke dawowa, canzawa ta yi cikin uniform É—in islamiya ta fito ba tare da kowa ya sani ba ta fice sai gidan su Ilham ko da ta tafi ta iske Ilham É—in ta na cin abin ci, gaisawa ta yi da maman Ilham É—in sannan ta zauna ta saka hannu suka cigaba da ci bayan su kare suka nufi dakin Ilham din ta canza kaya sannan suka fice da kafa da yake islamiya É—in cikin anguwar take.

Tun da suka taso daga islamiya zuciyarta ke bugu ta san wani dukan zata sha, tashin hankalin da za ta iske, bayan sun rabu da Ilham direct gidan su ta nufa ta na sako kai tare da sallama Inna ta lailayo mata wata irin ashar ta na ƙarasa tsakiyar gidan Inna ta wani kallan fincikota ta sakar mata wani lafiyayyen mari "Ke dan ubanki sai yanzu kika dawowa bayan kinsan ke ke yin wanke wanke, ba mutun ya hana ki fita ba ace rashin imanin shi yi yawa, shegiya ƴar iska mai kama da mayun turawa."

Ta wani irin tureta har sai da ta faɗi ta ce "Maza tashi ki yi min wanke wanke." Miƙewa Naila ta yi da ƙyar ta na sakin kuka ta wuce za ta shiga ciki Inna ta ce "Ka da ki kuskura ko da wasa ki shigar min ɗaki sai kin wanke kwanonin nan, jaka kawai." Juyawa ta yi ta nufi wajen wanke wanke ta shiga haɗa kayan ta cire hijab dinta ta soma wanke kayan ta na kuka fuskarta ta yi ja.

Haka take haka rayuwarta take shakararta bakwai, ba wata babbar bace yariyace da bata yi hankali ba yarinya ce da ya kamata har yanzu ta na tare da uwarta, ya kamata ace har yanzu ana yi mata wanke amma mutuwa ta yi mata yankar kauna, mutuwa ta ɗauki mahaifiyarta, bata san mahaifiyarta ba bata taɓa ganinta ba don wata ɗaya da haihuwarta mahaifiyarta ta mutu, aka barta wajen kawunta da matarsa wacce ko rashin imani ya san da zamanta.

Shi ma kawun ba imani ne da shi ba, suna treating dinta kamar karya marar galihu bayan sun haÉ—a pure blood da mahaifiyarta.

Su na da Æ´aÆ´a amma basu yi ma Æ´aÆ´an su kamar yanda suke yi mata, akwai Fa'iza ai sa'an su É—aya toh me ya sa ita baza ayi mata kamar yanda ake yi ma Naila ba.

Meemziey's pen ✍️
[22/09, 09:37] Amina Khaleel: https://www.arewapen.com/chapter?id=6a765bf456862e967f66aee6

Mrs Tajuddeen Abad

by

Meemziey

page_________2️⃣

Haka raywarta ta cigaba babu ranar da ba'a dukanta a zageta sannan a wulakanta ta, ta na zuwa boko ta na zuwa islamiya waje É—aya ne take samun sassauci wajen kawarta Ilham ko kuma ma ace ta zama Æ´ar Uwarta, watarana haka za ta fita bata ci abinci ba, akwai ranar da zata yini ta kwana bata ci ba, ba za su bata ba kuma ba za su bari ta tafi in da ake bata ba.

Da haka har takai Jss3 lokacin lokacin ta na da shekara goma sha hudu.

Zaune take cikin daki saman Æ´ar katifarta da har yau ba'a canza mata ba ta yi shuru ta na tunani, yanzu ta zama Æ´an mata, ta na da kyau sosai sannan fara ce irin farin nan na Larabawa don kai tsaye da ka kalleta abun da zaka fara gani kenan ta na kama da Larabawa, duk da farin nata ya dushe don baya samun kulawa sannan ga wahalar da take yi, duk da haka wani kalan natsatsen kyau ne da ita mai daukar hankali.

Inna ce ta shigo ɗakin a fusace ta tsaya ƙiƙam ta na kallon Naila wacce ta yi nisa cikin duniyar tunani ta ce "Ke don ubanki ba ke nace kiyi min guga ba." Firgit ta miƙe tsaye bakinta na rawa ta ce "Ki .....ki yi haƙuri Inna. " "Wuce ki ban waje kafin ranki ya ɓaci shegiya, kamar ƴar tsana." Sum sum ta fice ta na shiga palor ta ga kayan saman kujera wucewa ta yi wajen socket ta yi shimfiɗa sannan ta dawo ta kwashi kayan ta ajiye ta zauna ta soma guga, da yake akwai wuta.

Ta na tsakar guga ta manta ta rage ƙarfin iron din ta na dorawa akan wani leshi ai kuwa ya ƙone gabaɗaya in da ta ɗora iron ɗin da sauri ta ɗaga iron ɗin hankalinta tashe, ta na dago ido dai dai Fa'iza na shigowa palorn idanunta ya sauka kan leshin aikuwa ta bare baki ta ce "Inna ga Naila nan ta ƙone miki leshin ganin gomna." Ai kuwa da sauri Inna ta fito don yanda take ji da leshin nan bama gaskiya ba ne yafi ko wanne kaya tsada cikin kayanta shiyasa ake ce masa leshin ganin gwamna.

Inna na fitowa idanunta suka sauka kan leshin, wani kukan kura ta yi ta damƙi wuyan Naila da duk in da hankalinta yake ta tashi "Don baƙin ciki leshin nawa kika ƙone, shegiya hassada kike yi min, yau sai na ci ubanki, yau sai na illata ki, azzaluma ƴar iska."

Haka ta kamata ta na yi ta duka ganin abun bai yi kawai ta ce "Ke Fa'iza laƙa min iron ɗin nan." Da sauri Fa'iza ta laƙa iron ai kuwa ya yi zafi sosai Inna ta ɗauko shi Naila na kuka ta na fisge fisge ta na haɗa ta na Allah amma Inna ta ɗora mata iron ɗin nan da ya kwashi dan banzan zafi a baya har waje biyu, wani irin ƙara ta saki tare da ɗauke wuta, saboda azaba ma ɗib ta yi ta kasa kuka ta yi shuru ta na sauke wata irin ajiyar zuciya idonta alumshe.

Miƙewa Inna ta yi ta dauki lace dinta sai jimami take yi bata ji koh ɗar na ƙone Naila ɗin da ta yi ba, ita kuwa Naila wani irin sululi take ji da zafi fatar wajen ta ɗago gabaɗaya.

Tunani ta shiga yi, duniya ba abakin komai take ba, kowa zai mutu, babu fashi mutuwa da hisabi dole sai anyi su, ɗan murmushi ta saki, bawai murmushin jin daɗi bane, murmushin wahala ne, murmushin baƙin ciki, numfashi ta ja tare da saukewa, idanunta na lumshewa ahankali take awajen wani irin nauyayyan bacci ya ɗauke ta.

Tun karfe biyu da bacci ya dauketa bata farka ba sai shida lokacin wajen da ta ƙone ya wani irin ɗago sosai, da ta na baccin babu wanda ya tashe ta idan ma mutuwa ta yi ita a ciki.

Mikewa ta yi ta nufi dakinsu, hijab dinta ta dauko da ƙyar kanta na yi mata wata irin ciwo kamar zai rabe biyu, ta iske su Inna tsakiya gidan bata yi musu magana ba ta fice sai gidan su Ilham.
Chapter 2 · 0% Book details