← Book details Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 71

Sashe 46

Mrs Tajuddeen Abad Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Taj
Companyn Sadeek ya zo saboda akwai meeting da zasu yi a nan Company É—in, office É—in sadeek ya nufa ya jira sadeek É—in don already ya na cikin wani meeting ne, ya na shigowa office É—in ya karasa in da table din sadeek yake ya tsaya gaban desktop É—in sa, kallon desktop É—in dak kunnne ya yi sak kuma ya É—auke kansa ya na kallon files da suka watse a kan table É—in, bai san ya ya aka yi ba ya yi loosing balance mistakenly ya dafe mouse na desktop É—in sai abun ya yi clicking ya shiga wani folder, da sauri ya zo zai gyara abun sai kuma ya tsaya cak ya na kallon desktop É—in.

Wani kalan bugawa zuciyar shi ta yi kamar zata Faso ƙirjinshi, nan take idanunsa suka yi ja, a hankali ya kai hannunshi dake rawa kan mouse ɗin ya shiga wucewa duk clicking da yake yi ya yi dai dai da kamar ana yankar tsokar zuciyar wani irin rawa jikinshi ya ɗauka hankalin shi na tashi, da sauri ya fita daga cikin folder din saboda zuciyar shi na iya fashewa.

Ya koma can kan sofa ya dafe kanshi dake wani irin sara mishi, tunanuka na yawo akan shi da ji yake ma kaman kan nashi zai fashe, ya na nan zaune sadeek ya shigo ganin shi dafe da kai ya shiga tambayar shi menene me ke damun shi ko bai da Lafiya ne a ɗage meeting ɗin, ce masa ya yi babu komai kanshi ne ke san ciwo kuma zai iya meeting  ɗin, a haka dai suka nufi in da za'a meeting ɗin wanda daƙyar aka kare meeting ɗin ya bar company ɗin.

Gida ya koma the first person da ya fara haɗuwa da ita ya na shiga babban palor Naila  ce kawai ya faɗa jikinta ya rungume ta tsam babu ma ruwashi da mutanen dake palorn, hankali ta ya tashi ganin yanayin shi da ƙyar ta cire shi daga jikinta ta ja shi zuwa part ɗin su ta na tambayar sa lafiya, bai amsa ta ba sai cewa da ya yi kanshi na ciwo ne, ita ta san ba haka bane amma ta ƙyalesa tun da ba zai iya faɗa mata ba.

Washegari tare suka fita office don kuwa naila ta ajiye aikinta a gefe ta koma business woman ƙarfi da yaji, tun da suka fito yake rike da hannunta har cikin mota ko da ma suka isa office ɗin kin sakin hannunta ya yi at first ta ɗauka he is being clingy sai daga baya ta ga ashe possessiveness ne, and tun daga ranar zaka ga ko ina suke ya na laƙe da ita like kamar ya na sake faɗa ma mutane cewa she is mine, koh acikin office idan sadeek ya zo babu ruwan taj, zaka ga ya na kissing kumatun ta hannunta ko mai dai wani abu romantic haka..

Yau ma ta na tsaye tsakiyar ɗaki ta na sanye da kayan bacci dogwar riga mai tsantsi waya take yi da sadeek akan file da zai kawo mata ta yi approving sannan ta bama Taj ya yi signing da yake gobe weekend babu aiki so zai kawo mata file din gida, ta na tsakar waya taj ɗin ya rumgumeta ta baya ya na saka kanshi a wuyanta ya na shinshina "Me kake yi haka." Ta faɗa ƙasa ƙasa coz he is making her uncomfortable.

"U smell good baby." Ya faɗa har sadeek da suke waya da shi ya yi "Stop mana, meke damunka haka, me kake so?" Maƙe kafaɗa ya yi sai kuma ya ɗago kai ya kalleta " i want u baby,  yah illahi u smell damn good, oh my god i need u" da wani irin sauri naila ta katse wayan ta na zaro ido don bata san meke damun taj ba, ta na katse wayan ya saketa ya na komawa kan gado ya kwanta ya ce "Gobe su Mami zasu dawo. " Murmushi ta yi Allah ya dawo da su lafiya.

Ita ma ta hau gadon ta na janyo laptop ɗinta daga side drawer washegari su Mami suka dawo ita da Taslim da aka tura daga baya, sun yi kyau abin su sun sha hutu,  naila da kanta ta dafa musu abinci don bata je office ba, Mom jira kawai take yi ta samu lokacin da zata zayyana ma Mami duk abun da ya faru a gidan da bata nan, saboda tun da Mami ta je can ba'a samun number ɗinta koh ka yi trying bai zuwa.

Naila ta gwada ma Mom da Haulat boni gidan nan ta yi traumatising É—insu, duk sai da ta gyara musu zama, especially Haulat É—in.

Mom ganin Mami ta dawo ta zaci Naila zata bar mingling da abubuwan taj but to her greatest surprise tare suka fita aiki washegari, ai kuwa ta zauna ta na zayyane ma Mami abun da ya faru, ita dai Mami sauraren ta kawai take yi ita cikin zuciyarta daÉ—i take ji saboda me atleast an samu wacce take iya juya Taj É—in, and yanda Mom ke faÉ—a É—in Taj ne ya bama Naila goyon baya so ita meye bata aciki, haka dai Mom ta gama ta tashi ta tafi bayan Mami ta ce zata yi musu magana, shikenan aka rabu lafiya.

Yau su na da meeting a company ɗin n share holders,  shigowa suka yi cikin conference room ɗin, ya na gaba ta na biye da shi sanye da maroon color suit wanda wandon ya kasance palazo ne, ta yi rolling black veil akanta takalmin da da jakanta da suka kasance n companyn herms duk baƙaƙe, shigowa suka yi yazauna kan kujerar shi ita kuma ta zauna kan kujerar dake gefen shi.

Wani ne ya shigo cikin wajen ya na gyara suit dinsa da hannu ɗaya sai files dake riƙe a ɗayan hannunshi "Sorry am late." Ya faɗa ya na ɗagowa ya kalli mutanen cikin ɗakin idanunshi suka sauka kanta ta na zaune ta na duba file, wani irin seizing numfashin sa ya yi ya na dafe saitin zuciyar shi, ya na kallonta kakar idanunshi zasu fita files dake hannunsa suka zube ƙasa da shi duka.

Ya na jan numfash kamar mai asthma idanunshi na kanta "No this can't be ba ita ba ce." Ya faɗa gabaɗaya tasowa aka yi kowa ya na tambayarsa me ya faru,  bai amsa ba sai kallonta da yake yi, kamar ma bai hayyacinshi, ita dai hankalinta na kan file ɗin sai ta ɗago jin hayaniya daga ita har Taj miƙewa suka yi, ta kalleshi "meke faruwa." "I don't know, kawai ya na shigowa ya faɗi."

Jinjina kai ta yi "Ok." "Lets go and check." Ya yi gaba ta bishi baya su na zuwa aka buÉ—e musu waje, haÉ—a idanu ta yi da Bilal tsohon mijinta, ya na ganinta wajen gaba É—aya ya rikice, "Ka da ku bari ta matso kusa da ni, don let her come close to me." GabaÉ—aya kallonta suka yi taj ya ce "Kin san shi ne." ÆŠage kafaÉ—a ta yi kallon kowa taj ya yi ya ce "Ku kai shi asibiti, meeting cancelled. "

"Let's go." Ya ce ya na kallon Naila, wucewa ta yi sai da ta kai ƙofa ta juyo ta sakar ma Bilal ɗin murmushi da ya saka shi sake rikicewa, taj ya ga lokacin da ta saki murmushin shi bai ma san bilal ɗin tsohon mijinta bane, sai da suka fita ya kalleta ya ce "Who is he." "My Ex husband. " ta ce dai dai elevator ɗin na buɗewa ta shiga ciki, murmushi ta yi cikin zuciyata ita kaɗai ta san abun ta yi ma Bilal din wanda aka rubuta kawai mutane suka sani, but she traumatised him da har sai da ya koma ya na therapy bayan sun rabu, saboda ta zamar masa mugun mafarki, may be wata ɗayan da ta yi agidansa is the worse month of his life.

"Me kika yi masa haka why is he scared." Murmushi ta yi ta na kallon Taj "He was my first experiment,  psychological experiment,  i think har yanzu ya na samun side effects from that very experiment. " Ta ce ta na sake sakin murmushi coz she is enjoying it.

Office suka koma, shi kuma sai tunani yake yi what is it da ta yi ma Bilal da yake behaving haka, from abun da yake gani Bilal is the victim, Bilal na miji ne so menene zata yi masa da har yake jin tsoronta haka

Ita sai annashuwan ta ma take yi acikin office É—in kamar babu abun da ya faru.

Bayan kwana biyu.

Kallonta ya yi "Ina zaki tafi?" Zan ɗan fita ne but ba zan daɗe ba zan dawo, jinjina kai ya yi "Allah ya tsare, ki kula da kanki." Murmushi ta yi ta na ficewa daga part ɗin, parking lot ta nufa ta buɗe motar ta ta shiga, wajen Mr Sidi ta nufa, yau suka yi zasu haɗu zata kawo masa bayanan da ta tattara, ta yi tafiya mai nisa sannan ta ƙarasa address ɗin da ya bata, mai gadi ya buɗe mata gate ta shiga ta yi parking sannan ta nufi entrance ɗin wajen ta na shiga palorn, ta iske Mr Sidi zaune akan sofa ya na sanye da manyan kaya.

Sai kuma Alhj Rabi'u, da shi sai yau Naila ke ganinsa duk da ta san ya na cikin su Ammi ɗin tare suke shirya komai, wanda shi harƙallar da yake yu ne bata da kyau ya nemi Taj ya goya masa baya Taj yaƙi, sannan kuma ya saka aka kama kayan Alhj Rabi'u ɗin, toh tun shi ne Alhj Rabi'u ya riƙe grudge akan Taj ɗin.
Chapter 46 · 0% Book details